Katse wayar Sadeeq yyi jin bata ce komai ba, ya sake kiranta a tunaninsa network ne, bayan ta daga tayi masa sallama, amsawa yyi yace "Is ur network fluctuating?" A hankali tace "Ina jin ka yanxu" yace "Ohk, Cewa nayi when xan xo in gaisa da Umma if possible har da matata kinga shkkn ta samu Umma a garin Abuja ita ma, cos she have no body here" Khadijah ta wara ido tace "Lah, are you married?" yace "Sure, kusan 3 months kenan" murmushi sosai Khadijah tayi tace "Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya" yace "Ameen thumma Ameen, to yaushe xa mu xo?" Khadijah tayi murmushin karfin hali tace "In dai kuna da time, kar ku ma ta gan ni tayi wani tunanin daban fa" dariya sosai Sadeeq yyi yace "Noo, she's understanding, kawai daga few months da aure sai ta sa abu a ranta don ta gan ki, ba ma yar Nigeria bace, so she won't think like them in sha Allah" Khadijah tace "Yar ina ce?" Yace "She is an Ethiopian" Khadijah ta wara ido tace "Kace bata jin Hausa kenan" yyi dariya yace "Noo tana ji ba laifi, ai tana xuwa hutu gun aunt dinta a Katsina sai dai tana dadewa bata xo bane, but she speaks English well" Khadijah da ke ta murmushi tace "Maa sha Allah, I will love seeing her" Sadeeq yace "Toh ko ki shirya da 'yan gidan ku sai in xo in dauke ku, she will be very happy don bata da kowa, though shekaranjiya dai wata frnd din mum dinta ta xo daga can kasar ta su, yanxu haka ma tana gidana, but ita ma nan da kwana biyu xata wuce" Khadijah ta langwabar da kai tace "Allah sarki, to yaushe xaka xo ka kai mu, amma ni dai ina tsoro fa" dariya Sadeeq ya dinga yi yace "Tsoron me? Na fa ce maki she is not like you people in Nigeria, I can even tell her you are an old time frnd, idan kinyi insisting kina tsoro kuma sai in ce ke yar uwata ce" Khadijah tace "Haka dai ya fi" Sadeeq yace "Dubeta matsoraciya, idan na aureki na hada ku fa?" ta d'an hade rai tace "Ni ance maka aure xan yi yanxu" yyi murmushi yace "Mayar da wukar wasa nake, nima baxan iya handling two wives ba ai" murmushi kawai khadijah tayi, yace "Tun da gobe Monday xan xo da yamma sai in dauke ku, sai ki sanar da umma" Khadijah tayi shiru don bata son fashin islamiyya, can tace "Toh shi kenan Allah ya kai mu" yace "Ameen Khadijah, bari in bar ki kiyi bacci, sweet dreams" tace "Toh nagode bye" daga haka ya katse wayar, Khadijah ta sauke ajiyar xuciya jin Sadeeq yyi aure, thank God baxai shigo rayuwarta bane ya dame ta, duk da can kasar xuciyarta tana ganin girma da darajar abinda yyi mata a lkcn tana Katsina, he really helped her don da ba don shi ba kilan idan yunwa na kissa da ya kasheta, murmushi tayi ta koma ta kwanta tana rufa twins dinta da duvet, matar da yace ya aura ce ta fado mata, toh Allah yasa sa'arta ce ko xata samu warce xa su dinga xumunci sosai da, don ta gaji da rayuwa daga ita sai Nanny da boys dinta bata da kowa, Aysha dama kawai a makaranta kadai suke interact, Har ranta taji hankalinta ya kwanta haduwa da Sadeeq, ko ba komai dai akwai wanda ya santa ta san sa a Abuja yanxu sai dai fa bayan sudais bbu wanda xata sake bata lkcn ba labarinta gaskiya, its not as if Sadeeq didn't deserve to knw her story but maimaitawan xai dinga fama mata ciwon da take healing a hankali na xuciyarta, da wannan tunane tunanen bacci ya dauke Khadijah, da asuba bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduma tana azkar dinta Nanny ta shigo dakin da sallama, gaisawa suka yi tana kallonsu Sudais tace "Basu tashi cikin dare ba neman tea" Khadijah ta girgixa kai tace "A'a..." Nanny tace "Toh kafin dai ki gama shirin makaranta na san sun tashi, sai kiyi masu wanka, ni kuma xan tafi in hada breakfast yanxu" Khadijah tace "Toh" daga haka Nanny ta fita dakin, khadijah na fitowa daga wanka wajen karfe shidda da minti arba'in ta ga yaran xaune kan gado duk sun tashi, wara masu ido tayi ta nufesu ta durkusa tana murmushi a hankali tace "Good morning boys" kicin kicin suka yi da fuska suna kallonta kamar Aliyu ya hade rai, dariya hakan ya bata, tace "Toh bari in maku wanka sai ku tafi wajen nanny" daga haka ta koma bathroom din tana daure da towel ta hada masu ruwan wanka ta dawo ta dauke su gaba daya suka shiga bathroom din, a dakinta ta gama shirya su kafin ta tafi parlor da su nan Nanny ta sa tayi feeding dinsu, sai kusan karfe bakwai da rabi Khadijah ta gama shirin tafiya makaranta, tana isa bakin kofa ta juya tana kallon twins da suka bi ta da kallo, kamar hadin baki suka daga mata hannu a tare murmushi tayi ta daga masu ita ma sannan ta fita. Karfe hudu da kusan rabi Sadeeq ya kirata, bayan sun gaisa yace "xan taho yanxu Khadijah, am done for today a office" khadijah da ke dama ma su Sudais golden morn a parlor tace "Toh muna jira, Allah kawo ka lafiya" Tana gama ba ma yaran abinci tayi masu wanka ta shirya su cikin kayansu iri daya, sosai yaran suka yi kyau da kayan da ta sa masu, ta fiddo kayan da xata sa kenan Sadeeq ya kirata, daukan wayan tayi ta daga ta kai kunne yace "Am outside Khadijah" ta xaro ido tace "Toh don Allah yi hakuri, minti goma pls" yace "Alryt then, ina jira" a hanxarce Khadijah ta shirya sannan ta sa Hijab dinta har kasa kamar yanda ta saba, ta fita gun Nanny dake wankin kayansu shureim a bathroom dinta, ta tsaya daga bakin kofa tace "Nanny xa mu d'an fita da twins amma baxa mu dade ba" Nanny tace "Toh shkkn Allah ya kiyaye, amma kar kuyi dare kin ga yamma yyi" Khadijah tace "In sha Allah" daga haka ta fita ta shiga nata dakin ta fito tare da yaran, gabanta sai faduwa yake kar su ce baxa su bi ta ba, Har bakin kofa nanny ta rakasu tana daga ma yaran hannu su ma suna daga mata, tun kafin su iso motar Sadeeq ke kallon yaran, kawai ya bude motar ya fito yace "Waow, cute boys, ur siblings?" Khadijah ta kirkiri murmushi ta gyada masa kai daukansu yyi da daddaya da daddaya ya masu kiss yace "How are you boys" Kallonsa kawai yan biyun ke yi, ya bude front seat yana kallon khadijah yace "Toh shiga" tana shiga motar ya mika mata yaran gaba daya ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da suka hau kan titi yace "Ya sunan twins din?" Khadijah tace "Sudais and Shureim" yace "Maa sha Allah, they are handsome, but step siblings din ki ne su koh?" dariyar karfin hali Khadijah tayi tace "Uhm" yace "That's nyc" yace "Har na sanar ma Shaheedah xuwan ki, she is so happy" Khadijah tace "Da gaske" yana murmushi yace "Sure" tace "Allah sarki" nisa ne sosai da gidan Sadeeq don sai kusan karfe biyar da wani abu suka isa gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, bayan yyi parking yace "Welcm to our home Khadijah" murmushi kawai tayi ta bude motar ya xaga ya taimaka mata sauke yan biyun kasa sannan ta fito ta rufe motar, wata kyakkyawar mace ce da baxata wuce shekaru ashirin a duniya ba ta fito balcony din gidan, fara ce doguwa mai kyan gaske, ta karaso gun motar tana murmushi sosai tace "Sannun ku da xuwa bak'in mu" Khadijah dake ta kallonta tayi murmushi tace "Yauwa sannu" wara ido matar tasa da ya kira da shaheeda tayi tana kallonsu Sudais tace "Maa sha Allah, dear they are sooo cute" daga haka ta tsugunna ta jawo yaran jiki tace "Welcome boys" Khadijah ma sai kallon yaran nata take ganin sun ki ko da murmushi, Sadeeq ya dau Sudais yana murmushi yace "Lallai boys din nan sun iya miskilanci" Shaheedah ta dau Shureim tana dariya tace "Mu shiga ciki toh" daga haka ta fara tafiya Sadeeq ya kalli khadijah yace "Mu je" bin bayan shaheedah tayi ya bi bayanta yana rungume da shureim. It's not much sorry.... Suna shiga parlorn khadijah ta xauna kan daya daga kujerun ciki, Shaheedah ta ajiye shureim tana murmushi tace "Wai basa magana ne?" Khadijah dai bata san ko suna yi ba ko basa yi amma taji Nanny tace suna yi idan sun ga dama, ta dan yi murmushi tace "Ba sosai ba, har yanxu basu iya ba" Tasowa Sudais yyi ya dawo kusa da ita shureim ma ya sauka kan kujera ya bi twin din nasa, Sadeeq yace "Lallai, yayarku kadai ku ka sani kenan koh" Shaheedah tace "Dama mana" daki Sadeeq ya wuce, Shaheedah kuma ta nufi fridge ta bude ta dauko masu drink da ruwa ta daura kan tray da cups uku sannan ta dawo ta ajiye tana kallon khadijah tace "Ban ma san sunan ki ba" Khadijah tace "Sunana Khadijah" Shaheedah tace "Ayya, ni kuma Shaheedah" Khadijah na murmushi tace "It's nyc meeting you Shaheedah" Shaheedah ta mayar mata murmushin tace "You too" abinci ta koma kitchen ta dauko a warmer da plates da spoon, khadijah tace "Lahh wllh mun ci abinci kafin mu taho Shaheedah" Shaheedah ta bata fuska tace "Saboda ke fa na yi girkin" Khadijah tace "Ayya da baki bai kan ki wahala ba, kin ga su ba cin abinci ma suke ba sai dai golden morn ko custard" Shaheedah tace "Toh sai in masu ai akwai custard din din ke sai ki ci wannan" da sauri khadijah tace "Kafin mu fito ba basu suka sha, ko kin yi baxa su sha ba da gaske" Shiru Shaheedah tayi kafin tace "Kenan dai baxa ki ci abincin ba Khadijah" Khadijah tayi murmushi tace "Toh xan ci Shaheedah" Shaheedah tace "Yauwa na ji dadi" daukan yan biyun tayi tace "Ku bar Anty ta ci abinci mu tafi ku gaida Mamata" Khadijah ta kalleta tace "Ayya mama na nan ne" Murmushi Shaheedah tayi tace "Idan kin gama cin abincin sai mu je ku gaisa" daga haka ta wuce da yan biyun dakinta, Shaheedah na rufe kofar tace "Mama dubi yaran nan masu kyau maa sha Allah" warce ta kira da mama dake xaune dakin kan darduma tace "Bakin naki sun iso kenan" Shaheedah tace "Ehh har da kanninta ma ta xo, ga su su taya ki hira xan kai ma sa abinci" Daga haka ta fita ta bar yaran a dakin. K'adan Khadijah ta ci tuwo da miyar ganyen da Shaheedah ta kawo mata, cin abincin take amma gaba daya hankalinta na kan yaranta da bata gani ba kuma bata ji motsinsu ba, tashi tayi daga karshe ta dau warmer din tuwon da miya ta wuce kitchen da su, ta wanke plate din da ta ci abincin da cup sannan ta fito parlor ta xauna, dai dai nan Shaheedah ta fito parlorn tace "Lahh har kin gama Khadijah, ko dai ba ki ci ba" Khadijah ta kirkiri murmushi tace "Aa na ci wllh, bacci suka yi ne?" Ita kanta sai da taji kunyar tambayar, Shaheedah tace "Aa suna gun mama ne, mu je ku gaisa tana daki" tashi Khadijah tayi tace "Toh" sannan ta bi bayan Shaheedah suka wuce dakinta, Shaheedah na shiga tace "Mama xa ku gaisa da khadijah" daga haka ta bar bakin kofar Khadijah ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana kallon matar dake xaune kan darduma su shureim a kusa da ita, lkci daya taji komai nata ya tsaya ta kasa kwakkwaran motsi wajen da kyar cikin tsarkewar murya tace "Ummaa" Sai a sannan matar ta juyo da sauri ita ma jin muryar da ta dade tana muradin sake ji ko da a ranan da xata bar duniya ne, mikewa tsaye tayi tana kallonta cikin wani yanayi tace "Khadijah??" Shaheedah da ta saki baki tace "Lahh mama kin san ta ne dama?" Juyawa Khadijah tayi da sauri hawaye cike idonta ta bar bakin kofar, Kan kace me har ta isa gate ta fice daga gidan hawaye masu xafi na sakko mata, da sauri ta isa bakin titi ta tsayar da adai daita ta shiga, tana jin Shaheedah na kwalo mata kira alamar sun biyota amma taki waigawa tace mai adai daitan ya tafi, har khadijah ta isa gida kuka take cikin Napep kamar ranta xai fita, ta rasa dalilin kukan nata, taji xuciyarta yyi mata rauni ga xugin da ya fara mata, mai adai daitan a tuaninsa rasuwa aka yi mata ya dinga bata hakuri bai ma karbi kudin ba ta shige gida, nan parlor ta xube ta kara rushewa da kuka kamar xata tsaga gidan, Nanny ta fito a rikice ta shiga tambayarta me ya faru ina su Shureim sai a sannan khadijah ta tuna da yaran nata, Nanny duk ta rikice ta mike ta fita ta sake dawowa a rude tace "Khadijah tambayar ki nake ina yaran me ya same su, ina suke" Khadijah ta hade kai da kujera cikin rawar murya tace "Ummata na gani Nanny" Nanny ta tsaya kallonta kamar idanuwanta xa su fito, can ta durkusa kusa da ita da sauri tace "Umma? Ummarki dai? A ina kika ganta" Khadijah ta kara fashewa da kuka tace "A gidan da muka je" Nanny tace "Toh sai ta ce maki me, ko bata gan ki ba?" Nanny bata rufe baki ba sai ga Shaheedah ta shigo parlorn a sanyaye, khadijah na ganinta ta kara hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Shaheedah ta isa kusa da ita ta durkusa a hankali tace "Dama ke ce khadijahr da mama ke shigowa Nigeria saboda tun shekaru uku da suka wuce, dama ke ce khadijahr da mama ke yawan maganar ta a can kasar mu?" Khadijah ta dago hawaye wasu na bin wasu tana kallon Shaheedah, girgixa kai Shaheedah tayi tace "Allah sarki khadijah na samu labarin ki a gun mama tun ban yi aure na dawo kasar nan ba, Khadijah Mama ta shiga wani yanayi bayan rabuwar ku, ta je garurruka da dama na Nigeria tana neman ki, ta dalilin ki mama bata da isashen lafiya har yanxu, Wllh wannan xuwan ma tana sauka Nigeria Kano ta fara xuwa wai ko Allah xai sa ta gan ki, daga kano ta tafi Katsina sannan ta taho Kaduna duk wai ko xa ku hadu kafin ta taho gidana nan Abuja kuma gobe ma take shirin komawa kasar mu" Shigowar Umma parlorn ya sa Shaheedah tayi shiru tana kallonta, kana ganinta kasan ita ma tayi kukan, Umma ta karaso parlorn a sanyaye ta xauna kan kujera kusa da khadijah wasu hawayen na sakkowa idonta, Khadijah ta kasa kallonta ita ma tana hawayen, Cikin sanyin murya Umma tace "Ko da baxa ki saurareni ba Khadijah ina neman gafarar ki, ki yafe min, na maki abinda uwar da ta haife ki baxa ta maki, Khadijah don nace ki tafi ba har xuciyata nake nufin haka ba amma kika yi wucewarki kika saka ni cikin kunci da damuwa, duniyar tayi min xafi barin idan na tuna baki da kowa, ban yi ma mahaifin ki hallaci ba, but what will someone expect from a frustrated Mother, God knows i was frustrated.... Shi yasa nace ki tafi, amma ban taba tunanin xa ki tafi ba" sakkowa Kasa Umma tayi ta durkusa kusa da khadijah tana kuka tace "Ki gafarceni Khadijah.... Forgive me plss" Khadijah ta daura kanta a kafarta tana kuka sosai cikin rawar murya tace "Umma baki min komai ba, nima ki yafe min, I know i failed you, amma ba laifina bane Umma, ni ban taba iskanci ba, I was raped...." Umma ta dagota ta rungumeta tana controlling nata kukan tace "I thought as much daughter, na yanke hukunci cikin fushi da tashin hankali ne, na yarda da tarbiyar da na baki, Allah ya saka maki koma waye yyi maki wannan aika aikan, shi ma xai ga sakamakonsa tun a nan duniya" Sosai Nanny da jikinta yayi sanyi tayi murnan haduwar Khadijah da ummarta, ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tana gode ma Allah da ya bayyana ma marainiyar ummarta, Shaheedah da duk jikinta yyi sanyi ita ma ta ji dadin reunion din Aminiyar mahaifiyarta da step daughtern ta after three good years. Shaheedah ce ta fita karbo su sudais gun Sadeeq dake mota bai shiga gidan ba, a hankali tace "Dear kaga for ur sake, mama will be happy once again, tayi reuniting da daughter dinta" murmushin karfin hali yyi yace "Sure, but am still confuse ban gane komai a nan ba fa, khadijah dai nasan gidan wan mahaifinta is few houses away from ours, so ban san kuma meye relationship dinta da mama ba" Shaheedah tayi murmushi tace "It's a long story, idan mun koma gida xan baka labarin dear" Sai kusan bayan Isha Sadeeq ya dawo daukan Shaheedah, Khadijah taki yarda Umma ta bi su don gani take kamar baxa ta sake kara ganinta ba. Da daddare suna xaune kan gado wajen karfe daya su Shureim na jikin Umma sun yi bacci, khadijah na bata labarin rayuwar da tayi bayan ta bar gida, tun farkon labarin har ta kawo karshe Umma kuka take, duk jikinta yyi sanyi don ta san duk ita ja ma khadijah duk abinda ya sameta, shiru ta yi tana tunanin me xata ma sudais kuma a ina xa ta gansa, khadijah da ke share hawayen ta cikin raunin murya tace "Umma har yau bai kara dawowa ba, i will never forget him in my life..." Umma ta jawota jiki tace "In sha Allah xai dawo wataran, he will come back to you daughter" Kai kawai khadijah ke gyada mata a xuciyarta tana addu'ar Allah ya gwada mata wannan rana, Umma ta katse silence da ya biyo baya tace "A ranan da kika tafi Khadijah babu inda ban fita nemanki ba tun ina yi da kafa har na koma abun hawa, sai bayan isha na dawo gida a lkcn ina addu'ar Allah yasa kin dawo sai na ga akasin haka, na shiga tashin hankalin da bana fatan in kara shigarsa har karshen rayuwata don nasan baki da kowa Khadijah, Wa ennan makiran dake gidan dama tuni sun sanar ma Alhaji kafin ma in dawo, ina shigowa kuma ya bani takardata kamar jira yake, hakan yasa naji bakin ciki kamar ya kashe ni domin, ce maki nayi ki tafi kar ki kashe min aure duk da bai kai xuciya ba sai gashi sakin ma na walakanci yyi min don ce min yi 1st thing da safe in tattara ina wa ina wa in bar masa gidansa, hakan kuwa aka yi don ban jira gari ya waye ba na fita neman wanda xai siya kayan daki na, ina siyarwa kuma kafin sha biyu na bar masa gidansa, da kudin kayan ba tafi Ethiopia... Bana son in dinga tuna yanayin da na shiga rashin ki Khadijah, ni dai kawai ki gafarce ni domin ni na ja maki komai da ban kai ki gun yakumbo ba da duk hakan bai same ki ba, ita kuma Yakumbo bani da abinda xance a kan ta yanxu domin kuwa ta riga mu gidan gaskiya" Khadijah ta dago da sauri tana kallon Umma tace "Umma yakumbo ta rasu?" Umma tace "Ta rasu kusan shekaru biyu kenan, electric ring ne ya ja ta har lahira, wai ta sa ruwan xafi a daki" jikin khadijah yyi sanyi ta ma rasa abinda xata ce, bayan wani lkci tace "Allah ya ji kanta" Umma tace "Ameen" a hankali khadijah tace "Umma na ki yafe min" sai kusan karfe uku suka kwanta, washegari da safe Umma tayi ma su Sudais da Shureim wanka suka fito parlor, Nanny da ta gama breakfast a kitchen ta fito ta gaida Umma, Umma ta amsa mata da murmushi nan tayi mata godiya kan tsayawa ma khadijah da yan biyun ta da tayi all this while, satin Umma daya a gidan tace ma khadijah xata koma kasar su amma xata dawo, kuka khadijah ta fara yi tace "Umma kina son ki tafi ki kara bari na ne" Umma tace "Noo khadijah xan dawo, ki bari in je in yi sallama da dangina sai in dawo mu xauna, amma fa baxan xauna wannan gidan ba sai dai in kama mana haya a Kaduna, wannan kuma ki rufe masu kawai" a hankali khadijah tace "Kaduna Umma?" Umma tace "Ehh" sauke idonta Kasa tayi bata ce komai ba, Umma tace "Forget ur past Khadijah, life moves on, don wani baxa ki ki xama a garin ba Beside gari me girma ma a ina xaki gansa?" Kai kawai khadijah ta gyada mata, wannan kuma shine mafarin komawarsu Kaduna, suka bar gidan da Sudais ya mallaka ma twins dinta a Abuja, life in Kaduna was smooth for them, sai dai khadijah ta kasa kwantar da hankalinta ta xauna lafiya a garin, ko yaya sai taji abinda ya faru shekaru uku na dawo mata duk da a kinkinau gidan da Umma ta kama masu haya yake, Tunanin da ta kasa cirewa a ranta yasa ciwonta ke yawan tashi wani lkcn har da kwanciya asibiti, hakan ya dinga daga ma umma hankali ta shiga tunanin to wani garin kuma xa su koma, don gaskiya bata son kano, a hankali dai khadijah ta hakura bayan watannin su shidda Kaduna. Kasuwanci sosai Umma ke yi don har Dubai tana fita Allah ya dubeta lkci kankani dukiyarta ya bunkasa, yanda take ji da jikokin nata ko Khadijah bata samu wannan gatan ba, tamkar ta mayar da su ciki take ji, su ma kuma haka suke sonta don ko da yaushe suna manne da ita, duk anguwan babu wanda yasan yaran Khadijah ne yan biyun masu shiga rai duk tunaninsu umma ce ta haifesu Nanny ma na tare da su har lkcn, kuma kusan tare da ita Umma ke fita waje ta xama kamar yar uwarsu, yanxu kam su sudais da baki ya bude basa gudun uwar ta su da suka dauka yayarsu ce Umma kuma Mumynsu, a haka Umma ta yi iya kokarin ganin khadijah ta samu admission a University of Cambridge dake UK, Khadijah bata ji dadi da farko ba ganin pharmacy suka bata don ba shine burin sudais a kan ta ba, amma umma tayi convincing dinta to go for it, shine ta tafi a haka, farkon xuwanta kasar tare da Umma Nanny da yan biyun ta suka taho suka mata sati sannan suka koma nan kuma ta mayar da hankali tana karatu ba ji ba gani domin xama qualified pharmacy, and then..... 1st khaleel ya sa ta gaba a kasar, that not being enough sai gashi ta hadu da wanda bata burin sake gani har karshen rayuwarta, why???? Silence din kusan 3 minutes ne ya biyo baya a parlorn, a hankali Khaleel ya dago kansa yana kallon khadijah da ta hade kanta da gwiwa, har ransa yake jin shesshekar kukanta, gashi ya kasa cewa komai, he is just lost of words, jinginar da kan sa yyi da kujera na kusan minti biyu kafin ya tashi a hankali ya isa gabanta ya duka ya dago kanta yana kallon idanuwanta da suka yi jajir, ta yi saurin sauke idonta daga kallon nasa kwayar idon da su ma suka sauya kamanninsu xuwa ja wasu sabbin hawayen na sakko mata, har lkcn Khaleel ya kasa cewa komai sai kallonta yake, bayan wasu dakiku abinda ya fito bakinsa cikin xaxxakan muryarsa shine "Forget about sudais, he did what he did for the sake of Allah, eraze him of ur mind" Da sauri khadijah ta dago tana kallonsa, ya mike ya koma kujerar da yake xaune yace "Yeah, ki mance da kin ma taba sanin sa a rayuwar ki, I mean that sudais..." Khadijah dake ta kallonsa ko kiftawa babu tayi karfin halin cewa "Ko saboda me?" A takaice yace "Ohk, it seems biyansa abinda ya maki kike son yi kenan?? If that's ur wish kema xaki iya taimakon marayu ai, I see no reason for good six years xa ki dinga tunani daya ba, beside he needs nothing from you, domin Allah yayi kuma Allah ne xai biyasa" Khadijah ta hade rai ta mike tana masa wani kallo tace "I regret telling you who i am, of all my story... part din sudais kadai ka ji da kyau halan? Shi kadai ka iya recalling? I just wasted the time I was suppose to use for sleeping" Daga haka ta nufi daki ta bar masa parlorn tana share hawayen idonta, Khaleel ya bi ta da ido ko kiftawa babu, jinginar da kansa yyi da kujera ya lumshe ido a hankali, wani mugun tausayinta ne ke shigarta, Sudais? Abinda ya fadi kenan a xuciyarsa ya bude ido da sauri, can ya tabe baki ya mike, ya fi minti biyu a tsaye yana kallon agogon dake nuna karfe uku saura kafin ya nufi bedroom dinta, xaune ya ganta kasa ta hade kai da gwiwa, Aliyu ne kawai ya fado xuciyarsa... ya hade hakoransa yana imagination kala kala a xuciyarsa, can yyi wani murmushi ya karasa cikin dakin yana kallonta ya durkusa gabanta, da farko rasa abinda xai ce mata yyi, can a hankali yace "Am sorry Khadijah, you misinterpret what I meant, ur story.... It is just heartbreaking, it's sad... you've past through a lot in life at a very tender age, but am happy you proved to be a strong lady, strong lady indeed...." Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa babu har lkcn ta ki dago kanta, a hankali ya kai hannunsa ya dago ta suna hada ido ta rufe idon, murmushin sa mai kyau yyi yana kallonta, murya can kasa yace "Those cute boys...." Sai kuma yyi shiru, bayan wani lkci yace "You are going no where from UK, Aliyu ne xai bar maki UK ba ke xaki bar masa ba am giving you my words, kina nan har ki gama karatun ki" ta bude idonta a hankali tace "Ae ya riga yasan makarantar, he will surely keep on looking for me" hawaye ne ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Ni ban san me xan masa ba yake nema na" murmushi Khaleel yyi yace "Xai daina neman ki soon" Tana son kallonsa amma idanuwansa are not encouraging, ya lura da haka sai ta basa dariya ya mike yace "Alright then, life moves on, ki kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya hana ki walwala a kasar nan am assuring you, ki tashi kiyi wanka sai kiyi sllh if you wish and then go to bed, the night is far gone" Khadijah dake wasa da fingers dinta tace "But ina son xan je in ga su Umma..." Yace "When?" A hankali tace "Ko gobe" shiru ya d'an yi kafin yace "Alryt then Allah ya kai mu" Ya fi minti uku a tsaye har sai da ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake tayi saurin dauke kanta, yayi murmushi murya can kasa yace "Good nyt" kai ta gyada masa daga haka ya juya ya fita duk jikinsa a sanyaye, she is really a strong lady, yana fita ya kulle mata kofar, haka kawai khadijah taji ta samu relieve sosai don kusan ji tayi babu abinda ke damunta a ranta kuma, tashi tayi a hankali tayi yanda Khaleel ya ce mata, sai kusan karfe uku da rabi bacci me nauyi ya dauketa. Tun da ya fito daki Kanwar Abbansa Hajiya Mariya ke bin sa da kallo, kitchen ya shiga ya fito ya sake shiga ya fito kamar xai koma daki sai kuma ya sake shiga kitchen din sai gashi ya kara fitowa Hajiya Mariya tace "Aliyu" juyawa yyi da sauri yana kallon direction din da take don bai ma san tana wajen ba, har ya iso inda take kallonsa take, ya xauna gefen kujera yace "Na'am mum" da damuwa tace "Aliyu what's wrong with you pls, meye matsalar ka dubi yanda ka lalace, abun har ya kai ya kawo ka fara behaving kamar mara hankali, yanxu meye ma'anar shiga da ficen da kake a kitchen kamar wanda ya xauce" k'asa kallonta yyi ya sunkuyar da kansa, wanda hakan yasa jikinta yyi mugun sanyi, tasowa tayi ta dawo kusa da shi tace "Gaya min abinda ke damun ka Aliyu, you Neva knw if I can be of help, ko baka dauke ni kamar Anty fatima bane" Hawayen da ta gani idonsa ya kara daga mata hankali duk ta rikice tace "Subhanallahi, Aliyu, why the tears, don girman Allah ka gaya min meye ya faru, or have you gone wrong somewhere? Tel me son.." damuwa ce karara dauke fuskarta, ya girgixa kai yace "Just keep on praying for me mum, and... I will be going to Nigeria tomorrow, amma baxan jima ba xan dawo" daga haka ya mike ya bar ta gun xaune ta bi sa da kallo baki bude, tashi tayi ta wuce dakinta ta dau waya ta shiga kiran Mumy, ba a dau lkci ba ta daga bayan sun gaisa da damuwa tace "Anty fatima ni dai ko xa ki kira Aliyu ki ji me ke faruwa wllh gaba daya na rasa gane kansa yana cikin damuwa sosai, yanxu ma da na sa shi gaba sai ya fada min damuwarsa hawaye fa ya fara min kuma ya ki fada, I really don't knw his problem, wllh ko abincin kirki bai ci sai kinga yanda ya rame..." Mumy ta tabe baki tace "Ina ga ke ce baki taba lura ba sai wannan xuwan da yyi maki, amma Aliyu ai ko da yaushe cikin damuwa xa ki gansa, ni na saba ma ganinsa a hakan, ni dai bani da xurfin ciki haka ma mahaifinsa so I don't knw... Shi ya sani, na sha ce masa idan ma wani laifin ya aikata ma Allah yayi ta istigifari, or may be ya ji labarin auren da Abbansa ke shirin masa ne shi yasa hankalinsa ya kara tashi" da mamaki Hajiya Mariya tace "Aure kuma?? Yaushe?" Mumy tace "Yanxu ma shirye shiryen da ake ta yi kenan, idan ya dawo sai ya dau matar su yi ta yawon da yake yi tare, amma kar ki gaya ma sa, shi yasa ma yayan ki bai gaya maki ba, just let him... Kila idan aka yi auren xai dawo hankalinsa" Hajiya Mariya tace "Toh ai ya ma ce min gobe xai tafi Nigeria" Mumy tace "Toh dai dai kenan goben juma'ah dama xa a daura auren ke dai kar ki ma ce masa komai, sai ya xo muna jiransa" jikin Hajiya Mariya yyi sanyi sosai don har ga Allah bata ji dadin jin hakan ba duk da ita ma rashin aurensa na damunta amma aure without his knowledge kuma?? Sallama mumy tayi mata ta katse wayar.Tun da Khadijah ta fito rike da karamar jakarta daga cikin apartment dinta khaleel dake tsaye ya rungume hannunsa ke kallonta cikin bakin glass din idonsa kuma saboda ita ya sa glass din, abaya baki ne jikinta da mayafinsa, sosai kayan ya haska ta daga nisa kamar balarabiya, tana isowa gun da yake ya dauke kansa ya fara tafiya xuwa waje, taxi ya tsayar masu don motarsa na gun wani abokinsa, ya bude mata ta shiga sannan shi ma ya shiga, sai da suka dau hanya yace "Have you call home? I mean kin gaya masu kina tahowa?" Girgixa masa kai tayi, yace "Why?" Kamar xata yi kuka tace "Umma xata iya cewa kar in taho" khaleel ya hade rai yace "Toh tunda haka ne meye amfanin xuwan? Kawai ki fasa, da kin gaya min haka tun a gida ma ni baxan fito ba" Hararansa tayi daga sama har Kasa bata ce komai ba, ya xaro ido daga cikin glass dinsa, kamar me counting words din yace "Did... you... just... eye me?" ta sake juyawa ta maka masa wani hararan tace "You check for your self, kuma ni ban ce dole ka rakani airport ba, xaka iya komawa gida" lkci daya ya xare glass din idonsa suka hada ido, tayi saurin boye fuskarta a kafarta kamar xata yi kuka tace "Bana so" murmushi yyi bai ce komai ba ya mayar da glass din ya shiga danna wayarsa, har suka iso airport bbu wanda yace komai cikinsu sai dai lkci lkci yake satan kallonta, Khadijah ta bude cab din ta fita shima ya fita ta daya side din ya ba mai taxin kudinsa, kallon agogo yayi kafin su shiga airport din, khaleel ne yyi mata komai a airport din tana xaune ya dawo ya xauna gefenta ya mika mata ticket, xaro ido tayi tace "Noo, give me ur account details pls" wani kallo yyi mata yace "Toh Hajiya" daga haka ya dauke kansa, jikinta yyi sanyi bata iya tace komai ba, Wayarta ta ciro a jaka xata tura ma Vanessa text don bata ce mata xata yi tafiya ba, kamar ance ta kalli side dinta ta ga Aliyu xaune though nesa da su yana danna wayarsa, gabanta yyi mugun faduwa.... Lkci daya kuma babu abinda ya fado mata rai sai yan biyunta kamanninsu ya baci ne kawai, xuciyarta ya dinga bugawa ta dauke kai da sauri tana addu'ar Allah yasa ba jirgi daya xa su yi boarding ba, kallonta Khaleel yyi ganin yanda ta matso kusa da shi ba tare da tasan tayi hakan ba, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kai trying to control her self, da wani expression khaleel dake kallonta yace "What?" Ta girgixa masa kai da sauri kuma har lkcn ta ki dago kanta, bata kuma matsa daga kusa da shi ba, duk iya kallon khaleel a wajajen bai ga komai ba sai turawa da few bakaken fata dake wajen, a hankali yace "Khadijah" ta dago da sauri tana kallonsa, yace "What happened?" Girgixa masa kai tayi da sauri, a tsorace tace "I don't knw why I am afraid" ya d'an bude ido yace "Afraid? Of what" ta buda masa hannu kamar xata yi kuka, shiru yyi na few seconds, a hankali taji yace "Ohk shud I accompany you?" Ta dago tana kallonsa, dogon hancinsa da bakinsa kadai take gani banda idanuwansa, samun kanta tayi da gyada masa kai, yace "Ohk then" mikewa yyi ta bi sa da kallo tana boye fuskarta da mayafin jikinta ta saci kallon direction din Aliyu, yanxu ba danna waya yake ba ya dai jinginar da kansa da kujera yana kallon yaran turawa dake tare da uwarsu suna tafiya, da sauri ta dauke kanta. Har suka shiga jirgi Khadijah bata daina shisshge ma Khaleel ba, tayi sa'a kuma seat dinsa kusa da ita, suna keta haxo ta dinga bin jirgin da kallo cikin dubara amma ba ta ga alamar Aliyu ba, bacci ne ya dauketa daga karshe sai dai ta rufe rabin fuskarta da veil dinta, khaleel ya dinga kallonta, ya rasa gane irin tausayin da yake ma khadijah, ya san har ransa kuma he don't knw why, a hankali ta jinginar da kanta a shoulder dinsa, jawota yyi jikinsa ya lumshe idanuwansa, bayan awanni da dama Khadijah ta bude idonta a hankali, kallonsa tayi ta janye jikinta da sauri daga nasa, ya buda manyan idanuwansa yace "Are you hungry?" Ta girgixa masa kai, kamar ance ta kalli gefensu taga Aliyu xaune ya makala earpiece a kunnensa idonsa a lumshe, boye fuskarta tayi jikin khaleel jikinta na bari, khaleel ya riketa da mamaki yace "Are you okay?" Girgixa masa kai tayi a tsorace, bin jirgin ya dinga yi da kallo shi ma, lkci daya idonsa ya sauka kan Aliyu, haka kawai yaji gabansa ya fadi... Ya dinga kallonsa ko kiftawa babu don ko ba a fada ba kawai ya ga shureim da sudais a tattare da shi, lkci daya ya dauke kai, Khadijah da ta rufe fuska ta ki yarda ta kallesa, sauran journey din gaba daya daga ita har khaleel they where uncomfortable, khaleel ya kalli direction din Aliyu ya fi a kirga, gwara Khadijah tayi kokarin ganin bata sake kallon direction din ba, few hours kafin jirginsu ya sauka Abuja Khadijah ta d'an saci kallon gefensu dai dai lkcn da Aliyu ya juyo, hada ido suka yi sai dai fuskarta dama a rufe yake, ji tayi kamar an soka mata mashi a xuciya tayi saurin kauda kanta, shi ko yana ta kallonta bayan wani lkci ya dauke kansa. Har suka yi set down Khadijah ko da wasa ba ta juya kanta ba. Khaleel ya jira mutane suka fara sauka kafin ya mike, ita ma ta tashi da sauri, kamar xata shige jikinsa haka ta dinga bin