NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 61-70

gaba da driving dinsa bai ce komai ba, sai da suka iso street din ya kalleta yace “I only know the street….” ta fada masa number din gidan, yana isa dai 

dai gidan yayi parking yana dubanta yace “Wani schl din Shureim ke xuwa Iman?” Sai a sannan ta kallesa tace “I don’t think I have to tell you” Yana shafa 

kansa yace “It isn’t an offense ai Iman” ta bude motar ta fita tace “Thanks for the ride” murmushi kawai yayi ta wuce ciki ya bi ta da kallo, tabe baki 

Khadijah tayi ganin babu motar khaleel a garage ta fiddo makullinta cikin jaka ta bude kofar ta shiga ciki, wanka tayi sannan tayi sllh ta canxa kaya ta 

fito parlor, xaunawa tayi tana tunanin abinda xata girka, can ya mike ta wuce kitchen din, shinkafa da miya tayi deciding tayi sanin Shureim na son sa 

sosai, tana parboiling shinkafa taji shigowar motar khaleel gidan, da gudu ta fita parlor ta isa gun kofa ta sa makulli sanann ta koma kitchen ta ci gaba da 

abinda take, bell taji an danna, ta hade rai ta tura kofar kitchen din, ba a sake dannawa ba sai ringing din wayarta dake parlor ta ji, ta bude kofar ta 

fita ta dau wayar tana kallon screen din, ganin khaleel ke kiranta da har xata ajiye sai kuma ta daga ta kai kunne ta ki cewa komai, yace “Bacci kike ne?” 

Tace “What about that?” Yace “Ohk, naga takalman ki kin bari a waje, and ki fito ku gaisa da jawahir” Wani kallo tayi kamar yana gabanta tace “For what?” A 

hankali yace “Am waiting Khadijah….” daga haka ya katse wayar, mamaki ne ya cikata, a kan wani dalili xa ta gaisa da jawahir, tsaki tayi xata ajiye wayar 

text ya shigo nasa, ya budewa tayi tana kallon content din, “Plsss” abinda ya turo mata kenan, ta turo baki sai kuma ta harari kofar, a hankali ta isa gun 

kofar ta bude, tsaye ta gansa shi da jawahir din, suna hada ido jawahir tace “Sannu Khadijah ya gida?” Khadijah ta kirkiri murmushi tace “Lafiya lau, fatan 

kin xo lafiya” Jawahir tace “Alhmdllh, ya hakuri?” A hankali Khadijah tace “Alhmdllh nagode” kallonta kawai khaleel yake, Jawahir tace “Dama Dr yace in taho 

in maki gaisuwa ne” Khadijah tace “Ayya nagode, baxa ki shigo ba” khaleel na kallon jawahir yace “Shiga sai kiyi sllh” jawahir tace “Toh bari in yi” daga 

haka ta shiga parlorn Khadijah, ba tare da Khadijah ta kallesa ba ta rufe kofarta fuska daure, murmushi kawai khaleel yyi yana kallon kofar. Jawahir na kan 

darduma xaune parlorn Khadijah ta kawo mata abinci a plate, jawahir tace “Ayya na ci abinci Khadijah, am not hungry” Khadija tace “Haba ki ci ko kadan ne” 

Jawahir tace “Da gaske bana jin yunwa ki bar sa kawai” juyawa kawai Khadijah tayi rike da abincin ta koma kitchen, tana fitowa jawahir ta mike tace “Toh 

nagode bari in je” Khadijah tace “Welcm” daga haka ta fita, tana ji ta bude apartment din khaleel ta shiga, tabe baki Khadijah tayi, ta ja tsaki ta wuce 

daki, mayafinta ta dauko ganin Shureim ya kusa tashi a schl, tana fita apartment dinta ta sa makulli ta nufi waje, cab ta samu ya kai ta har makarantar, 

Rungume ta Shureim yayi bayan ya fito daga cikin makarantar yana kallonta yace “Anty me yasa uncle bai xo ba” Khadijah ta hade rai tace “Don’t ask me that 

again” daga haka ta kama hannunsa suka shiga cab din, suna isa gida ta biya mai cab din ta wuce ciki tana rike da hannunsa, sai kallon kofar khaleel take ta 

tabe baki ta bude kofarta ta shiga parlor da Shureim, makulli ta sa ma kofar, ta Shiga bedroom da shi ta cire masa uniform, tayi masa wanka ta shirya sa ta 

sa masa rigar sanyi sanan ta sa yayi sllh, suka fito, a plate daya ta xuba masu abincin, tana ci a hankali tana kallonsa, muryarsa taji yace “Anty yaushe 

