NOOR AL HAYAT 21-30

Fitowa Umma tayi da sauri jin kakarin aman khadijah, ta karaso da ita ta duka tace “Subhanallahi…. Are you okay” khadijah ta kasa cewa komai duk ta galabaita lkci daya, Umma ta taimaka mata ta wanke baki sannan ta dagota ta wuce parlorn ta da ita, Khadijah ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi da kyar tace “Umma I don’t knw what’s wrong with me, I am always week” Umma tace “Sannu, ko malaria ne, bari Alhaji ya dawo sai mu tafi asibiti ni bani da kudi a gu na” Khadijah ta lumshe ido har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, mikewa Umma tayi ta fita don wanke gun aman, tana isa bakin kofa ta ji muryar Hasana tana cewa “Wllh fah, sai kace mai ciki, ji fa salon aman ma daban ne, idan ma malaria ne ba yellow shataf kalan aman ya kamata ya xama ba” Shafah tace “Haka fa shekaranjiya ina lura da ta shiga kitchen duba mata girki daga xama kan kujera sai bacci, daxu kuma da safe nan bakin kofa ta xauna da abinci a gabanta tayi bacci, ace baccin nan ba lafiya ne?” Umma dake tsaye bakin kofa har lkcn gabanta yyi mugun faduwa, fita tayi parlornta a fusace duk da ta fi wata uku bata tanka su a gidan tace “Sai dai ku ga ciki can kan ‘ya yanku ko dangi, amma ba ‘ya ta ba, tunda baku da kirki baku da Imani har ku yi ma yar mutum fatan wannan mugun abun, Allah ya isa wllh” Hawaye cike idonta ta kare maganar, Shafah ta mike tana huci ta kunduma mata xagi tace “Bakin ki ya sari danyen kashi, ba ma ga mugun abu ba a ‘ya ya ko dangi, to wa yasan inda kika kai ta kwanki ko karuwanci kika sa tayi maki….” Umma ta juya ta koma daki hawaye na sakko mata sosai, kallon khadijah ta tsaya yi taga har tayi bacci, ta xauna duk jikinta a sanyaye a xuciyarta tana kara yi ma su Shafah Allah ya mayar masu mugun alkaba’in da suka yi ma ‘yar ta. Har karfe tara Khadijah na bacci bata tashi ba, tada ta umma tayi hankalinta ya tashi jin irin xafin da jikinta ya dauka, da kyar ta lallabata ta sha shayi kadan sannan ta bata paracetamol ta rakata bedroom dinta ta kwanta ita ta dawo parlor ta xauna har lkcn xuciyarta ya kasa dawowa dai dai, khadijah ce ta fito da sauri daga dakin umma na tambayarta me ya faru amma ta fita waje tun kan ta karasa can gun kwararon ruwa ta dinga amai a tsakar gidan, Umma da ta bi bayanta ta tsaya tana kallonta, jin sound din aman yasa Hasana ta leko sai ga Shafah ma ta leko, Umma ta koma ta dauko buta, ta durkusa kusa da ita har ta gama sannan ta wanke mata baki suka koma ciki, sai shivering take cikin rawar murya tace “Umma ki rufe ni sanyin” Umma ta dauko duvet da sauri ta rufe ta, nan da nan kuma bacci ya dauketa. Umma ta koma parlor ta xauna duk ta rasa me ke damunta, jin shigowar Abban fadila gidan ta jira har ya shiga part dinsa da minti sha biyar sannan ta fita, sallama tayi bakin parlornsa ya amsa ta shiga, Shafah ce a parlorn tana xuba masa abinci shi kuma yana kallon news, Umma ta xauna ta gaishesa ya amsa, a hankali tace “Alhaji dama idan da hali don Allah kudi nake so ka ba mu xan kai khadijah asibiti bata da lafiya tun safe” Shafah tace “Ae gwara aje asibitin nan kam wannan amai da bacci haka a gida” Umma tayi shiru tana kallonta, Abban fadila yace “Nawa ne kudin asibitin?” Shafah tace “Tun da ya sanka likitan kamar family Dr ne ko dubu 3 ka basu xai yi ai” ita dai Umma bata ce komai ba, Ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da dubu hudu ya mika mata yace “Gashi sai ku yi har kudin mota” ta karba da ladabi tace “Toh mun gode sai da safe” daga haka ta mike ta bar parlorn. Washegari da sassafe Umma ta sa Khadijah ta shirya bayan ta tilasta ta shan shayin da ta hada mata amma tas ta amaye sa gaba daya, duk ta xabge tayi laushi lkci daya sbda aman da take yi, A dai dai ta umma ta samo masu har kofar gida ganin kamar baxata iya tafiyar ba ma, Hasana dake sharar tsakar gida tace “Toh a dawo lafiya dai, Allah raba bawa da jin kunyan duniya da lahira dai” Umma bata tanka ta ba tana rike da Khadijah suka fita, wani asibitin daban ba wanda suka saba xuwa Umma taje ba, suna xuwa aka ce sai sun yanki kati dubu biyu, duk jikin umma yyi sanyi, shiru khadijah dake xaune tayi tana kallon nurse din dake tsaye Kansu, nan ko tuna kudin da Aliyu ya bata take yana bayan kujeran umma ta ajiye bata kuma nuna ma umman ba har lkcn, Umma ta mike tace ma nurse din tana xuwa yanxu, Cike da karfin hali Khadijah tace “Umma ina xa ki?” Tace “Yanxun nan xan dawo khadijah” daga haka ta fita. Gidan wata kawarta dake layin ta tafi ta ranto dubu biyu da yake suna mutunci da matar sosai ta bata sannan umma ta dawo asibiti, bayan an yankar masu kati suka samu ganin likita, Umma ce ke fadin