sa har suka sauka matakalan jirgin, tsaye ta hango Aliyu nesa da jirgin yana kallonsu bayan shi ya sauka, taji kafafuwarta sun kasa daukar ta don tasan kila ya ganeta ne, har suka sauka Khaleel bai gansa ba don wani abokin sa bature ya dauke hankalinsa suna gaisawa, Aliyu dake ta kallon idanuwan khadijah da su kadai yake iya gani ya nufo ta, dai dai gabanta ya tsaya lkci daya ya fixge veil din fuskarta yana kallonta, rikicewa tayi, khaleel ya juya da sauri, ganin abinda Aliyu yyi ya cakumosa cikin tsawa yana masa wani mugun kallo yace "How dare you?" Daga sama har kasa Aliyu ke kallon Khaleel da ya ki sake sa, Aliyu ya dake yace "Who are you?" khadijah na ganin haka a rikice ta ajiye jakar hannunta tace "Noo plss Dr ka kyale shi..." Khaleel na kallon kwayar idon Aliyu strictly yace "Stay away from her or else you regret it...." Yana fadin haka ya sakesa, Aliyu yyi wani murmushi yace "And who are you to tell me that? Her boyfriend? Husband or??" Juyowa khaleel yyi a mugun fusace ya sake cakumosa Aliyu ma ya cakumesa yana mayar masa da irin kallon da yake masa, khaleel yace "Both! Husband and boyfriend" dariya Aliyu yyi yace "You are very very stupid, idan ma mijinta ne kai ka shirya rabuwa da ita domin kuwa she is not meant for you" Khadijah na ganin abun ya kai haka ta shiga tsakaninsu da sauri cikin kuka tace "Wayyo na shiga uku, don Allah don annabi ku rufa min asiri ku yi hakuri" tayi facing din khaleel dake hade fist dinsa yana ma Aliyu wani irin kallo ta rikesa hawaye na sakko mata tace "Plss am begging you ka kyale sa don Allah Dr" lkci daya khaleel ya sake Aliyu ya kama hannunta ya dau jakarta, Aliyu ya fiddo complimentary card dinsa a aljihu ya saka a na Khaleel yana kallon kwayar idonsa yace "I will be waiting for ur call young man" still khaleel yyi kamar xai cire ya jefar sai kuma ya bari ya juya kamar xai tashi sama ya bar wajen Khadijah ta dinga bin sa xuciyarta na bugawa, Aliyu ya bi su da kallo yana murmushi a hankali yace "I will surely get you soon Iman, not when I have set my eyes on you" ta waigo ta kallesa tayi saurin dauke kai, har suka shiga cab Khadijah waigawa take taga ko ya biyo su, sai dai ta kasa ganewa don mutane ne da yawa ko ganinsa bata sake yi ba, duk ta kasa samun nutsuwa, tana kallon Khaleel da har sannan fuskarsa ke a daure kamar xata yi kuka tace "Plss Dr kar ka sake kulasa" Kallonta khaleel yyi a fusace xuciyarsa na heaving yace "That's idan bai shiga rayuwar ki ba, Billah xan iya yi masa komai, I don't care... Ina da wanda ya tsaya min a kasar nan, look... my father...." Sai kuma yyi shiru, lkci daya idanuwansa suka canxa kamanni, Khadijah jikinta yyi sanyi sosai, muryar khaleel ne ya dawo da ita tunanin da ta tafi, cikin sanyayyan muryarsa yace "Don't forget this is Abuja, ina xa mu? Thinking Kaduna kika ce min Umma take" A hankali tace "Dole sai mun bi train xuwa Kaduna" yace "Why not flight" ta hararesa tace "Bayan mun baro airport din, kawai kaje xaka tara mana crowd a airport ko meye na kulasa" bai ce komai ba sai kallon tagar taxin yake, khadijah ta sanar ma mai taxin train station xai kai su, Tsaki taji khaleel ya ja yace "Seriously It's being long aka ba ta min rai haka... Da ba don airport bane we ought have teach each other a lesson da guy din nan, I don't even care about d securities there..." Khadijah dai sai kallonsa take ganin how serious he was, Juyowa yyi ya kalleta tayi saurin dauke kanta, murya can kasa yace "It's because of you khadijah, don ke na kyalesa da mun yi karamin exercise a wajen nan" ta tabe baki tace "Ni dai babu ruwana" yayi murmushi da ya bayyana dimples dinsa yace "Billah ke kuwa ke da ruwa baby" kallonsa tayi da sauri, ya tsuke fuska kamar ba shi ya fada ba ya fiddo wayarsa yana dannawa, tayi murmushi tana ci gaba da kallon waje, suna isa station suka samu jirgin kasa mai xuwa Kaduna, Khaleel ya yankar masu ticket, sai da jirgin ya tashi khadijah ta kallesa tace "Are you a Nigerian" kallonta yyi, ta sauke idonta, yyi murmushi yace "Sure, A Nigerian... From Kaduna also, why do you ask, ko ban yi kama da ku ba ne" bata ce komai ba, shima bai ce komai ba, bayan few hours suka isa station din train dake kaduna, Napep suka dauka da xai kai su har gida, Yace "Do I have to accompany you har kofar gida" Khadijah ta kallesa sannan ta sa mai Napep ya tsaya tace "Sauka toh ka hau wani adai daitan ka tafi gidan ku" wara ido yyi yace "Like serious??" Ta langwabar da kai tace "Sure" murmushi yyi ya sauka yace "Ohk then" tace "Yeah, thanks" daga haka ta sa mai Napep din ya wuce khaleel ya bi su da kallo. Khadijah na isa gida ta sauka ta bude Jakarta, tunawa tayi ba kudi wajenta ta basa hakuri tace bari ta amso a ciki sannan ta shiga gida, sudais da shureim ne parlor suna kallon cartoon, suna ganinta suka mike a guje suka yi kanta suna mata oyoyo ta rungumesu gaba daya cike da murnan ganin yan biyunta, Umma dake kitchen ta fito da mamaki tana kallonta, da kyar ta yakice yaran a jikinta ta nufi Umma ta rungumeta tace "Ummata na dawo" Umma na kallonta tace "What happened Khadijah??" Ta marairaice tace "Umma ina missing din ku ne na taho fa" Umma ta hade rai tace "Kina da hankali kuwa, kamar warce xata taho daga kano, yaushe kika koma da har xaki taho yanxu" shiru ta yi bata ce komai ba, Umma ta saki baki tana kallonta a mamaki, juyawa khadijah tayi ta nufi jakar Umma dake ajiye parlorn ta bude ta fiddo kudi tace "Umma bari in kai ma mai adai daita" daga haka ta fita ta kai ma sa kudin sa twins dinta na rike da ita, suna dawowa parlor duk suka haye kanta Shureim yace "Anty ina wannan uncle din nan dake UK, did he tell you to greet us?" Khadijah tayi murmushi tace "Sure sweetheart" Sudais yace "Anty is he also from Nigeria, I like him" Umma dake kallonsu tace "Wani uncle suke fadi?" Khadijah ta saci kallonta tace "Neighbor dina ne fa Umma" Umma tace "Ba mace bace kwanaki da muka je?" Khadijah tace "Ayya, Nancy ai ta tashi" Shiru Umma tayi kafin tace "Toh dai a kula, Allah ya ci gaba da tsare ku" A hankali khadijah tace "Ameen" Umma tace "Toh don me wai baxa ku xauna tare da Vanessa ba?" Khadijah tace "Umma am nt comfortable a gidanta ne" Umma tace "You have no choice, bana son xaman ki gida daya da namiji" da sauri khadijah ta kalleta, murmushi tayi tace "Umma he is a Nigerian, kuma I think bahaushe" Umma tace "So?" Shiru Khadijah tayi, Dai dai nan wayar dake jakarta ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo tunawa da tayi wayar khaleel ne, shiru ta yi tana kallon number kafin ta daga, muryarsa taji yace "Are you home?" Ta saci kallon Umma Kafin ta mike tace "Uhn" daga haka ta wuce daki yaranta suka bi bayanta Umma ta bi su da kallo. Flight Aliyu ya bi ya taho kaduna, Ji yayi gaba daya ba wani sauran damuwa a tare da shi, lkci lkci sai yyi murmushi, har ya isa gida a taxi tunanin Khadijah yake, he is just happy seeing her today, bayan ya sauka taxi mamakin me ake yi a gidan ya dinga yi ganin mutane da manyan motoci har su Usman da Sanusi shadda ce sabuwa jikinsu, suna ganinsa suka washe baki suna masa sannu da dawowa, ya amsa gaisuwarsu ya entrance din gidan, ganin takalma da yawa alamar mutane ne sosai parlorn ya xaga ta baya, iklima ce bakin tap a durkushe tana kwarara amai, ya karasa yana kallonta ganin uban kunshin da aka mata ga kitso an yaryara mata a kai, yace "Baki da lafiya ne?" Jin muryarsa ta dago da sauri, lkci daya ta mayar da kanta ta sunkuyar, tana maida numfashi da kyar tace "Sannu da dawowa yaya Aliyu" bai damu da ya amsa ba yace "Me ake yi a gidan nan?" Shiru tayi da farko kafin tace "Aurenmu" Few seconds yyi amfani da wajen apprehending abinda ta fada, cike da confusion yace "Aurenmu? Aurenmu da wa?" Still bata kallesa ba tace "Ni da kai" bude baki yyi yana kallonta dai dai fitowar Anty khadijah tayi wani shegen haske ta xama katuwar gaske, tana ganinsa ta saki guda tace "Saukar yaushe ango?" Aliyu na xaro ido yace "Anty ban gane ba, ango kuma?" Anty khadijah na taunar cingam da ya cika waje da kara tace "Tafi Anty fati na daki xata maka bayani yanda xaka gane my son" daga haka ta nufi 'yar ta tace "Ki taso mu je, mai make up din ta gaji da jira" janta tayi suka Wuce ciki suka bar Aliyu tsaye baki bude, har lkcn shi dai bai fahimci komai ba. Wucewa ciki yyi direct ya tafi sama Dakin Mumy ba tare da ya kula da mutanen dake parlor ba, ita da frnds dinta sai mahaifiyar Abbansa da suke kira da yaya ne xaune dakin, yyi hankalin gaishesu kafin yace "Mumy I don't get what's happening in this house" Yaya tace "Bikin ku ake yi da 'yar uwar ka" Aliyu ya yo waje da ido yace "Wace yar uwar tawa?" Yaya tace "Iklima, Allah bai yi da Hanan ba" Wani kallo Aliyu ya dinga yi mata kafin yace "Allah ya kiyaye, wace iklimar? Iklima da ta gagari kowa gidan nan xa a makala min, No Mumy I have never failed you but... No mum me yasa xaki min xabin da xai cutar da ni, mumy kema kinsan iklima ta fi karfina, Mumy ki rufa min asiri..." Tsawa Mumy tayi masa ta mike tana masa wani mugun kallo tace "Get out Abuturrab, idan an kai ma iklima gidan ka kayi gunduwa gunduwa da namanta ko kuma ka koro mana ita, fita nace" Juyawa Aliyu yyi ya fice daga dakin, Yaya tace "Fatima, da gaske yarinyar ta gagari kowa? Ni dai an san ba saninta nayi ba, kar ku cutar min jika" Mumy ta hade rai tace "Yaya yar yar uwata ce uwa daya uba daya fa" tana fadin haka ta fita dakin, kawayenta suka bi ta da kallo. Washegari da yamma khadijah na xaune parlor tare Umma da Nanny dake yankan alaiyahu, reading material dinta ne hannunta tana dubawa, Umma tace "Wai da wa su sudais ke waya haka ne tun daxu Khadijah?" Khadijah ta dago kanta tana kallonta a hankli tace "Umma wani ne" Umma tace "A ina kika san sa? Ko in ce a ina suka san sa" Murmushi kawai khadijah tayi bata dai ce komai ba, jin little sudais na kiranta ta juya tana kallon direction din dakin sai ga shi tare da d'an uwansa, wayar hannunsa ya mika mata yace "Uncle yace we shud hand over the phone to you" Khadijah ta amshi wayar tana satan kallon Umma dake kallonsu ta mike ta wuce daki, rufe kofar dakin tayi ta xauna gefen gado ta kai wayar kunne tace "Yes? Ina ji" Yace "Yea I knw kina ji, can I come over to see d boys now?" Shiru Khadijah tayi tana kallon agogo kafin tace "Xan gaya ma Umma tukun" yace "Alryt then, I will be waiting for ur call" a hankali tace "Tohm" daga haka ya katse wayar, tunanin me xata ce ma Umma ta dinga yi kafin ta mike ta fita, xauna gefen kujera tayi murya can kasa tace "Umma someone is coming over now" Umma ta daga kai ta kalleta tace "Who?" Ta d'an turo baki tace "Wani ne" murmushi Umma tayi tace "Allah kawo sa" khadijah ta mike ta koma daki, text ta tura ma