✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨ Khadijah ce kadai xaune daki da daddare tun bayan incident din daxu da rana ta ki fita dakin, Baby ta shigo daga dakin Mumy tana kallon Khadijah tace "Iman you look sad since afternoon, ko don abinda anty Khadijah tayi maki ne a schl?" Khadijah ta girgixa mata kai tace "A'a am not feeling fine ne" Baby ta buda ido sosai tace "Toh ki gaya ma Mumy mana, or you can tell Yayanmu that is a doctor" Khadijah tace "I will be alright in sha Allah" juyawa baby tayi ta fita, dakin ya Aliyu ta shiga ta xauna gefensa har ya gama wayar da yake sannan ya kalleta yace "What happen" tace "Yayanmu Iman ce naga she is sad all day, I asked what's wrong tace min she is not feeling fine" ya kalli kofa kamar xai tashi sai kuma yace "Ta fi ki kira min ita" Mikewa baby tayi ta fita ta koma dakinta, "Yayanmu yace in kira ki" abinda ta fadi ma khadijah dake kokarin kwanciya kenan, Khadijah ta hade dai tace "But I didn't tell you to announce I am sick" baby tace "What ever... Ko ince masa baxa ki xo ba" daga haka ta juya ta fita, mikewa khadijah tayi ta sa Hijab ta bi bayanta, dai dai fitowar Anty khadijah daga dakinta xata sauka downstairs, da da ne tana ganin Iman tayi hanyar dakin Aliyu irin ko ya kira su tare da baby xata mata mugun kallo ta hanata shiga dakin, yanxu kam sau daya ta kalleta ta dauke kai tayi wucewarta, a sanyaye khadijah ta shiga dakin don tuni baby ta shiga, ta tsaya daga bakin kofa tace "Ga ni Yayanmu" yace "kika ce baki da lafiya, what's wrong?" Ta kalli baby tace "Kawae I told her am nt fine, ba wai bani da lafiya ba" Baby tace "Ke ma kina son ki fara karya kamar iklima koh?" Murmushi Khadijah tayi, Aliyu ya kalli baby yace "You can leave" mikewa tayi tace "Ohk" sannan ta fita, yana kallon khadijah yace "Come over Iman" karasawa cikin dakin tayi, ya jawo study chair dinsa ya ajiye mata, ba musu ta xauna tana facing dinsa, a hankali yace "But I told you not to worry koh?" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "I am without worries" shiru yyi yana kallonta, ta ki dago kanta, murya can kasa yace "Iman" dagowa tayi da manyan idonta tana kallonsa, yace "Tel me when you lost ur parent" lkci daya hawaye ya cika idonta, ya girgixa kai yace "Noo ban ce kiyi kuka ba" ta gyada masa kai tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "My dad told me I lost my mum when I was just 3, we where together tun daga sannan, shi yake kai ni schl da islamiyya, I love my dad... He took good care of me, kullum a eatry Abbana ke siyo mana abinci, I mean all the 3 daily meals, but there is always custard, cornflakes, golden morn, ice-cream in the fridge and different biscuits and chocolates at home all for me, duk sanda Abbanmu xai je trip abroad he always go together with me, not until he married my step mum when I was 8 years old, and she took over from where he stopped, my step mum is more than kind, tana so na, she does to me what ever I like, ko Abbanmu na nan ko baya nan, muna tare har na kai 14 years...." Katse ta Aliyu yyi yace "Ita yaranta nawa step mum dinki?" Tayi murmushi tace "Ni kadai ce yarinyarta, she never gave birth with my dad" Aliyu ya gyada kai yana kallonta, ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "One faithful Friday Abbanmu xai je port Harcourt wajen junior brother dinsa da aka kira sa ba shi da lafiya ya xo ya tafi da shi, we bade him fare well har parking lot da Asuba tare da Ummata" ta fashe da kuka tace "That was the last time we saw him, sai aka kira Umma aka ce yayi accident and he is gone" kamo hannunta Aliyu yayi murya can kasa yace "Allah ya ji kansa, yayi masa rahama, dont cry pls" cikin rawar murya tana gyada masa kai tace "Ameen" yace "After that?" Ta xame hannunta tace "We cried a lot da ummata, but at the end tace in daina kuka saboda my dad won't be happy with me idan ina masa kuka ban masa addu'a ba, and from then ban sake kuka ba don bana son abbana yyi fushi da ni, ko da yaushe addu'a nake masa Allah ya basa aljanna, we stayed for plenty months tare da Ummata a gidan mu kadai, kawai ranan sai ga uncle dina ya xo wai xa a yi sharing property din Abbanmu, I don't knw how but at the end, kawai ummata tace min ita xata tafi gidansu ni kuma uncle dina yace xai tafi da ni gidansa in xauna a can, a week after kuma ya sake dawowa... A ranan muka rabu da ummata ya rufe gidan, ya tafi da ni katsina gidansa ita kuma ta tafi gidansu ita ma" Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa bai yi, labarin rayuwar wahala da tsangwama da tayi gidan kawunta ta shiga basa, da irin hidiman da sadeeq ya mata da yanda Mahaifiyarsa ta hanasa daga karshe har xuwa ranan da Umma ta xo ta gudu da ita ta kai ta gidan sabon mijin da take aure a kano, nan ma duk ta basa labarin 3 days stay dinta a gidan da abubuwan da suka faru kafin Umma ta kawo ta nan Kaduna wajen step sister dinta yakumbo, bata boye masa duk kalan wahalan da ta sha gidan yakumbo ba da irin duka da xaginta da take, har daga karshe makwabtan ta suka dinga xuga ta a kan ta kawo ta gidan aiki, har dai yakumbo ta kawo ta nan gidan tare da Abuuu.... Khadijah tayi shiru tana kallon Aliyu da ya kasa kallonta, kai kana ganinsa kasan tausayinta ne kawai ya cika sa, jin tayi shiru ya dago da kyar yace "Kiyi hakuri Iman, all this will come to past one day it's just a matter of time" ta gyada masa kai kawai, Ya shafa kansa yace "Kuma ki dinga hakuri da abinda Anty Khadijah ke maki, wataran baxata yi ba kin ji" a hankali tace "Toh" yace "And Saleem babu ruwanki da shi, soon xai tafi Germany ki kwantar da hankalin ki kin ji" nan ma tace masa "Toh" yyi mata murmushinsa mai kyau ya lakaci hancinta yace "Good girl" ita ma murmushin tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Yanxu islamiyya xa ku dinga xuwa from morning to evening tunda ba schl kuma" kallonsa tayi bata ce komai ba, yace "Toh tashi ki tafi kar ki kara sa ma kanki damuwa kinji" kai ta gyada masa ta dau wasu novels guda biyu da ta gani kan study desk dinsa tace "Can I read them" yace "Noo, I will get you the one to read tomorrow" tace "Ohk" sannan ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Bayan kwana biyu Mumy na daki ranan asabar misalin karfe sha daya da yake babu aiki, Su siyama, Baby da Khadijah har Iklima duk sun tafi islamiyya, Anty khadijah ta shigo dakin Mumy a shiriye rike da yar karamar jaka, daga nan bakin kofa tace "Anty fati xan je gidan wata kawata dake nan Zaria bata ji dadi ba, in sha Allahu xan yi kwana biyu xuwa uku kafin in dawo" Mumy tace "Zaria kuma, wace k'awa gare ki a Zaria, amma baki taba ce min kina da k'awa a Zaria ba, kuma ni tun da kika xo gidan nan ban taba ganin wata k'awa ta xo wajen ki ba, hasali ma ce min kike ba ki da kawaye...." Katse ta Anty khadijah tayi fuska a murtuke tace "Toh karya nayi kenan Anty fati, da can na taba ce maki xan je gidan k'awa ta? yanxun ma lalura yasa xan je wajenta, kuma da ba a Zaria take ba a Abuja take a anguwar mu, aiki ne ya mayar da mijin ta Zaria" Mumy tace "Toh Allah ya kyauta, Allah ya kiyaye" Anty Khadijah tace "Ameen, Anty fati don Allah ki sa ido kan Iklima kin san ba wai can take son cin abinci ba" Mumy ta harareta tace "Baxan sa ba" Bata ce komai ba ta juya ta fita daga dakin, Aliyu ne kadai xaune parlor, ko kallonsa bata yi ba ta nufi kofar fita, ya bi ta da kallo kafin yace "Allah ya kiyaye hanya" ficewarta tayi ta rufe kofa ba tare da ta tanka sa ba. Karfe biyar na yamma bayan Aliyu ya dawo aiki ya kira baby ta shigo dakinsa yace "Me ya hana ku xuwa islamiyya" ta xaro ido tace "Yayanmu na safe fa muka je yau" yace "Ohk je ku shirya da Iman mu fita" cike da murna tace "Waow, su siyama fa Yayanmu?" Yace "Ban da su" juyawa tayi da sauri ta fita baki har kunne, a dakin Mumy ta tarda Khadijah dake fiddo ma Mumy turarrukan da ta aiki driver ya siyo mata a shopping mall, Iklima kuma na xaune saman gado tana kallo, Baby tace "Mumy wai Yayanmu yace ni da Iman mu shirya xa mu fita anguwa" Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Toh ku je ku shirya" iklima ta sakko saman gadon kamar xata yi kuka tace "Mumy ni ba dani xai je ba kenan" Mumy tace "Toh ni na sa ki ki dinga masa fitsara? Wannan kuma ya rage na ku ke da shi" Fita iklima tayi dakin tana kuka, Baby ta fiddo atamfar da Mumy tayi masu iri daya da khadijah da mayafi tace "Wannan xa mu sa Iman" ita dai khadijah bata ce komai ba, baby ta kyalkyale da dariya tace "Allah sarki ban da iklima" Khadijah tayi murmushi tace "Yayanmu has a very good heart nasan xai je da ita" Baby tace "Tab kinsan yanda Yayanmu ya tsani mai rashin kunya" Khadijah bata ce komai ba ta fara sa kayan da baby ta dauko masu. iklima na fita mumy ta tashi ta tafi dakin Aliyu, daga bakin kofa ta tsaya tace "Abuturrab amma tare da Iklima xa ku je" Ya hade rai yace "A'a ni ban ce xan je da ita ba mumy" mumy tace "Toh sai a fasa tafiyar ai" daga haka ta juya ta shiga dakin Anty Khadijah ta ga iklima xaune can karshen gado tayi tagumi tana rera kuka, Mumy tace "Sai ki shirya ku tafi gaba daya" mumy na fadin haka ta juya ta wuce, ko kunya babu iklima ta tashi ta fiddo sabon kayan ta da takalmi mai tsini da jaka, ta sha uban make up ta sa spec, ta feshe jikinta da turarurrukan uwarta sannan ta sakale mayafinta a kafada ta fito, dakin su baby ta shiga su ma har sun gama shiryawa baby na ganinta ta kwashe da dariya har da faduwa kan gado ta dinga kyakyatawa, Khadijah tayi murmushi ta dauke kanta, Baby ta kuma dagowa ta kalli Iklima ta kwashe da dariya, Iklima ta maka mata harara tace "Ai dama ke mahaukaciya ce" Baby ta mike xaune tace "You are not even ashamed of ur self, yanxu wa yace xai je da ke, har da wani sa dogon hill da spec, ji wani make up kamar na yan kasuwar tasha" Juyawa iklima tayi ta shiga dakin mumy, can sai ga ta ta fito tana huci tace "Mumy na kiranki" Baby tayi tsaki tace "Ae a haka xa ki kare da reporting din mutane" Dakin mumy ta wuce tana hararanta, har mumy ta gama ma baby fada bata ce komai ba, tana fita ta kira Khadijah suka sauka downstairs su jira ya Aliyu tana kumbure kumbure. Babu yanda Aliyu ya iya haka ya tafi har da iklima, baby ce gaban motar, iklima da Khadijah kuma a baya, babu abinda ya fi ba Aliyu takaici irin shegen make up din da tayi a fuska. Smart kids ice cream spot ya nufa da su, bayan ya siya masu ice cream da pizza da fries ya mayar da su gida duk da ba haka ya so ba amma saboda iklima ya fasa duk abinda yyi niyya. Ranan lahadi da daddare Anty khadijah ta dawo gidan, Mumy da Aliyu dake xaune parlor suka bi ta da kallo ganin yanda ta yi wujiga wujiga, bata yarda ta tsaya parlor ba sannu da gida kawai tayi ma yar uwar tata ta wuce sama da sauri, Aliyu ta kalli Mumy yace "Daga ina take mum?" Mumy tace "Allah kadai ya sani" Anty khadijah na shiga daki ta bude press dinta ta tura jakarta sannan ta rufe ta tube kaya ta shige bandaki, sai da tayi wanka ta sauya kaya sannan ta fito tana kwala ma siyama kira ta xo ta xuba mata abinci, xaunawa tayi parlor, Mumy dake ta kallonta tace "Lafiya na gan ki haka" da sauri ta kalli mumy tace "A ya kika gan ni?" Mumy tace "Atoh, kinga wani duhu da kika yi kamar warce taje kauye" Anty khadijah tace "Kauye kuma, Zaria fa nace maki xan je, kuma gashi har naje na dawo" Mumy tace "Toh Allah rufa asiri" Sai a sannan Aliyu ya gaisheta, fuska a murtuke ta amsa can ciki, ya mike yyi wucewarsa sama, tana kallon mumy tace "Ina d'a na saleem?" Mumy tace "Ya je Abuja jiya da kika tafi, ina jin daga can ma xai wuce Germany, toh wai ke da kika ce kwana biyu xa ki yi Khadijah ya aka yi kika dawo yau, jiya da safe fa kika tafi?" Anty khadijah ta hade rai tace "Kai Anty fati, to kwana biyun bai yiwuwu ba" daga haka ta mike ta wuce kitchen don xuba abinci ganin siyama bata sakko ba. _Littafin Noorul Hayat na siyarwa ne, kindly patronize ur Novelist and read happily_???? ✨ *NOOR-AL-HAYAT* ✨ Da safe har su siyama suka tafi makaranta Anty khadijah bata sakko ba kamar yanda ta saba, tun bayan da ta kori kyauta da asuba take fitowa amma yau shiru, Khadijah ta taya mumy suka yi breakfast tun asuba sannan ta kwashi wanke wanke ta tafi tana yi duk da ba ita ce da yi ba baby ce, amma ganin tana bacci take taya ta, Mumy kuma ta wuce bedroom dinta, yanxu kam khadijah ta saba bata jika jikinta idan tana wanke wanke, ta gama wanke plates din gaba daya ta shigo kitchen tana ajiye ko wanne a maxauninsa, d'an dukawa tayi ta dalilin cikinta dake ciwo tun cikin dare, ta rasa irin ciwon cikin, Aliyu ya shigo da shirin fita office, tana ganin sa ta mike da sauri, yace "What's wrong?" Murmushi tayi tace "Good morning" yace "I asked what's wrong with you" tace "Ba komai, kawai cikina ke min ciwo amma yana sauki" yace "Since when?" Tana ci gaba da ajiye plates din hannunta tace "Da na tashi daxu" Yace "Ohk xan ajiye maki magani a bedroom, idan kin yi breakfast sai ki sha" tace "Toh nagode, in yi maka cup din coffee?" Yace "Ohk thanks" daga haka ya juya ya koma parlor, ta dau cup ta yi making masa coffee a ciki sannan ta fita ta kai masa, ya amsa yana kallonta yace "Nagode" murmushi tayi ta juya ta koma kitchen. Ita kadai ce kwance dakin banda juye juye babu abinda take, baby ta shigo daukan system dinta ganinta haka ta isa gabanta da sauri tace "Iman, what's wrong are u okay" mikewa xaune khadijah tayi jin xuciyarta na tashi ta wuce bayi da sauri, amma ta kasa aman, sanin Mumy bata nan baby ta tafi dakin Anty khadijah dake parlor da yar ta suna kallo suna yin lunch din da mumy tayi kafin ta fita aiki, wayarta baby ta dauka tayi dialing number Aliyu da sauri, sosai Aliyu yayi mamakin ganin number Small mun dinsa, can dai ya dauka hade da sallama, Baby tace "Yayanmu it's me baby, Iman ce bata da lafiya, she is even vomiting gashi mumy bata nan, nobody is at home sai Anty khadijah" Yace "Toh gani xan xo yanxu" katse wayar yyi, tayi deleting kiran a log sannan ta ajiye wayar ta fita da sauri ta koma dakinsu, Aliyu ya bar duk abinda yake cikin few minutes sai gashi ya dawo, hawaye kawai khadijah take da ya tambayeta inda ke mata ciwo, Anty khadijah na ganin ya shigo gidan ta hayo sama kamar me neman abu iklima na biye da ita, kamar dai daxu yanxu ma magani ya bata, sannan ya kira mumy ya sanar da ita bata da lafiya xa su tafi clinic ya dubata, Mumy dai tayi mamakin yanda aka yi ya sani har ya dawo shi da yake gun aiki, amma dai kawai tace masa toh, Hijab khadijah ta sa ta bi sa suka fita, Baby tace "yayanmu xan iya bin ku" ya kalleta yace "Clinic din?" Da sauri tace "Aa yi hakuri" murmushi yyi sanin tun tana yar karama take tsoron asibiti dama, suna isa asibitin office dinsa ya wuce direct da khadijah, sai dai ba shi ya dubata ba wani likitan ne daban ya dubata yasa aka mata series of tests, nan ya mata allura aka bata drugs, tun da aka yi alluran dama take kuka, Aliyu ya nuna mata gadon duba masu ciki yace "Kwanta can kiyi kukan da yawa" ba musu ta kwanta ta ci gaba da kukan nata a haka har bacci ya dauketa. Sai kusan la'asar ya tada ta, ta bude ido a hankali sannan ta mike xaune yace "How you feeling now?" Bata ce komai ba, yace "Toh taso kiyi alwala" ba musu ta mike, bayan ta gama sallah suka fita office din, Eatry ya kai ta ya siya mata abinci sannan ya mai da ta gida. Bayan kwana biyu, Aliyu na tsaye kitchen yana mamakin wa kuma ke shan coffee a gidan bayan shi, cos ya sami powder din ba yanda yake ajiye sa ba, hada coffee din yyi ya fita kitchen din, duk da shirin fita office da yyi komawa bedroom dinsa yyi ya kwanta bayan ya gama shan coffee din jin kansa na juya masa, Mumy ta gama shirin tafiya gun aikinta ganin bai fita ba tun safe ta shiga dakinsa, kwance ta samesa idonsa a rufe, tace "Abuturrab" ya bude ido da sauri tace "Are you okay" yace "Sure I am fine, it's just headache anjima xan tafi aikin" Mumy tace "Toh Allah ya sauwake, sai ka sha magani, ni na tafi" yayi mata Allah ya tsare sannan ta fita, Anty khadijah dake xaune parlor tayi ma Mumy Allah ya kiyaye, Mumy tace "Ameen" sannan ta fita. Mumy na fita Anty khadijah ta shiga kitchen ta daura tea pot a kan gas, ta dau Lipton da kayan kamshi kamar dai yanda ake dafa ruwan shayi ta xuba a tea pot din, kulle kofar kitchen din tayi ta ciro wani kulli da ta tusa cikin bra dinta ta bude ta juye gaba daya garin ciki a tea pot din sannan ta rufe, bata bar kitchen