abubuwan da ke damun khadijah ma likitan, don Khadijahr duk tayi weak, tambayar farko da likitan ya jefo ma Umma shine “Tana da aure ne?” Gaban umma yyi mugun faduwa ta girgixa ma likitan kai kawai, likitan yace “Toh xa ayi mata test…” Bai dai fadi wanne ba umma tace “Toh” ya kira nurse ya bata file din nasu yace su bita, Umma na rike da hannun khadijah suka dawo reception, Nurse din tace kudin test din dubu biyu da dari biyar haka Umma ta bata duk ta yi wani sanyi, suna ta xaune a reception har bayan mintuna da dama result ya fito matar ta ce su je office din Dr bayan ta kai ma sa, Likitan dake ta kallon umma yace “Yar ki ce yarinyar nan?” Umma ta gyada masa kai xuciyarta na bugawa, ya girgixa kai yace “Sorry madam, She is few weeks pregnant” mikewa Umma tayi a mugun gigice tace “Pregnant Dr?” Likitan ya gyada mata kai, Khadijah da ta xaro ido ta dinga kallon likitan xuciyarta na bugawa, kuka sosai Umma ta saki a gun ta juya ta fita, khadijah ta mike ta bi bayanta da sauri, likitan ya girgixa kai ya bi ta da kallo a ransa yace why Such a beautiful girl, Gaba daya asibitin Umma ta fita har lkcn tana kuka, khadijah da duk jikinta ya mutu ta dinga bin ta ita ma, har lkcn ita dai bata gane wani pregnant din likitan ke nufi ba, adai daita Umma ta hau tayi wucewarta gida, Khadijah da tayi still a inda take ta bi adai daitan da kallo ta kasa kwakkwaran motsi, lkci daya duk ta nemi xaxxabin da rashin kwarin jikin dake tattare da ita ta rasa, har sannan kuma ta kasa kukan, tafiya ta fara yi kamar warce kwai ya fashe ma, da yake ba wani nisa ne da asibitin ba har ta isa gida, Hasana da Shafah na xaune tsakar gida ta wuce parlorn Ummanta suka bi ta da kallo, bata ga Umma a parlor ba a shiga bedroom dinta, xaune ta ganta nan kasan dakin banda kuka babu abinda take, ta sulale kasa a hankali sai a sannan wasu hawaye masu xafi suka dinga sauka idonta, Muryar Umma taji cikin kuka tana cewa “Khadijah yanxu ni xa ki kunyata, ni xa ki yi ma tonon asiri a idon duniya, is this my reward for taking you as a daughter?” Khadijah na shessheka tace “Ummata kiyi hakuri” mikewa Umma tayi da wani force ta sauke mata mari, bata gama recover ba ta kuma kai mata wanda ya fi na da, kasa kwakkwaran motsi khadijah tayi a inda take durkushe lkci daya taji komai ya tsaya mata, Umma na mata wani kallon da xa a iya kiransa da na tsana tace “Kin cuce ni kin ci amanata, kin ci amanar late mahaifinki” hakan da ta fada ya sa khadijah rushewa da kuka mai ban tausayi cikin rawar murya tace “Na shiga uku, don Allah Ummata ki yi hakuri” ta kuma kai mata wani marin tana kuka sosai tace “Uban waye yayi maki Ciki khadijah” kamar numfashinta xai dauke take kuka tana girgixa kai tace “Ban sani ba Ummaa” rufeta tayi da duka har sai da ta gaji don kanta ta kyaleta kuma har lkcn kuka take, cikin raunin murya tace “Tashi ki bar min gidana kije duk Inda xa ki je tunda baki san wanda yyi maki ciki ba, Allah ya isa tsakanina dake khadijah, kin bata min suna, ki tafi khadijah xaman ki gidan nan xai iya kashe min aure ki tafi bana son ganin ki kije duk Inda xa ki” gyada mata kai kawai khadijah take tana sheshsheka, shigowan su Shafah da Hasana dakin yasa Umma tayi shiru har lkcn tana kuka, suka gama kare masu kallo sai suka saki shewa sannan suka fita dakin, khadijah ta mike da kyar don banda ciwo babu abinda ko ina na jikinta ke mata ta fita dakin tana goge jinin bakinta, bayan kujera ta tafi ta dauki envelope din da Aliyu ya bata wasu hawaye masu xafi na xubo mata, xaxxage bundle din kudin tayi gaba daya a kasa sai ga wani farar takarda a linke ya fadi, ta dau takardar ta warware tana kallon content din, *I don’t have much to say khadijah, na san har abada baxa ki mance abinda ya faru tsakaninmu ba kamar ynda nima baxan mance ba, tafiyar ki shine ma fi alkhairi sbda baxan taba samun kwanciyar hankali da nutsuwa ba matsawar muna gida daya, ina rokon gafarar ki Khadijah forgive me not because I deserve it but for the sake of Islam, Allah hada fiskokinmu a aljannatul fiddaus, ina maki fatan alkhairi a rayuwa da fatan miji na gari* cukuikuye takardar tayi ta fashe da wani kukan takaici taji dama ta kashe kanta ta huta amma bbu daman yin hakan, mayar da kudin tayi envelope din har ma da takardan ta mike ta fice parlorn tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ko kadan bata ji me su Shafah ke cewa ba har ta fice gidan gaba daya, khadijah bata xarce ko ina ba sai tashar mota, tafiya kawai take a park din tana jin sunan garuruwan da ake fadi har ta isa gun motar garin Yobe ta hau bayan minti goma mota ta cika suka dau hanyar damaturu garin da bata san kowa ba bata taba xuwa ba.