khaleel na address din unguwarsu da house number. Cikin minti talatin khaleel ya iso gidan, Khadijah ta sa Hijab ta fito daga dakinta ta shiga na umma tana kallonta tace "Umma yana waje" Umma tace "A wajen xa ki bar sa baxai shigo ba" murmushi kawai khadijah tayi ta fita, tun da ta fito gate take kallon motar da khaleel ya xo da shi har ta isa gun motar ta tsaya tana wasa da fingers dinta, bude motar yyi ya fito ya xaga ta inda take, farar gizna ne jikinsa sai walkiya yake da hula, wani kyau yyi na musamman ya dawo kamar balarabe cikin shigar hausawa, Ita dai bata taba ganinsa da irin shigar ba ta dauke kai daga kallonsa tace "Dama kana sa manyan kaya?" Ya d'an bude ido ya rungume hannunsa ya jingina da motar yace "Dama kina sa Hijab?" Dariya ya bata amma bata yi ba tace "Aa sai kananun kaya in yi sagging wandon" xaro ido khaleel yyi yana kallonta, tayi murmushi bata kalli direction din sa ba, Kallonta ya tsaya yi na few seconds kafin yace "Where are the boys?" Tace "Suna ciki" yace "Amma kin san ba wajen ki na xo ba dai koh" shiru ta yi trying her best not to look at him, can tayi murmushi tace "Alryt then" daga haka ta nufi gate, Wara ido yayi yace "Khadijah" sai da ta isa gate tace "Bari in turo maka su" yace "Wait..." Amma tuni ta shige gidan, murmushi yyi yana shafa beard dinsa, ba a dau lkci ba sai ga yaran sun fito suna ganinsa suka taho da gudu suka rungumesa ya daga su sama gaba daya happy seeing them, kai kana ganin yaran kasan su ma ba karamin farin cikin ganin khaleel suka yi ba, ya bude back seat din motar ya sa suka shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, wayar sa ya dauka ya shiga kiran Khadijah, kin dauka tayi yayi murmushi ya tada motar ya bar layin da yaran. Tun da Aliyu ya dawo masallaci da asuba ya sa makulli dakinsa, shi dai ya kasa gaskata wai iklima aka aura masa, yarinyar da idan ta fita tun safe sai dare wani lkcn xata dawo gida, uwar kuma tace gidan kawunta take xuwa, yau idan ka ga wannan wayar hannun iklima to gobe wani daban xa ka gani, islamiyyar ta ki xuwa, bokon kuma anyi withdrawing, rike kansa yyi xuciyarsa na masa kunna, kwankwasa kofar dakinsa aka yi for the countless time, ko kallon direction din kofar bai yi ba, "Yaya nice baby ka bude plss" muryar da ya ji kenan, ya lumshe idanuwansa ya bude, mikewa yyi da kyar ya nufi kofar ya bude yana kallon Kanwar tasa, ta shigo ya rufe kofar, da damuwa tace "Yayanmu kayi hakuri, I don't knw what came over Mumy, bn san me yasa tayi haka ba bayan ita da kanta kullum complain take a kan iklima... Her character is so obvious to everyone, kowa yasan abinda take but mumy tayi kamar bata sani ba ta hada ku...." Aliyu ya xauna gefen gado ya rike kansa, Baby tayi tagumi tana kallonsa, bayan kusan minti goma tace "Kayi hakuri yaya" ya dago da jajayen idanuwansa yana kallonta yace "Go make me a cup of coffee" Baby na fita daga dakin dai dai fitowar Anty khadijah da ke ta kai kawo kamar warce tayi ma sarki karya, barin da taga Aliyu ya bude ma Kanwar tasa kofa, xuwa yanxu gidan ya watse sai yan uwa na jini, bin baby tayi downstairs tace "Takwara me Aliyun yace maki?" Baby taki kallonta tace "Abu yace in kai ma sa" Anty khadijah dake ta bin ta tace "Me kenan?" Baby tace "Coffee" Anty khadijah tace "Atoh ni har na gaji da maganar bai ci komai ba tun daxu, yanxu abinda xa ayi kawai kiyi wucewar ki xan hada masa in ba matarsa ta kai ma sa, mutum ya sha hanya haka kuma ya makale daki tun jiya babu abinci" Baby tace "Anty amma ai baki san yanda yake son coffee dinsa ba, ni xan masa" Anty khadijah ta galla mata harara tace "Toh uwar iyayi, kin tashi gabana ko sai na mare ki, idan nayi masa kar ya sha" daga haka ta wuce kitchen baby ta bi ta da wani kallo, Anty khadijah na shiga kitchen ta tura kofar kitchen din ta rufe ta yi saurin ciro wani kulli a bra dinta, "Son da xai mata sai ya fi wanda yake ma uwarsa da kowa na duniya... In dai ya sha maganin nan" muryar gardin da ya bata maganin kenan ke kai kawo a kunnen Anty khadijah kamar yana kusa da ita, har wani rawa hannunta yake ta juye gaba daya a cup sannan ta debi coffee powder ta xuba a kai ta xuba ruwan xafi ta jefa kwayan sugar biyu, sama ta tafi da sauri ta shiga daki gun iklima dake kwance, Anty khadijah tace "Ni fa dadina dake shegen son jiki, daga d'an xaxxabi dubi yanda kika wani yi laushi kamar warce tayi watanni ba lafiya, a haka xa a kai ki gidan Aliyun gobe" Iklima da ta lullebe da bargo tace "Ni wallahi ki rabu da ni don ba ke ce ke jin abinda nake ji ba, duk kin bi kin dame ni tun daxu" Anty khadijah tace "To uwata sai ki rufe ni da duka ai, ni ki tashi ki kai ma Aliyun coffee" iklima ta xaro ido tace "kaji ta, Salon ya koro ni.... Mutumin da tun jiya yake daki" Anty khadijah tace "Toh don ubansa ba sai ya koro ki ba, kilan ma a can xa ki kwana ki tashi kina bata lkci..." Gun kayan kwalliyan Iklima na amarya Anty khadijah ta nufa ta dauko wani turare can kasa a karamin kwalba ta bude ta shashshafa mata a ko ina na jikinta, iklima da ke ta wani yatsine fuska ta koma ta kwanta tace "Mama wllh jiri nake gani, anya xan iya fita" hararata Anty khadijah tayi tace "Xan je in dauko maki shayin a dai don ki fita nan ki shiga dakinsa baxa ki ce min baxa ki iya ba" daga haka ta wuce kitchen ta dauko coffeen dake rufe a mug ta kawo ma iklima, da kyar ta tashi ta karba tana duddukawa ta fita dakin, a hankali ta tura kofar dakin Aliyu dake kwance ta shiga ta rufe Ta isa kusa da gadon ta ajiye mug din hannunta a kasa, bude ido Aliyu yyi jin yanda kamshi ya bade dakin suka hada ido da iklima, karasowa kusa da shi tayi tace "Yayanmu sannu da hanya ga coffee din na maka" Wani mugun kallo Aliyu ya dinga mata yace "Kina hauka ne xa ki shigo min daki" tace "Da daban xama matar ka ba ina shigowa ne" bude kofar dakin aka yi sai ga baby ta shigo sau daya ta kalli iklima ta harareta ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tace "Ga abinci yaya mumy tace in dibar maka" daga haka ta bude warmer din abincin iklima ta yamutse fuska ta dauke kai da sauri, lkci daya aroma din abincin ya cika dakin, da tari ta fara, sai kuma ta toshe baki, da gudu ta mike kafin ta isa kofar bathroom ta wanke tiles din dakin da amai, kallonta Aliyu yake ko kiftawa babu ta dinga amai kamar xata shide, baby ma sai kallonta take, tashi yyi ya isa gabanta da wani expression yana kallon gaba daya jikinta, mikewa tayi bayan ta gama ta fada kan gado tana sauke numfashi ya koma kusa da ita yana kare mata kallo da kyau, squeezing fuskarsa yyi yace "What??" Lkci daya ya juya ya fice baby ta bi bayansa da sauri, Mumy na haurowa sama tare da Anty khadijah dake bata shawarar kawai gobe su Aliyu su wuce gidansu yau dai su kwana a gidan, ganin Aliyu Mumy ta daure fuska don tun daxu yaki fitowa har ita ta yi masa magana amma ya ki bude kofar, yana kallon mumy cikin wani yanayi yace "Mumy ita mai cikin xa ku ce kun aura min?" Kallonsa Mumy ta tsaya yi cikin rashin fahimta haka ma Anty khadijah, baby dake tsaye gun ta xaro ido tana kallonsa, Da mugun mamaki Mumy tace "Halan Aliyu ya fara xarewa ne ni Fatima?" Yace "Xarewa kuma Mumy wllh ciki ne da iklima, don't forget my profession idan ma baku yarda ba yanxu sai a kira wani likitan, gashi can yanxu ma amai ta gama yi" Anty khadijah ta saki ta salati ta fashe da kuka tace "Aliyu, ita yar tawa xaka ma wannan gagarumin sharrin don a rufa ma asiri an aura mata kai? Ita iklimar ce ke da ciki?" Aliyu ya mata wani kallo yace "Sharri Anty? sai a tafi asibiti yanxu ai, ni dama nasan a day like this na nan xuwa very soon, ina ce har guest lodge na taba ganin iklima na same ki daki na gaya maki few years back, me kika ce min then? Cewa kika yi na tsaneta na sa mata ido, Duk yawon da take ta kai dare kin taba tsawata mata, of course no sai dai kice gidan kawunta taje, so it's nt a thing to be surprise don iklima na dauke da ciki ynxu" tuni sauran yan biki dake gidan suka shiga fitowa corridor din, Mumy dai ta saki baki ta kasa cewa komai, Anty khadijah dake ta xufa tace "Tunda abun yar tone tone ne sai mu yi ta ai Aliyu, wato har kai kana da bakin da xaka bude ka kira 'ya ta yar iska ka mance lkcn da kake tashan naka iskancin, ka mance irin yanda kayi ma yar mutane fyade a cikin gidan nan, wanda ta dalilinka ta bar gidan har yau bata dawo ba, duk ka xata ban sani ba koh???" Lkci daya komai na Aliyu yyi still ya tsaya kallonta ko kiftawa babu, Anty khadijah ta juya tana kallon mumy tace "khadijah dai da kika sani, yarinyar da kika dau aiki ta yi wucewarta ko sallama babu shekaru kusan shidda baya, ya fada maki abinda yyi mata ta bar gidan da bakin sa yau...." Aliyu ya lumshe idanuwansa da suka kada lkci daya ya ji kansa na sara masa, kallonsa mumy ta dinga yi kamar idonta xai fito haka kanninsa gaba daya da bak'in da suka fiffito, Anty khadijah na girgixa kugu tace "Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka?" Bude ido yyi da kyar yana kallon Mumy. Anty khadijah na kallon Aliyu da kyau tace "Ko baxa kayi bayanin ba in taya ka ne dakta?" Bude ido Aliyu yyi da kyar yana kallonta, lkci daya idanuwan Mumy suka kawo ruwa kana ganinta kasan ba karamin shock ta shiga ba, Aliyu ya isa gabanta ya duka kan gwiwowinsa cikin sanyin murya yace "Mumy..." Dakatar da shi tayi hawayen idonta na sakkowa tace "Irin tarbiyar da nayi maka kenan Aliyu.... Yanxu yar mutanen kayi ma haka?" Ya rufe fuskarsa jikin kafarta cikin rawar murya yace "That's the greatest mistake of my life mum, shine abinda na kasa gaya maki shekaru shiddah kenan, mumy ba halina bane kema kin sani, ban san ya aka yi ba ranan, it look as if I was possessed, I ruin the little girl... Mumy I...." Kasa ci gaba yyi hawaye na sakko masa, Anty khadijah ta tabe baki tace "Lallai Abuturrab baka jin kunyar karya? abu ya faru ba sau daya ba ba sau biyu ba ka kirasa mistake? Tunda abun ba arxiki har ya kai ga ka fara yi ma 'ya ta sharri to wllh nima baxan duba abinda ke tsakanina da mahaifiyar ka ba, gwara in tona maka asiri, idan ni baka ji kunyar toxarta ni da iklima ba to nima baxan ji kunyar ramawa ba a matsayin ka na d'an yayata" daga haka ta bar wajen ta shige daki... Aliyu ya bi ta da kallo, duk abun nan da take fada fa ba ji yake ba mamakinsa shine ya aka yi tasan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah bayan bata gida ranan, how is that? Fitowa Anty khadijah tayi daga dakin rike da iklima da ta sa ma Hijab suka sauka downstairs kamar xata tashi sama tana matsar kwalla tace "Da raina kayi ma yar cikina irin wnn sharrin koh Aliyu, duk matsayina gun uwarka baka gani ba saboda na rufa maka asiri da yawace yawacen da kake nace a aura maka 'ya ta shine xaka mana wannan cin mutuncin