din ba sai da ya tafasa sosai sai kamshi ruwan lipton din yake, sannan ta juye a karamar flask bayan tayi shifter din shaft din garin, ta kashe gas ta wanke tea pot din ta kife ta dau babban flask din gidan ta bude ta tuttule ruwan Lipton dake ciki a sink ta rufe ta ajiye sannan ta bar kitchen din ta koma parlor ta xauna. Karfe sha biyu saura Anty khadijah ta sa su baby da iklima su shirya wai xa su rakata, ba don ran baby ya so ba ta tafi dakinta shiryawa don tasan masifa xata yi ta masu a duk inda xa su, Bayan baby ta sa Hijab dinta ta kalli Khadijah da ke gyara mata kayanta da ta sassauke ta ajiye saman gado tace "Don't worry fa Iman, ni ma kawai wahala nasan xan je mu yi, following Anty khadijah is always one of my worst night mare... beside Yayanmu is at home ai yana bacci, he will keep you company, you won't be that lonely" khadijah tayi murmushi tace "Alright bye" daga haka baby ta fita, Anty khadijah na fitowa dakinta ta bude kofar dakin Aliyu a hankali dai dai lkcn da ya bude idonsa suka yi ido hudu, fuskewa tayi ta daure fuska ta shiga dakin ta tafi gaban madubinsa ta dau turarrukansa ta dinga fesawa irin shi ya kawo ta din nan, sannan ta fice daga dakin ta rufe masa kofa. baby ta ba handbag dinta da makullin motar tace "Gashi ku je ku jirani a mota da Iklima saura ku yi damben da ku ka saba kafin in fito" baby sai da taje ta fara yi ma yayanta sallama a dakinsa sannan ta sauka kasa, tana sauka Anty khadijah ta bude dakin babyn tana kallon khadijah dake ta gyaran kaya ta hade rai tace "Idan kin ga dama, kina gama gyaran kayan ki tafi ki kai ma Aliyu abinci don bai yi breakfast ba, ruwan Lipton din sa na nan a karamin flask na Babban flask ya kare" Khadijah tace "Toh Anty" ta maka mata harara tace "Kya nemi Antyn ki dai" daga haka ta juya ta fita ta rufe kofar. Khadijah na ji suka fita gidan a mota, ta ci gaba da gyaran da take a hankali har ta gama sannan ta fita, kitchen ta wuce don debar ma Ya Aliyu breakfast kamar yanda Anty khadijah ta ce mata, tsaye tayi inda karamin flask din yake ta kai hannu kan cabinet din kitchen din ta dangwalo wani garin magani da ta gani a xube wajen, ta dinga kallon bak'in maganin can ta tafi sink ta wanke hannunta, ta dawo ta dau napkin din kitchen din ta share wajen ta wanke napkin din a sink sannan ta shanya ta gama daura masa kayan break din a tray da karamin flask din ta fita xuwa dakinsa, kwance ta samesa idonsa biyu, ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tace "Yayanmu ga breakfast din ka, in hada maka shayin" ya girgixa mata kai yace "Noo don't worry xan yi da kai na, ke ba ki bi su ba?" Khadijah ta girgixa kai tace "A'a..." Shiru ya d'an yi sai kuma can yace "Toh ki je sanusi ya kai ki saloon kiyi gyaran gashin ki" turo baki tayi ta make kafada tace "A'a ni gashina bai yi datti ba Yayanmu, kuma on Sunday mumy ta kai mu ai" yace "Toh me ma ya hanaku xuwa islamiyya?" Ta wara ido tana murmushi tace "Ka mance yau Thursday" ya lumshe ido ya bude yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, bayan tafiyarta da kusan minti goma ya mike xaune a hankali yana son daurewa ya bar gidan ya tafi clinic, gaba daya ya rasa gane me ke damunsa, it seems he is sick, cup ya dauka ya debi ruwan Lipton dake flask kadan, sannan ya xuba madara da cube biyu na sugar ko bin ta kan Milo bai yi ba ya juya shayin da spoon ya ajiye ya huce, mikewa yayi ya shiga bathroom ya sake wanka sannan ya fito, ya dau wani kayan da xai sa ya ajiye saman gado ya xauna bakin gadon ya dau cup din shayin da ya riga ya huce ya kai baki ba tare da ya bi ta kan dankali da kwai dake rufe a plate ba.... Yana gama shanye shayin ya ajiye cup din. Kallon cup din kawai Aliyu yake bayan few minutes wondering is this really a tea he drank, cos even the taste... komawa yayi ya kwanta saman gado bayan kusan minti biyar ya rufe ido sosai, He just can't imagine what is ringing all over is head a lkcn, ya sake mikewa xaune da sauri trying hard to control his self daga urge din da xuciyarsa ke masa, loudly xuciyarsa na bugawa sosai yace "Not... Iman" ya kai hannu da nufin sa kayansa ya bar gidan gaba daya amma ya kasa, komawa yayi kan gado yyi cike da karfin hali ya kwanta, jin sanyi na shigarsa ya rufa da duvet, dai dai nan aka bude kofar dakin ya juya da sauri, khadijah ce ta shigo rike da leda karami tace "Yayanmu ga shi sanusi yace in baka aiken da kayi masa daxu, naga drugs ne dama baka da lafiya ne?" Kin cewa komai yyi ya rufe ido kamar mai bacci, ta isa kusa da shi ta durkusa tace "Toh ka ta shi kasha Yayanmu" tana fadin haka ta fiddo duk maganin tana duba prescription amma bata ga ni ba, guda daddaya ta cire gaba daya hudun ta dau table water da ta gani dakin ta dawo gefensa tace "Ka tashi kasha Yayanmu" ya bude idonsa da ya kada yace "Ajiye ki fita" bai taba mata magana yanda yyi mata ba a lkcn amma a tunaninta ko rashin lafiyan ne, kamar xata yi kuka tace "Toh ka fara sha don Allah Yayanmu" lkci daya ya ji kamar an cire gaba daya sympathy dake tare da shi, Ya mike kamar wani xaki ya fixgota cikin tsawa yace "I said leave Iman" hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa, cikin rawar murya tace "Ohk" daga haka ta ajiye masa magungunan cikin leda ta ajiye ruwan ma ta mike, da sauri ya jawota ta fado jikinsa ta xaro ido a tsorace tace "Yayanmu" ya rungumeta gam hade da lumshe ido muryarsa na rawa yace "I don't want this to happen Iman, I...." Kasa ci gaba yayi jikinsa ya dau rawa, yasan he have tried for that long, the urge... He just don't understand it, it's unbearable.... It's different. Aliyu never gave her a chance to raise any alarm duk da kokarin yin hakan da ta dinga yi, kai kana ganinta kasan bata taba tsorata da shiga tashin hankali irin na moment din ba, gashi yyi depriving dinta damar rokonsa ta kuma yi masa tuni da cewa ita marainiya ce ko xai ji tausayinta, domin kuwa ya rufe bakin ta, and that was how everything happened, tana ji tana gani Aliyu ya raba ta da pride dinta, daga nan da ta rufe ido bata sake budewa ba sai bayan wasu mintuna. Kwance ta ganta dakin baby an rufeta da duvet, ta dinga bin dakin da kallo a hankali kamar me son tuna wani abun, ta runtse ido ta dalilin sara mata da taji kanta ke yi sosai, bude ido tayi da sauri kuma a tsorace don a lkcn komai ya dawo mata, xata mike xaune taji wani xafi gaba daya jikinta, kara ta saki ba tare da ta shirya yin hakan ba duk jikinta na rawa tana kiran Ummanta, dai dai nan aka bude dakin, bata san lkcn da wani karfi ya xo mata ba tayi ignoring axaban da take ji ta mike a gigice tana neman sauka kan gadon cikin tashin hankali take cewa "Don Allah yaya Aliyu kayi hakuri ina rokan ka, wlh mutuwa xan yi, kar ka xo don Allah" ya isa har gabanta yana kallonta da idanuwansa da suka yi ja xata gudu ya rikota ya xaunar da ita gefen gado shi ma ya xauna ba tare da ya bari sun hada ido ba muryarsa na rawa yace "Don Allah ki yafe min Iman, sure I cheat you, but..." Kasa ci gaba yyi ya sake hannunta ya rike kansa da yyi masa nauyi hawaye na xuba idonsa, ita ma kukan take a raunane tana son tashi wajen amma ta kasa, sauka yyi kan gadon ya durkusa kan kneels dinsa hawaye na xuba idonsa ya daura kan sa kan kafarta trying hard to speak yace "Ki dubi girman Allah ki yafe min Khadijah, I didn't do that intentionally, forgive me plss, I don't knw wat came over me, ba halina bane Iman, don Allah ki yafe bi...." Kuka kawai khadijah take tana ja baya jikinta na rawa, cikin sarkewar murya tace "Na ji, amma ka tafi don Allah ina rokon ka, please go" ya fi minti biyar durkushe gabanta kansa a duke har lkcn hawaye ya ki tsaya masa, ya ji duk ya tsani kansa, of all people why Iman, cike da karfin hali ya mike ya fita dakin. Khadijah ta fada kan gado ta dinga kuka, tun bayan rasuwar Abbanta sai a lokacin ta ji ba ta son duniyar gaba daya, xuciyarta ya karaya taji ita ma da Allah ya dau ranta a lkcn ta huta. Bacci me nauyi ne ya dauketa afterward, bata tashi farkawa ba sai da su baby suka dawo misalin karfe biyar na yamma, ta dinga kallon baby da ta tasheta da idanuwanta da suka kumbura sosai, baby ta ja baya da mamaki tace "Iman, what's wrong did you cried?" Hannu ta kai jikinta ta ji yyi mugun xafi, ta fita da sauri don kusan tare suka shigo gidan da Mumy, dakin ya Aliyu ta fara shiga ta ga baya nan, sannan ta sauka downstairs don har lkcn mumy da Anty khadijah ba su hauro sama ba, Anty khadijah duk ta gaji da xancen da mumy ke mata ta kagu ta wuce sama don kin xama ma ta yi a parlorn tana tsaye, da damuwa baby tace "Mumy kamar khadijah bata da lafiya...." Katse ta Anty khadijah tayi da sauri tana kallonta tace "Me ya sameta?" Mumy kanta sai da ta kalli Anty khadijah, can Anty khadijah ta ankare ta tabe baki tace "Abun ka da xuciyar musulunci ban da haka ina ruwana, a kan yarinyar da ake min gori a gidan nan dubi yanda na xabura don ba ta da lafiya kamar iklima ce ba lafiya" mumy na kallon baby tace "Me ya sameta" baby tace "Nima ban sani ba, her eyes are swollen kuma jikinta yayi xafi sosai" mikewa Mumy tayi ta wuce sama, sai da Anty khadijah ta shiga kitchen ta dau flask din da ta xuba ruwa taji an diba sannan tayi murmushi ta bi bayan mumy da sauri, Cire bargon Mumy tayi tana kallon khadijah, ita kanta sai da ta tayi mamakin irin xafin da jikinta yyi ga wani shivering da take idanuwanta sun kumbura, Anty khadijah dake ta kallonta ta shimfida damuwa karara fuskarta tace "Me ya same ki haka" khadijah bata iya tace komai ba sai rawa da jikinta yake, Fita Anty khadijah tayi ta nufi dakin Aliyu da sauri ta bude, ganin baya dakin ta shiga don kara tabbatar da cewa ba xanin gadon da ta gani dakin bane daxu da ta shigo sannan ta fita daga dakin, Mumy ta kalli baby tace "Dauko min wayata" Da sauri baby ta fita sai ga ta ta dawo da wayar, Mumy ta shiga kiran Aliyu, yana gidansa kwance for the 1st time tun da Daddy yyi furnishing masa gidan, idonsa a lumshe suke ya bude a hankali jin karan wayarsa ya dinga kallon kiran ganin Mumy ce har ya katse, sake bugowa aka yi, yayi karfin halin mikewa don xaxxabi ne sosai jikinsa, ya dau wayar ya kai kunne bayan ya daga cikin sanyin murya yyi mata sallama, da damuwa Mumy tace "Aliyu where are you, Khadijah bata da lafiya sosai, ka taho yanxu idan ya kama ku tafi asibiti ne sai ku wuce" Da farko rasa abinda xai ce ma Mumy yayi lkci daya hawaye ya cika idonsa, har sai da tace "Hello Abuturrab, are you there?" Yyi karfin halin gyada kai yace "Xan taho yanxu Mumy" daga haka ya katse wayar ya ajiye ya rike kansa hawaye na sakko mishi. Aliyu ya fi minti goma xaune cikin mota bayan ya iso gida, gaba daya ya rasa me ke masa dadi duniyar, har ya fita kamanninsa saboda damuwa, Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso inda take kallonsa Mumy take cos he looks so sick, shi kam ya kasa dagowa balle ya kalleta, Tace "Abuturrab are you okay, ciwon kan ne har yanxu" ya gyada mata kai a hankali yace "Na sha magani mum da sauki" daga haka ya wuceta ta bi sa da ido, bin bayansa tayi tace "Toh bacci ka je clinic din kake yi?" Bai juyo ba yace "Eh" da damuwa tace "Maimakon ka tsaya gida ka huta Aliyu tunda baka da lafiya, da sai ka kira asibitin ka bada uxurin ka, xa ma ka iya dubata yanxu ko kawai mu wuce asibiti" tsaye yyi bakin kofa ya rasa abinda xai ce mata ya kuma kasa juyowa duk jikinsa yyi sanyi, Cike da karfin hali yace "Xan tafi asibitin da ita likita xa su duba ta a can" mumy tace "Toh kai ma gaskiya a dubaka wani irin ciwon kai ne haka lkci daya tun safe, sanusi sai ya kai ku clinic din" Bude kofa aka riga sa yi Anty khadijah dake tsaye bakin kofar tana kallonsa da kyau tace "Me ya same ka kai kuma, baka da lafiya ne?" Gefenta ya bi ya shiga gidan ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "I am better now" Anty khadijah ta kalli Mumy mamaki shimfide fuskarta tace "Dama baya da lafiya ne Anty fati?" Mumy tace "Tun safe kafin in fita aiki yace min yana jin ciwon kai ban san wani kalan ciwon kai bane haka har yanxu, ni na xata ma baxa shi aikin ba ganin har na fita yana gida" Anty khadijah ta bi bayansa da sauri ganin har ya kai stairs, ta hada har da d'an gudunta har hakan ya ba Mumy mamaki, Tsaye Aliyu yyi bakin kofar dakin ya kasa shiga, ta labe jikin stairs tana jiran ya shiga ita ma ta shiga, a hankali ya murda kofar ya sa kai ya shiga, Tana ganin haka ita ma ta shige, Baby da ke xaune gefen Khadijah da ke kwance da damuwa tace "Yayanmu Iman bata da lafiya she is just crying, and her temperature is very high" hawaye cike idonta take magana, khadijah na jin sunan da Baby ta kira ta bude ido da sauri hade da yunkura ta mike xaune, Aliyu ya kasa kallon direction din, wani sabon kuma khadijah ta saki a raunane, Anty khadijah dai na tsaye kofa tana kallonsu, Aliyu bai iya ya kalli khadijah ba yace "Ki sa ta shirya xa mu je asibiti yanxu" baby tace "Toh" daga haka ya juya suka yi ido hudu da Anty khadijah, tabe baki tayi ta juya ta bar wajen tana cewa "Haka dai aka iya, da yar uwar ka ce ba lafiya ai baxa ka bi ta kan mu ba ma" shi dai ba ce komai ba ya fita. Hijab baby ta ba Khadijah, Khadijah taki sawa tana girgixa mata kai cikin kuka tace "Ni bana son xuwa asibitin, idan nayi bacci I will okay, baxan iya xuwa ba" baby tace "Nooo, ki sa mu tafi don Allah" kin yarda Khadijah tayi hakan yasa baby ta fita sai ga ta sun shigo tare da mumy, mumy ta karaso kusa da ita ta amshi hijab din ta sa mata tace "Kiyi hakuri ki tashi ku je asibitin kin ji, Allah ya sauke" daga haka Mumy ta dago ta, Aliyu dai na tsaye corridor yyi backing kofar, muryar Mumy ya ji tana cewa "Toh ka kai ma Sanusi makullin sai yyi driving din koh" Juyowa yyi xai yi magana amma ya kasa ganinta tsaye tare da Khadijah tana rike da hannunta, Wani mugun tausayinta ya dinga ratsa shi ganin irin karfin halinta cos he was thinking baxata iya fitowa ba, bai yarda sun hada ido ba kamar yanda ita ma kanta ke a kasa, ya fara sauka stairs Mumy ta bi bayansa tana rike da hannun Khadijah baby na biye da su a baya, Anty khadijah dake tsaye bakin kofar dakinta ta saki baki ta bi Khadijah da ido a ranta tace wa yaga boss lady, don kusan kalau take tafiyar ta, nan kuwa daga ita har Aliyun basu san mugun karfin hali take ba, she is in pain all over, only trying her best to be okay, Mumy ta bude bayan motar ta shigar da ita tasa baby ma ta xauna a baya kusa da ita, sanusi ne ya ja motar cos da gasken Aliyu bai jin xai iya tukin, har suka isa asibitin kansa na jingine da kujera, baby kuma na rungume da Khadijah da ta ki bude ido tana kukan xuci. Sanusi na parking Aliyu ya bude motar ya fita, Baby ta fito tana kallon khadijah tace "Iman ki sakko we are at the hospital" A hankali khadijah ta fito cikin motar tana rike da hannun baby, Aliyu ya kalli baby yace "Ku koma tare da sanusi" xaro ido tayi tace "Yaya but Mumy tace in tsaya da ita, wa ye xai tsaya kusa da ita idan anyi hospitalising dinta, look shes very sick fa" irin kallon da ya dade bai mata ba ya shiga yi mata a lkcn, Bata sake cewa komai ba ta shiga motar hawaye cike idonta, Khadijah ta fashe da kuka a hankali tace "Don Allah kar ki tafi ki bar ni" Baby na share hawayen ta tace "He said I shud leave Iman" Aliyu ya juya ya wuce ciki sai ga nurse ta taho ta shiga da Khadijah asibitin, sanusi ya ja motar yana ma khadijah Allah ya sauwake ya kama hanyar gida. Nurse din na rike da hannun Khadijah da ke ta hawaye ta wuce office din Aliyu da ita kamar yanda yyi instructing dinta, baya office din hakan yasa ta fito ta shiga office din kusa da nashi ta samesa xaune, ruwan xafi yasa ta fara kai ma khadijah bathroom dinsa tayi wanka sannan ya bata magunguna da alluran da xata mata, daga haka kuma ya bar asibitin, kulawa sosai nurse din ta bata don ta bata tausayi yanda ta ga jikinta duk da ba ta san takamaiman abinda ke damunta ba, tana mata alluran kuwa bacci ya dauketa nan dakin Aliyu. Aliyu na gidansa har ya samu bacci ya daukesa.... ring din wayarsa ya tashe sa, dubawa yyi da kyar ya ga Mumy ce, ya kai hannu ya daga a hankali ya kai kunne, da damuwa tace "Aliyu ya jikin Khadijah, or shud I come over naji shiru shiru" yace "Noo mum, da sauki anjima sanusi yaje can asibiti ya mai da ta gida" Mumy tace "Kai kana ina?