NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 71-80

Khadijah ta hade kanta da gwiwa a hankali ta ki cewa komai, ya fi minti biyu yana kallonta, can ya shafa kansa murya can kasa yace “Talk Iman…” lkci daya 

ta dago kanta ya dinga kallon jajayen idanuwanta, ta hadiye abu da kyar ta make kafada tace “I think I’ve changed my mind” muryar ta na rawa ta fadi haka, 

ya dinga kallonta a sanyaye yace “Why Iman??” k’in cewa komai tayi, wasu sabbin hawayen suka shiga xubo mata, da damuwa sosai yace “Why did u change ur mind 

Iman, am I not trustworthy” goge idonta tayi tana kallonsa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idanuwansa, murya can kasa ya ji tace “Ina son xan wuce 

gida yanxu” Ya bude ido ya kalli agogon wrist dinsa a sanyaye yace “To mu je in kai ki” shi ya fara mikewa sannan ita ma ta tashi a hankali tana share 

idonta, har suka iso gun motarsa bai ce komai ba, sai da ya bude motar ya shiga sannan ita ma ta shiga, gaba daya she was absent-minded during the ride, 

idonta ne ya sauka kan wani karamin agogo mai kyau na yara cikin a cikin motar, ta kai hannu ta dauka tana kallon agogon ko kiftawa babu, agogon da khaleel 

ya taba siya ma su Shureim ne lkcn da suka xo hutu wajenta da xa su koma, ita dai ta san na Shureim na nan don da shi ma suka xo, Aliyu dai bai ce komai ba 

yana driving a nutse, ganin ta kallesa kafin tace komai murya can kasa yace “For little Aliyu….” Kasa cewa komai tayi da farko, a sanyaye tace “Where did 

you get it from?” Ya d’an yi murmushi kamar baxai ce komai ba shi ma, sai kuma yace “When he had an accident that very day agogon na aljihunsa, da muka tafi 

asibiti na cire” Khadijah ta sauke idonta bata ce komai ba, a hankali ta xuge zip din jakarta xata sa a ciki ya karba a hannunta, da mamaki take kallonsa, 

yace “Nima ina so, shi yasa na bar shi ma a mota” ta hade rai tace “Toh nima ai ina so” A hankali yace “But ai Shureim ma na da shi” bata sake saurarensa ba 

ta kai hannu xata karbe, bai san lkcn da ya sake steering ba ta fasa ihu a tsorace, parking yayi daga karshe inda ya dace yayi, ta dinga kallonsa xuciyarta 

na bugawa, yayi kokarin ganin bai yi dariya ba, dauke hannunsa yyi wajen ganin xata kwace agogon, Tace “Bana so ka bani abun yarona” a hankali yace “Nima ai 

yarona ne Iman” wani kallo tayi masa tace “A tunanin ka??” Murmushi kawai yayi yana kara kallon agogon, Mika mata yayi yana kallonta a hankali yace “Toh na 

hakura” kasa amsa tayi, ya dinga kallonta yana mika mata, dauke kai tayi ta turo baki tace “Toh na ara maka, xaka ban watarana” Murmushin sa yayi mai kyau 

murya can kasa yace “Toh ina godiya Iman” Ya mayar da agogon inda yake ya ajiye, ya juya yana facing dinta yace “But why did you change ur mind Iman?” 

kallonsa tayi sai kuma ta dauke kai, kamar baxata ce komai ba bayan few minutes a sanyaye tace “It’s Dr Ayman, and it looks as if it’s of no use telling 

you….” sai da gabansa ya fadi sosai, ya dake cike da karfin hali yace “What about him” ta jinginar da kanta da kujerar da take xaune, ji tayi abun ya dawo 

mata sabo, muryar ta na rawa tace “Kawai don nayi masa magana shine ya min walakanci” Aliyu ya ji komai nasa ya tsaya, a hankali yace “May be…. may be he 

misunderstood you Iman….” Ta fashe da kuka tuna abinda Dr Khaleel yace mata, ya lumshe ido ya bude yace “Toh wani maganr kika masa?” Babu abinda ta boye 

masa a maganarsu da khaleel na jiya, jin yanda take kuka Aliyu ya lumshe ido yace “Look…. pls ki daina wanann kukan I really don’t like it, stop it now” a 

fusace yayi maganan ta hadiye kukan da take tana goge idonta, ya jinginar da kansa jikin kujerar motar a hankali cikin sanyi yace “He really misunderstood 