ka saka min da sharri" gidan ta bari gaba daya tare da yar ta, Mumy ta juya ta koma dakinta a sanyaye, Aliyu ya kasa daga kai ya kalli kanninsa da sauran relatives dake wajen. Anty khadijah na fita da kafa suka karasa bakin titi da iklima, hankali tashe take tambayarta yaushe rabon da ta ga al'adarta, iklima ta turo baki tace "Oho nima ban sani ba" dundu ta kai mata tace "Kaji min shegiya wai baki sani ba, ni nake maki al'adar? To wllh sai dai ki daura ma ubanki hawan jini ba ni ba, mu je asibitin ai xa su mana bayani a can, in ma ya kama in kashe ni Wllh sai in kashe Ki a can din, tunda duk abinda nake maki bakya gani ni xaki ja ma abun kunya ni xaki kunyata a idon duniya" Ganin sun shiga Napep yasa Anty Khadijah tayi shiru sai girgixa kafa take tana Allah Allah ta ganta a asibiti har suka isa asibitin dai, iklima kam ko dar sai ma gyangyadi da take ta yi a napep din, suna shiga asibitin likita ya tabbatar ciki gare iklima, Anty khadijah ta daura hannu a ka tana xaro ido tace "Na shiga uku na lalace ni Khadijah, iklima yanxu ni xa ki ma haka, a ina kika je aka maki ciki, don na sake maki sai ki tona min asiri iklima? Ni xa ki kunyata?" Shi dai likitan kallonsu kawai yake, Anty khadijah ta share xufar dake keto mata ta hadiye yawu da kyar tace "Likita ko nawa kake bukata ka fada xan baka ka raba ta da wannan bala'in dake tare da ita ka rufa mana asiri" likitan yace "A'a ba ma haka a nan Hajiya ku yi hakuri, ku je wani asibitin..." Anty khadijah ta fashe da kuka a karo na farko tace "Haba bawan Allah, kai baka taimako ne, wllh dariya xa a mana ka rufa min asiri ina da makiya da yawa duniyar nan, ka ji tausayina ka taimaka mani" Likitan yace "Wato kin fi so kiji kunyar lahira a kan ta duniya kenan Hajiya?" Da sauri Anty khadijah tace "Eh wllh" sake baki yyi yana kallonta, can ya gyada kai yace "Gaskiya ne, toh Allah ya shirye ku, kuyi hakuri ku fita akwai patients da xan yi attending ma yanxu, mu ba ma aborting ciki a nan" tashi Anty khadijah tayi tana masa matsiyacin kallo tace "Yanda ka ki taimakona kai ma haka yar ka xata jajibo maka abun kunya ka rasa madafa in sha Allah, mara imani kawai..." daga haka ta ja Iklima kamar xata tashi sama suka fita, haka Anty khadijah suka dinga yawo hospitals tana neman inda xa a cire ma iklima ciki har dai ta samu wani da kyar, kudi ba na wasa ba ta bada aka yi aikin, unconsciously ta tafi da iklima gidan wata da suka hadu a kauyen da take yawan xuwa suka kulla abota suke kawance kamar xa su hadiye juna, kwanan matar uku gidansu Aliyu lkcn biki, jiya ta baro gidan bayan an gama komai ba rabon xa ayi komai a gabanta, Hajiya Laure sai kallon iklima dake kwance take da mamaki bayan Anty khadijah ta mata bayanin komai tana matsar kwalla, can Hajiya Laure ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ai baki ga ta kuka ba Hajiya Khadijah neman mafita xa ayi, yanxu dai a takaice bbu auren kenan?" Anty khadijah ta tsayar da kukan da take da sauri tace "Aure kai, aure na nan daram dam ba inda ya je, ai ko hauka nake baxan ce masu cikin ne ba har an cire, nunawa xan yi kawai gidan ki na kawota da xuciya ta debeni" Hajiya Laure tace "Gaskiya ne, toh wai kin ma yi yanda aka ce maki wajen nan da muka je ranan kuwa?" Anty khadijah tace "Ba gashi nan ta sa nayi asara ba yanxu don nasan ba sha xai yi ba, ni wllh da tun kafin bikin nasan da shegen cikin nan da na je an cire, sai ma kin ga ko gama xama halitta cikin bai yi ba, a can wani gutter na jefar kafin mu shigo nan don likitan cewa yyi mu tafi da shi kar mu ja masa matsala" Hajiya Laure tace "Alhmdllh da abun ya xo a haka ba sai da aka kai ta gidansa ba, amma shi ma dai ya aka yi har yasan tana dauke da cikin?" Anty khadijah tace "Toh ai likita ne shi din" Hajiya Laure ta xaro ido tace "Kai haba, to yanxu baxai gane cirewa aka yi ba?" Anty khadijah tace "Yo ya gane mana ai wllh sai yyi xaman aure da 'ya ta ko ya ki ko ya so, sai ya xauna da ita don ubansa" Hajiya Laure tace "Toh kuma har yanxu uwar ta sa ba ta kira ki ba?" Anty khadijah tace "Tana can na tara mata xafi, ina labarin da na taba baki a kan wata yarinya da ta taba dauka da dadewa??" Hajiya Laure tace "Eh, eh na tuna, wannan dai da kika ce a sunan me aiki ta dauketa, da kika sa Aliyu ya lalata ta" Anty khadijah tace "Yauwa er gari ita, Toh yau dai na tona abinda Aliyun yyi mata, tunda nima tonan asirin ya min, suna can na bar su ban san ya ake ciki ba" Hajiya Laure ta kyalkyale da dariya tace "Amma baki da kirki Khadijah, Toh amma baki tunanin uwar na iya neman yarinyar yanxu ko ta sa ya nemo ta? kin fa ce min sonta take kamar ita ta haifeta" shiru Anty khadijah tayi da wani irin shock baki bude tana kallonta, salati ta sake daga karshe tace "you have a point, wllh Anty fati xata aikata, wannan shine anyi ba ayi ba, xama bai gan ni ba laure bari in koma gidan ayi komai a gabana, xan bar iklima nan ki sa mata ido don Allah" daga haka ta mike ta suri jakarta har tana tuntube ta fice dakin Laure na cewa tayi a hankali. Aliyu ya kusa awa daya tsaye bayan ya koma dakinsa, gaba daya a sanyaye yake bai san ta ina xai fara ba, bai san me xai ce ma Mumy ba, hakan yasa hawaye ya kawo idonsa tunda yake bai taba jin tsanar Anty khadijah ba sai ranan a ransa, dama tasan abinda ya faru tsakaninsa da Iman, then how? Bayan bata gidan abun ya faru, ranan daga shi sai Iman ne a gidan, kofa ya nufa daga karshe gwiwowinsa a sake ya shiga dakin Mumy, ita da aminiyarta Hajiya Balaraba ne a dakin, Mumy tayi tagumi kana ganinta kasan ta yi kuka ne sosai, tun da ya shigo Hajiya balaraba ke kallonsa, ya kasa kallon su ya isa gaban mumy a sanyaye ya duka cikin raunin murya yace "Mumy don girman Allah kiyi hakuri ki gafarce ni, i knw you Neva expect such, but... Mumy ban san ya aka yi ba ni ba halina bane, har yau ban san ya aka yi hakan ba kuma na kasa samun natsuwa, for the past 5 years neman Iman nake...." Katse sa Mumy tayi tace "Kake neman ta tayi maka me, dama kai ka sa yarinyar ta bar gidan nan Aliyu?" Ya kasa dago kansa a hankali yace "Mumy I was confused, I was thinking that's the only way out for me... I was restless staying under the same roof with her, mumy nasan na cuceta, amma ni nasan ba yin kai na bane don ba halina bane..." kasa ci gaba yyi sbda cracking da muryarsa ya shiga yi ya hade kansa da gado, Bude kofar dakin aka yi Anty khadijah ta shigo, Mumy ta goge hawayen idonta ta daga kai tana kallonta, Anty balaraba ta tabe baki ta dauke kai, karasowa Anty khadijah tayi ta xauna gefen gado ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Yanxu Anty fati ki ji kaxafin da Aliyu yyi ma iklima amma ke abinda ya dame ki daban? Did i and my daughter deserve this" Mumy tace "Ki rabu da ni Khadijah, ki fita ki ban waje, ba don ba don ba wllh yau sai in ce ke din makiyiya ta ce, bakya so na, baki daukeni yar uwar da muka fito ciki daya ba" Mumy na magana ne tana kuka, Aliyu ya mike ya nufi kofa, Sai da ya isa bakin kofa ya juya yana kallon Mumy cikin sanyin murya yace "Na maki alkawarin xan nemo Iman in sha Allah mum, I will repair the damage I made in sha Allah" Mumy ta masa wani mugun kallo tace "And how are you to repair the damage?" Kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace "By marrying her in sha Allah" Girgixa kai mumy tayi tana wani murmushi tace "Noo, babu aure tsakaninka da ita, xaka iya aikata komai domin ta yafe maka idan ta ga xata iya amma banda aure, babu aure tsakaninku, and I told you that long ago, I have my reasons, leave kar ka ci gaba da bata min rai, get out Aliyu" shiru Aliyu yyi yana kallon Mumy a sanyaye, Anty khadijah ta sauke wani ajiyar xuciya tana hamdala a ranta. Tun Khadijah na daurewa ganin twins dinta shiru har dauriyar ya fara karewa, da farko Umma na ta tambayarta inda suka je ita ma ta hakura ta daina ganin ta ki fada sai cewa take yanxu xa su dawo, khadijah ta shiga daki daga karshe ganin har anyi magrib ta dau wayarta ta shiga kiran khaleel da layin da ya kirata daxu, har ya katse bai daga ba, sai da ta kira kusan sau uku ya dauka yace "Uhn me yara to, ki ma cire ran ganinsu yau" xaro ido tayi tace "This is after seven plss..." Ya katse ta yace "Toh ki taho ki daukesu, I can give you the address" daga haka ya kashe wayar, ji tayi hankalinta ya tashi lkci daya hawaye ya kawo idonta, ta sake kiransa bai dauka ba, ta kira yyi sau hudu kafin ya daga, cikin rawar murya tace "Don Allah ka dawo da su dare yyi, Umma ce fa ke ta tambayarsu" Yace "Hmm toh naji" kashe wayar yyi ta xauna bakin gado a sanyaye. Bayan kusan minti talatin khadijah dake ta xaune daki hankalinta ya ki kwanciya ta kalli wayarta da sauri jin yana ring, ganin khaleel ne ta mike ta sa Hijab ta fita tana addu'ar Allah ya sa twins din ya dawo da, Nanny kadai ce parlor ta ce mata tana xuwa sannan ta fita waje, hade rai tayi dai dai lkcn da su shureim suka sakko daga cikin motar ko wannensu rike da leda khaleel ma ya fito, rungumeta suka yi gaba daya cike da farin cikin ganinta, fuskarta daure tace "Oya mu wuce ciki..." Suka juya suna kallon khaleel da ya rungume hannunsa, jallabiya ne sanye jikinsa ya dinga kallon yaran suka daga masa hannu sudais yace "Uncle are u coming tomorrow plss" Khaleel yyi murmushi yana gyada kai yace "Sure" khadijah bata basu daman sake ce masa komai ba ta tunkudasu cikin gida, Hijab dinta taji khaleel ya riko ta juyo da sauri, murya can kasa yace "Wait" ta kalli yaranta da har sun shige gate, ta kwace Hijab din fuskarta daure tace "Meye haka pls" yana kallonta a hankali yace "Ba gaisuwa xa ki wuce?" Hararansa tayi tace "Wanda na maka daxu a waya fa?" Jinginar da ita yyi da mota, yace "Daban" ta sauke idonta kasa xuciyarta na bugawa jin bai ce komai ba ta dago kanta taga kallonta yake, da sauri ta kara sunkuyar da kanta, yyi murmushi murya can kasa yace "Can I come gobe mu gaisa da Umma?" Ba tare da ta dago ba tace "Why?" Yace "Haka nan, twins suka ce in xo in gaida Ummansu she will like me" kin cewa komai tayi, bayan few seconds yace "Khadijah" dauke kai tayi tace "Allah ya kai mu" Ya d'an yi murmushi yace "Ameen, to yaushe xa ki koma?" Sai a sannan ta kallesa, lkci daya ta sauke idonta tace "Monday in sha Allah" ya dan wara ido yace "Har Monday?" Shiru tayi, murya can kasa yace "Alryt then, we go together" kai ta gyada masa kawai, yace "Toh sai da safe" ta saci kallonsa a hankali tace "Allah ya kai mu" daga haka ya bata hanya ta wuce ciki ya bi ta da ido. Umma dake parlor ta bi ta da kallo har ta shiga daki sannan ta mike ta bi bayanta, xaunawa gefen gado tayi tace "Saurayin ki ne wanda ya xo Khadijah?" Khadijah ta xaro ido tace "Saurayi kuma Umma, aa ba saurayina bane" Umma tace "Kawar ki ce kenan, it's