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Na taho nan gida na ne, I need sleep" da mamaki mumy tace "Kuma ka bar ta ita kadai asibiti gashi ka ki barin Baby ta xauna da ita Abuturrab" yace "Nurses din xa su kula da ita mum" Mumy ta d'an yi shiru kafin tace "Toh shkkn, Allah ya sauwake, kai ya jikin naka?" Yace "Alhmdllh am better now" tace "Ohk, amma da ka daure kai ka je ka maido ta gida don Allah, bbu dadi hakan kamar bata da gata, idan baxa ka ba ni in je" yace "Toh mum xan je yanxu kiyi hakuri" daga haka ta yi masa sallama ta katse wayarta. Bayan magrib Aliyu yyi wanka bayan yyi sllh ya canxa kaya ya bar gidan, yana isa clinic din ya kira nurse da ya bari da Khadijah a waya yace tayi mata alluran karshe na ranan ta fito tare da ita yana waje, nurse din tayi yanda yace sannan suka fito tare da Khadijah, bin nurse din da ke rike da hannun ta take kamar iska xae kadeta ta fadi, duk ta rame lkci daya, yana kallon nurse din bayan sun iso a hankali yace "Hope you did all what I instruct you to" nurse din tace "Yes but, I don't knw why she's finding it difficult to walk, kuma tun daxu take complaining chest pain, Dr bashir ya bata magani dai daxu, har da shi ma cikin wa ennan" ta fadi tana nuna masa drugs din da Khadijah xata kai gida, Khadijah dai na tsaye kanta a kasa duk a tsorace take ga xuciyarta dake bugawa da sauri da sauri, Aliyu ya gyada kai yace "Thanks nurse Maryam" Nurse din tayi murmushi ta sa Khadijah ta shiga gaban motar ta rufe tana mata Allah ya kara lfya, tada motar Aliyu yyi ya bar haraban hospital din, har suka isa gida bai ce komai ba, yana lura da hawayen da take yi tana gogewa da Hijab dinta tun bayan da suka fito clinic har ynxu da suke gida, ya gama parking ta bude motar a hankali ta fita, ya bi ta da ido ganin yanda take tafiya har ta shiga gida, sae sannan shi ma ya fito ya rufe motar ya shiga gidan. Mumy dake xaune parlor da su siyama da Anty khadijah ta mike ganin Khadijah tace "Sannu khadijah, ya jikin" Khadijah ta kasa dago kanta tace "Naji sauki Mumy" Anty khadijah sai kallonta take babbu kiftawan kirki, Aliyu na shigowa parlorn ya haura sama, Mumy ta kama hannun Khadijah ta wuce sama xuwa bedroom dinta da ita, da kyar khadijah ta iya cin pepper soup din da mumy ta mata, duk bakin ta babu dadi, a nan dakin bacci ya dauketa. Cikin dare misalin karfe biyu xaxxabi ya kuma rufe ta, dakin Aliyu Mumy ta shiga ta samesa xaune kan darduma ta xauna gefen gado ta jira ya sallame sallahn da yake da damuwa tace "Aliyu har yanxu fa jikin Iman" yace "Xaxxabin kuma?" Mumy tace "Ehh dama" yace "Mumy to ta kara shan drugs din..." Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace "Toh shkkn" sannan ta mike ta fita, magungunan ta sake bata ta rufe ta da duvet sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauketa. Da safe tea Khadijah ta sha bayan mumy ta tilastata da kyar, da tayi ma Aliyu maganan alluranta da ya rage yace driver ya kai ta sai karfe goma shi xai fita aiki, sanusin ne ya kai ta ya maido da ita, kafin yamma taji saukin jikinta sosai sai dai ta rasa irin ciwon da take jin kirjinta ke mata, kuma hakan na faruwa ne in dai ta tuna incident din ranan sai taji mugun faduwar gaba, har lkcn Aliyu bai barin su hada ido a gidan kuma bai ce mata komai, idan tana wuri ma bai yrda ya tsaya a gun, Anty khadijah dake lura da komai har wani farin ciki da nishadi na musamman take ji a gidan, har Mumy ta dinga mamakin yar uwar tata, duk fadace fadace da xage xagen ta rage yanxu hatta Khadijah ta daina hantara nan ko shirin sake komawa inda taje kwanaki kamar yanda aka ce mata ta dawo idan ta tabbatar komai ya wakana a lkcn ma xa a fara aikin, tunanin karyan da xata yi ma Mumy kawai take ta tafi inda xata. Aliyu na bedroom dinsa da daddare baby ta shigo, ta xauna kusa da shi tace "Yayanmu I want to ask you something pleaseee" yana kallonta yace "What?" Ta langwabar da kai a hankali tace "Iman tayi maka wani laifi ne, naga you no longer talk to her, ko ta gaisheka sometimes you do pretend you didn't hear, why please, ka gaya min me tayi maka, gashi ita ma she is always sad yanxu, I've caught her severally tana kuka cikin dare..." Katse ta yayi yace "Na fara wasa da ke da yawa koh?" Da sauri ta girgixa masa kai, ya hade rai yace "Toh tashi ki tafi" mikewa tayi da sauri ta fita ya ci gaba da danne dannen laptop da yake yi. Washegari da sassafe Anty khadijah ta shirya har da kwallarta take ce ma Mumy xata Abuja an kirata wai Yusuf d'anta ba lafiya yana asibiti, mumy jikinta yyi sanyi har da bata dubu goma ta hau mota, ta karba ta yi mata godiya ta bar gidan. Karfe goma saura Mumy ta tafi aiki gidan ya rage khadijah da baby sai Iklima don su siyama sun tafi makaranta, Aliyu ma na sama a dakinsa, tun bayan abinda ya faru tsakanin khadijah da Aliyu ta rage xaman cikin gidan sae Mumy na nan, always a baya xaka ganta xaune ita kadai, yau ma xaune take tayi nisa a tunanin da take kamar ance ta juya taga Aliyu tsaye d'an nesa da ita, mikewa tayi a tsorace tana komawa baya, ya dauke idonsa daga kallonta yace "Iman" hawaye ya cika idonta ta kasa amsawa, karasowa yyi kusa da ita ya tsaya tana komawa baya a hankali, yace "Za ki gane gidan step mum din ki?" Khadijah sai kallonsa take xuciyarta na bugawa, ya hade rai yace "Am asking" a hankali tace "Kila in gane" yace "Ohk... Am coming back now" daga haka ya juya ya koma ciki, ba a dau lkci ba ya dawo, envelope ne rike hannunsa ya mika mata taki amsa gabanta sai faduwa yake, yace "Collect it" hannunta na rawa ta karba, yana gyada kai yace "Go Iman, go back to ur step mum, I can't continue my life the way I want living with you in the same roof, you are now a barrier to my happiness pls ki tafi Iman go anywhere, leave our home, bana son Ina ganinki ina jin haushin kai na cos nobody is above mistake, just go plss" A hankali ta juya masa baya hawaye na sakko mata tace "Ohk xan tafi... thank you very much for all what you've done to me throughout my stay in your home, Allah saka maka da alkhairi duk hidiman da ka min, but ina neman alfarmar ko xan iya yi ma Mumy sallama kafin in tafi, don ban mata hallaci ba idan na tafi bata sani ba" a takaice yace "Noo, just go Iman" ta fashe da kuka sosai tace "Ohk nagode" juyawa yyi ya nufi cikin gida... Sai kuma ya juya da sauri yana kallonta yace "And one more thing... Forgive me plss" ta juyo hawaye na sakkowa idonta tace "I have done that already" yace "Thank you" daga haka ya juya ya shiga ciki ya rufe kofa. Share hawayen idonta da ya ki tsayawa ta dinga yi, dama Hijab ne jikinta kawai ta nufi gate ta fita gidan, da kafa ta karasa bakin titi ta samu napep tana kallonsa a hankali tace "Tasha xaka kai ni" yace "Toh" daga haka ta shiga napep din, har suka isa tasha bata sani ba tayi nisa a tunanin da take, mai napep din ya dawo da ita duniyar tunanin da taje, sai a sannan ta tuna kudin da xata basa, da sauri ta leka cikin envelope din da Aliyu ya bata taga kudi ne me yawa a ciki ta xaro dubu daya hawaye na sakko mata ta shiga tashar ta nufi inda taji ana kiran kano, dama mutum daya ake jira tana shiga motar ta bada kudinta bbu bata lkci suka dau hanyar kano. Tun da suka iso kano Khadijah ta fito daga cikin tashar kanoline take ta kalle kalle tsaye a bakin titi, duk mai adai daitan da ya tambayeta inda xata sai dai ta kafe sa da ido nan kuwa tunanin da take daban, hadarin da ya shiga haduwa a garin ne yasa ta dawo reality, da kanta ta tafi gun wani mai napep a hankali tace "Tudun yola xan je" yace "Dai dai ina a tudun yola" tace "Idan mun je xan gane" Bata damu da kudin da ya kira mata ba ta shiga adai daitan suka dau hanyar anguwar da ta kira masa, tun suna hanya aka fara yayyafi har suka kawo Tudun yola, ita dai ta san ranan da suka taho daga katsina da ummanta taji ta ce ma mai napep Tudun yola to amma bata san ina a Tudun yola ba, tun mai napep na biyeta suna xaga anguwar har yyi parking yace "Bani kudi na ki sauka, ke da baki san inda xa ki ba kika sa na dauko ki" sauka tayi daga cikin napep din ta basa kudin da yace daga cikin envelope ya bata canjinta ya ja adai daitan sa yyi gaba, hawaye ya cika idonta ta saka kai gabas tana ta tafiya, to ina xata ga gidan ummanta, jin ruwan ya taho da karfi yasa ta samu yar rumfa ta tsaya, ta kusa minti talatin tsaye karkashin wajen, kowa ya shige gida, wasu kuma sun shiga shagunansu saboda ruwa hanyar kamar anyi shara, ita kadai ce a waje ga wani sanyi da ta dinga ji, an dau fiye da awa daya ana ruwan kafin ya tsagaita sai yayyafi, fitowa tayi daga inda take tsaye ta ci gaba da tafiya a gajiye, bata yi wani nisa tana tafiya ba taji ance "Lahh Mama dubi yarinyar nan mai kukan kitso" Juyawa tayi taga wata mata ce da 'yar ta da suka hadu a saloon ranan da Umma ta kai ta gyaran gashi, uwar ta rankwashi yarinyar da baxata wuce Khadijah ba tace "Toh ina ruwanki salon tsokana" matar tace "Sannu yan mata" Khadijah ta gaisheta ta amsa ganin xata wuce tayi saurin cewa "Anty don Allah ban san hanyar gidanmu bane, ko xa ki kai ni gun mai saloon din nan ta san ummata" matar ta saki baki tace "Baki San hanya ba kuma, daga ina kike haka?" A hankali khadijah tace "Daga kano nake na mance hanyar gidan ne" Matar dake ta yi ma khadijah kallon mamaki tace "Ikon Allah, sai dai saloon din da nisa daga nan gashi da sauran hadari, amma mu je mu hau adai daita sai in ajiye ki shagon" Khadijah ta d'an risina tace "Nagode Anty" daga haka ta bi matar da 'yar har suka isa inda masu adai daitan suke, ta fadi inda xa su sannan suka dau hanya, kamar yanda matar ta fada bbu laifi tafiyar da nisa, suna isa saloon din suka tarar mai saloon din ta fito xata rufe shago ta wuce gida saboda ruwa, Matar suka gaisa da mai saloon din sannan tayi mata bayanin Khadijah, mai saloon din tace "Tab, to ai gidan Hajiya Amina da nisa daga nan, cikin ruwan nan yaushe mutum xai fara takawa xuwa gidan ai sai dai adai daita" Matar tace "Toh don Allah ki taimaka ki dau adai daitan ki kai ta gidan idan ya so mamartata sai ta baki kudin adai daitan da kika biya" mai saloon tace "Sai dai haka" daga hakan suka yi sallama da matar Khadijah tayi mata godiya, wani adai daitan mai saloon ta samu suka shiga har kofar gidan Umma, a nan hankalin khadijah ya kwanta ta dinga kallon kofar gidan, khadijah ta sauka tana murmushi tace "Anty nagode xan je in karbo maki kudin napep din" daga haka khadijah ta shiga ciki da sauri, bbu kowa tsakar gidan saboda ruwan da aka yi, Khadijah ta kwankwasa kofar parlorn Ummanta a hankali, Bude kofar Umma tayi tana tambayar waye? Umma ta xaro ido hade da bude baki tace "Khadijah??" Rungumeta khadijah tayi cike da farin ciki tace "Ummata" Umma ta ja ta suka shiga ciki da mugun mamaki tace "Daga ina kike haka" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma" Umma tace "Ke da wa?" Khadijah tace "Ni kadai Umma ki ban kudi in kai ma mai adai da ita a waje, mai saloon din nan da kika kai ni ranan ce ta rakoni, ban san gidan ba" Umma ta dau kudi ta fita da sauri, Godiya tayi ma mai saloon din ta ba mai adai daitan kudin kawo ta da yayi da mayar da ita da xai yi sannan ta koma ciki. Umma ta dinga kallon khadijah tana share hawayen da ya ki tsaya mata a sanyaye bayan Khadijah ta gama yi mata bayanin duk abinda ya faru tun daga ranan da ta bar ta gidan yakumbo har ixuwa yanxu da take gabanta, abu daya ta boye mata a labarin da ta bata shine kuma abinda ya shiga tsakaninta da Aliyu kawai dai ce mata tayi yace ta tafi saboda Anty khadijah bata sonta, Khadijah ta share hawayen dake sakko mata ita ma cikin rawar murya tace "Umma me yasa baki son in xauna a wajen ki, don Allah kada ki sake kai ni ko ina, let me stay with you plss" ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Umma da ita kanta ba karamin rama tayi ba, Umma tayi gathering courage ta jawota jikinta a hankali tace "Khadijah ba laifi na bane kinga kishiyoyina ba kirki ne da su ba saboda su ya sa na kai ki gun yakumbo amma ta ci amanata ko don ba uwar mu daya ba, da wani mugun gidan ta kai ki haka xa a cutar min ke ina nan ban sani ba, har kadunan naje kwanaki in duba ki aka ce ai ta tashi a gidan, gashi bbu wanda yasan inda ta koma, haka nayi kwana biyu kafin in dawo nan kano, duk layukan ta basa xuwa har na gaji na daina kira, kullum fatana shine Allah yasa kuna lafiya ashe abinda ta maki kenan, to Allah ya saka maki, ita kuma wannan baiwar Allah da ta rike ki a gidan ta har na wnn lkcn Allah ya saka mata da alkhairi" Khadijah dake ta sauraren ta a hankali tace "Ameen" Umma ta mike tace "Bari in karbo maki abinci a makwabta bani nayi girkin gidan ba" daga haka Umma ta fita parlorn, khadijah ta jinginar da kanta da kujera a sanyaye, kadan ta ci shinkafa da miyar da Umma ta amso mata ta sha ruwa sannan ta fita yin alwala don ta yi sallah, Shafah da fitowarta kenan ita ma ta saki baki tana kallon khadijah, can ta kwalo ma Hasana kira, Hasana ta fito ita ma, Shafah tace "Kin ga ashe bak'i muka yi a gidan yau" a hankali khadijah ta gaishesu, dariya Hasana tayi tace "Lallai kam bak'i" daga haka ta juya ta koma bangarenta, Shafah ma ta wuce ciki tana dariya. Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da sallah, Umma dake yankan alaiyahu alamar dai ita xata amshi girki tace "Kina ji na khadijah, babu ruwan ki da mutan gidan nan ki rufa min asiri kinji, duk me xa su maki kar ki tanka su, ko don Alhaji ya bar ki ki xauna gidan nan" Khadijah ta gyada mata kawai, mikewa Umma tayi ta fita da alaiyahun waje sai da ta shiga kitchen ta kira Abban fadila, yana dauka bayan ta gaishesa tace "Alhaji dama alfarma nake son tambaya gun ka" yace "Ina ji" tace "Dama khadijah ce xata xo ta d'an kwana biyu nan, sun yi hutu idan ba damuwa don Allah" Yace "Toh kin gaya ma su Shafah?" Shiru Umma tayi bata ce komai ba, yace "Sai ki sanar da su don bana son abinda xa a xo ana min tashin hankali a gida" daga haka ya katse wayarsa, Umma ta ajiye wayarta a sanyaye , ko wace irin rayuwa ce wannan ta fada yanxu ita kam, tun da tayi auren nan bata da kwanciyar hankali sannan kamar warce aka daure kafarta a gidan tana xaune a hakan har lkcn. Fita tayi ta tafi dakin Shafah ta samesu tare da Hasanar daga nan bakin kofa ta tsaya tace "Sannun ku, Khadijah ta xo daxu daga kaduna nace in gaya maku..." Shafah ta mata wani kallo tace "Au haba, to ta sha kabo..." Hasana tace "Lallai kam, sannunta da xuwa" juyawa Umma tayi ta fita ta koma kitchen ta daura girkin tuwo a gas, ko da Umma ta koma parlornta dauko maggi bacci ta tarda Khadijah na yi kan kujera, ta tasheta ta shiga daki ta hau gado, abu daya yasa ta jin hankalinta ya kwanta game da Khadijah, kuma shine yanayin da ta ganta, kowa ya ganta yasan bata tare da wahala sai dai 'yar ramar da tayi. Sosai Khadijah tayi kokarin ganin bata kula duk yaran gidan ba kamar yanda Umma ta yi mata huduba duk da irin cakalarta da suke yi a satin ta daya a gidan, ita kanta Umma hakuri take da kowa na gidan don kamar warce aka rufe ma baki komai suka mata bata tankawa duk ta yi sanyi kamar ba ita ba, Shafah da Hasana wani mulki na musamman suke xubawa a gidan, sai abinda suka ce ayi ake yi ga ikon bala'i... A can Kaduna kuwa, kamar wasa aka nemi Khadijah a gidan aka rasa har yamma, Mumy da farko ita a tunaninta ko Aliyu ne ya fita da ita don har ta tanadi rashin mutuncin da xata yi masa amma tana kiransa yace mata shi bai fita da ita ba, na hankalinta ya tashi sosai ta dinga tambayar baby ko iklima ta yi mata wani abun ne don Anty khadijah bata nan balle tace ita ce, shi kam Aliyu dama yana tabbatar da Khadijah ta tafi ya wuce clinic, ganin yanda mahaifiyarsa ta ishesa da kiran ba a ga Khadijah ba yasa shi komawa gida, and he tried his best pretending he knws nothing about her disappearance. Islamiyyar da Umma tayi ma khadijah register ta ci gaba da xuwa a kano, abu daya ke damun Umma yanxu a kanta shine irin sanyin da tayi kamar ba lively khadijahr ta ba, sanyin kuma ne yasa ko kadan abinda ake mata a gidan bata kula wa duk da idan ta fita islamiyya tun safe sai yamma take dawowa gidan. Kwanan khadijah talatin da 'yan kai a gidan Umma ne ta fara fito da wani habit na bacci, ko me take yi sai ta fara bacci a kai, islamiyya ma idan taje duk bacci take, hakan yasa wani lkcn bata dadewa xata dawo gida, Umma da abun ya fara isarta ranan ta bar mata kaya ta linke tana shigowa taga tana bacci kan kayan, duka ta kai mata tace "Wai lafiyar ki kuwa Khadijah, wannan wani irin bacci ne?" Khadijah ta farka a firgice tana mitsika