you, but ke ma ba haka ya kamata ki gaya masa ba” ta kallesa tace “Toh ya xan ce masa?” Ya d’an yi murmushin karfin hali yace “You where direct, which is 

not suppose to be so” turo baki tayi ta rungume hannunta tace “Ae shikenan” Aliyu ya shafa kai murya can kasa yace “You want me to talk to him?” Ta buda ido 

sosai tana kallonsa da sauri tace “Kace masa me?” Ba tare da ya kalleta ba yace “I will only explain to him what you meant by wat u said to him, kila…” ta 

hade rai ta katse sa tace “Noo, you don’t need to, ba ruwana da shi, and am wishing him d best also” Aliyu na kallonta da kyau yace “Then forget him, kuma 

kar ki sake xubda hawayen ki” Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace “But I can’t forget him just like that, yayi min hallacci a rayuwa” ba tare da Aliyu 

ya kalleta ba yace “Me ya maki?” Hararansa tayi da kamar baxata ce komai ba, sai kuma a takaice tace “He nursed my Heartache, he always made sure I was 

fine” Kallonta kawai Aliyu yake, “Wani irin heartache?” Tambayar da ya mata kenan har sannan yana kallonta sauke idonta tayi daga karshe tace “Ciwon 

xuciyata” da wani expression yake kallonta kafin yace “Kina nufin kina da ciwon xuciya?” Shiru tayi bata ce komai ba, jin hawayen talaici na xubo mata ta 

shiga gogewa, lkci daya jikinsa yayi sanyi, cike da karfin hali yace “I… i am the cause ko Iman?” Taki cewa komai, jin taki magana yace “Iman” sai a 

sannan ta juya tana kallonsa, sai ya rasa ma mai xai ce mata duk jikinsa ya mutu, tada motar sa yyi cike da karfin hali yace “Let me get you something to 

eat” Bata ce komai ba ya nufi wani gidan cin abinci da ita, suna isa bayan yayi parking ya juya yana kallonta a hankali yace “Mu je” daga haka ya bude motar 

ya fita ita ma ta fito, one side of the eatry khaleel ne xaune da cup din coffee gabansa ya jinginar da kansa da kujera har coffeen ya gama hucewa bai fara 

sha ba, kallonsu ya dinga yi ko kiftawa babu, ganin kujerar dake kallon nasa xa su zauna ya juya masu baya, Aliyu ya mika mata order list din da aka basa, 

kamar baxa ta karba ba da farko sai kuma ta amsa, ya dinga kallonta tunani iri iri a xuciyarsa, bata yi second talatin tana kallo ba ta mayar masa a sanyaye 

tace “Just anything” ya karba yana gyada mata kai, abinci iri daya ya sa aka kawo masu, duk da gaba daya ya ji ba ya da appetite hakan bai hanasa dinga cin 

abincin a hankali ba, ita ma haka, gaba daya suka fada duniyar tunani kowa da wanda yake, ita tana ganin yan biyunta tare da shi barin late Sudais, kuma ta 

dalilin haka har ranta tasan she is now comfortable with him even if it’s not 100% unlike before, shi kuma yana tunanin in har bai auri Khadijah ba till the 

end of him baxai taba samun rest of mind ba, a hankali ya dago daga karshe yana kallon yanda take cin abincin kamar ana tilastata sai turo baki take, suka 

hada ido ta yi saurin sauke idonta, ya d’an yi murmushi yace “Naga bakya ci” a hankali tace “Ina ci mana” shi ya fara matsar da abincin gabansa jin ya 

ishesa gaba daya duk da ba da yawa ya ci ba, ta kalli abincin nasa tace “Ka koshi?” Ya gyada mata kai, yanda yayi da bakinsa kamar Shureim idon bai son cin 

abinci, tayi shiru tana kallonsa, yayi murmushi yana shafa kansa ya matsar mata da sauran abincin nasa yace “Ko xaki kara?” Wani Harara ta maka masa ta tura 

masa nata tace “Sai dai ma ka kara da nawa” sunkuyar da kansa yayi yana dariya, tayi murmushi a sanyaye tana kallonsa komai yayi wani lkcn sai ta ga exactly 

her kids, it’s just too obvious, ya dau tissue yana goge bakinsa a hankali yace “Ranan Aunt dita ke tambayar ki, coz I told her a nan kike karatu….” 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button