high time you settle down with a husband daughter..." Khadijah ta kalleta da sauri, Umma tace "Ehh, kuma ban son ya wani dau lkci, in dai kina da wanda ya kwanta maki kika yaba hankalinsa, ki fito da shi, kin ga wannan dama ce da xa mu samu na xuwa katsina.... Idan ma kawun nan ki baxa su daura maki aure ba baxa ki rasa wanda xai daura maki ba" Rasa abun cewa Khadijah tayi, don ita dai tasan bata da saurayi, Umma tace "You think over it daughter" daga haka ta mike ta bar dakin. Kasa bacci daren ranan Khadijah tayi maganar da Umma tayi mata ya tsaya mata sosai, ko kadan aure ba ya cikin tsarin da tayi ma rayuwarta, babu abinda ke sake daga mata hankali sai ganin how serious Umma tayi xancen, gashi ta ma kasa ce mata ta hadu da Aliyu saboda bata ma son xancen, sai dai kuma ko don Aliyun ma ya kamata tayi auren ko xai fita rayuwarta da yake kokarin shiga yanxu, har asuba bata wani ritsa ba, sai a sannan ta fara da ta sanin dawowa ma da tayi. Aliyu ya kalli Mumy a karo na farko tun shigowar ta dakin tana masa magana babu yabo babu fallasa tamkar dai umarni ma take ba sa, ya d'an yi murmushi sannan yace "Mumy ba fa aure tsakanina da Iklima...." Strictly Mumy tace "Haka kace?" Yace "Ehh mumy, domin kuwa da ciki aka daura auren, yanxu kuma naga alamar sun je sun xubar da cikin" Mumy ta dinga masa wani kallo ko kiftawa babu, juyawa tayi ta fice daga dakin rai a bace, yyi murmushi ya na ci gaba da analysis din da yake tun safe amma ya kasa arriving komai, ya lumshe ido keenly, yana naxari... it all started bayan ya sha coffee da safe ranan, and then? Kawai ya dai ji ya kasa fita aiki, and... Bude kofar da aka yi ya bude ido ya juya da sauri, Saleem ne ya shigo dakin Aliyu ya masa kallo daya ya dauke kai, murmushi ya dinga yi ya ki cewa komai, aliyu ya kallesa a karo na biyu, ya mike yace "Ya aka yi malam?" Dariya saleem yyi yace "Wani xance naji yan gidan nan ke yi yaya, is it for real?" Wani kallo Aliyu ya dinga masa cikin cool voice dinsa yace "Get out and close the door behind you saleem" Saleem ya daga kafada yana murmushi yace "But I neva expect that from you, ni da ake ma warning a da, sai gashi kuma....." Dariya yyi ya fita ya rufe kofar, Aliyu ya xauna xuciyarsa na tafarfasa ya ji duk ya tsani yan gidan nasu gaba daya, ya hade kansa da table din gabansa.... Khadijah na kitchen tana girkin lunch misalin sha biyu Shureim ya kawo mata waya dake ring, Karba tayi ta daga ta kai kunne, muryarsa ya daki kunnenta, yace "How was your nyt?" Tace "Twas good, ya gida" yace "Alhmdllh, ya twins?" Tace "They are fine" yace "Alryt. Anjima xan xo" tace "Allah ya kai mu" daga haka yyi mata sallama ya katse wayar, ta juya xata mika ma Shureim wayar, wani mugun faduwa gabanta yyi ganin irin tsayuwar da yyi yana jiranta, lkci daya Aliyu ya fado mata ta mika masa wayar a sanyaye, yaron ya karba ya juya ya fita ta ci gaba da abinda. Aliyu ya fito daga bedroom dinsa rike da makullin mota xai bar gidan ganin he is nt arriving at anything better a tunanin da yake tun safe, baby ma da fitowarta kenan daga dakinsu ta juya ta koma ganinsa, tun ranan da Anty khadijah ta fadi ma yan gidan abinda ya faru tsakaninsa da Khadijah kusan duk suke canxa hanya idan sun gansa, gaisuwa ma sai sun ga dama, duk wannan baya masa ciwo sai irin yanda Saleem ke making jest of him ko da yaushe cikin masa dariya yake, he is just trying hard to control his self baya kulasa, Mumy ce ta fito daga dakin Anty Khadijah tana kwalo ma Saleem kira hankali tahse, shi dai Aliyu na tsaye don har ita bata bin ta kansa a gidan, Saleem ya fito tace "Maxa ka dauko makullin motar iklima ce ba lafiya, kayi sauri don Allah" Aliyu na jin haka ya sauka Downstairs ya bar parlorn ya hau motarsa ya fice a gidan, direct gidan Farouq ya nufa, yana isa bakin gate ya kira sa ya sanar da shi yana kofar gida, fitowa yyi daga motar bayan Farouq yace ya shigo yana ma compound, Aliyu ya shiga gidan yana amsa gaisuwar mai gadi, can ya hango Farouq su biyu xaune kan biyu daga cikin kujerun dake wajen, har ya isa wajen idonsa na kan wanda ke xaune tare da farouq, shi ma dai dai nan ya dago kai suka yi ido hudu, kallon kallo suka shiga yi da wani ex gaba daya fuskarsu, Farouq dake nuna ma Aliyu kujera yana murmushi yace "The great Dr, mu dai mun je daurin auren ka baka nan, ban kuma kira ka ba saboda ba aji mutuwar sarki a baki na ba" kin xama Aliyu yyi yace "Ehh naga alama, I was just passing by dama nace in shigo mu gaisa so ba dadewa xan yi ba, ana jirana a mota, I will leave now" Farouq ya masa wani kallo yace "Bana son walakanci fa, daga xuwa sai tafiya, yaushe ma ka dawo Nigeria" tuni Aliyu ya juya ya bar wajen da sauri, Farouq ya mike yace "What's the meaning of this Aliyu!" Ba tare da ya juyo ba yace "Sure, a gaida min su Haiydar da Madam am in a haste" Farouq ya bi sa da kallo baki sake kafin ya kalli abokin sa dake xaune yana danna waya, dago kai khaleel yyi shi ma ya kallesa yace "Kila don ya gan ni ne yasa ba ya son xaunawa...." Farouq ya ma khaleel wani kallo, sai kuma yyi dariya yace "Toh ai ina ya san ka da xai ki xama saboda kai kai kuma da wani xargi, that's Aliyu for you, haka nan yake ba wai don saboda kai bane it's his habit" murmushi Khaleel yyi yace "Toh ya ji dadi, nima yanxu xan wuce ina da inda xan je" daga haka ya mike Farouq yace "Haba dai, so early yaushe rabon mu hadu Dr Ayman?" Khaleel yace "Assuming babu inda xan je I will stay kai ma ka sani" Farouq yyi murmushi ya mike yace "Toh shkkn, wai ya Jawahir din ka, saura watanni nawa bikin?" Khaleel yyi murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Uku kawai" Farouq yace "Toh Allah ya kai mu, my regards to her, Anty kuma kace mata plsss tayi hakuri ina nan xuwa in gaisheta" Shi dai khaleel bai ce komai ba suna tafiya har suka fita gidan, sai da suka isa gun motar khaleel, khaleel ya juya yana kallon Farouq strictly yace "Don't dare say anything about me to that guy that just left Umar, tell him nothing about me if he shud ask" da mamaki Farouq yace "Anything? Like? Ka taba sanin sa ne?" Khaleel yace "No ban san shi ba, I just know xai yi ma tambaya a kai na, kar kuma ka gaya masa komai" daga haka ya shiga motarsa Farouq ya dinga kallon sa yace "shi aliyun?" Dariya yyi yace "Yanda kake haka yake shi ma ai, banbancin ku kadan ne, soo nasan baxai ma min tambaya a kan ka ba, beside shi ma a UK yake ai, a Dr also" Shi dai khaleel bai ce komai ba ya ja motarsa ya bar wajen. Yau dai Khadijah mayafi ta daura kan atamfar jikinta ta fito amma ba tare da su Sudais ba, duk da bata yi kwalliya ba amma tayi kyau ne ba kadan ba, ta glass khaleel ke ta kallonta ganin jingina tayi da motar bata bude ba ya sa ya bude ya fito ya xagayo ta inda take, ba tare da ta kallesa ba tace "Ina yini?" A hankali yace "Cool, ya boys dina" tace "They are inside, mu je sai ka gaisa da Umma" daga haka ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo da farko kafin ya bi bayanta, Sosai Umma ta tarbi khaleel da yaki kallonta kansa a kasa, xaman ma bakin kujera ya xauna kana ganinsa kasan duk a takure yake, Umma ta tambayesa mutanen gida yace duk suna lafiya, dariya ya ba Khadijah don bata tana xaton yana da kunya haka ba don ko da wasa ya ki dago kansa, Umma da ta lura da haka ita ma ta bar masu parlorn, sai a sannan khaleel ya dago kamar munafuki, khadijah dake ta murmushi tana xuba masa lemo a cup tace "Kamar gaske" mikewa yayi ya mata wani kallo murya can kasa yace "Karya ce dama, am outside" da sauri ta kallesa tace "Me xa kayi a waje" yace "I can't stay here" ta bata fuska tace "Abinci fa xan xuba maka" yace "Ni bana jin yunwa, kawai ki turo min twins" daga haka ya nufi kofa kamar ana hankada sa, Khadijah ta bi sa da harara har ya fita, tsaki ta yi ta xauna kujera tana turo baki, Ba a dau lkci ba ya fara kiranta a waya har ya katse bata dauka ba, ya sake kira ta ki dauka, text ya turo mata yace "Plss Khadijah, ina mota fa ni baxan iya xaman parlorn ba, idan baxa ki fito ba ki turo min su sudais kawai" tashi tayi ta wuce dakin Umma don suna can suna kallo basu ma san ya xo ba, Umma na ganinta tace "Barin sa ki ka yi shi kadai a parlor?" Khadijah ta tabe baki tace "ya fita yana waje" Umma tace "Saboda me?" Tace "Wai baxai iya xama a parlorn ba" Murmushi Umma tayi tace "Shi kuma haka yake da kunya, Khadijah ina kika samo balarabe?" Xaro ido Khadijah tayi lkci daya ta fashe da dariya tace "Ba balarabe bane fa shi" hararata Umma tayi tace "Ya xa ki ce min ba balarabe bane" Murmushi Khadijah tayi tace "Toh ni dai haka yace min" Umma tace "Ya dai ce maki hakan ne, to ki fita ki samesa tunda baxai xauna parlor ba" Tare da su Sudais ta fita, khaleel ya fito daga motar yana kallonta bayan yyi pecking yaran da suka yi murnan ganinsa yace "Har da walakanci koh?" Tace "Nima ae shi ka min" shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace "Baki san ina da kunya sosai ba ko" Khadijah bata san lkcn da tayi dariya ba ya dinga kallonta don bai taba ganin dariyarta haka ba, har da rike ciki, ganin yanda yake kallonta ta hadiye dariyar tana murmushi tace "Amma a nan Nigeria kake ajiye kunyar idan xa ka UK koh?" Xaro ido yayi ba don yaranta dake gun ba da babu abinda xai hanasa jawota jikinsa tayi bayanin abinda take nufi, dariya kawai khadijah take tana kallonsa, khaleel ya kasa cewa komai, kawai ya 6uge da shafa lallausan bak'in gashin kansa, ta sata kallonsa ta sake kyalkyalewa da dariya, yyi murmushi ya cire glass din idonsa murya can kasa yace "Xa ki yi bayani ai xa mu koma UK din" ta hade rai tace "So?" Yana murmushi yace "Nothing, ki gaya ma Umma xa mu je shopping da su sudais plss har da ke" khadijah da bata sake kallon fuskarsa ba tace "Noo ban da ni" yace "Plss" tace "Ni baxan je ba da gaske, su dai ka tafi da su" da kyar da kyar khaleel ya lallabata bayan ta sa ya rufe idanuwansa da glass din da ya cire sannan ta yarda xata bi su, amma bayan ta gaya ma Umma idan xata yarda, ganin tare da su sudais ne Umma ta yarda suka tafi bayan tace kar su dade, front seat ya bude ma su Shureim suka shiga, ganin haka ta bude back seat ta shiga, sai da suka yi nisa khaleel yace "Mu je ki gaida mum dita nima, it's just malali here ba nisa...." Da sauri khadijah tace "Noo plss, sai in je a wa?" Yana kallonta murya can kasa yace "A surkarta to be" shiru khadijah tayi ta na kallonsa da mamaki, ya mayar da dubansa kan titi yana driving, da sauri tace "Noo, sae dai a matsayin friend dinka, and am not ready for that Dr don ban ce ma umma xan je ko ina ba daga inda kace xaka kai mu" a hankali yace "Ohk then, amma xa mu biya gidansu jawaheer mu dauketa, I think she wants to shop also" kallonsa Khadijah ta tsaya yi ta