ido, Umma ta harareta tace "Tashi ki je kiyi sallah bana ma son linkin kuma, wani iskanci komai aka sa ki sai ki buge da bacci" mikewa khadijah tayi a hankali ta fita bayan ta dau butan Umma, Hasana dake tsakar gida ta cika gidan da radionta Shafah kuma na kitchen suka bita da harara a tare, babu abinda ke kona masu rai a gidan irin yanda Umma da khadijah ke kin kulasu a gidan, duk da ita Umma sun san ba banxa ba rashin kulawar, to ita khadijah fa, Hasana tace "Ohh daga Hutu dai sai kuma aka rashe" Shafah dake juya miyar ta na yakuwa dake kan wuta tace "Ke ma dai kya gani, dama yau nake son tambayar Alhaji dalilin da yasa xa a munafurce mu ayi mana karya, ai sai ace mana ta dawo nan din ne da xama ba wai a mayar da mu yara ba" Hasana tace "Yara ko dai shashashai, bari dai ya dawo din ma ji dalilin rainin hankalin" Khadijah dake durkushe kasa sai yamutse fuska take ta dalilin kamshin miyar Shafah da ya kauraye tsakar gidan, mikewa tayi da sauri jin cikinta na hautsinewa ta juya xata koma parlorn Umma taji amai ya taho mata, dawowa tayi ta durkushe wajen ta dinga kwarara amai Shafah da Hasana aka yi tsit daga mita da habaicin da suke suna kallonta. Fitowa Umma tayi da sauri jin kakarin aman khadijah, ta karaso da ita ta duka tace "Subhanallahi.... Are you okay" khadijah ta kasa cewa komai duk ta galabaita lkci daya, Umma ta taimaka mata ta wanke baki sannan ta dagota ta wuce parlorn ta da ita, Khadijah ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi da kyar tace "Umma I don't knw what's wrong with me, I am always week" Umma tace "Sannu, ko malaria ne, bari Alhaji ya dawo sai mu tafi asibiti ni bani da kudi a gu na" Khadijah ta lumshe ido har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, mikewa Umma tayi ta fita don wanke gun aman, tana isa bakin kofa ta ji muryar Hasana tana cewa "Wllh fah, sai kace mai ciki, ji fa salon aman ma daban ne, idan ma malaria ne ba yellow shataf kalan aman ya kamata ya xama ba" Shafah tace "Haka fa shekaranjiya ina lura da ta shiga kitchen duba mata girki daga xama kan kujera sai bacci, daxu kuma da safe nan bakin kofa ta xauna da abinci a gabanta tayi bacci, ace baccin nan ba lafiya ne?" Umma dake tsaye bakin kofa har lkcn gabanta yyi mugun faduwa, fita tayi parlornta a fusace duk da ta fi wata uku bata tanka su a gidan tace "Sai dai ku ga ciki can kan 'ya yanku ko dangi, amma ba 'ya ta ba, tunda baku da kirki baku da Imani har ku yi ma yar mutum fatan wannan mugun abun, Allah ya isa wllh" Hawaye cike idonta ta kare maganar, Shafah ta mike tana huci ta kunduma mata xagi tace "Bakin ki ya sari danyen kashi, ba ma ga mugun abu ba a 'ya ya ko dangi, to wa yasan inda kika kai ta kwanki ko karuwanci kika sa tayi maki...." Umma ta juya ta koma daki hawaye na sakko mata sosai, kallon khadijah ta tsaya yi taga har tayi bacci, ta xauna duk jikinta a sanyaye a xuciyarta tana kara yi ma su Shafah Allah ya mayar masu mugun alkaba'in da suka yi ma 'yar ta. Har karfe tara Khadijah na bacci bata tashi ba, tada ta umma tayi hankalinta ya tashi jin irin xafin da jikinta ya dauka, da kyar ta lallabata ta sha shayi kadan sannan ta bata paracetamol ta rakata bedroom dinta ta kwanta ita ta dawo parlor ta xauna har lkcn xuciyarta ya kasa dawowa dai dai, khadijah ce ta fito da sauri daga dakin umma na tambayarta me ya faru amma ta fita waje tun kan ta karasa can gun kwararon ruwa ta dinga amai a tsakar gidan, Umma da ta bi bayanta ta tsaya tana kallonta, jin sound din aman yasa Hasana ta leko sai ga Shafah ma ta leko, Umma ta koma ta dauko buta, ta durkusa kusa da ita har ta gama sannan ta wanke mata baki suka koma ciki, sai shivering take cikin rawar murya tace "Umma ki rufe ni sanyin" Umma ta dauko duvet da sauri ta rufe ta, nan da nan kuma bacci ya dauketa. Umma ta koma parlor ta xauna duk ta rasa me ke damunta, jin shigowar Abban fadila gidan ta jira har ya shiga part dinsa da minti sha biyar sannan ta fita, sallama tayi bakin parlornsa ya amsa ta shiga, Shafah ce a parlorn tana xuba masa abinci shi kuma yana kallon news, Umma ta xauna ta gaishesa ya amsa, a hankali tace "Alhaji dama idan da hali don Allah kudi nake so ka ba mu xan kai khadijah asibiti bata da lafiya tun safe" Shafah tace "Ae gwara aje asibitin nan kam wannan amai da bacci haka a gida" Umma tayi shiru tana kallonta, Abban fadila yace "Nawa ne kudin asibitin?" Shafah tace "Tun da ya sanka likitan kamar family Dr ne ko dubu 3 ka basu xai yi ai" ita dai Umma bata ce komai ba, Ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da dubu hudu ya mika mata yace "Gashi sai ku yi har kudin mota" ta karba da ladabi tace "Toh mun gode sai da safe" daga haka ta mike ta bar parlorn. Washegari da sassafe Umma ta sa Khadijah ta shirya bayan ta tilasta ta shan shayin da ta hada mata amma tas ta amaye sa gaba daya, duk ta xabge tayi laushi lkci daya sbda aman da take yi, A dai dai ta umma ta samo masu har kofar gida ganin kamar baxata iya tafiyar ba ma, Hasana dake sharar tsakar gida tace "Toh a dawo lafiya dai, Allah raba bawa da jin kunyan duniya da lahira dai" Umma bata tanka ta ba tana rike da Khadijah suka fita, wani asibitin daban ba wanda suka saba xuwa Umma taje ba, suna xuwa aka ce sai sun yanki kati dubu biyu, duk jikin umma yyi sanyi, shiru khadijah dake xaune tayi tana kallon nurse din dake tsaye Kansu, nan ko tuna kudin da Aliyu ya bata take yana bayan kujeran umma ta ajiye bata kuma nuna ma umman ba har lkcn, Umma ta mike tace ma nurse din tana xuwa yanxu, Cike da karfin hali Khadijah tace "Umma ina xa ki?" Tace "Yanxun nan xan dawo khadijah" daga haka ta fita. Gidan wata kawarta dake layin ta tafi ta ranto dubu biyu da yake suna mutunci da matar sosai ta bata sannan umma ta dawo asibiti, bayan an yankar masu kati suka samu ganin likita, Umma ce ke fadin abubuwan da ke damun khadijah ma likitan, don Khadijahr duk tayi weak, tambayar farko da likitan ya jefo ma Umma shine "Tana da aure ne?" Gaban umma yyi mugun faduwa ta girgixa ma likitan kai kawai, likitan yace "Toh xa ayi mata test..." Bai dai fadi wanne ba umma tace "Toh" ya kira nurse ya bata file din nasu yace su bita, Umma na rike da hannun khadijah suka dawo reception, Nurse din tace kudin test din dubu biyu da dari biyar haka Umma ta bata duk ta yi wani sanyi, suna ta xaune a reception har bayan mintuna da dama result ya fito matar ta ce su je office din Dr bayan ta kai ma sa, Likitan dake ta kallon umma yace "Yar ki ce yarinyar nan?" Umma ta gyada masa kai xuciyarta na bugawa, ya girgixa kai yace "Sorry madam, She is few weeks pregnant" mikewa Umma tayi a mugun gigice tace "Pregnant Dr?" Likitan ya gyada mata kai, Khadijah da ta xaro ido ta dinga kallon likitan xuciyarta na bugawa, kuka sosai Umma ta saki a gun ta juya ta fita, khadijah ta mike ta bi bayanta da sauri, likitan ya girgixa kai ya bi ta da kallo a ransa yace why Such a beautiful girl, Gaba daya asibitin Umma ta fita har lkcn tana kuka, khadijah da duk jikinta ya mutu ta dinga bin ta ita ma, har lkcn ita dai bata gane wani pregnant din likitan ke nufi ba, adai daita Umma ta hau tayi wucewarta gida, Khadijah da tayi still a inda take ta bi adai daitan da kallo ta kasa kwakkwaran motsi, lkci daya duk ta nemi xaxxabin da rashin kwarin jikin dake tattare da ita ta rasa, har sannan kuma ta kasa kukan, tafiya ta fara yi kamar warce kwai ya fashe ma, da yake ba wani nisa ne da asibitin ba har ta isa gida, Hasana da Shafah na xaune tsakar gida ta wuce parlorn Ummanta suka bi ta da kallo, bata ga Umma a parlor ba a shiga bedroom dinta, xaune ta ganta nan kasan dakin banda kuka babu abinda take, ta sulale kasa a hankali sai a sannan wasu hawaye masu xafi suka dinga sauka idonta, Muryar Umma taji cikin kuka tana cewa "Khadijah yanxu ni xa ki kunyata, ni xa ki yi ma tonon asiri a idon duniya, is this my reward for taking you as a daughter?" Khadijah na shessheka tace "Ummata kiyi hakuri" mikewa Umma tayi da wani force ta sauke mata mari, bata gama recover ba ta kuma kai mata wanda ya fi na da, kasa kwakkwaran motsi khadijah tayi a inda take durkushe lkci daya taji komai ya tsaya mata, Umma na mata wani kallon da xa a iya kiransa da na tsana tace "Kin cuce ni kin ci amanata, kin ci amanar late mahaifinki" hakan da ta fada ya sa khadijah rushewa da kuka mai ban tausayi cikin rawar murya tace "Na shiga uku, don Allah Ummata ki yi hakuri" ta kuma kai mata wani marin tana kuka sosai tace "Uban waye yayi maki Ciki khadijah" kamar numfashinta xai dauke take kuka tana girgixa kai tace "Ban sani ba Ummaa" rufeta tayi da duka har sai da ta gaji don kanta ta kyaleta kuma har lkcn kuka take, cikin raunin murya tace "Tashi ki bar min gidana kije duk Inda xa ki je tunda baki san wanda yyi maki ciki ba, Allah ya isa tsakanina dake khadijah, kin bata min suna, ki tafi khadijah xaman ki gidan nan xai iya kashe min aure ki tafi bana son ganin ki kije duk Inda xa ki" gyada mata kai kawai khadijah take tana sheshsheka, shigowan su Shafah da Hasana dakin yasa Umma tayi shiru har lkcn tana kuka, suka gama kare masu kallo sai suka saki shewa sannan suka fita dakin, khadijah ta mike da kyar don banda ciwo babu abinda ko ina na jikinta ke mata ta fita dakin tana goge jinin bakinta, bayan kujera ta tafi ta dauki envelope din da Aliyu ya bata wasu hawaye masu xafi na xubo mata, xaxxage bundle din kudin tayi gaba daya a kasa sai ga wani farar takarda a linke ya fadi, ta dau takardar ta warware tana kallon content din, *I don't have much to say khadijah, na san har abada baxa ki mance abinda ya faru tsakaninmu ba kamar ynda nima baxan mance ba, tafiyar ki shine ma fi alkhairi sbda baxan taba samun kwanciyar hankali da nutsuwa ba matsawar muna gida daya, ina rokon gafarar ki Khadijah forgive me not because I deserve it but for the sake of Islam, Allah hada fiskokinmu a aljannatul fiddaus, ina maki fatan alkhairi a rayuwa da fatan miji na gari* cukuikuye takardar tayi ta fashe da wani kukan takaici taji dama ta kashe kanta ta huta amma bbu daman yin hakan, mayar da kudin tayi envelope din har ma da takardan ta mike ta fice parlorn tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ko kadan bata ji me su Shafah ke cewa ba har ta fice gidan gaba daya, khadijah bata xarce ko ina ba sai tashar mota, tafiya kawai take a park din tana jin sunan garuruwan da ake fadi har ta isa gun motar garin Yobe ta hau bayan minti goma mota ta cika suka dau hanyar damaturu garin da bata san kowa ba bata taba xuwa ba. *What I want some people to get here is that, wnn labarin khadijah ne, kun riga da kun san rayuwarta a yanxu, she is living a normal life just dat abubuwa da yawa na memory dinta ne har ynxu, what I am writing now is her past ya riga ya wuce so I don't knw why wasun ku ke damun Kansu being emotional, this is not what is happening presently, it's just her past story* Da tsakar rana Khadijah suka iso garin damaturu, ta fito a hankali daga motar tana bin ko ina na park din da kallo, wani jiri ke dibar ta a lkcn ga sanyin da take ji ba kadan ba, tana tafiya a hankali har ta fita park din, kallon masu adai daitan dake ta tambayata Inda xata ta dinga yi lkci daya hawaye ya cika idonta, bata ce komai ba ta dinga tafiya, bata san iyakar lkcn da ta dauka tana tafiya ba, jin baxa iya ci gaba da tafiyar ba ta samu karkashin wani bishiya da ta hango duk anyi littering dinsa da 6awon rake ta xauna tana sauke numfashi a hankali, cikin Hijab dinta ta ajiye envelope din hannunta, bacci ne ya dauketa lkci daya a hakan saboda iskan da leaves din bishiyar ke ta bayar wa, bata san lkcn da ta dauka tana bacci ba hayaniyar wasu almajirai ya tada ta, ta gyara xamanta da sauri tana kalle kallen wajen envelope dinta a hannunta, a hankali ta tashi da kyar ta ci gaba da tafiya kamar bata son yi kwata kwata ko yunwa bata ji sai kasala, wannan karan ma tafiya me nisa tayi da kafa ganin wani masallaci ta dau buta dake cike da ruwa ta samu gefe ta xauna ta daura alwala sannan ta tafi jikin wani shago tayi sallahn da bata yi ba, mayar da butan tayi ta ci gaba da tafiya, har aka kira magrib tafiya kawai khadijah take, ganinta a wani kasuwa ta dinga xaga kasuwar, a hankali a hankali kasuwar ta fara watsewa ta shimfida dankwalinta gaban wani shago da aka duk aka rufe tayi magrib da isha ta jingina da table din gaban shagon, wasu hawaye suka dinga bin kuncinta, sanyi sosai ke shigarta ga xaxxabi kan kace me kasuwar yyi tsit kowa ya wuce gida, duk da uban sauron da suka yi yawa a wajen hakan bai hana bacci me nauyi sake daukarta daga xaunen da take a gaban shagon ba, bata kuma farka ba sai da kiran sallar asuba ya farkar da ita, ta dinga bin wajen da kallo, can ta tashi da kyar tana tafiya a hankali kamar iska xai hura ta ta fadi ga wani ciwon xuciya da ta tashi da, banda xugi da axaba bbu abinda yake mata, duk wnn abun sai lkcn taji yunwa na damunta sosai, masallaci me hade da na mata take ta nema amma duk iya tafiyar da tayi bata ga alamar ko daya ba, wani wajen ta samu ta xauna nmta hade kai da gwiwa tana kuka cike da rauni, har gari ya waye mutane suka fara hada hadarsu tana xaune Inda take, cike da karfin hali ta tashi ta nufi titi ta tsaya jiran adai daita, bbu bata lkci wani ya ja ya tsaya, ta shiga a hankali nace "Central mosque xaka kai ni" yace "Na ina?" Tace "Wanda ya fi kusa dai" ba wani tafiya me nisa suka yi ba yyi parking bayan mmsun iso kusa da wani babban masallaci, kudin dake jikinta har lkcn ta fiddo ta ciri dubu daya ta basa yace ba shi da canji, a hankali tace "Toh ka tafi" sannan ta shiga masallacin, bangaren mata ta nufa ta daura alwala bayan ta xaga bayi sannan nmta shiga cikin masallacin ta tada sllh, tana ta xaune bayan ta idar tayi nisa tunanin da take jin agogo yyi stucking karfe tara ta mike a hankali ta fita ta dau tsintsiya tana taya bayin Allahn dake ta sharan masallacin shara, suna gamawa ta fito da kudin ta don duba abinda xata siya ta ci, waina da miya ta siya da ruwa ta dawo cikin masallacin, a haraban ta xauna ta bude ledan abincin tana daukan guda ta kai baki taji cikinta ya hautsine, tayi saurin tashi ta nufi gun da ake alwala da gudu nan ta dinga amai a wajen kamar xata shide, da kyar ta tashi daga karshe duk jikinta ba kwari nmta koma cikin masallacin nmta kwanta ba tare da ta sake bin ta kan masan ba, tana mayar da numfashi, dukunkunewa tayi waje daya jin sanyi na shigarta ta ko ina, wanda hakan na da nasaba da xaxxabin da ya rufeta lkci daya, sai azahar ta farka jin ana kiran sllh. Daren ranan a masallacin khadijah ta kwana, amma washegari da safe wata dattijuwa dake share sharen masallaci tace ta nemi gun da xata dinga kwana daga ranan don masallaci ba wajen kwana bane da ace kwana ake barin mutane ke yi a ciki da bai yi kyan gani ba yanxu, cike da fada take maganan, jikin khadijah yyi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, karfe sha dayan safiyan ta bar masallacin, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a lkcn sbda yunwa ce kawai ke dawainiya da ita ga xaxxabi, ramar da tayi ya fito sosai, karfin hali ta dinga yi tana tafiya, tafiya kuma ba na wasa ba tayi ba tare da tasan takamaiman inda xata je ba, ganin she can't move any further don kafafuwarta sun ma Gmgaza daukar ta kuma ta fara tunanin xuwa wani masallacin ta kwanta, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa da ta gaji sai ta tsugunna idan ta huta sai ta mike, kawai d'aga kai tayi ta ga wata mata da ta shiga titi da nufin tsallakawa wani mota da ya taho da uban gudu ya kwasheta sai da tayi sama da ita snn ta fado kan titin, duk da nesa da ita aka yi hatsarin amma irin ihun da ta fasa a tsorace xaka ce ita motar ta buge tsabar tsoratar da ta yi, daga nan kuma bata sake sanin abinda ya faru ba ta dai bude idonta da yyi mata nauyi ta ganta kwance wani daki da yyi kama da na asibiti da ruwa a hannunta, dafe xuciyarta dake mata xugi sosai tayi ta dinga bin dakin da ido a hankali lkci daya kuma tana son tuno abinda ya faru amma ta kasa, a hankali ta sauke idonta kan wani mutumi dake xaune d'an nesa da ita idanuwansa da hankalinsa gaba daya kan wayar dake hannunsa, duk da a xaune yake hakan bai boye tsayinsa ba, sajen dake kwance gefen fuskarsa kadai take gani da uban gashin da ya tara a kai, da dogon hancinsa duk ta side view take kallonsa, ta shiga kkrin mikewa xaune da kyar har lkcn tana