NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 61-70

ta fara magana tace “Wllh Anty deejah na gaji da Ayman, abinda yake min ya fara isata, am just tired” Maryam ta xauna kusa da ita tace “Toh fah, me kuma ya 

hada ku?” Mikewa Jawahir tayi rai bace tace “Don rainin hankali sai yayi ta wani hada ni da yarinya da ban san meye tsakaninsu ba, I really want to know 

wacece yarinyar nan, sanann ta wani dinga daga min hanci tana amsa min da kyar kamar dole…. Da yaje Nigeria gaba daya lkcn sa ita yayi dedicating ma, ashe 

ma gidansu daya a nan ban sani ba sai daxu da ya fita yake gaya min, Ni kuma abinda yasa ma na sake ma yarinyar fuska tun farkon da muka hadu a Nigeria naga 

tana min yanayi da Safeenah ne, ban da haka tayi kadan in ganta da saurayina in raga mata, sannan ni a tunani na matar aure ce don ina ganin yaran nan nasan 

nata ne but now I am totally confuse….”

Deejah ta kamo hannunta a hankali tace “Kilan it’s not what u are thinking lil sis, may be they are just frnds and neighbors, Kar ki bari shaidan ya ci 

galaba a kan ki, na kuma san ki da hakuri sosai jawahir so meye nasa wannan a ran ki?” Kamar xata yi kuka tace “Anty da kyar fa take amsa min magana idan na 

mata, kamar ma haushi na take ji shi kuma sai yayi ta sa ni in mata magana, to idan ba budurwarsa bace ita me yasa xata dinga haka” Deejah ta sauke ajiyar 

xuciya tace “But ni dai she was very free with me da muka hadu a cafteria jiya” Jawahir ta jinginar da kanta jikin kujera cike da damuwa bata ce komai ba, 

tausayinta Deejah ta dinga ji, Maryam dai na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, mikewa Jawahir tayi ta dau jakarta ta wuce sama, Xaunawa Maryam tayi, 

Deejah na kallonta tace “Maryam ko dai budurwar Ayman ce Khadijah kar ki boye min?” Maryam ta bude ido tace “A’a gaskiya ban sani ba, ni ban ma taba ganinsu 

tare ba ko a schl” Tare Aliyu ya sakko da Hajiya Mariya dake rike da Shureim, shi kuma yana rike da ledan na lotion da turaren yara da small mum din tasa ta 

ba Shureim, Maryam na kallonsu tace “Ya Aliyu dama ba kwana xai yi ba” Aliyu ya kalleta yace “Aa” Hajiya Mariya ta xauna kan kujera tana kallon Shureim dake 

gabanta tace “Ka gaida mumy ka ji boy?” Ya wara idanuwansa irin na Aliyu yace “Mumy ai tana can Nigeria, Anty xan gaida maki” Murmushi Hajiya Mariya tayi 

tana shafa kansa tace “Toh ka gayar min da Anty son” Aliyu ta kalla tace “Toh yaushe Antyn xata xo ta gaisheni” Aliyu yyi yar dariya yace “Ai Antyn nan sai 

a hankali ba xuwa xata yi ba” a hankali Hajiya Mariya tace “Kar ka damu, Allah xai dai dai ta ku ko don albarkacin yaron nan” murmushi kawai Aliyu yyi bai 

ce komai ba ya kama hannun Shureim xa su fita yace “Toh bari in mayar da shi mum, it’s getting late” Shureim ya daga ma Hajiya Mariya da ta bi sa da kallo 

ganin sak mahaifinsa yana daga mata hannu, mikewa Maryam tayi ta bi bayansu, sai da suka fita waje ta kamo hannun Shureim ta durkusa tana gyara masa hular 

sweater dinsa tace “Darling ni baxa kace min bye bye ba” Dariya yayi yana kallonta ya daga mata hannu yace “Byee” mikewa tayi tana murmushi ta daga masa 

hannun ita ma sannan ta ce ma Aliyu sai ya dawo ta juya ta koma ciki, Aliyu ya sa Shureim mota sannan ya xaga ya Shiga ya tada motar ya nufi gida da shi, 

sai da suka kusa isa gidan ya juya yana kallonsa yace “Wani school kake xuwa Boy?” Shureim ya fada masa sunan makarantar, yace “Did you like the schl?” 