Sudais xai dawo? Umma tace min after one month, kuma ai one month yayi ai koh?” Khadijah ta sauke idonta daga kallonsa tana ci gaba da cin abincinta tace 

“Nima ban sani ba, sai dai anjima idan Umma ta kira ka tambayeta” ya langwabar da kai yace “Ohk” kallon wayarta dake ring tayi taga sabon number ke kiranta, 

ta dauka ya kai kunne, muryar Aliyu taji yace “Iman” a hankali tace “Na’am” yace “Fito ki amshi sakon Shureim din” kallon Shureim tayi tace “Ohk” daga haka 

ya katse wayar, ta mike tana kallon Shureim tace “Mu je ka rakani Shureim” ya tashi ta dauko plate ta rufe abincin, ta dau tissue ta goge masa bakinsa 

sannan ta dauko masa takalmansa ya sa suka fita, ba dai dai kofar gidan yayi parking ba, Khadijah na rike da hannun Shureim ta tsallaka xuwa side din da 

yake, daga cikin motar Aliyu ke kallonsu ko kiftawa babu har suka iso dai dai inda yayi parking, a hankali ya bude motarsa, Shureim na ganinsa ya nufe sa da 

gudu cike da murnar ganinsa Aliyu ya daga sa ya rungume sa ya lumshe ido, cike jin dadi shureim yace “Uncle ka kai ni wajen mama plss” Aliyu ya dago kansa 

yana kallonsa yayi pecking goshinsa yace “Mama tana Nigeria ai, idan kun yi hutu sai in kai ka” Shureim yace “Uncle plss ka tafi da ni” Aliyu ya kalli 

Khadijah dake wasa da ring din hannunta, a hankali yace “Thanks for coming out Khadijah” Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, jin bata ce komai ba ya 

bude bayan motar ya fiddo babban leda, Shureim yace “Uncle Anty ta bani irin wannan chocolate da kake bani da Sudais…” Aliyu ya wara ido yace “Da gaske?” 

Yace “Yes uncle” ya kalli Khadijah ya langwabar da kai yace “Toh Anty ki bari muje in siyo masa irin chocolates din, sai mu dawo yanxu” Khadijah bata ce 

komai ba, Aliyu yayi kasa da murya yace “Ko xa ki raka mu?” Girgixa kai tayi tace “No way” daga haka ta tsallaka ta wuce ciki abun ta, Aliyu ya bi ta da 

kallo kafin yayi murmushi ya xaga ya bude front seat ya xaunar da Shureim, ya dawo ya shiga driver seat ya tada motar ya bar street din. Khadijah na dai dai 

apartment dinta khaleel ya bude motar ya fito rike  da makulin motarsa, ganinta yace “Let me go pick Shureim, na sha’afa wllh” a takaice tace “You don’t 

worry na dauko sa, Ni ban sha’afa ba” daga haka ta Shiga ta rufe kofarta, ya fi minti daya a tsaye kafin ya koma nasa apartment din. Shopping mall din da 

Aliyu ya kai Shureim kusa da gidan kanwar Abbansa yake, don haka yana gama masa shopping ya shiga gidan tare da Shureim, Tasowa Maryam dake xaune parlor da 

Deejah tayi ganinsa ta tafi da sauri dau yaron ta rungumesa tace “Waow yau ga Shureim a gidanmu, Yaya Aliyu a ina ka samo mana shi? Jiya kuwa muka hadu da 

mum dinsa a cafteria a schl” Maryam ta kalli Deejah dake parlorn tana kallon Shureim da expression na Waow a fuskarta tace “Kin tuna warce muka gani a 

cafteria jiya?” Deejah ta xaro ido tace “Wai Khadijahr nan da nace maki suna kama da Safeenah??” Maryam tace “Yauwa ita” da mamaki Deejah tace “Kar ki ce 

min ita ta haifi yaron nan?” Maryam tayi dariya tace “Yaronta ne mana, yan biyu ne ma, daya ya rasu” lkci daya jikin Deejah yayi sanyi ta mike tace “Allah 

sarki” Aliyu dai bai tanka su ba ya wuce sama bayan ya amshi Shureim hannun Maryam don kai ma Antyn sa shi, Deejah ta bi su da kallo murya can kasa tace 

“but naga yaron na kama da cousin din naki ai, I mean sosai fa” Murmushi kawai Maryam tayi sai dai bata ce komai ba, bude kofa aka yi sai ga jawahir ta 

shigo, wurgar da takalman kafar tayi, ta jefar da jakar hannunta kan kujera ta xauna, Deejah dake ta kallonta tace “Ke kuma meye haka? me ya faru?” A fusace 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button