dafe da xuciyarta dake mata axaba ba kadan ba wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, sai a nan ya kallo direction dinta, mikewa yyi da sauri ganin ta tashi ya karaso kusa da ita yace "Hello... how you feeling now?" kallon jajayen lebbensa kawai take don bata taba ganin haka ba, ya buda dara daran idanuwansa yace "Hey... Are you there?" Kin cewa komai tayi still, ya juya ya fita ba a dau lkci ba ya dawo likita na biye da shi, likitan ya tsaya kanta yace "Hi... How you feeling madam?" Ganin yanda duk suka tsura mata ido, ta sauke nata idon a hankali tace "Alhamdulillah" likitan yyi murmushi yace "Maa sha Allah, hope bbu Inda ke maki ciwo ynxu koh?" Ta gyada masa kai duk da axaban da xuciyarta ke ta yi matan, yace "Good" snn ya juya ya fita, kallon mutumin dake tsaye ya rungume hannayensa tayi cikin sanyin murya tace "Me nake yi a nan?" Sai a snn ya kalleta yace "Kar ki damu xa a sallame ki nan da anjima ki wuce gida, before then ki bani number 'yan gidanku a kirasu, sure they are all disturb yanxu, you passed out since in the morning... And this is...." Ta kalli agogo da sauri kafin ya fada taga karfe bakwai, ta kallesa tace "Bakwai na safe?" Ya girgixa kai yace "No, Night" shiru tayi bata sake cewa komai ba kamar me naxari, sai a sannan kuma ta tuno abinda ya faru daxu, ta fashe da matsanancin kuka tace "Wayyo matar ta mutu koh?" Hade rai yyi yace "Nooo, an kai ta asibiti ita ma, am sure she's recovering also" tsoro ne sosai tare da ita tana kallonsa, ya langwabar da kai yace "Ina xuwa" daga haka ya juya ya fita ta bi sa da ido, ko minti biyar bai yi da fita ba sai ga wata nurse da magunguna a leda, ta ajiye kan gado tana mata sannu tace "Idan kin samu abinda kika ci xan dawo in nuna maki dosage" daga haka ta fita. Da sallama ya shigo ward din rike da takeaway din abinci ya karaso ya ajiye kan table dake kusa da gadon yace "Ga shi ki ci abinci ki sha magani kafin a sallame ki...." Bata ce komai ba ya mika mata wayarsa yace "Before then, fara kiran mutanen gidan ku ki sanar da su kina asibiti" shiru tayi bayan ta karbi wayar, ya fada mata sunan asibitin sannan ya fita, hawaye ya cika idonta ta saki kuka a hankali tana tausayin kanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin... kallonta yyi sannan ya kalli abincin ya d'an daure fuska sai kuma ya karaso ya bude ya sa cokali ya mika mata ba musu ta karba tana kallon jollof rice da naman, yace "Kin kira su?" Gyada masa kai tayi yace "They are coming to take you now right?" Nan ma kai kawai ta gyada masa, yace "Alryt, ki ci abincin nurse xata shigo ta nuna maki dosage din maganin yanxu, I've paid the bill, Allah kiyaye gaba I will be on my way now..." Kai kawai ta gyada masa tana iya kokarin ganin bata bar hawayen dake taruwa idonta ya xubo ba a hankali tace "Nagode" ya buda ido sosai yace "No thanks" ta lura sauri yake don tuni har ya kai kofa, ta kalli wayarsa dake gefenta a hankali tace "Your phone" ya juyo da sauri yace "Ohh thanks har na mance" daga haka ya dau wayarsa ya fita ward din, ta rufe abincin ta ajiye ta hade kanta da gwiwa hawaye mai xafi na sakko mata, bayan kusan minti goma da tafiyarsa nurse din daxu ta dawo, da sauri ta goge hawayenta, nurse din tace "Kin ci abincin koh?" A hankali khadijah tace "Na ci" nan ta nuna mata dosage din drugs din sannan tace "Sai ki sha yanxu, an riga an sallame ki, yace yan uwanki na hanya koh?" Ta gyada mata kai tace "Toh Allah ya kawo su lfya" daga haka ta fita, ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata kuna, sai a snn envelope din kudin dake hannunta da ta fadi ya fado mata, bata wani damu ba don tasan me rabo ya dauke shikenan kuma, bayan wani minti ashirin din nurse din ta shigo tana mata wani kallo tace "Wai har ynxu ba su iso ba yan uwan naki?" Tana kallonta a sanyaye ta gyada mata kai kawai, nurse din ta tabe baki ta juya ta fita, taa ta xaune ta rasa me ke mata dadi har lkcn kanta na bisa gwiwanta nurse din ta shigo da likitan daxu, likitan yace "Ke daga wani garin yan uwanki xa su xo ne har yanxu basu iso ba, ko karya kawai kike ma mutane?" Hawaye cike idonta cikin rawar murya tace "Ehh" ya xare glass din idonsa yana xaro idon yace "Karyan kike?" Ta fashe da kuka a hankali tace "Ni bani da yan uwa, ban san kowa ba, ban san ina xan je ba" a mugun fusace yace "You must be joking, Look malama fita ki bar ma mutane asibitin su, get out yanxun nan, maxa dau sauran abincin ki ki fita kar in kira masu gadi su yi waje da ke" jikinta na rawa ta sakko ta dau abincin da yace tana jin kamar jiri xai kada ta hawaye na sakko mata sosai ta nufi kofa, nurse din ta bi ta da kallo, murya can kasa tace "Dr ko xaka kira shi wanda ya kawo ta tun da kasan shi?" ya jefa mata wani kallo yace "Toh me xai yi mata idan na kira sa, sanin wacece ita yayi aka gaya maki? He just helped her tayi collapsing a gefen titi daga anyi hatsari" khadijah ta bude kofa xata fita likitan yace "Tsaya malama" tsayawa tayi ta juyo tana kallonsa a tsorace, ya ciro wayar sa a lab coat din jikinsa yyi danne dannensa kafin ya sa hands free wayar ya fara ring, sae da ya kusa katsewa aka daga, likitan ya ce "Sudais, ga patient din da ka kawo mana taki tafiya fa...." daga daya bangaren aka ce "I don't get you" a d'an fusace likitan yace "I also didn't get what she meant by saying she don't have relatives and she don't knw where she's heading, don Allah ka xo ka fidda min ita a asibiti plss" Wanda ya kira da Sudais cikin expression din mamaki yace "Ji min walakanci fa, toh ni da ka kira ni me xan yi? If I am not mistaken I told you I don't knw her Yusuf, then why calling me? Me yasa kake kirana? Wait wllh sai ka gaya min me yasa ka kirani ma dai, are you not just suppose to tell her to leave kayi discharge dinta???" Likitan ya kalle Khadijah a fusace yace "Ke malama maxa nemi Inda dare yyi maki kada in sa a xo a fitar da ke yanxun nn, get out plss" kai ta gyada masa jikinta na rawa hawaye na sakko mata, Da sauri Sudais din yace "Wait Yusuf, you knw what? kaga dare yyi ynxu ka bari gobe da sassafe kace ta wuce plss since she's lying she don't have relative" likitan yace "Sai dai idan xata sake biyan kudin gado, don da ace haka ake yi a clinic din da ba mu samu ci gaba ba" Shiru Sudais ya d'an yi kafin yace "Toh naji xan biya ka, though I hate lies and liars let her just be safe there kafin ta wuce gobe, just dat 1st thing tomorrow morning send her away, good nyt" daga haka ya watse wayar, ko kallonta likitan bai yi ba yace "Bani hanya" ta bar bakin kofar da sauri yyi ficewarsa kamar xai tashi sama, Nurse din ta karaso kusa da ita tace "Me yasa kika yi karya yan mata, ke ba musulma bace?" Khadijah ta girgixa mata kai hawaye mai xafi na xubo mata, nurse din ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh tafi ki kwanta" daga haka ta fita ta bar ta tsaye, karasawa tayi kan gadon ta kwanta tana share hawayenta, wajajen karfe sha biyu ta tashi xaune jin yunwa na nemanmatat illa ta bude abincin daxu, amai ne ya taho mata bayan ta kai baki ta sauka kan gadon da sauri ta shiga bayi ta dinga amai kamar xata amaye hanjinta, jikinta a mace ta fito ta kwanta bisa gado tana sauke ajiyar xuciya ta kudundune waje daya daga haka bacci ya dauketa sanyi na shiga jikinta. Kasa tashi sallan asuba Khadijah tayi washegari ta dalilin xaxxabin da ya rufe ta, jin an bude kofar ward din ta bude idanuwanta a hnkli taga gari ya waye sosai, likitan da mutumin jiya da ya kira da Sudais suka shigo ward din a tare, tun daga bakin kofa sudais dake sanye da milk jallabiya ke mata wani kallo har karaso gadon yace "jiya da na baki waya wa nace ki kira?" Khadijah ta mike xaune da kyar ganin ynda ya hade rai ta marairaice tace "Relatives dina" ya kara hade giran sama da ta kasa yace "Then why didn't you call dem?" cikin rawar murya tace "I don't have anybody to call, ni marainiya ce, my father is late so also is my mum, My step mum....." Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, cikin tsawa yace "Karya kike yi, shut ur mouth plss" likitan dai rungume hannu kawai yyi yana kallona yana murmushi, ta hade kai da gado tana kuka cikin rawar murya tace "ku yarda dani don Allah, wallahi ni bana karya, laifi nayi ma step mum dita tace min in bar mata gidanta, I love my step mum and she loves me same, but tace in tafi sbda laifin da nayi, she raised me up as a mother even after my late dad passed away 5 years back, don Allah kada ku ce in tafi ban san kowa ba a garin nan ban taba xuwa ba, ku taimakeni ku kaini gidan marayu in dinga kula da yaran wajen don Allah" tsawa likitan yyi mata da ya firgitata ta dago da sauri, yace "You are mad, wa xa ki raina ma wayo, ni ko wannan da ke kusa dake?" Ya fadi hakan yana nuna sudais, Shiru tayi tana kallonsa, kafa mata ido shi ma yyi, can ya karaso kusa da ita yana kallon kwayar idonta da kyau, ya kai hannunsa ya bude eye lids dinta, can ya kalli fingers dinta sai kuma ya kalli Sudais dake tsaye, daga kafada yyi ya nufi kofa yace "I have better patients to attend to Sudais..." daga haka yyi ficewar sa daga cikin ward din, a sanyaye khadijah ta kalli Sudais dake mata wani kallo yana rungume da hannunsa, harara ya watsa mata bayan mun hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, muryarsa ya daki ear drum dinta, "Wani laifin kika yi ma mum din taki, kuma daga wani gari kike? Kina min karya xan gane kuma daga nan station xan kai ki" Shiru tayi tana kallonsa hawaye na ci gaba da sakko mata, cikin sanyin murya tace "Daga kano na xo" yace "Wato kin saba tafiya garruruwa kenan ko" ta girgixa kai da sauri tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace "Wallahi A'a" yace "Toh wani laifin kika yi mata?" Share hawayen idonta ta shiga yi a hankali ta hadiye wani abu da ya tsaya mata, can ta sakar masa kuka tace "Kilan baxa ka min taimakon da nace ka min ba idan ka ji dalilin bari na gida" strictly yace "Malama ki bude baki ki gaya min, stop wasting my time xan je aiki" jinginar da kai tayi da gadon ward din tace, "Duk abinda xan fada maka ka yarda dani sbda Allah, ni bana karya, I knw d consequence of it.... Domin ka min taimakon da nace ka kai ni orphanage yasa xan fada maka ni wacece" Bai tanka ta ba hakan yasa a hankali tace "I lost my mum at a very tender age, and my beloved last year" ta kallesa taga he is listening but not looking toward her direction, ta lumshe ido, a haka ta fara basa labarinta tun daga farko har xuwa yanxu da yake gabanta, bbu abinda ta boye ma Sudais, Kallonsa tayi a karo na farko tun da ta fara gaya masa ita wacece, hawaye masu xafi suka shiga xubo mata, Sudais ya dinga kallonta da wani expression da ta kasa fassarawa a fuskarsa, tana girgixa kai a raunane tace "I told you all but the blank truth about me, believe me plss" kasa ce min komai yyi sai bayan kusan minti biyu yana nuna ni da yatsa da wani irin mamaki yace "You mean... You are pregnant?" Ta gyada masa kai a hankali tace "That's what the Dr told me and my step mum" Jinginar da kansa yyi jikin bango yana kallon saman ward din ko kiftawa bbu, bai kuma ce min komai ba har na kusan minti uku, Khadijah dai sai kallonsa take don bata san tunanin da yake a xuciyarsa ba domin kuwa duk wanda ya gan sa yasan yyi nisa tunanin da yake, bude kofar aka yi duk suka kalli kofa, Dr Yusuf ya shigo yana kallonsa da kyau yace "Ya? Ka gama sauraren karyar ta Malam?" Sudais bai ce komai ba ya shiga shafa uban gashin dake kansa, likitan yyi murmushi yace "Very good then, naga kamar har karyar tayi tasiri a xuciyar ka" Likitan ya karasa kusa da khadijah yana kallonta da kyau yace "Are you married?" Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, wani murmushin ya sake yi ya kalli Sudais, Sudais ya lumshe manyan idonsa ya bude su a hankali yace "Yea xaka cire mata cikin soon as possible....." Wani kallo Dr Yusuf ke yi masa, Sudais ya dafa kafadarsa yace "Yeah... She told me about d pregnancy, an illegal one at it's early stage, i think you just have to flush it Yusuuf, I will pay what ever amount it will take" tunda ya fara magana khadijah ke kallonsa baki bude, can ta fashe da kuka tace "Noo plss, it's illegal but it doesn't deserve that, Allah xai yi fushi da ni, baxan iya ba..." wani mugun kallo Sudais ke mata ya karaso kusa da ita cikin tsawa yace "You are very very stupid, shegen xaki haifa?" Ta kuma rushewa da kuka tace "Eh, saboda Allah ne ya bani, kuma it's not my fault it came this way, beside soul din ba shi da laifi da har xan xubar da shi..." Yusuf ya rungume hannu yana kallonta, Sudais ma wani kallo yake mata lkci daya yana mamakin furucinta cos she look young to think that way, ya matsa dab da ita yace "Then ya xama dole ki koma gidansu Aliyu kika kirasa ko wa???" Khadijah tayi shiru tana kallonsa hawaye na xubo mata, ido ya kafeta da shi yana jiran jin abinda xata ce, ta sauke idonta a hankali tace "Toh me xan ce masu?" Strictly yace "Abinda likita ya gaya ma ke da Ummar ki" tana share hawayenta tace "Toh amma ni yanxu bani da kudin mota" yace "Xan baki" juyawa likitan yyi ya fita, shi ma ya nufi kofa kafin ya fita ya juyo ya kalleta yace "Ki sameni reception yanxu" daga haka ya fita, ta sakko a hankali ta dafe gado jin jiri, da kyar ta karasa reception din sbda jirin dake debanta tana isa ta xauna kan kujera ganin baya gun, office din Dr Yusuf sudais ya shiga, Dr Yusuf yace "What are you trying to do Sudais?" Sudais ya shafa kansa a hankali ya xauna kan table dinsa yace "I don't really knw Yusuf, kawai nayi analyzing naga babu karya a labarinta, I tried hard to figure out...." Yusuf ya katse sa da sauri yace "Da alama lauyancin ka bai fada maka gaskiya ba yau, look at you... sau nawa muke ganin cases irin wannan, tayi ciki ta gudu ta bar gida ta xo nan ta shirga maka karya a matsayin ka na barrister har karyar yyi sinking kan ka? Don't let me call u a disgrace to ur profession..." Sudais ya girgixa kai yace "Babu karya a xancen da ta min, and profession dina yasa nayi figuring din hakan, she told me nothing but the truth" Dr Yusuf yace "Toh naji gaskiya ta fada maka, what do you intend doing now?" Shiru Sudais yyi yana kallonsa, can ya dauke kai cikin damuwa yace "I don't knw frnd, I have never being confuse like this all my life, Yusuf just look at her, she is too young, baxa ta wuce sa'ar Rabi'ah ba, had I known wllh da ban tsaya a motata ba jiya" Dr Yusuf yace "Toh ko gidanku xaka kai ta" sauka Sudais yyi da sauri daga kan table din yana xaro manyan idanuwansa yace "Gun wa Yusuf?" Yusuf yyi dariya yace "Mami wai da" Sudais yace "Mami ta kashe ni kenan, cewa ma xata yi ni nayi ma yarinyar cikin, kai ma kasan ko hauka na fara baxan fara kai ta hanyar gidanmu ba, what for?" Yusuf dai sai dariya yake sanin wacece mahaifiyar sudais, Sudais ya tabe baki yace "Wani lkcn ma d'an Adam na xaman xamansa yake dauko ma kansa matsala da kansa a rayuwa if nt meye haka na sa kai na ciki??" Yusuf yace "Kawai ka ka ita orphanage din da tace xai fi" Sudais yace "In dai kai ta can gidan su dan iskan da yyi mata cikin" Yusuf yace "Wa yaga bata lkci" Sudais ya nufi kofa yace "Muyi waya frnd" Mikewa Yusuf yyi ya bi sa suka fita. Ba tare da Sudais ya kalli khadijah dake ta xaune duk ta gaji a reception ba yace "Mu je" mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, gun motarsa dake parking space ya nufa, ya bude ya shiga, ganin bata shiga ba Yusuf yace "sai ki shiga" a hankali ta kai hannu ta bude motar ta shiga, Sudais na kallon Yusuf yace "I will give you a call" Yusuf yace "Alright then" daga haka ya ja motar muka bar asibitin, bbu wanda yace komai cikinsu, yyi driving din kusan minti sha biyar suka iso wani anguwar masu kudi, nesa da gidansu Sudais yayi parking, ba tare da ya kalleta ba yace "I will be right back" daga haka ya fita ya fara tafiya, tafiyarsa kadai ma abun kallo ne, ya wuce gidaje kusan hudu kafin ya xo na su, Mahaifiyarsa Mami ce xaune parlor da wata bakuwa da tayi, ya karasa ya gaishesu da ladabi, bakuwar ta amsa da fara'a tace "Wannan uban gashin da aka bari fa Barrister, sai kace a turai" Ya kirkiri murmushi yace "Sunna ce...." Katsesa Maminsa tayi fuska daure tace "A hakan da ka bar shi irin na wa ends basu da mafadi, am very serious kada ka shigo min gida anjima baka asks gashin nan ba, ka jira idan ka koma UK din sai ka kara barin gashin, wnn iskancin