NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 31-40

Mami na kallon Aliyu da wani expression tace “Aliyu??? is this the life you chose for ur self? Is this the home training I gave to you” Sudais ya sauke kansa daga kallonta lkci daya jikinsa yyi sanyu ya sauko downstairs a har sannan yana rike da yaran, a hankali yace “No Mami, I didn’t choose this life for my self….” Katse sa ta yi cikin tsawa tace “Aliyu ka fada min wacece yarinyar nan? Who is she? Meye hadin ka da ita?” Ya hadiye abu da kyar yace “Mami… Mami ba lallai ki yarda da abinda xan ce maki ba, but Mami ki kira Yusuf xai gaya maki wacece ita kilan shi ki yarda da shi” wani mugun kallo Mami ta dinga yi masa xuciyarta na tafarfasa tace “In kira Yusuf? saboda ina tsoron ku? To bani da wannan lkcn, Aliyu dama abinda ka dawo yi a Abuja kenan? Mace ka dauka ka ajiye gida ku ke rayuwa tare…. Wa iyaxubillah” Hajiya Rukayya tayi saurin dakatar da ita tace “Haba, ki sauraresa tukun Hajiya” daga haka ta mayar da dubanta kan sudais tace “Ka gaya mana wacece ita Aliyu” Sudais ya kalli khadijah da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta, rasa abinda xai ce yyi duk jikinsa yyi mugun sanyi, Hajiya Rukayya tace “Toh bani number Yusuf din, ni xan kira sa” Mika masa wayarta ta yi ya amsa ya sa mata number Yusuf yana fara ring Hajiya Rukayya ta karba, Yusuf na dagawa Mami ta karbe daga hannun Hajiya Rukayya, daga daya bangaren Yusuf yayi sallama, Mami ta amsa tace “Yusuf kana ji na?” Shiru yyi jin kamar muryar Mami, a fusace tace “Ba da Yusuf nake magana ba” Yusuf ya kwalalo ido yace “Ehh ina nine mami, ina kwana,” bata damu da amsa gaisuwarsa ba tace “Yusuf ka gaya min wacece yarinyar da Aliyu ya ajiye gidansa da yara” Sai da gaban Yusuf ya fadi ya mike daga xaunen da yake, can ya koma ya xauna a hankali yace “Mami it’s not what u are thinking wllh yarinyar nan da kike gani taimakonta kawai Sudais yyi, she is an orphan….” Lkci daya idon Mami ya kada ta katse sa hade da kunduma masa xagi tace “An orphan??? Bata san hanyar orphanage ba ko kuma kai me yasa baka yi mata taimakon ba sai shi, ya ajiye mace da ba muharramarsa ba kace yana taimakonta Yusuf, tun da uwar ka ta haife ka ka taba jin haka?? su kuma yaran na waye?” A sanyaye Yusuf yace “Nata ne Mami” Mami na jin haka ta katse wayar tana kallon Hajiya Rukayya lkci daya idonta ya kawo ruwa tace “Kina jin halin yaran yanxu koh Rukayya, yanxu ka haifi yaro baka haifi halinsa ba, ni dama da dadewa na lura da takun Aliyu, mu Aliyu xai kunyata a idon duniya? irin tarbiyar da ni da ubansa muka yi masa kenan” durkushewa Khadijah tayi a wajen tana kuka a hankali tace “Umma kiyi hakuri don Allah ki yafe masa” Tsawa Mami tayi mata tace “Rufe min baki, tarbiyar da iyayenki kema suka maki kenan kiyi rayuwa gida daya da namiji?” Cikin rawar Murya Khadijah tace “My parent are late, bani da kowa shi yasa ya taimakeni, Umma kar ki ce ya barmu don Allah…”  sudais da ya ji kafafuwansa sun gaxa daukarsa ya xauna kan kujera ya ajiye su shureim da suka wani  rirrikesa, cikin sanyin murya yace “Mami don girman Allah kiyi hakuri, ba yanda kike tunani abun yake ba, I just….” Katse sa Mami tayi cike da takaice tace “Ba yanda nake tunani abun yake ba Aliyu?” Sudais ya daga kai da kyar yana kallonta ganin hawayen dake idon mahaifiyarsa ya ajiye yaran ya mike ya isa gabanta ya durkusa cikin rawar murya yace “Noo Mami pls kar ki xubar da hawayen ki a kai na, na maki alkawarin na daina duk abinda nake daga yau, ki gafarce ni don Allah mamina” duk ya rikice mata, Mami na hawaye