NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 61-70

Barrister Sudais….” Sai kuma ta fashe da kuka, ya dago kanta gabansa na faduwa, da kyar ya iya cewa “what about him Khadijah?” Tace “He proposed before 

you…” Shiru yayi yana kallonta ko kiftawa babu, a sanyaye tace “He said he want to marry me, and you know I can’t tell him no Doctor, aure ma bai isa na 

biyasa abinda ya min a rayuwa ba, he deserves more than that from me, though nasan 6 years back I will confess I was in love with him, but yanxu I only 

respect him as someone that brought light to my life after my Lord, sai gashi ya dawo yace yana son aure na, baxan iya cewa bana son Sudais ba, baxan iya 

cewa baxan auresa ba, but I am afraid of his wife” shi dai khaleel bai ce komai ba, kana ganinsa kasan jikinsa yayi sanyi sosai, mikewa yayi a hankali bayan 

few seconds yace “Ohk then, Khadijah, Allah yasa hakan yafi alkhairi, wishing you all the best” daga haka ya juya xai fita ta tashi da sauri hawaye na sakko 

mata tace “But I know I love you so much Dr, bayan Sudais you are the next in my life, da ba don kai ba da ban san abinda xai sameni ba few months back, you 

made me lively once more in life, may be….” sai da ya isa bakin kofa ya juyo yana kallonta ya katse ta yace “Forget I did that to you Khadijah” daga haka 

ya fita, ta bi sa da ido xuciyarta na bugawa.

Duk yanda Khadijah ta so yin kuka ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciyarta kasa yin hakan tayi, ita ta dai san ta fadi ma khaleel haka ne don ta 

wanke kanta ko da wani abun xai faru gaba wanda bata ma fatan hakan but she never expect such harsh reply from him, why will he just decide to leave? Sai a 

sannan ta fashe da matsanancin kuka, ashe dama ba sonta yake ba, ashe dama playing dinta kawai yake, gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi a ranta, tayi 

kukan har ta ji babu dadi, duk jikinta yayi sanyi. Tana kwance bayan Isha ita kadai a daki, xuwa sannan ta daina kukan da take kuma ta samu relieve amma 

banda xafi babu abinda xuciyarta yake mata, ji tayi an bude kofar parlor, duk da wutan bedroom dinta a kashe yake hakan bai hanata dinga kallon kofar dakin 

ba, lkci daya kuma aka bude kofar Shureim ya shigo dakin, bai kunna wuta ba ya karaso ya hau saman gadon ya kwanta kusa da ita a hankali yace “Anty are you 

sleeping?” Shiru tayi bata ce komai ba idonta a lumshe, tana ji yayi addu’ar bacci yayi lamo jikinta, a hankali tace “Ka ci abinci?” Ya dago kai yana 

kallonta yace “Uncle ya bani na ci” Jawo sa tayi jikinta bata ce komai ba, sai da taji yayi bacci sannan ta kwantar da shi ta mike da kyar ta sakko kan 

gadon tana jin kanta na sara mata ta fita parlor don rufe kofa, a kan centre table ta ga Key a ajiye ta karasa gun kofa ta murda taji a rufe, alamar ya rufe 

ta waje ga Key a ajiye kan centre table, Dawowa parlorn tayi a sanyaye ta dau books din Shureim ta duba taga yayi assignment dinsa ta ajiye cikin jakarsa 

sannan kashe wutan parlorn ta koma daki ta kwanta ta lumshe ido. Har kusan karfe goma na dare ta kasa bacci, bude ido tayi da sauri jin wayar ta na ring ta 

mike xaune ta dau wayar tana kallon mai kiranta, A hankali ta daga ta kai kunne tayi sallama, daga daya bangaren ya amsa yace “Hope ban tashe ki bacci ba 