kam ba a gidana ba" kansa a kasa yace "Toh Mami" daga haka ya mike ya wuce bedroom dinsa, press ya bude ya fiddo wani makulli ya sa aljihu sannan ya fito yayi masu sallama ya fita, bacci ya tadda khadijah ke yi, dauke idonsa kanta yyi ya tada motar ya bar layin, tafiyar wani minti sha biyar din yyi ya isa wani anguwar daban yyi parking a gaban wani gida, ana ganin gidan ansan sabon gini ne, ya fita ya bude gate din gidan da makulli sannan ya dawo ya ja motar ciki yyi parking ya fita ya koma ya rufe gate din, tuni khadijah ta bude ido tana bin gidan da kallo, dawowa yyi yace "Come down" ba musu ta fito, tafiya ya fara yi xuwa entrance din main house din ganin haka ta bi bayansa sai dai gabanta faduwa yake kawai, ya sa makulli ya bude kofar shiga parlorn ya shiga, kasa shiga tayi tana lekan parlorn, ya juyo yana kallonta, hawaye ne cike idonta, wani kallo yyi mata ya shiga parlorn ya bar wajen, a hankali ta taka ta bi bayansa, tuni ya wuce bedroom ita kuma ta xauna nan kan kujera a parlorn, bayan wani lkci ya fito yace "Ki shiga ciki kiyi wanka, xan fita in dawo yanxu" daga haka ya fita ya rufe kofar, tashi tayi da kyar ta shiga dakin da ya fito, towel ta gani kan gado sai sabulu ta karasa ta dauke su ta bude kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga taga har ya hada mata ruwa me dumi, wanke bakin ta ta fara yi da mouth wash, bayan kusan minti ashirin ta fito daga bayin da kayan da ta cire a bucket ta wanke, sai taji ta samu karfi jikinta, hijab kadai ne da bata wanke ba ta daura kan towel din jikinta sannan ta fito parlor, wani kofar dake parlor ta shiga taga kitchen ne, ta dauko sweeper da mop ganin gidan is very dusty, tun daga dakin da tayi wanka ta fara gyaran ta fito har parlor duk da sanyin da take ji sosai, tana goge goge a durkushe ya shigo parlorn ya ajiye ledojin hannusa ba tare da ya kalleta ba yace "I didn't tell you to do anything madam, ga kaya nan ki shiga ciki ki canxa ki fito yanxu" ta mike tsaye tace "Toh nagode" bai tanka ta ba ta dau ledan ta shiga dakin, dogayen riguna ne na kanti da undies sai Hijab biyu da perfumes, cikin lkci kankani ta gama shiryawa ta fito parlorn, xaune yake ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yayi nisa tunanin da yake, why is he involving him self in such case ya fa san daga irin gidan da ya fito ya san waye iyayensa, jin ta fito tun da ya kalleta sau da ya bai sake kallonta ba har ta iso nesa da shi ta durkusa tace "Na sa kayan" ledan abinci ya nuna mata yace "Breakfast" ta mike ta isa gun ledan ta bude, a hankali ta ja baya tana rike numfashinta sbda aroma din abinci, Fried Irish ne da soyayyen kwai da plantain sai ketchup, yace "You can go to the kitchen and make a cup of tea for ur self" kai kawai ta gyada masa, ta mike ta shiga kitchen din tana fatan ta iya shan shayin, ta gama hadowa ta fito, ganin kallonta yake bayan ta ajiye shayin ta dau Irish daya a hankali ta kai ba ki, ji tayi cikinta ya fara hautsinewa tun kafin ta fara taunawa, ta dau shayin ta kai baki da sauri don ta kora, tana sha tayi saurin ajiye cup din da sauri ta shige dakin da tayi wanka tun kafin ta karasa cikin bathroom din aman ya xubo mata, tun da ta fara amai sai yau tayi Wanda ya galabaitar da ita don bbu komai cikina, ta kasa motsi wajen duk jikinta ya mutu, ganin shadow dinsa ta juyo hawaye kwance fuskarta, tausayi karara ta gani a kwayar idonsa, yyi saurin dauke kai murya can kasa yace "Sorry" daga haka ya shiga bayin ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya xuba ruwa wajen, kasa tashi tayi ta jingina da bango, ganin jira yake ta tashi, ta runtse ido tayi karfin halin tashi bata xarce ko ina ba sai kan gado ta fada kai tana mayar da numfashi, ya karaso yace "Toh me xa ki ci yanxu" kai kawai ta iya girgixa masa, yyi jim yana kallonta kafin ya juya ya fita a koma parlor, xaunawa yyi yana tunanin how many hours will take them to kaduna. Tashi sudais yyi daga karshe ya koma daki, ganin yanda ta dukunkune waje daya ya isa gadon a hankali yace "Are you cold" bata amsa ba don idonta a rufe suke, ya dauko duvet ya rufe ta da shi, murya can kasa tace " thank you" ya tsaya yana kallonta don har sannan bata bude idon ba, juyawa yyi ya fita ya bar dakin ya tafi balcony ya xauna ya tsura ma motarsa dake parking space ido, tsoronsa daya mami hakan kuma yasa har lkcn xuciyarsa ke contemplating kan Khadijah, but is he that heartless after all, mikewa yyi daga karshe tunawa da yyi ko wanka bai yi ba gashi an kusa azahar, har ya kusa motarsa sai kuma ya tsaya, but can he go and leave her all alone here, bayan kusan minti biyu ya shiga gidan ya wuce bedroom ya ganta a kasa tana kakarin amai, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, ta fashe da kuka tana mai da numfashi, wayarsa ya fiddo a aljihunsa ya fita, bayan kusan minti sha biyar ya dawo dakin Yusuf na biye da shi a baya, bude ido tayi a hankali daga kwancen da take a kasa, Jin hannu a forehead dinta taga Dr Yusuf tsaye kanta sudais na daga gefensa, Dr Yusuf yace "Sorry, ya kike jin jikin ki..." Bata iya tace komai ba don ji tayi bakinta ya mata nauyi, yace "Me kike son ci yanxu?" Ta girgixa masa kai a hankali, ya kalli Sudais dake rungume da hannunsa yace "Try making a cup of tea with just milo for her pls" Sudais ya juya ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da cup din warm milo, Yusuf ne ya dinga forcing dinta ta shan tea din, cikin rawar murya hawaye na sakko mata tace "Wllh xai sa ni amai" Yusuf yace "Kadan xa ki sha" da ta kurbi kadan xata ajiye ta koma ta kwanta Yusuf xai hanata, sai da tayi rabin cup din sannan ya kyaleta ta ajiye ta kwanta tana sauke ajiyar xuciya, bata san sanda karfi ya xo mata ba lkci daya ta tashi duk sai da ta kwarare shayin nan kasan tiles, Sudais dake tsaye ya juya a hankali, can ya sake juyowa, ganin yanda Yusuf ya tsaya kallonta ya duka yace "Tashi ki je bayi ki wanke bakin ki" dafa gado tayi ta mike tana ganin jiri ta shiga bayin, Sudais ya shiga gyara gun aman, komawa gefen gado Yusuf yyi ya xauna ya shiga hada drips da injections, kwanciya tayi bayan ta fito, sai da yyi mata alluran sannan ya sa mata ruwan drip din, tsabar xaxxabi bata ji xafin syringe ba a lkcn, ya lulluba ta da bargo suka fita shi da Sudais dake ta tsaye. Khadijah bata san irin baccin da tayi ba ta dai bude ido taga dim light ne a dakin alamar wai dare yyi ta kalli drip din hannunta taga kamar sabo ne, cike da karfin hali ta mike xaune, ta fi minti goma xaune aka bude kofar dakin, Sudais ya shigo ya kunna wuta yana kallonta yace "Kin tashi?" Kai ta gyada masa, ya karaso yace "How are you feeling now?" A hankali tace "Da sauki" Yace "what did you want to eat?" Murya can kasa tace "Sallah xanyi" yace "Sallah?" Ta gyada masa kai, ya kalli ruwan hannunta, karasowa yyi ya cire mata tube din jikin alluran yace "But be careful kar ruwa ya shiga ciki" ta gyada masa kai, kasa mikewa tsaye tayi da farko don gani take xata iya faduwa, yace "Baxa ki iya ba?" Da kyar ta mike cike da karfin hali ta shiga bayin, ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito, taga har ya shimfida mata darduma ya ajiye mata hijab ya fita, tun tana sllhn a tsaye har ta kasa ta fara yi a xaune, sai bayan da ta idar ya shigo dakin yana tsaye daga bakin kofa yace "Me xa ki ci?" Tayi shiru don a lkcn bbu abinda ke ranta bnda danwaken da Kyauta ta taba yi ranan a can gidan, ganin taki cewa komai ya karaso yace "Ki fadi abinda kike so xan je in siyo ynxu" ta kallesa kafin ta sauke idonta a hankali, yace "What did you want" murya can kasa tace "Danwake, amma tunda dare yyi kawai ka bar sa" tsaye yyi na d'an lkci kafin ya juya bai ce komai ba ya nufi kofa, har ya bude kofar xai fita ya juyo yace "But.... I don't knw ur name" tana kallonsa a hankali tace "Khadijah...." Ganin yanda yake kallonta tace "Khadijah Muhammad" ya gyada kai yace "I will call you... Iman.... Cos you have the name of My mum" daga haka ya fita, ji gayi komai ya tsaya mata a lkcn, taji kamar ya fama mata wani ciwo ne a xuciyarta, har ya dawo kuma bata daina kukan da take ba kamar ranta xae fita, lkci daya hankalinsa ya tashi bayan ya ajiye warmer din danwaken, da damuwa yace "Me ya faru, why r u crying" cikin rawar murya tace "Don't call me Iman plss don't bana so" da mugun mamaki yake kallonta, can a hankali yace "Ohk I won't" daga haka ya bude warmer din ya xuba mata danwaken a plate yana kallonta yace "Manja ko Man gyada?" Tayi shiru tana goge hawayen idonta, can a hankali tace "Man gyada" xuba mata yyi kadan, ya ajiye abincin da yajinsa a gabanta, bata iya ta ci da yajin ba, haka ta dinga ci gaya ko maggi bbu, gani take idan ta sa yajin xata yi amai, ba laifi ta ci me yawa, amma ta kasa shan ruwan da ya kawo mata, shi dai yana ta tsaye dakin yana danna waya lkci lkci yana kallonta, ganin bata sha ruwan ba yace "Why didn't you drink d water" a hankali tace "amai, amma kila idan na sha mai xafi baxan yi ba," wani kallo ya fara yi mata kafin ya tabe baki ya fita, ba a dau lkci ba ya dawo da ruwan dumi, cikin ikon Allah kuma bata yi aman ba da ta sha, sai da ya sa ta wanke baki snn ya maida mata drip din, tana kallonsa bata san lkcn da tace "Are you a doctor?" ya girgixa kai ba tare da ya kalleta ba yace "I am nt, but a lot of my frnds are" Komawa baya yyi bayan ya gama yace "Did you need anything, I mean anything?" Ta girgixa masa kai, xai yi magana wayarsa ta fara ring, ya dauka yana kallon screen din da sauri, gefen gado ya koma ya xauna ya daga ya kai kunne a hankali yace "Mami am on my way now, na tsaya yin wani abu ne, but nan da few minutes xan iso, Ki yi hakuri...." Sai bayan da ya mayar da wayar aljihu yace "Am going home now, anjima kadan Yusuf xai turo nurse da xa ta tsaya dake, she's on her way now" a hankali Khadijah tace "Toh na gode" yace "No thanks" daga haka ya fita ya rufo mata kofar. Ko minti sha biyar bai yi da fita ba aka bude kofar dakin wata mata da baxata wuce 30 ba ta shigo dakin, ta karaso kusa da khadijah tace "Sannu ya jikin ki" ta gaisheta don ta gane ta tace da sauki, nurse din tace "Ba kya bukatar komai koh?" Khadijah ta gyada mata kai, tace "Toh ki kwanta kiyi bacci, Allah ya kara lfya" ba musu ta koma ta kwanta, nurse din ta juya ta fita, duk khadijah ta bude ido cikin dare sai ta ganta coincidentally ta shigo duba ruwan dake makale hannunta, duk da drip din kuma hakan bai hanata dinga jin xaxxabi sosai ba, sai kusan asuba ta cire mata drip din bayan ya kare, ta samu da kyar ta shiga bathroom, baki ta wanke tayi wanka ta dauro alwala ta fito, duk yanda ta so yin sllh a tsaye kasawa tayi don jiri ne ke dibanta sosai ga rawan sanyi da take, daga karshe tayi a xaune ta kwanta nan kan darduma, ji tayi ana tada ta ta bude ido da kyar taga nurse din ce, tace "Kin yi wanka ne?" Khadijah ta gyada mata kai, nurse din tace "Da ruwan sanyi?" Girgixa mata kai khadijah tayi tace "Akwai ruwan xafi a heater" nurse din tace "To tashi ki koma kan gado" da taimakonta khadijah ta koma kan gadon ta kwanta ta lullubeta ta fita. Takwas saura taji hannu forehead dinta ta bude ido da sauri, Dr Yusuf ta gani tsaye kanta yace "How are you feeling?" Ta tashi xaune tana gyara hijab dinta tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau, ya jikin?" Ta sunkuyar da kai tace "Da sauki" ya kalli nurse din yace "She is having a running temperature" nurse din tace "Eh tun da tayi wanka da asuba" ya kalli khadijah yace "Da ruwan sanyi kika yi wankan?" Ta girgixa masa kai, ya kalli nurse din yace "Je ki bude mota akwai drips da injections da na taho da su daga clinic" tace "Ohk sir" daga haka ta fita, d'aga kai khadijah tayi taga kallonta yake, ya dauke idonsa yana girgixa kai ya nufi window ya dage curtains din yana kallon waje, bude kofa aka yi Sudais ya shigo da sallama, kananun kaya ne jikinsa lkci daya kamshin turarensa ya cika ko ina na dakin, a hankali cikin dubara ta toshe hancinta, Tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya nufi gun Dr Yusuf, bayan sun gaisa Yusuf yace "Ya su Mami" Sudais yace "They r ol fyn, amma daga clinic kake" Yusuf ya girgixa kai yace "No, yanxu dai xan je clinic din" Sudais yace "ohk how is she feeling now" kafin Yusuf yace komai ya nufo ta yana kallonta yace "Kin tashi lafiya?" Khadijah da har lkcn ta rufe hancinta tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau, why are you uncomfortable" ta girgixa kai a hankali tana yamutse fuska tace "The perfume" kallon Yusuf yyi ya tabe baki, Nurse ta shigo da abinda Yusuf ya aiketa ta dauko, gaida sudais tayi ya amsa duk da sun gaisa a waje, Sudais ya maida dubansa kan Khadijah yace "Toh me xa ki ci" girgixa masa kai tayi tace "Bana jin yunwa yanxu" Yace "But you need to take something" shayi yasa Nurse ta hado mata mara xafi, ganin Cup din shayin kadai ya dinga tada mata xuciya har da hawayenta, hankali tashe tace "I said am nt hungry plss" Yusuf dai na tsaye kusa da window yana kallon su, Sudais ya karbi shayin ya hade rai ya mika mata yace "Collect it now, ina ruwan wani da rashin jin yunwar ki" Karba tayi ta runtse ido ta rike breath dinta ta kai baki amma ta ki sha, can ta bude ido a hankali tana kallon sa kamar xata yi kuka, taga yanda ya hade rai yana kallonta, kauda fuskarta tayi tace "Don Allah kayi hakuri Allah baxan iya sha ba amai xan yi" yace "Sha kiyi aman" bata ce komai ba kuma bata sha ba, ta kalli Yussuf taga ya rungume hannu yana kallon su kawai, Nurse din tace "Ki daure ki sha kin ji yan mata" runtse ido ta kara yi bata ce mata komai ba, wani tsawa da ya tsorata ta Sudais ya mata yace "Wa kike tunanin xaki dinga ba wahala" bata san lkcn da ta kai shayin baki ba ta kurba, sauka tayi daga kan gadon da sauri jin amai ya taho mata nurse din tayi saurin karban Cup din hannunta ta ajiye, ta shiga bayi tana amai, ita ta taimaka mata ta gyara jikinta ta cire mata hijab ta wanke gun sannan suka fito tana rike da hannunta, bin su Sudais yyi da kallo har ta xaunar da khadijah gefen gado ta kwanta tana maida numfashi, Shi dai Yusuf har lkcn bai ce komai ba, ya karasa gun da nurse din ta ajiye ruwan drip din ya dauka ya fara hadawa, ita ya bar ma ta sa mata sannan ya kalli Sudais yace "Barrister.... I will be on my way now" Sudais ya bi bayansa suka fita. Xa a iya cewa kusan a gidan Sudais ya wuni ranan don da ya fita xai dawo, Nurse din kuma karfe sha biyu ta wuce, duk shigowar da xai yi daki kuma sai Khadijah ta farka daga baccin da take, wani lkcn ya mata sannu, wani lkcn kuma kawai ya juya ya fita. Tun bayan awaran da ta sa ya siyo mata ta samu ta ci kadan bata sake yarda ta ci komai ba don shi dinma damunta yake tayi gashi ta kasa yin aman, Karfe shidda saura ta bude ido jin budewar kofar, shi da Yusuf suka shigo, Yusuf ya mata ya jiki, ta gaishesa, Sudais na kallonta yace "I think Gobe xa mu je can Kaduna..." Sai a snn ta kallesa hnkli tace "Toh" Yusuf yace "Why nt ka bari ta fara samun Lafiya, she's so sick" Sudais ya nufi kofa yace "Noo, she's leaving tomorrow, for how long am I going to keep her here?" sai kuma ya juyo yace "Or is she going to stay here for ever? You knw presently I will be bringing a woman in here...." Daga haka ya fita, Yusuf ya bi sa da ido, can ya kalle Khadijah yace "What's ur name?" A hankali tace "Khadijah" yace "Khadijah are you sure you are nt lying about ur self" hawaye ne ya cika idonta tana girgixa masa kai tace "To God who made me, I didnt lie." Yau din ma nurse din ce ta kwana gidan tare da Khadijah, karfe bakwai da yan mintuna na safe sudais ya shigo gidan, parlor ya xauna bayan ya ajiye flask din hannunsa suka gaisa da nurse din yace "Don Allah ki sa ta shirya anytime soon xa mu kama hanya..." Ruwan xafi nurse din ta sa ma khadijah tayi wanka, ta fito bayan ta yi wankan tana rawan sanyi, nurse din ta ajiye mata daya daga kayan da sudais ya siyo mata dake cikin leda da lotion sannan ta fita, da kyar khadijah ta daure ta tashi ta shirya ta sa Hijab, sai sannan nurse din ta dawo tana kallonta tace "Ki fito yana jiran ki" daga haka ta fita khadijah ta mike a hankali ta bi bayanta, cup din kunun da sudais ya sa aka siyo mata nurse din ta dauka ta bata, amsa tayi tana kallon cikin cup din, can ta dago a hankali ta kalli sudais dake kallonta ta sauke idonta tace "Ina kwana?" Yace "How you feeling?" Ta gyada kai tace "Da sauki." A