NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 61-70

kuka ba” Tana gyada masa kai da kyar tace “Ai na daina, Allah ya ji kansa, ya hada ni da shi a aljanna” Barrister sudais yace “Ameen, Allah ya kara maki 

hakuri” Murya can kasa tace “Ameen” yace “Toh yi ma Umma magana xan mata gaisuwa” Ta mike tace “Toh” daga haka ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Umma ta fito, 

da ta amshi gaisuwar sudais tana sa masa albarka, Bai dade parlorn ba yace mata xai koma gida, tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita parlorn, ita dai har 

ranta taji Sudais ya kwanta mata, ta kuma san har abada baxa ta mance hallacin da yayi mata ba, don ko ita yayi ma, bata kuma san da me xata saka masa ba. 

Karfe tara da yan mintuna, Aliyu ya shigo parlorn, har sannan Umma na ciki bayan ta sallami wasu bakin, suka gaisa ya kara mata gaisuwa tace “Allah ya ba mu 

hakuri gaba daya, daxu su hajiya ma suka xo, mun gode kwarai” shi dai bai ce komai ba, Umma sai ta ga kamar sudais ne xaune gabanta ya girma, hakan yasa duk 

jikinta ya kara sanyi, Aliyu da ya rasa abinda xai ce yyi karfin hali daga karshe yace “Mama tana Ciki ne?” Umma tace “Ehh tana ciki bari in mata magana” 

Daga haka ta mike ta wuce ciki, bayan wani lkci ta dawo tana kallonsa tace “Aliyu tayi bacci kuwa” yace “Toh shkkn Mama, sai na dawo gobe Allah kara hakuri” 

tace “Ameen, Allah bada lada” tana son tambayarsa Shureim amma bata san ta ya ba, ta kasa daurewa daga karshe kafin ya fita tace “Aliyu ina shureim din fa?” 

Juyowa yyi yace “An tafi da shi mama” tace “Can gidan ku?” Ya girgixa mata kai, Umma tace “Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya” daga haka ya fita, umma ta 

san khaleel ne ya tafi da shi can gidan nasu. Ta koma cikin dakin Khadijah ta rufa mata bargo, Nanny dake dakin tace “Umma da ki kwana nan, tunda akwai baki 

dakin ki” Umma tace “A’a ke ki tsaya tare da ita babu komai duk daya ne” daga haka ta fita dakin.

Karfe goma na safiyar washegari Khadijah na kwance daki ta rufe ido kamar mai bacci don gaisuwar da ake mata na shureim na kara daga mata hankali, hakan 

yasa duk wanda ma ya xo umma da Nanny yake ma gaisuwar, Umma ce ta shigo dakin ta taba ta duk da tasan ba bacci take ba, Khadijah ta bude idanuwanta da suka 

mata nauyi tana kallon umman nata, cikin kwantar da murya umma tace “Taso mu je an xo maki gaisuwa” ta d’an hade rai tace “Umma ba ga ku ba bacci fa nake” 

Umma tace “Mahaifiyar khaleel ce shi yasa ma na tashe ki” shiru khadijah tayi tana kallon umma, can Khadijah ta mike xaune a hankali, umma ta kama hannunta 

ta tashi daga kan gadon, hijab ne har kasa jikinta, hakan yasa ta bi bayan umma dake rike da hannunta suka fita parlor, balarabiyar matar na xaune parlor da 

jikokinta su uku sai shureim dake jikinta shi ma, Suna hada ido Khadijah ta sauke kanta a sanyaye ta karasa cikin parlorn ta xauna, da gudu shureim ya taho 

ya rungume ta yana kallonta yace “Anty are you sick?” Kallonsa Kawai khadijah take taji kamar ta fashe da kuka, Ummu dake ta kallonta da tausayi tace “Sannu 

Khadijah, ya karin hakuri?” kasa cewa komai tayi da farko, can dai tayi karfin halin bude baki da kyar tace “Alhmdlh Mumy, nagode” Ummu tace “Allah yayi 

masa rahama, ke kuma Allah baki dangana, ya sa mai ceto ne” Umma tace “Ameen thumma Ameen” don khadijah kasa amsawa tayi, Shureim na kallonta da damuwa yace 