tace “Ni idan na gafarce ka Allahn ka fa? Wani tsinannen taimako ne wannan without the consent of ur parent, wani taimako ne wannan kuna rayuwa gida daya kamar mata da miji, yanxu ba don na san halin ka ba ance maka baxan yarda yaranka bane wa enan yaran?” Idonsa ya kada sosai cikin raunin murya yace “Mami nayi abinda nayi ne domin taimako amma daga yanxu na bari in sha Allah, forgive me plss Mami, nasan ban kyauta maku ba” Mami tace “Ka hada ina ka ina ka ka koma Damaturu yau ba sai gobe ba, sannan ina jiran makullin gidan yanxu ka same ni gidan Hajiya Rukayya” Tana fadin haka ta juya ta fita a parlon, kai kana gani kasan tana mugun son d’an nata ne, Hajiya Rukayya tace “Heed to what ur mother said right away Aliyu, ita kuma idan tace bata da iyaye ai baxa ta rasa dangi ba ta tafi wajensu” shi dai sudais bai ce komai ba, Hajiya Rukayya ta juya ita ma ta fita, Sudais ya dafe kansa da yyi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya dagule ga kukan Khadijah da yake ji har ransa, su kansu yan biyun kuka suke, lkci daya idanuwansa suka kada, mikewa yyi daga durkushen da yake ya wuce dakinsa ya dau makullin mota ya fita gidan gaba daya, Nanny da duk taji abin da ya faru ta iso gun khadijah dake kuka sosai ta dafa ta a hankali tace “Dama ba mijin ki bane mutumin nan maman twins?” Khadijah ta dago tana kallonta hawaye na sakko mata ta girgixa mata kai tace “Taimako na kawai yayi tun ban haifi yaran nan ba, ni bani da kowa sai shi yanxu” Hawaye ne ya cika idon Nanny tace “Dangin ku fa?” Cikin rawar murya Khadijah tace “Ban san dangin Mahaifiya ta ba, dangin Abbana kuma baxa su karbe ni ba, Ummata kuma ta tafi ta bar ban san inda xan ganta ba” tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka tace “Ni yanxu ban san ya xan yi da yaran ba” kuka sosai Nanny take duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ta jawo ta jiki cikin sanyin murya tace “Kiyi hakuri wataran sai labari Allah baxai hanaki yanda xa kiyi ba, kar ki sake kuka don Allah” mikewa Nanny tayi ta tafi gun su Shureim dake ta kuka wai Sudais ya fita ya bar su. Bayan awanni kusan uku Nanny ta gaji da lallashin Khadijah da ta ki hakura da kukan da take, xuwa lkcn kuma su Shureim sun yi bacci, Da kyar Nanny ta lallaba ta taje tayi sllh don duk a sanyaye take, tana xaune kan darduma Sudais ya shigo gidan, kallonsa Khadijah ta dinga yi har ya xauna kan kujera, a sanyaye ta taso ta durkusa gefensa tace “Am sorry I caused you all this, kayi hakuri don Allah ka yafe min” Tana magana hawaye ce idonta, ya kirkiri murmushi yace “It’s nothing Amira, tafi ki hada kayan ki gaba daya a sama” shiru ta yi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya gyada mata kai cike da assurance, tashi tayi jiki ba kwari ta wuce sama, ya kalli Nanny da ke parlorn ita ma duk a sanyaye yace “Ki hada kayan yaran da naki gaba daya” mikewa tayi ta wuce sama ita ma, Nanny ce ta fara sakkowa parlorn da jakunkunan kayan su shureim, Sudais dake kallonta yace “Ki kai cikin booth, its open” fita tayi waje da kayan, tana dawowa yace ta je ta taya khadijah, Kuka Nanny ta samu Khadijah nayi a dakin, bata iya tace mata komai ba ta shiga taya ta hada kayanta, Nanny ce ta sauko da jakan ta kai cikin motar, shi dai Sudais na xaune yyi nisa tunanin da yake, jin wayarsa na ring ya dauka da sauri yana kallon mai kiran, tashi yyi ya daga wayar yace “Mukhtar ka iso ne” daga daya bangaren abokin nasa yace “Ehh ina waje” fita yyi ya samesa waje, Mukhtar yace “You mean wannan gidan xaka siyar Barrister?” Sudais ya shafa kansa