hankali ta fara shan kunun tana tsoron kar tayi amai, cikin ikon Allah bata ji Aman ba, ta ajiye kusan Rabin cup tace ya isheta, mikewa yyi yace "Ina jiran ku a waje, you help me lock d door pls ga makulli a jiki" ya fadi hakan yana kallon nurse sannan ya juya ya fita, Khadijah ta bi sa da ido yana sanye cikin bakar suit da wando sai farar T-shirt da necktie banda kyalli bbu abinda cover shoe din kafarsa ke yi, nurse din ta kai flask da kunun cup din kitchen sannan ta fito tana kallon khadijah tace "Toh tashi muje" dafa kujera tayi ta mike nurse din na gaba ta bi bayanta har suka fita nurse din ta rufe kofar da makulli ta cire sannan ta tafi gun motarsa Khadijah na bin ta. Yana daga cikin motar ta mika masa ya karba yace "Shigo in rage maki hanya madam" nurse din tace "Toh" ita ta shiga gaban motar khadijah ta shiga baya, sai bayan sun fita gidan ya fito daga motar ya rufe gidan sannan ya koma ya ja motar suka bar layin, dai dai wani junction nurse din ta sauka tana masa godiya, kudin mota ta bata sannan ya ci gaba da tukinsa. Tun da suka fara tafiya khadijah ke jin xuciyarta ke tashi duk ta xama restless, yana lura da ita ta madubi bai dai ce komai ba, bayan wani lkci tace "Amai nake ji plss" yana kallonta ta madubi yace "Amai??" Toshe bakin ta yyi da hannunta da sauri, ya gangara gefen titi ta bude motar da sauri ta sauka ta dinga kwarara amai bakin hanyan, fitowa yyi ya tsaya jikin mota ya rungume hannu yana kallonta, ta gama Aman tana maida numfashi da kyar, bude front seat yyi ya dauko table water ya mika mata ta karba ta wanke bakin ta da fuskarta sannan ta mike kanta a kasa, ya nuna mata front seat yace "Shiga" a hankali ta karasa ta shiga ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga, kasa yyi mata da kujerar ya ci gaba da driving dinsa. Har suka yi nisa sosai a tafiyar bacci take, sudais dake kallonta lkci lkci ya gangara gefen titi yyi parking, suit din jikinsa ya cire ya rufa mata ganin sanyi take ji duk da bai kunna ac ba, ta bude ido a hankali tana kallonsa, ya ci gaba da driving dinsa. Sai da suka shigo traffic a kano ta farka, ya kalleta yace "Xa ki ci wani abu ne?" Da sauri ta girgixa masa kai, yace "Ko xa ki ci apple?" Shiru tayi tana kallon mai hawking apple dake tsaye gefen glass dinsa, ya dau suit dake jikinta ya cire kudi sannan ya mayar ya rufa mata ya sauke glass ya siya apples guda shidda ya ajiye kusa da ita, daya ta dauka ta kai baki a hankali gabanta na faduwa, taji bakin ta ba dadi ta dinga taunan Apple din a hankali tana tsoron kar ta ji amai, har ta ci rabi bata ji aman ba kafin su bar kano har ta cinye biyu daga nan kuma bacci ya dauketa. Khadijah bata sake farkawa ba sai da suka shigo garin kaduna kusan karfe uku, ganin ta tashi yace "Wani anguwa ne gidansu Aliyun yake?" A hankali tace "GRA" bai ce komai ba ya dinga driving a hankali sbda traffic, cikin minti ashirin suka shigo Gra, khadijah ta dinga yi masa kwatance har suka iso dai dai kofar gidansu Aliyu Sudais ya juya yana kallonta. ✨ *NOOR-AL-HAYAT* ✨ Bude motar Sudais yyi ya fita yana kallonta yace "Come down" a hankali ta fito gabanta na faduwa, ya nufi gate din gidan ta bi bayansa kamar me tausayin kasa, da farko Usman mai gadi ya tsaya tambayarsa wanda yake nema amma ganin khadijah ya fito da sauri yana kallonta da mamaki yace "Khadijah?" Ta kirkiri murmushi ta gaishesa, tuni Sudais ya shiga gidan, Khadijah ta bi bayansa Usman yace "Duk kika daga ma kowa hankali ana ta neman ki har station Hajiya ta kai report, to Alhmdllh tunda Allah ya bayyana ki, Alhmdllh" ita dai Khadijah bata ce komai ba ta kalli parking space xuciyarta na bugawa ta ga ba motar Aliyu da na Mumy, Sudais ya danna bell din entrance na gidan a hankali, sau uku yana danna bell din kafin a bude kofar, Anty khadijah ce tsaye bakin kofar kana ganinta kasan bacci take, idanuwanta suka bude sosai ganin khadijah dake gefen Sudais a tsaye tsoro dauke fuskarta, Sudais da yana ganin ta yyi guessing ita ce Anty khadijah ganin kallon da take ma khadijah yace "Assalamu alaikum" hade rai Anty khadijah tayi tace "Wa'alaikumus salam" daga haka ta kalli khadijah tace "Lafiya? Daga ina? Wa ku ke nema?" Sudais yace "Aliyu muke nema" daga haka ya shiga parlorn, Khadijah ta kasa shiga saboda tsoro, Wani kallo Sudais yyi mata yace "Come in" a hankali ta daga kafa ta bi gefen Anty khadijah ta shiga cikin parlorn ita ma, tuni Sudais ya isa kan kujera ya xauna, Anty khadijah dake kallonsa da mamaki tace "Malam nan din fa gidan matan aure ne ka shigo, lafiya? wa kake nema?" Yace "Shi yasa nayi sallama kuma kika amsa min kafin in shigo hajiya" Anty khadijah tace "Me kuma ya hada ku da Aliyu ku ke neman sa?" Sudais yace "Xai fi kyau idan ma bai nan ki yi hakuri ki kira mana shi ya dawo, and mahaifiyarsa hope tana nan?" Anty khadijah tayi mitsi mitsi da ido cike da masifa tace "Nima uwarsa ce ae halak malak, sannan Aliyu bai ma kasar gaba daya idan xaka fadi abinda ke tafe da kai malam ka fada don bacci nake ka taso ni..." Shiru Sudais yyi na d'an lkci kafin ya nuna mata khadijah yace "Kin san wannan yarinyar koh?" Ta kalli khadijah ta kara tsuke fuska tamau tace "Kwarai kuwa, yar aikin da muka dauka kwanaki kenan ta lalata mana xumunci ta shisshige ma d'a na, ta raba ni da shi ina ji ina ganin bana iya cewa komai, wannan shari'ar kuma sai a lahira don duk da barin ta gidan har yau abubuwan da ta cakuda bai gyaru ba, Allah ya isa tsakaninmu da ita" Kuka Khadijah ta fara yi a hankali ta durkusa inda take tsaye, Sudais ya ciro handkerchief dinsa ya share fuskarsa yana kallon khadijah yace "Dena wannan kukan xa kiyi ki bude baki da kanki kiyi mata bayani yanxu" Anty khadijah ta dawo tsakiyar parlorn da sauri tana xaro ido tace "Bayanin me?" Khadijah ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata, kare mata kallo Anty khadijah ta shiga yi, can ta fashe da dariya irin na mugunta lkci daya kuma ta tsayar da dariyar tana ma Sudais wani matsiyacin kallo tace "Xuwa kayi da ita tace mana tana dauke da ciki?" Sudais yace "Alhmdllh fine, unfortunately kin ma san halin d'an naki kenan" Khadijah ta hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Anty khadijah ta fashe da wani shegen dariya kamar bokanniya tayi mai isarta tayi shiru sannan ta nuna masa kofa fuskarta kamar bata taba dariya ba idonta yyi mitsi mitsi tace "Tun muna mu uku a nan bamu fi haka ba ku tashi ku fice mana a gida" a tsawace ta kare maganar, sudais ya tabe baki yace "Tsawar ki ko ihun ki fa baxae razana ni ba malama... Don haka hold it xai maki amfani gaba a wani wajen" Anty khadijah na huci tace "Xan nuna maka a nan ma yana da amfani, har wannan karuwar xata xo ta makala ma d'ana cikin shegen da tayi a wani wajen saboda ita matsiyaciya ce" Sudais yace "Toh abu mai sauki sai mu je asibiti a ga kwanakin cikin nawa, idan yyi dai dai da kwankin da ya koreta ta bar gidan to nasa ne in sha Allah" Anty khadijah tayi shiru jin abinda sudais yace, auuuu wato Aliyun ne ma ya koreta ashe, ita dai ta dawo kauyen da taje bayan kwana biyu da tafiyarta taji wai ba a ga khadijah ba ko sama ko kasa har station an kai report, Ranta yyi mugun baci a lkcn don bata so Khadijah ta tafi haka nan bata walakanta ta ba kmr yanda ta yi alkawari, me yasa xata tafi bata gama cika burin ta a kan ta ba har hawaye sai da tayi sbda bakin cikin kudin mota da kudin magani da tayi asara, suree a lkcn tayi mugun mamakin yanda Aliyu bai wani damu can ba kamar yanda mahaifiyarsa da baby suka damu amma ita bata taba kawo cewar shi ne ma ya koreta ba, Muryar Sudais ya dawo da Anty khadijah "Hajiya kin yi shiru daga nayi xancen asibiti" abinda ya fada kenan yana kallonta, ta yi masa wani shegen kallo tace "Ji gantalalle, to tunanin da nake daban malam, kuma asibitin ya ci kaza kazan sa baxa a je ba, idan ma cikin Aliyu take dauke da, idan ma ba nasa ba... bbu wanda ya isa ya shigo mana da shege cikin xuri'ar mu, I can swear with the Qur'an fasikanci ba halin Aliyu bane idan ma yyi Ita ta koya masa don kullum dakin sa take yini, wa ya sani ma ko har kwana tana yi can, yayata ba mai xama bace don yanxu xancen da nake ma bata kasar, kullum nice ke tare da su, wai hanata shige ma Aliyu da nake har shi ya janyo min bakin jini gun ta, ta janyo d'a na ya daina ganina da gashi a gidan, yanxu tun muna magana irin ta mutane ba mu dawo na mahaukata ba ku tashi ku fice min a gida kar ku ga d other side of me, ku fita nace" a tsawace ta kare maganar, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace "Toh cikin nasa dake jikinta tayi ya da shi kenan?" a takaice Anty khadijah tace "Ta xubar, don kaf xuri'ar mu ba shege kuma baxa a fara a kan d'a na ba, idan kuma taga xata iya sai ta raini cikin ta haifa ma kanta ajalinta...." Khadijah dai banda kuka babu abinda take, Sudais ya mike yace "Good, I made her brought me here for just 2 reasons, na farko... is to find out how sincere she is, and na karshe... Is just to let you and ur son knw d pains u are about putting the innocent orphan coz ni dai nasan definitely baxa ku taba accepting cikin ba, kun rabata da warce take da ita a duniya, kun goga mata bakin fenti da ba lallai ya gogu ba har karshen rayuwarta, amma Hajiya ina son ku sani, kamar yanda marainiyar nan tayi bankwana da farin ciki to wallahil azeem kuma hakan ne xai same ku a a xuri'ar ku barin shi Aliyun, He will know no peace da hakkin marainiya a kansa, who knows tunda tace likita ne shi signs na pregnancy din ya gani ya koreta, in sha Allahu sai kun yi da kun sanin abinda ku ka aikata ma yarinyar nan" yana kai wa nan ya karasa gabanta ya ciro ID card a gaban rigarsa ya nuna mata yace "Barrister Aliyu Umar, or just sudais.. we might meet some other time in sha Allah.... Or probably not" ya fadi hakan yana gesturing da hannunsa, khadijah da gabanta yayi mugun faduwa ta dago da sauri tana kallonsa wasu hawayen masu xafi na xubo mata, wani dariya Anty khadijah tayi tana tafe hannu tace "Are you threatening us?" Ya girgixa kai yana murmushi yace "Noo, not at all, kilan idan kika gaya masa aika aikan da yyi xai iya biyota, here is my complimentary card..." Ya ajiye card din gefen kujera, dauka tayi ta yayyage ta xubar nan kasa a gabansa tana huci tana kallonsa, yayi murmushi ya kalli khadijah yace "Tashi mu je" khadijah ta mike a hankali ta bi bayan sudais da har ya isa kofa, tana goge hawayen ta har ta iso gun motarsa, shi ya bude mata motar ta shiga ya rufe ya xaga ya shiga maxaunin driver, har suka hau titi bai ce komai ba ta hade kai da gwiwa tana rera kuka ko xata ji saukin tukukin da xuciyarta ke mata, A bakin hanya sudais yyi parking ganin masallaci ya fita don yin sllh da bottle water ya dawo motar, bayan ya sha ruwan ya ci gaba da driving dinsa, ya hade rai yace "Will you stop those tears and start thinking of how to face reality" ba shiri tayi shiru tana shessheka ya ci gaba da tukin sa. Dab da isha suka shigo kano, direct ya nufi hotel bayan yyi parking yace "Gobe da safe xa mu je gidan Step mum dinki" a tsorace take kallonsa, ya bude motar ya fita yace "Ki fito" daga haka ya wuce reception, daki biyu ya amsar masu, ya siya masu abinci a nan reception din sannan suka wuce sama, yana tsaye daga bakin kofar dakin da ya bude mata ta shiga na hotel din yace "Make sure you try and pray, ki daure ki ci abinci kiyi wanka sannan ki kwanta" spare ki ya cire yace "Don't leave the key jikin kofar" daga haka ya juya ya shiga nasa dakin, wanka kawai yyi, yyi sallah abincin ma bai iya ya ci da yawa ba ya kira mami, bayan sun gaisa ta tambayesa ya hanya, yace "Alhmdllh mami gobe xan dawo in sha Allah" tace "Toh maa sha Allah, in ji anyi nasara" yace "In sha Allah mami" tace "Toh Alhmdllh" a hankali yace "Am very tired mami xan kwanta" tace "Toh Allah huta gajiya" yace "Ameen" daga haka ya kwanta nan da nan bacci me nauyi ya daukesa, bai farka ba sai karfe uku, mikewa yyi xaune da sauri ya dau shirt dinsa ya sa ya dau spare key dinta da ya cire ya fita dakin ya nufi nata, saka makullin yyi ciki yana addu'ar Allah yasa ta cire makulli jikin kofar, yana murdawa ya bude ya tura kofar dakin, xaune ya ganta ta jinginar da kanta jikin gado, ya karasa da sauri ya durkusa gabanta yace "Kin samu kin ci abincin kuwa Amira?" Shiru yyi yana kallonta ganin yanda idonta ya kumbura, ya sauke idonsa kan ledan abincin da ya ajiye mata jiya da daddare, bude ledan yyi yaga bata taba abincin ba, ya wani hade rai yace "What's wrong with you, tun dare kike kuka har yanxu?" Ta girgixa masa kai da sauri muryarta na rawa ta nuna masa kirjinta tace "Yana min ciwo" sauke ajiyar xuciya yyi murya can kasa yace "Kin yi wankan?" Ta girgixa masa kai, yace "Sallah fah?" Nan ma girgixa masa kai tayi, mikewa yyi ya shiga bathroom da ke dakin ya hada mata ruwan wanka ya fito yace "Tashi ki je ki yi wanka, you will feel more better" a hankali ta tashi ta wuce bathroom din, yana ta xaune har ta fito da kayan ta da Hijab ta kwanta kan gado ta dukunkune waje daya, ya mike ya rufa mata bargo, ba a dau lkci ba ya ga alamar bacci ya dauketa, tashi yyi ya kashe wutan dakin ya nufi kofa ya fita ya rufe. Da asuba bayan sudais ya idar da sllh ya koma dakinta yaga har lkcn bacci take ya koma dakinsa shi ma ya kwanta. Da safe ya fita hotel din don nema mata kunu, wani almajiri da ya gani kan hanya ya ba kudin ya tafi gun masu siyar da kosai ya siyo masa kunu, yana ta jiransa gaban wani store har yaron ya dawo da kunun a cikin leda, karba yyi yyi masa godiya ya bar masa canjin dari takwas din don na Dari biyu yaron ya siya, ya mike ya amshi ruwa bakin store din da yake ya dawo kan bench ya xauna ya bude bottle water din ya sha kadan ya xubda sauran sannan ya juye kunun ledan a ciki ya mike ya koma hotel din, tashinta yyi daga baccin da take ganin tun jiya bbu abinda ta ci, ta tafi bayi ta kuskure bakinta kamar yanda ya ce mata, da alwala ta fito yana ta xaune yana jiran ta gama sallah, duk ta galabaita kafin ta idar, ya dawo kusa da ita ya mika mata bottle din kunun bayan ya bude yace "Gashi ki sha ko ba yawa kin ji" kai ta gyada masa ta karba ta kai baki a hankali har wani rawa hannunta yake, kusan rabi ta sha kunun ta ajiye ta jinginar da kanta da gado, yace "Ki daure ki kara kadan" ta girgixa kai da sauri tace "A'a xan yi amai idan na sha kuma" rufewa yyi yace "Toh ki kwanta kafin in yi wanka xa mu je can gidan step mum dinki" shiru ta yi ta bi sa da kallo har ya fita dakin, da yake ba ya rabo da spare clothes a motarsa can ya tafi ya dauko kayansa yana gama wanka ya canxa. Ko da ya dawo dakin idon Khadijah a lumshe yake duk da ba bacci take ba, tausayin kanta kawai take don bata san wani irin rayuwa xata fara yanxu ba kuma, ita da ba kowa gareta ba a duniyar, muryarsa da taji ya sa ta bude ido da sauri don bata ji shigowar sa ba, ta mike xaune yace "Let go, it's almost nine yanxu" tashi tayi ta sauka daga kan gadon, ya dau ledan abincin jiya da bata ci ba ya fita tana biye da shi a baya, nan reception ya bada makullan dakin ya nufi wajen hotel din xuwa Parking lot, ya bude mata front seat ta shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da ya hau kan titi yace "Ina ne gidan step mum din naki yake?" Kamar xata yi kuka tace "Wllh tsoro nake ji kuma tace kar in kashe mata aure, I don't want to be the cause of that" yana kallon titin gabansa yace "Kar ki damu you will remain inside the car, while we talk" kai ta gyada masa a hankali hawayen dake makale idonta ya sakko, yace "Clean those tears now" da sauri ta goge idonta, tana ta nuna masa hanyar gidan bayan sun shigo anguwar, ganin sun kusa a hankali tace "Plss ka tsaya da motar a nan kaga gidan can" ya tsayar da motar ya na kallon gidan da take nuna masa, kashe motar yyi yace "Ya sunan step mum din ki?" Tace "Hajiya Amina" bude side dinsa yayi ya fita, ta bi sa da kallo ganin yanda yake tafiya har ya isa kofar gidan ya tsaya, wani yaro ne ya fito gidan dake kusa da gidan ya kirasa, yaron ya taho sudais ya duka yana kallon yaron yace "Big boy... shiga gidan nan kace ana sallama da Hajiya Amina" yaron yace "Toh" sannan ya shige gidan da sauri, ba a dau lkci ba sai ga Shafah da Hasana sun fito ko wacce daga mai riga a kai a matsayin mayafi sai mai wando, Sudais ya dinga kallonsu daga sama har Kasa, Shafa dake ta kallon sudais tace "Sannu da xuwa bawan Allah" yace "Ina kwanan ku" a tare suka amsa masa, ya shafa lallausan gashin kansa da ke kara masa kyau yace "Dama Hajiya Amina nake son gani" a tare suka hade rai Hasana tace "Yar uwar ka ce?" Ya girgixa kai tace "Halan kudi xaka karba gunta? Toh Allah sa dai ba yawa, don kuwa Amina xamanta ya xo karshe gidan nan tun shekaranjiya don kuwa Alhaji ya saketa, yanxu haka ko tsinkenta babu a gidan" Kallonsu Sudais yake a sanyaye, Hasana tace "Atoh, ban da mugunta ki tura yar mutane karuwanci don ba ke kika haifeta ba yarinya marainiya bata da kowa duniyar nan banda Allah, dama an ce idan mutum xai gina ramin mugunta yyi ta yar karama.... To ita kam da xurfi tayi sa gashi ta afka ciki" Sudais da ko kadan bai san ma abinda suke cewa ba yyi karfin halin cewa "Toh don Allah kun san garinsu?" Shafah tace "Halan kudin da yawa, matar da har gorin cin bashi take mana ashe a boye take nata" Hasana tace "Mun dai ji kishin kishin a gari ta siyar da duk kayan dakin nata wai xata koma kasarsu, ka san 6are ce ba yar Nigeria ba" Sudais yace "Ina ne kasar ta su?" Shafah tace "Wai ko Ethiopia ko morocco ko Sudan oho dai... amma nan Africa ne, mu dai Allah ya raba mijinmu da alakakai" juyawa sudais yyi ransa a dagule ya nufi motarsa yana shiga ya hade kai da steering yana tunanin ta ina xai fara, ya xai yi da yarinyar nan da kowa ke kira da marainiya, khadijah da ke ta kuka tun bayan fitarsa cikin rawar murya tace "Ummata na fushi da ni har yanxu koh?" Dago kansa yyi yana kallonta da idanuwansa da suka sauya kala. Tada motar sudais yyi bai ce komai ba suka bar layin, ban da kuka babu abinda khadijah take har da shessheka, duk a tunaninta Umma ta ki hakura ne ta kori sudais, yana driving a hankali yace "Bana son wannan kukan da kike cika min kunne da shi plss, if you are in pain it's better you pray, plss kukan ki yana damuna da yawa" a hankali khadijah ta hadiye kukan tana share hawayenta a sanyaye, bayan wani lkci sudais yayi breaking silence din cikin motar a hankali yace "Ur step mum is gone Amira" da sauri khadijah ta kallesa xuciyarta na bugawa sosai tace "To where?" Yana ci gaba da driving dinsa yace "Dama ba Nigerian bace Ita?" Khadijah na kkrin mayar da wasu sabbin hawayen da ke taruwa idonta tace "She told me she is not a Nigerian... I don't knw her country" ya lumshe ido ya bude yace "Toh ta koma kasar su in ji Co wives dinta, since the day before yesterday ta wuce" cikin rawar Khadijah tace "Me yasa?" Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, sai dai baya son gaya mata aurenta ya lalace kamar yanda su Hasana suka gaya masa, Bayan kusan minti biyar murya can kasa yace "Look, you just have to face reality Khadijah, keep all those tears and crying aside, don't cry any longer it has no use" kai kawai take gyada masa kuka na cin ta amma bata yarda ta yi ba, nan ko shi ma hankalin sa a tashe yake kamar yanda nata yake a tashe amma yayi kokarin boye hakan yana lallashinta ita, bai san yanda xai yi da ita ba, bai san inda xai kai ta ba, bai san inda xai ajiyeta ba, bai ma san ta ina xai fara ba, tunanin hakan yasa yace "Ya Allah" bai san ya fito fili ba sai da khadijah dake ta share idonta ta kallesa, ya shafa kansa yana ci gaba da driving dinsa, Nearest filling station ya shiga domin kara Fuel kafin ya dau hanyar Damaturu, tun da suka shigo station din xuciyar khadijah ke tashi jin warin fetur, ta dai rufe fuskarta da Hijab din jikinta a hankali, Sauke glass yyi yana fadi ma mata mai siyar da man na nawa xata xuba masa, tana fara xuba man khadijah ta fara kkrin bude mota ya juya yana kallonta da mamaki yace "What?" Ganin yanda ta toshe baki yyi saurin bude lock din motar ta fita, tana fita kuwa ta shiga kwarara amai nan kasan wajen, sudais ya dafe kai a hankali a ransa yace Ai shi ya shiga uku.... Ganin wata mata ta fito daga motar dake bayan nasa yasa shima ya bude motarsa a hankali ya fito, matar ta riketa tana mata sannu kamar yanda kowa na gun ke yi mata, sudais ya xagayo ya tsaya ya ma rasa abinda xai ce, mai siyar da fuel din ta tafi gun siyar da drinks a filling station din ta karbo ruwan gora daya ta dawo matar da ke rike da khadijah ta bude ta mika mata khadijah ta karba da kyar tana wanke fuskarta da ruwan, mijin matar dake rike da khadijah ya fito shi ma yana ma khadijah sannu, matar ta kalli Sudais tace "Bari ta shiga motar sai ku wuce" barin wajen sudais yyi matar ta taimaka ma khadijah ta shiga motar sannan ta rufe, mai siyar da mai ta debo kasa tana xubawa wajen aman, Cike da karfin hali sudais yace "Toh mun gode kwarai" matar tace "Ayya ba komai, Allah ya sauwake, ya kuma raba lafiya" Sudais ya juya da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ameen mun gode" daga haka ya xaga driver seat ya kara yi ma mai siyar da mai da mutanen wajen godiya ya shiga ya tada motar suka bar filling station din, Har suka hau kan titi bai ce komai ba tunanin da yake a ransa daban, can ya saci kallonta yaga idonta a lumshe ta jinginar da kai da kujera, kwantar mata da kujerar yyi ta bude ido da sauri, sai a sannan murya can kasa yace "Sorry" Bata iya ta amsa masa ba ta mayar da idanuwanta ta rufe daga nan bacci ya dauketa. Buga kujerar motar da take kai taji ana yi cikin bacci, ta bude ido a hankali Sudais dake kallonta yace "Come down" kalle kallen inda suke ta shiga yi taga kamar gidan Sudais ne, ganin har ya fita yasa ta bude motar a hankali duk jikinta ba kwari ta fito ta bi bayansa, yana tsaye parlor yana jiranta bayan ta shigo, ya nufi wani bedroom ba wanda ta fara xama ba ya bude ya juyo yana kallonta yace "Go inside xan kawo maki bedsheet yanxu ki shimfida sai ki kwanta ki huta" daga haka ya wuce ba a dau lkci ba ya dawo da bedsheet din ya bata sannan ya fita ya kulle kofar, yanda yace tayi haka tayi ta kwanta a gajiye ga baccin da ke idonta, nan da nan bacci ya sake dauketa, sai kusan azahar ta farka da kyar ta dalilin sanyin da ta dinga ji alamar xaxxabi, cike da karfin hali ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idarwa ta jinginar da kanta da gado hawaye na sakko mata, ta dau lkci me tsayi a haka aka yi knocking kofar, da sauri ta dago kanta tana goge hawayen idona, jin an kara bugawa ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, tsaye ta gansa bakin kofar rike da leda babba da karami, bai ce komai ba ya shiga dakin ta bi bayansa, sai da ya ajiye ledan hannunsa yace "Tun daxu kike kuka kenan?" Kai ta gyada masa, yace "Good, kukan me kike?" Kamar ya dada tunxurata ta kuma fashe masa da kuka sosai ta durkushe wajen har da shessheka, cikin raunin murya tace "Ni bani da kowa yanxu, I don't knw if I have any use, i...." Ta fashe da wani matsanancin kukan, ya durkusa kusa da ita shi ma a hankali yace "Noo, you have use Amira, kar ki sake cewa baki da kowa, or don't you have trust in Allah?" Ta kallesa da sauri tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace "I do" ya d'an yi murmushi yace "Then have faith in him" ledan da ya ajiye ya nuna mata yace "Ki yi wanka ki canxa kaya, take some fruits after that sai kiyi sllh ki kwanta ki huta sosai" daga haka ya mike ya fita ya kullo mata kofar, ta fi minti goma a durkushe yanda ya bar ta daga karshe ta tashi ta bude ledan taga sabulu har da toothpaste da brush, sannan ga inners da dogayen riguna uku da hijab, duk jikinta yyi sanyi, ta mike ta shiga bathroom din ta yi wanka ta fito, Apples kadai ta iya ci cikin fruits din bayan ta gama shiryawa sannan ta kwanta lkci daya kuma bacci ya sake dauketa. Buga gefen gadon taji ana yi cikin bacci ta bude ido a hankali, ganinsa gefenta ta mike xaune da sauri, yace "Ur temperature is running high, are you feeling pain anywhere?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" yace "Ba ki yi sllh ba....." Kallon agogo tayi taga karfe bakwai ya wuce, ta kallesa da sauri tace "Dare yayi?" Yace "Yea, you slept all day ai" sunkuyar da kai tayi, yace "Me kike son ci yanxu?" Shiru tayi kamar me naxari, yace "Say it" a hankali tace "Kila gyada" ya d'an bude ido yace "What? Groundnut?" Shiru tayi tana kallonsa, da wani expression a fuskarsa yace "Ina xan samo gyada da daddaren nan?" A takaice tace "A titi" kauda kansa yayi, khadijah dake ta kallonsa bayan kusan minti biyu a hankali tace "Ka barshi kawai bana jin yunwa tunda dare yyi, am not even hungry..." wani kallo yyi mata ta gefen ido ya mike ya nufi kofa kamar xai tashi sama ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka nmta wanke baki sannan ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma bayan ta idar da sllh, yanda xata koma kan gado ne ta kasa tashi duk jin jikinta take kamar ba nata ba, gaba daya bbu karfi tattare da ita, har bacci ya fara daukarta a xaunen taji an bude kofa, ta dago da sauri, karasowa yyi kusa da ita ya ajiye ledan hannunsa ya koma gefen gado ya xauna, Kallonta kawai yake yace "Ga gyadar, after I've gone round of d whole of damaturu" Khadijah ta wara ido tace "All the round of damaturu?" Bai ce komai ba ya hade girar sama da ta kasa, a hankali tace "Nagode" bude ledan tayi taga dafaffen gyada ce da Wanda aka gasa a wani ledan daban, dafaffen ta fara ci, da ta juya xata ga ita yake kallo, duk sh was uncomfortable na kasa cin gyadan, can dai ta sake kallonsa tace "Bismillah" bai ce komai ba, can ya sakko ya xauna kusa da darduman, ya dau gyada daya ya bude, haka ya dinga bude su har suka yi yawa sannan ya mika mata ta karba tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace "Eat" ba musu ta fara ci, ya kuma bude mata wasu masu yawa, ya mika mata, haka ya dinga mata har tace masa ta koshi, yace "Are you sure?" Tana yatsina fuska tace "Kamar amai xan yi" hade rai yyi sosai yace "Don't try dat malama, kinsan garin da naje na samo gyadar nan" khadijah ta ja baya tana nodding masa kai, can ya shafa kai a hankali murya can kasa yace "Just relax xaki daina jin aman" ta kuma gyada masa kai ta jingina da jikin gado ta lumshe ido, ji tayi aman xai taho mata, ta toshe bakinta da hannu biyu tana girgixa masa kai kamar xata yi kuka tace "Wayyo xuwa xai yiii" tashi yyi da sauri ya shiga bathroom ya debo ruwa, ya dawo ya durkusa kusa da ita ya cire Hijab din jikinta, ya watsa mata ruwan a fuska da gashinta, har ranta taji sanyin ruwan ta koma baya da sauri tana sauke ajiyar xuciya, a hankali yace "Sorry" wani ajiyar xuciya ta kara saukewa jin aman ya d'an lafa mata, ta kallesa da kyar tace "Xan kuskure baki" table water dinsa da ya shigo da ya mika mata ta tashi ta wuce bathroom da sauri, bata fito bayin ba sai da ta amayar da gaba daya gyadar da ta ci, ta fito da kyar ta xube nan tsakiyar dakin tana satan kallon sa tana mayar da numfashi, wani kallo ya dinga mata Daga inda yake xaune, bata sake kallonsa ba ta lumshe ido, lkci daya kuma bacci ya dauketa, gashin kanta taji ana gyara mata ta bude ido da sauri ta gansa durkushe gefenta yace "Ki rufe gashin ki ki hau saman gado" ba musu ta mike xaune ta hade uban gashinta waje daya ta tufke, xata mike tsaye jiri ya kwasheta ta koma da sauri ta xauna yace "Be careful" gyada masa kai tayi ta kuma tashi ta koma kan gadon ta kwanta, ac dake dakin ya rage yace "In kashe maki wutan?" Ta girgixa masa kai, yace "Sai da safe" daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin. Kafin asuba Sudais ya shigo ya fi sau biyar duba ta don da ya bude kofa xata farka, gaba daya ya kasa bacci tunanin yanda xai yi da khadijah ya damesa gashi mami Bata san ya dawo ba ma, shigowarsa na karshe ne ya rufe ta da blanket don xaxxabi ne sosai jikinta, da asuba da ya shigo tashinta tayi sllh amai tayi ba kadan ba kafin ta dauro alwala ta fito, ruwan wanka ya hada mata bayan ta idar da sllhn, da kyar ta yi wankan ta fito, ta kasa shiryawa ta kwanta nn kan gado ya lullubeta da bargo, bayan kusan minti sha biyar ya dawo gefenta yace "Daure ki tashi ki shirya mu tafi clinic" bata ce komai ba don har fuskarta ta rufe, ya cire bargon suka hada ido, sauke idonsa yyi yace "Tashi ki shirya" daga haka ya fita dakin, har ya dawo bata tashi ba, yace "Ke fa nake jira" cikin sanyin murya tace "Ni baxan iya ba" yace "Toh ni xan sa maki kayan?" Bata ce masa komai ba, yace "Look bana son in dawo in gan ki cikin bargon nn it's better ki daure ki tashi kiyi abinda xa kiyi" juyawa yyi ya fita, cike da karfin hali ta mike xaune hawaye cike idonta, kamar ynda yace mata haka ta dinga daurewa har ta sa kayan a nan inda take kan gadon, tana gama sa wa ta koma ta kwanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin, tsayawa yyi kusa da gadon yace "Toh tashi mu je" rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta mike xaune a hankali tana sauke numfashi, Wayarsa ce ta fara ring, ya daga yana kallon screen din kafin ya xauna da sauri ya daga ya kai kunne tare da sallama yace "Good morning Mami" murmushi yyi yana shafa gashin kansa a hankali yace "Ku yi hakuri Mami ban kira ba, amma in sha Allah yau xan taho, am done with what am doing" bayan wani lkci yyi mata sallama ya mayar da wayar aljihu, yana kallon khadijah yace "Tashi mu je" daga haka ya nufi kofa, a hankali ta sakko da kafafuwanta kasa tayi karfin halin mikewa, har suka isa compound din gidan bai juyo ba, sai da ya isa gun motarsa ya juyo yana kallonta, can ya bude motar ya shiga, ta karasa ta bude front seat ta xauna ta lumshe ido don ji take kamar wani aiki me wahala tayi, wani babban private asibiti suka tafi, bayan yyi parking ya juyo yana kallonta da kyau yace "Har mu bar clinic din nn bana son jin bakin ki, am nt asking for ur opinion or anything, I am doing wat I think is right, am I clear?" A hankali ta gyada masa kai, yace "Good" da yake da safe ne ba su wani dde ba suka samu ganin likita bayan ya biya kudin kati, ta xauna daya daga kujeran dake kallon likitan, ya xauna shi ma yana facing dinta, hannu ya ba likitan suka gaisa, likitan na kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "How you madam, though u look sick" khadijah tayi murmushin karfin hali, likitan yace "Allah ya sauwake, ya raba lafiya," kallon Sudais dake shafa beard dinsa yyi yace "Drugs xan rubuta maku yanxu da xata dinga sha, there is nothing more I think.... She will get better gradually" Sudais ya ce "Ba abinda ya kawo mu ba kenan Dr, though I knw it might look wrong, but... she got pregnant by mistake, it's just some weeks old, so plss I want u to get rid of it...." Tunda ya fara maganan likitan ke kallonsa da expression din mamaki, Sudais yyi kasa da murya yace "Yes plss" likitan yace "Sorry we don't do that hear sir, xaku iya tafiya wani asibitin" kallon Sudais khadijah take kamar idanuwanta xa su fito, Sudais yyi kasa da murya sosai ya marairaice yace "Yeah, I knw it's very wrong Dr... But she is my.... Wife, the last pregnancy wasn't funny, and.. She's breastfeeding an eight month old baby now" kamar ana forcing dinsa yyi magana, likitan sai kallon khadijah yake, Sudais ya ciro handkerchief ya share goshinsa don har xufa ya keto masa yace "Plss Dr, ka taimaka for d sake of d eight month child" Likitan ya girgixa kai yace "I think xai fi a daina breastfeeding babyn, she shud take care of d one she's carrying now, sai kaga Allah ya taimaka komai ya xo da sauki" Sudais yace "Nooo Dr, don Allah ka cire mata I will pay what ever amount u request for plss" likitan ya mike ya nufi show glass dake office din ya dauko wani allura da syringe, ya dawo yace "I will give her this injection sauran drugs din kuma xan rubuta maka kaje pharmacy ku siya" Sudais ya sauke ajiyar xuciya yace "Thanks very much Dr, nagode sosai" Lkci daya khadijah t fashe da kuka ta mike tace "Nooo, ni bana son a cire min don Allah ku yi hakuri" bude baki Sudais yyi yana kallonta da mamaki, ta hade hannuwanta tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata a hankali tace "Don Allah kayi hakuri, I don't want to abort d pregnancy, Allah will be angry with me plss" Likitan ya ajiye alluran ya rungume hannuwansa yana kallonta yace "Ba mijin ki bane kenan?" Hawaye na ci gaba da sakko mata ta gyada masa kai alamar eh, Sudais dake mata wani irin kallo ya mike yace "Sae ki san inda dare yyi maki kuma daga nan" daga haka ya fice daga office din kamar xae tashi sama, a hankali take kuka tana kallon likitan dake kallonta yana girgixa kai, can ta nufi kofa cikin sanyin jiki ta fita, babu motarsa a parking space, ta fita gate tana share hawayen da ya ki tsaya mata.