Amira” ta lumshe ido a sanyaye tace “Ba bacci nake ba” Shiru ya d’an yi na wani lkci kafin yace “Gaya min me ya faru, what’s wrong with you” Ta bude ido da 

sauri cike da mamaki tace “A’a ba komai, am just tired, me ka ga?” Sudais ya girgixa kai yace “Noo, I know you well Amira, we stayed together for two years, 

from ur voice, there is something wrong, ki gaya min meye plss” Tace “Lahh da gaske ba komai barrister, today was very hectic shi yasa” D’an murmushi yayi 

yace “Ohk then” trying to brighten up tace “Ya Namecy na fa?” Yace “Ga ta tayi bacci” Khadijah tace “Toh a shafa min kanta” Sudais yace “Alryt, Shureim yayi 

bacci?” Khadijah ta gyada kai tace “Uhm” yace “Ya kamata ya ci gaba da karatun sa a nan, I think I will be coming over next week sai inyi enrolling dinsa” A 

hankali Khadijah tace “Ai ya fara ma” Yace “School din?” Tace “Ehh” yace “Shine baki fadi min ba Amira?” Ta langwabar da kai tace “Kayi hakuri” yace “Ke 

kika sa shi schl din” ta girgixa kai tace “Dr Ayman ya sa shi” Sudais ya d’an yi shiru sannan yace “That’s nyc” Khadijah tace “Next week din xaka taho?” 

Yace “Sure, Akwai abinda xan yi, but few days xan yi, so do you need anything?”  tace “A’a bana bukatar komai, Allah ya kawo ka lafiya” yace “Ameen, let me 

leave you dear, it’s late and kilan xa ki lectures gobe koh?” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi mata sallama bayan ya tunasar da ita tayi addu’a 

sannan ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta kwanta ta ja masu duvet da Shureim. Washegari kafin karfe bakwai ta gama komai, ta ba Shureim indomie da ta girka 

masu a baki don kar ya bata uniform dinsa, Yana gamawa ta mike ta basa jakarsa ya goya ta dau nata jakar tana rike da hannunsa ta nufi kofa, tana gama rufe 

kofarta Shureim yace “Anty yau ma tafiya xa mu yi mu bar uncle?” Ta kallesa kamar baxa tace komai ba sai kuma a hankali tace “He is still sleeping dear” 

daga haka ta ja sa suka fita gidan, cab ta samar masu kamar jiya tayi dropping dinsa a schl sannan ta wuce nata makarantar duk da bata da lectures din safe, 

Wani waje ta samu ita kadai ta xauna, har ga Allah mai lallashinta take nema a lkcin, she need someone to console her, ta share hawayen da ya cika idonta 

trying hard to control her self, bata samu courage din kiran Umma ba har lkcn, tana ta xaune har lkcn lectures yayi bata tashi ba sai da ta ga kiran 

Vanessa, ta mike jiki ba kwari ta bar wajen. Bayan sun fito daga lectures sha biyu saura, Khadijah ta wuce cafteria ba tare da ta bari su Vanessa sun lura 

da ita ba, tana ta xaune nan tayi tagumi kamar ance ta daga kai ta ga Aliyu xaune yana kallonta, a hankali ta sauke kanta kasa, bayan kusan minti biyar ta 

sake daga kai tana kallonsa taga wayarsa yake dannawa, mikewa tayi ta dau wayarta dake ajiye kan table da jakarta xata fita taji a hankali yace “Iman” kasa 

kallonsa tayi tana tsaye, ya mike ya iso kusa da ita yace “Gida xa ki wuce?” Tana kokarin ganin bai ga hawayen idonta ba ta gyada masa kai, daga haka ta 

fita cafterian ya bi bayanta, har suka yi nisa bata ce masa ba shi ma bai ce mata ba, kuma kusan a tare suke tafiyar Daga karshe yayi breaking silence din a 

hankali yace “What’s wrong Iman?” bata san lkcn da ta fashe da kuka ba kamar jira take, nan da nan ya rikice mata yace “Subhanallah, me ya faru Iman, plss 

ki gaya min, wani abu ya faru ne” ta kasa ce masa komai sai kuka take xuciyarta na mata xafi, Har ransa ya dinga jin kukan nata, bai san lkcn da cikin tsawa 

yace “Plss I don’t like this Iman, ki daina wannan kukan” Tsayar da kukan nata tayi amma hawaye na ci gaba da sakko mata, wuri Aliyu ya samu ya xauna jin 

kafafuwarsa sun masa nauyi ya rike kansa, lkci daya jikinsa yayi sanyi xuciyarsa yayi masa rauni don kukan nata bashi da maraba da irin wanda tayi a ranar 

da kaddara ta afka masu six years back, A hankali ta nufi inda ya xauna ta xauna kusa da shi tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Bayan kusan minti daya ya 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button