yace “Ehh shi” Mukhtar yace “Haba, Toh ai wannan yafi wancan wllh, ya xaka siyar da abu ka siya wanda bai kai sa ba kuma har da ciko, amma sun ma same ka da yawa” Sudais yace “kai dai bani takardun wancan gidan, and don’t forget gidan is almost furnished” Barrister Mukhtar ya bude motarsa ya fiddo envelope ya mika ma Sudais ya karba yace “Duk da haka dai, duka duka kayan nawa ne a ciki” Sudais ya amsa envelope din yace “Nagode, bari in dauko nawa” daga haka ya koma ciki ya wuce bedroom dinsa ya dauko wani envelope dake dauke da takardun gidan nasa yana dawowa ya mika ma colleague dinsa yace “Kafin dare xa a kwashe komai na nan din, soo you help me explain to them” Mukhtar da mamakin Sudais ya cika sa ya karbi envelope din yace “Toh shkkn” daga haka suka yi sallama Mukhtar ya wuce, Sudais na komawa ciki ya sa Nanny ta dauko twins suka shiga mota, Ganin Khadijah bata fito sudais ya wuce sama ya bude kofar dakin duk da kukan da ya sameta tana yi kawai cewa yayi “Ke nake jira Amira” daga haka ya juya ya fita, Khadijah ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fita, a gaban motar ta xauna Nanny kuma na xaune da yaran a baya suka bar gidan bayan Sudais ya sauka ya rufe gate, tafiyar kusan minti ashirin suka yi sai kallon agogo sudais yake har suka iso wani anguwa, anguwa ce mai kyau shi ma kamar wancan, yyi parking dai dai gate din wani bungalow babba ya fita ya bude gate din ya ja motar suka shiga gidan, sosai gidan ya hadu bayan yyi parking ya bude motar ya fito yana kallon Nanny yace ta fito da yaran da xuwa lkcn sun tashi daga baccin da suke, kallon khadijah yyi ta bude motar ita ma ta fito, Sudais ya nufi entrance din shiga gidan ya bude kofar da makullin dake cikin envelope sannan ya shiga, parlorn na da girma amma bai kai na can gidan sudais ba, sannan dakuna uku ne ko wanne da bayi sai kitchen da dinning area, da kuma bathroom da toilet a parlorn, gidan ya hadu, sai dai fa bai kai na sudais ba, Har TV akwai a parlorn bayan kujeru da center table da dinning table da chairs a area din da aka tanadar don ajiye su, kasa xama khadijah tayi a parlorn, Sudais dake tsaye shi ma ya nuna mata kujera ta xauna, sai a sannan ta xauna cikin sanyin jiki, ya dau little sudais dake ta daga masa hannu wai ya daukesa, Sudais na kallon Nanny murya can kasa yace “Madam ina son ki min alfarma daya na xaunawa tare da su even if it’s just for few years to come for the sake of this twins, I will pay all the money in sha Allah” Nanny da jikinta yyi sanyi tace “Ba damuwa yallabai, Allah ya saka da alkhairi” Nan take sudais ya bata check na shekarun da ya fada, sannan ya nufi Khadijah yana kallonta ya ajiye mata envelope din hannunsa a kafarta a hankali yace “Gashi Amira this is for my boys, da sunansu na siya gidan nan don haka na su ne, mallakin su ne” kasa cewa komai tayi tana kallonsa, ya durkusa gabanta a raunane yace “I have always wanted the very best for you Amira, like… sending you out to UK kiyi karatu ki xama likita, a ko da yaushe hakan yana rai na amma saboda kananun yaran ki…. I decided sai sun kai ko da shekaru biyu ne sai ki tafi tare da su…. Am sad I couldn’t fulfill that but you can ur self, promise me ko bayan babu ni, xa kiyi karatu ki xama babban likita, I mean ki min alkawarin xa ki cika min wannan burin nawa a kan ki” jin bata ce komai sai kallonsa take a tsorace ya kamo hannunta yana kallon kwayar idonta, he understand she’s shock, ya lumshe ido ya mika mata check na kudi, da farko kasa magana yyi can yyi gathering courage with a breaking voice yace “Am