ma rasa abinda xata ce masa, ai ko suka isa anguwarsu jawaheer din yyi parking ya dau waya ya kirata yace yana waje, khadijah tayi karfin halin cewa "Toh su sudais su dawo baya" Khaleel yace "Noo xata xauna baya ita ma, no probs" Ba a dau lkci ba jawaheer ta fito, she is a real definition of black beauty, kyakkaywa ce ita din ta karshe, ta bude front seat tace "Sweetheart ashe da gaske xaka xo din" ganin su sudais da Shureim ta wara ido tace "Waoww cuties, ina ka samo su swthrt? They are so cute" gaisheta yan biyun suka yi, duk ta yi masu kiss a goshi, Khaleel dake kallonta yace "Yarana ne" dariya ta yi tace "Kai dear, don Allah waye su, sun min kyau wllh" ya kalli khadijah ta madubi yace "Ga Aunt dinsu a baya nan" sai a sannan jawaheer ta kalli baya da sauri tace "Ohh ban lura ba, hello" Khadijah tace "Hi" jawahir na murmushi tace "You've got sweet siblings" murmushi khadijah ta kirkira, kamar baxa ta ce komai ba sai kuma murya can kasa kamar ana tilastata tace "Thanks" jawahir ta bude bayan motar ta shiga ta rufe khaleel ya ja motar suka bar wajen, ta madubi yake ta kallon khadijah da ta kauda kai tana kallon waje, ita kuma jawahir na ta basa labari da siririyar muryarta da ya cika motar. Farouq dake ta kallon Aliyu da d'an mamaki yace "Ko meye dalilin da yasa kake son sanin sa Dr?" Aliyu ya hade rai yace "Idan xaka gaya min ka gaya min" Farouq yace "He is my good friend, tare muka yi karatu a England degree and masters, his mum from Saudi Arabia, the most simplest woman I have ever known, his dad a Nigerian from kano, shi kadai ne namiji gidansu with 4 siblings duk mata, Dr Ayman ba shi da matsala, he is free with everyone sai dai he don't make friends easily, he is a genuine... He was among those that graduated with d best result during our time, yanxu haka PhD dinsa yake a Uk..." Katse sa Aliyu yayi yace "Am not asking you about his life history or how intelligent he is, ina gidansu yake?" Farouq ya dinga kallonsa da tuhuma kafin yace "I don't think i wil tel you that Aliyu" murmushi Aliyu yyi yana shafa beard dinsa. Tun da suka shiga shopping mall din Khaleel ke kallon khadijah ganin yanda ta daure fuska, duk yanda khaleel yayi da ita ta dauki abubuwan da take bukata nuna masa ta yi bata bukatar komai, Jawaheer da twins suka dinga daukan abinda suke so a gun, khaleel dai na biye da su a baya, xagawa Jawaheer tayi gun chocolates da biscuits duk wanda yaran suka dauka ita ma sai ta dauka, khaleel dake ta kallon khadijah bayan jawahir ta bar wajen yace "Wait, wai me yasa baxa ki dau komai ba Khadijah, or did I offend u in any way plss?" Khadijah ta tabe baki ba tare da ta kallesa ba tace "To lallai ne sai na dauki abu a mall? Kuma don ban dauka ba sai ya xamanto anyi offending dina? Am not just interested" Shiru yyi yana kallonta, a hankali ya juya ya bar ta tsaye gun ya koma gun twins da jawahir, nesa da su wani mutum ne tsaye yana dauke da wata yarinya da baxata wuce shekara uku ba an mata kitso irin na yara gashinta har kusan bayanta, kusa da shi kuma wata mace ce rike da trolley tana xuba kayan da ta dauka, kallon su Shureim kawai yake ko kiftawa babu, har sai da matarsa dake gefensa tace "Barrister mu je mana" sai a sannan yyi saurin dauke idonsa kan yaran ya bi bayan matarsa, ya sake juyawa yana kallon yaran da khaleel ke rike da hannunsu har ya bar wajen ya daina ganinsu, khaleel ya biya kudin abubuwan da suka siya yana kallon khadijah da ke bakin kofar fita tana jiransu, ganin kallon da yake mata ta dauke kai da sauri dai dai lkcn da idonta ya sauka kan barrister sudais dake tahowa rike da kyakkyawar daughtern sa, matarsa na biye da shi tana rike da ledan siyayyar da suka yi, still Khadijah tayi a gun da take tsaye taji komai nata ya tsaya cak, yanda take kallonsa shi ma haka yake kallonta ko kiftawa babu har ya iso dab da ita ya sauke idonsa kasa ya mika ma security dake bakin kofar receipt din kayan da ya biya aka mayar masa sannan ya fita mall din, matarsa na biye da shi. Khadijah ta bi sudais da kallo cikin shock sosai, fita tayi da sauri tana ci gaba da kallon sa xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya juya bai san ta fito ba suka kara hada ido yayi saurin dauke kansa, motarsa ya nufa ya bude, matar ta bude back seat ta ajiye ledan hannunta sannan ta bude seat din gaba xata shiga ta dakata da sauri tana kallonsa tace "Lahh Barrister na bar masu wayata a counter..." Bata jira cewarsa ba ta juya da sauri ta koma mall din, Sudais ya kara daga kai ya kalli khadijah, bata san lkcn da ta nufesa ba tana kallonsa ta fashe da kuka sosai cikin raunin murya tace "Why are you pretending you don't knw me? Did I deserve that Sudais.... Me yasa kake yin kamar baka taba sanina ba" sosai hawaye ke xuba idonta, Ya kasa kallonta ya kuma kasa cewa komai ba, ganin Jiddah na fitowa mall din ya sa ya shiga motarsa ya rufe, gwiwa a sake Khadijah ta koma baya tana kallonsa ko kiftawa babu kai kana ganinta kasan she is over shock, Tun daga nesa jiddah ke kallon khadijah da tayi saurin share idonta, har ta iso tana mata wani kallo daga sama har kasa tace "Baiwar Allah, do you have any problem? Tsayuwar me kike a nan" Khadijah bata kalleta ba ta juya da sauri ta bar wajen ta koma can jikin wani mota xuciyarta na mata xafi, ta fashe da wani matsanancin kuka, me yasa ko da yaushe a cikin mall take haduwa da abinda ke mugun daga mata hankali, yau ga ta ga sudais yyi kamar bai taba sanin ta ba, me tayi masa xai mata haka, ta sulale wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, bata yi deserving yyi mata haka ba da ya bari ko godiyar abinda yyi mata a rayuwa ta kara masa don tasan baxa ta iya biyansa ba kuma ba lallai su sake haduwa ba. Jiddah na shiga motar ta kalli sudais fuska a murtuke tace "Wacece ita Aliyu?" Buda hannu yyi alamar bai sani ba, ganin kallon da take masa yace "Kawai ce min fa tayi in ara mata waya xata yi making call, ni kuma nace bani da airtime, that's all madam" tsaki jiddah tayi cikin bacin rai tace "Da ta fada a gabana in koya mata hankali yau wllh, irin yan iskan matan nan ne masu bin maxajen mutane a titi, banda haka ta baka ajiyar kati ne xata ce ka ara mata waya?? dear idan baka son matsala da ni wllh ka bar ko da responding wa ennan mutanen, idan xa su shekara suna ma magana kar ka ko da kalli inda suke balle ka bude baki ka basu amsa ka xama kamar deaf and dumb, domin kuwa yawancinsu da asiri suke xuwa, ni dai na gaya maka kada a fara jin kan mu kuma" "Toh" kawai Sudais yace ya tada motarsa ya bar harabar mall din tana ci gaba da mita, Khadijah taji xuciyarta ya mata nauyi ta dinga kuka ko xata samu relieve amma kamar ana kara mata ciwon da take ji, babu irin neman da khaleel bai mata cikin mall din ba amma bai ganta ba, jawahir ma sai dube dube take tana neman ta, atm dinsa ya mika ma jawahir yace "Dear gashi you pay the bill" tace "But the pin?" Fada mata yyi ya fita mall din ta bi sa da kallo a sanyaye, little Sudais na kallon jawahir yace "Anty ba mu ga Antynmu ba" jawahir ta duka tana masu murmushi tace "Yanxu Dr xai nemo mana ita cuties" daga haka ta mike ganin an xo kanta a gun biyan kudin. Tafiyar few minutes sudais yyi ya tsayar da motar, Jiddah dake kallonsa ganin yanda ya ja tsaki tace "Ya aka yi Abban Amira?" Ya d'an dafa kansa yace "Wannan matsalar dai da nace maki motar ta bani last week, I don't knw what's wrong with this car" tace "Yanxu baxai tashi ba kenan?" Yace "Sai wani ikon Allah, gashi ban san ko Ahmad na garage ba da na kirasa ya taho yanxu... Am just bored of this car" ta hade rai tace "Toh ni ya xa muyi yanxu ga ranan yamma" ya kalli cute angel dinsa me suna Khadijah yana kiranta da Amira ya ja hancinta ganin yanda take kallonsa da kwala kwalan idonta yace "Kar Amirata ta sha wahala bari kawai in tsayar maku da adai daita ku wuce gida ni xan taho daga baya" Jiddah tace "Wai to ka kara gwada tada motar mana, ba girman ka bane barrister a gan ka bakin titi mota ta lalace" Murmushi yyi ya bude motar ya fita ya tsayar da adai daita ya gaya masa sunan anguwar su sannan ya xaga ya bude motar yana kallon jiddah yace "Ki fito ku wuce yanxu xan taho nima in sha Allah" ta hade rai tace "Aa mu je gaba daya kawai, ai babu me satar motar idan ya so sai Ahmad yaje gida ya karbi makulli ya lallaba ya kai motar gareji" kallonta ya tsaya yi kafin yace "Plss be a good wife and humbly come down kinga na tsayar maku da d'an sahu, you don't worry about me I will be okay sai kace ba namiji ba" da kyar ya lallaba ta ta sauka ta shiga napep din ya mika mata Amira da kayan da suka siya a supermarket, yana tsaye har napep din ya sha kwana sannan ya shiga motarsa da sauri ya tada yyi reverse ya koma mall din at high speed kamar xai tashi sama. Babu irin duban da khaleel bai ma khadijah ba a haraban Shopping complex din, har yyi give up a xaton sa gida ta wuce sai dai kuma haka kawai ya ji ransa ya baci, ya juya kenan xai koma ciki ya hangota durkushe bayan mota, da mamaki ya dinga kallonta lkci daya ya isa gabanta ya durkusa yace "Me ya faru Khadijah me kike yi a nan?" Ta kasa cewa komai sai shessheka take hawaye na sakko mata, a rikice yace "Ki min magana don Allah khadijah, me ya faru" ganin ba shiru xata yi ba ya daga ta ya nufi gun motarsa bai damu da mutanen dake kallonsu a gun ba ciki har da jawahir da ta fito da su shureim ya bude back seat ta shiga ya rufe, Sudais ya taho gun khaleel da sauri hankalinsa tashe yace "Uncle what's wrong with my Anty" Daukan sa Khaleel yayi yana murmushi yace "She is having a headache" kokarin sauka ya shiga yi a jikinsa kamar xai yi kuka yace "Uncle ina son in xauna kusa da ita I don't like d front" bude masa bayan motar khaleel yyi ya shiga sannan ya rufe, shi dai shureim na tsaye can kawai ya fashe da kuka, jawahir ta duka tana kallonsa da mamaki tace "Me ya faru handsome" Khaleel na ganin haka ya karasa ya daukesa shi ma ya bude back seat din ya xaunar da shi sannan ya rufe, jawahir dai na tsaye tana kallonsu ya bude mata front seat ta karaso ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver, Khadijah ta hadiye kukan da take da kyar ganin yanda yan biyunta suka rikice su ma suna kukan tana yin shiru su ma suka yi shiru, khaleel sai kallonta yake ta madubi duk ya ji ba shi da nutsuwa kamar ya jawo ta jikinsa ya lallasheta, Jawahir ma sai kallon khadijah da yaranta take, Khaleel na fita mall din da motarsa sudais ya shigo shi kuma da tasa motar, ko parking din kirki bai yi ba duk da maganar da securities din gun ke masa ya wani rikice ya dinga duba nook and cranny din wajajen yana nemanta har ciki sai da ya shiga amma babu khadijah, ya fito jikinsa a sanyaye ya hade kansa da motar sa.