“Anty uncle yace min sudais travelled, why will he travel alone, why didn’t we go together plss, and now I am missing him, plss I want to go to him, I 

promise I will never fight him again….” umma ta jawosa jikinta tana kokarin boye hawayen idonta tace “He will be back soon sweetheart, and I am sure he is 

missing you too” Shureim yace “Toh Umma I want to talk to him on phone, am missing him” Ummu dake ta kallon shureim tace “Shureim har ka gaji da wasa dasu 

fadeel, ain’t they ur frnds anymore” ya juya ya kalleta yace “Noo Ummu I like them, but sudais is my brother, they will like him also” Ummu tace “Toh taho 

mu wuce tunda ka gaida Anty” kallon khadijah da kanta ke kasa shureim yyi ya dawo kusa da ita a hankali yace “Anty, is sudais coming back soon? I want the 

both of us to be frnds with fadeel and Adeel” Ummu ta mike tace “Toh xo mu wuce Shureim, idan ya dawo xa a kawo sa wajen ka” da haka suka fita parlorn bayan 

shureim ya daga ma khadijah hannu, Umma ta rakasu har bakin mota, sai a sannan taga tare suke da Khaleel dake xaune motar, ganin umma ya sakko ya gaisheta 

da ladabi sannan ya mata gaisuwa ta amsa tana murmushi tace “Allah ya saka da alkhairi, ya bar xumunci” yace “Ameen” sai da suka shiga motar gaba daya 

sannan Umma ta koma cikin gida, bata tadda Khadijah a parlor ba hakan yasa ta wuce daki ta ganta kwance, mamaki ya cika umma ta xauna kusa da ita da damuwa, 

yanxu kuma rashin kukan nata ya fara damunta don wani lkcn gwara mutum yyi kukan da kukan xuci, Umma ta yi shiru na d’an lokaci kafin a hankali tace “Look 

daughter, cry… even if it’s a little so you will feel relieve, kiyi kuka don Allah bana son wannan rashin kukan naki kuma, kin dai san matsalar ki, kar 

kije ki tada ciwon ki, it will be worst gaskiya idan haka ya faru” Jin bata ce komai ba umma ta mike a sanyaye ta fita, ba a jima da tafiyar mahaifiyar 

khaleel ba su mumy suka xo gidan, yau kam sun d’an dade kafin su wuce kuma khadijah ta fito ta amshi gaisuwar saleem, da yamma shaheedah ta xo gidan da 

sadeeq, shaheedah tayi kuka don bata ba sudais mutuwa so early ba, duk taji tausayin khadijah sosai, su Vanessa duk suka kira khadijah yi mata gaisuwar 

sudais da har lkcn a xaton su kanninta ne yan biyun. Da daddare ta fito wanka Shaheedah ta mika mata wayarta da yake vibrate, karba tayi ganin Khaleel ne ta 

daga ta kai kunne, cikin sanyin murya yace “Khadijah…” A hankali tace “Na’am” yace “Xa ki iya fitowa yanxu?” Shiru ta d’an yi kafin tace “Toh gani nan 

xuwa” shiryawa tayi ta sa hijab ta fita xuwa dakin umma, ta durkusa kusa da ita tana kallonta tace “Umma ina xuwa khaleel na kirana” Umma tace “Toh sai kin 

dawo” daga haka ta mike ta fita, cikin sanyi take tafiyar kamar mai tausayin kasa har ta isa waje, yana tsaye ya jingina jikin motarsa, kanta a kasa ta isa 

gefensa ta tsaya, murya can kasa tace “Ina yini?” Kallonta kawai yake bai ce komai ba har ta dago a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa kasa daga kallonta 

da yake yi, cikin sanyayyan muryarsa yace “Ya hakuri khadijah” ta hadiye abu da kyar tace “Alhmdllh” yace “Ban san me xan ce maki ba shi yasa ban kira ki ba 

khadijah, I know it’s very sad, it’s a great lost, but don’t forget ba wayon ki yasa Allah ya baki shi ba, and there is always a reason for everything, and 

you knw God plans best, don haka ki sa ma xuciyar ki dangana, you have ur handsome shureim, he will act as both him and his twin to you, this is part of ur 

fate, and it’s already written, plss kin san condition din ki Khadijah kar ki kara sa mutuwar sudais a ran ki I know its very painful, but idan wani abu ya 

same ki i will be very sad, come to think of ur only son, for my sake and his don Allah kiyi hakuri, forget about Sudais, but don’t forget to pray for him 

always, Allah ya hada mu gaba daya a aljanna” cike da damuwa ya kare, Khadijah tayi murmushin karfin hali tana share hawayen da ya taru idonta, tun ranan da 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button