going Amira, this is a check of 20 million, I think that all I’ve got for now, kiyi kokarin ganin with this little am giving you kin inganta rayuwar ki da na boys din ki, sannan ki ci gaba da rike mutuncin ki na ‘ya mace duk inda xa ki samu kan ki, I wish na yi kokarin nema maki Umman ki kafin in tafi, I wish na kwato maki hakkin ki a gun dangin mahaifin ki, amma duk hakan bai yiwu ba Amira, ki kyale su xa su mayar maki a lahira idan Allah ya yarda, as for the twins..” Kasa ci gaba yyi, yyi shiru na wani lkci bai son ta ga hawayen idonsa, can yyi karfin halin cewa “I knw i will always love them tamkar yaran da na haifa a cikina, kar ki bari su yi rashi na Amira, ki dinga masu abinda nake masu, I mean ki so su kamar yanda nake son su, you are all they’ve got now, ke kadai gare su, idan kuma kika samu abokin rayuwar da kika ga ya kwanta maki kiyi aure amma ki fara sanar da shi ke wacece, a duk xaman mu Amira idan na taba saba maki da sani na ko akasin haka ki gafarce ni” kansa a kasa yace “I think that’s all, akwai foodstuffs da na siyo daxu a kitchen, goodbye Amira, it’s great knowing you in my life, wishing u better future ahead….” Ganin xai tashi Khadijah ta sakko kasa ta rikesa ta fashe da matsanancin kuka cikin rawar murya tace “Na shiga uku, don Allah kar ka tafi ka bar ni ni kadai, you are all I have with my kids, ka ce min fa baxa ka taba barina ba, don girman Allah kar ka min haka Aliyu, idan ka tafi ya xan yi…” Kasa kallonta yyi, ta daura kanta a kafarsa tana kuka sosai cikin raunin murya tace “Kasan ni marainiya ce, I don’t have anybody, ya xan yi da yaran idan ka tafi ka bar ni da su Aliyu, don Allah kar ka tafi ko don su, ban san inda xan ga ummata ba kar ka tafi ka bar ni ni kadai a duniyar nan” Hakan da khadijah ta fada yasa Nanny ta fara kuka tausayin khadijah da yan biyun ya cika ta, Sudais yyi iya kokarin ganin hawayen idonsa bai sakko ba amma hakan bai yiwu ba, ya dago ta da kyar shi ma hawaye na xubo masa yace “Life goes on with or without me Amira xaku yi rayuwarku da yaran, you just have to manage the little I gave you cos I knw living in Abuja is expensive, surely watarana xa ki hadu da ummanki har ma da dangin mahaifiyar ki, I have to go now saboda Mamina, baxan iya tsallake maganar ta ba kiyi hakuri, ke dai kiyi min alfarmar kula da yan biyun ki, kuma ki daina jin haushinsu ki ja su a jiki, su kenan gare ki a yanxu, kar ki shafa masu laifin mahaifin su” daga haka ya mike ya isa gun twins din ya duka yana kallonsu a sanyaye, dariya suka fara masa suna daga hannu ya daukesu, ya manna masu kiss gaba daya ya lumshe ido murya can kasa yace “Long life to you both in sha Allah my boys, Allah ya albarkace rayuwarku ku xamto *hasken rayuwar* mahaifiyar ku” tashi yyi ya nufi kofa trying hard to control his self, Khadijah na kuka sosai cikin sanyin murya tace “Thanks very much Aliyu, Allah ya biya ka abinda kayi mana, and I will always pray for you in my life, kai din ka xame min _hasken rayuwa_ a lkcn da rayuwata tayi min duhu, daga ranan da na fara ganin ka ka yaye min bakin cikin dake tare da ni, you will always be the *light of my life* Aliyu” Sudais bai iya ya juyo ba har ya isa kofa, yaran na ganin xai fita suka fara kuka, bai yarda ya juyo ba har ya bude kofar ya fita yana goge hawayen idonsa, yana fita kuma ya bude wayarsa ya cire sim  din da Khadijah ta san sa da shi ya jefar nan cikin flowers din gidan ya fita ya hau motarsa, and that was how Barrister Aliyu left Khadijah and her twins. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button