Gyada masa kai Shureim yayi, Aliyu yyi parking dai dai gidan yana kallonsa a hankali yace “Anty ce ta kai ka schl din?” Shureim yace “A’a uncle dina ne ya 

kai ni” Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba, can ya dauko wayarsa ya shiga kiran Khadijah, Tana xaune parlor tana karatu kiran ya shigo wayarta, tana ganin 

number ta gane ta daga ta kai kunne, Aliyu yace “ki d’an fito ki dau Shureim” Katse wayar tayi ta mike ta shiga daki ta sa hijab ta fito, kamar mai tausayin 

kasa take tafiya har ta isa inda motar Aliyu yake, fitowa yyi daga motar ya xagaya ya bude side din Shureim ya sauko da shi, Khadijah ta karaso ta kama 

hannun yaronta ba tare da ta kalli Aliyu ba tace “Sai da safe” Riko Hijab dinta yayi yana kallonta, ta juya suna hada ido gabanta ya fadi tayi saurin 

sunkuyar da kanta, murya can kasa yace “Sai da safe kuma? baki amshi sakon sa ba” Bata ce komai ba ya saketa ya bude bayan motar ya dauko babban leda ya dau 

ledan da Hajiya Mariya ta ba Shureim ya sa a ciki da ledan da yayi masa shopping duk ya hada su waje daya ya mika mata, karba tayi yace “Xa ki iya” Bata ce 

komai ba ta kama hannun Shureim ta fara tafiya, ya bi su da kallo, Shureim ya juya yana daga masa hannu, murmushi yayi ya daga masa hannun shi ma a sanyaye 

har suka wuce ciki. Manyan sweaters da head warmer ke cikin ledar da Aliyu ya bata na Shureim sai kaya kala hudu, ta bude daya ledan taga chocolates, 

biscuits sweets da dai abubuwan ci na yara, ta bude ledan da Hajiya Mariya ta basa taga lotions masu tsada da turare, tabe baki tayi ta mike ta wuce ciki da 

kayan, sai da ta ajiye kayan inda ya kamata a daki sannan ta fito da ledan chocolates din parlor, turus ta tsaya ganin khaleel xaune parlorn, ta dinga bin 

parlorn da kallo ganin bata ga Shureim ba, Mikewa khaleel yayi yana kallonta, sake ledan hannunta tayi ta juya da sauri xata koma ciki yace “Khadijah” 

tsayawa tayi amma ta ki juyowa, kawai ganinsa tayi gabanta yana kallonta, tayi saurin juyo masa baya, a hankali yace “Gaya min me na maki?” Ta turo baki 

tace “Toh ni na ce ka min wani abu ne?” D’an murmushi yayi yace “Saboda Aliyu kika canxa min Khadijah?” Shiru tayi ta rasa ma abinda xata ce masa, lkci daya 

jikinta yayi sanyi, jin shi ma bai ce komai ba ta juyo a hankali tana kallonsa, hawaye ya cika idonta tace “Me yasa xan canxa maka saboda Aliyu?” A sanyaye 

yace “Nima ban sani ba Khadijah” hawaye idonta ya xubo tace “Ko dai kai ne ka canxa min saboda budurwar ka” tana fadin haka ta fashe da kuka, kallonta ya 

dinga yi shi ma jikinsa yayi sanyi, da wani expression fuskarsa yace “Why? Why will I change because of Jawahir?” tana hararensa cikin kuka tace “Toh nima 

me yasa xan canxa saboda Aliyu?” Ya lumshe ido ya bude a hankali yana kallonta, rasa abin fadi yayi, har ransa yake jin kukanta, ya bude hannayensa cikin 

sanyin murya yace “Can… I console you?” Make kafada tayi ta juya masa baya, ya lumshe idanuwansa a hankali ya rungumota, cikin sanyayyan muryar sa yace 

“You know I love you Khadijah, and… I want you to be the mother of my kids, i want to marry you Khadijah, but you met me with Jawahir, I was with her 

before you, kin ga baxan mata walakanci ba saboda ke, jawahir na da saukin kai sosai, she don’t have problem, and I don’t want to betray her… Beside ita 

daban a rai na haka ke ma, Give me a chance to show you how much I love you plss Khadijah” kasa cewa komai Khadijah tayi, duk gaba daya jikinta yayi sanyi, 

jin tayi shiru ya juyo da ita a hankali yana kallonta, Bata yarda sun hada ido ba ta sulale nan kasa ta xauna, dukawa yayi gabanta yana kallonta murya can 

kasa yace “Say something plss Khadijah… Nace Ina son auren ki baki ce komai ba” Ta hade kai da gwiwa jin hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace “But 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button