NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 61-70

Aliyu yace kar ta sake kuka bata kara ba sai yanxu da take gaban khaleel, a hankali tace “In sha Allah Dr, baxan sa damuwa a raina ba, ae ban ma san Allah 

xai bani shi ba, so baxan butulce masa ba, na hakura Allah ya haskaka kabarinsa ya sa can ya fi masa nan, kuma ya raya min d’an uwan sa” cikin rawar murya 

ta kare maganar, khaleel ya lumshe ido yace “Ameen Khadijah, am happy with ur words” Bata ce komai ba ta dinga kallon motar da yayi parking bayan na 

Khaleel, Aliyu ne ya fito cikin motar, kallo daya khaleel yayi masa ya dauke kansa, Aliyu ya iso inda suke yana kallon khaleel ya basa hannu khaleel ya amsa 

amma fa da kyar, Aliyu na kallon cikin idanuwansa yace “Ya hakurin mu?” Khaleel yace “Mun gode Allah” Aliyu ya kalli khadijah suka hada ido tayi saurin 

sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, cikin gidan Aliyu ya shiga, khaleel na juya wristwatch din hannunsa yace “Wajen ki ya xo?” Ta girgixa kai tace “A’a” 

Khaleel bai sake cewa komai ba bayan wani lkci yace “Alryt then, xan koma Khadijah, Allah ba mu hakuri gaba daya, sleep without worries plss” ta gyada masa 

kai tana kallonsa, yana daga kai suka hada ido tayi saurin dauke kanta, yyi murmushin sa mai kyau yace “Amma kin ci abinci kuwa? Tell me the truth plss” ta 

girgixa masa kai a sanyaye tace “I don’t have appetite” yace “Toh idan na siyo maki abu yanxu make me the promise xa ki daure ki ci” tace “Akwai abinci fa a 

gida” yace “Ai na sanin, just promise me xa ki ci plsss” murmushi tayi tana fidgeting fingers dinta a hankali tace “Toh nagode” yace “Yauwa, I will be back 

soon” tace “Toh Allah ya kiyaye” daga haka ya xata xai shiga motarsa ita kuma ta shiga cikin gidan, xaune ta tadda Aliyu kan farar kujera a wajen compound 

din, kallo daya tayi masa ta dauke kai xata wuce ciki, taji a hankali yace “Iman” kasa ci gaba da tafiya tayi, maganganunsa na jiya da safe na mata yawo a 

kai, can ta juyo ta kallesa ta gan sa tsaye, yace “Plss just few minutes” tana ta tsayuwa idonta a kan yatsunta har ya iso gabanta yace “Few minutes pls” Ta 

dake da kyar tace “Toh” juyawa yayi ya nufi gun kujerun ta  bi bayansa, ya xauna kan kujerar ta xauna ita ma. Kallonta kawai yake ta ki kallon sa ta hade 

rai, murya can kasa ta ji ya fara cewa “Iman ba dan ni ba don Allah ina son ki mance abinda ya faru tsakaninmu six years back…..” Da sauri ta dakatar da 

shi tace “Toh ni nace maka ban mance bane?” Ya girgixa kai a hankali yace “I mean ki yafe min ki cire a ranki da gangan na maki hakan wllh ba da gangan 

bane, it’s a set up, though ba lallai ki yarda da hakan ba, amma don Allah kiyi hakuri mu dinga xumunci” Ji tayi kamar ta fashe da kuka don ya fama mata 

ciwon da ya ki healing har yanxu a xuciyarta, A sanyaye yace “Kin ji Iman, ki raga min ko albarkacin daya yaron da ya rage a tsakaninmu even if I didn’t 

deserve it” Khadijah ta kasa cewa komai, Bayan wani lkci ta daga kai a hankali tana kallonsa ta ga kallonta yake, da sauri ta sauke idonta tace “Ni fa na 

mance, ya kuma wuce a gu na” yace “Toh nagode sosai, amma xaki bani yaron?” Da sauri ta daga kai tana kallonsa, cikin rawar murya tace “I can’t give you my 

son, kayi hakuri…” Yana gyada kai a hankali yace “No offense, amma xa ki bari ai mu dinga xumunci da shi, I mean in dinga xuwa ina ganinsa, once in a 

while kuma xa ki bari ya xo gun mumy koh” shiru tayi ta kasa cewa komai, murya can kasa yace “Kin yi shiru” a xuciyarta tace “Nasan maganin ka” a fili kuma 

tace “Toh” Wani murmushi yayi yace “Toh nagode sosai, Allah ya raya sa” tace “Ameen” kamar ance ta juya taga khaleel ya shigo gidan rike da leda, mikewa 

tayi da sauri ya karaso har gabanta yana kallonta ya mika mata ledan, ta d’an risina ta karba a hankali tace “Nagode” ya d’an yi murmushi yace “No thanks” 

daga haka ya juya ya nufi gate, Aliyu ya bi sa da kallo ko kiftawa babu, khadijah tace “Xan wuce ciki sai da safe” mikewa yayi yace “Toh ina yake, I mean 

the boy? Though ban san sunan sa ba” da kamar khadijah baxata ce komai ba sai kuma murya can kasa tace “Sunansa Muhammad, ana kiransa Shureim, sunan late 

half dinsa Aliyu ana kiransa Sudais” kallonta yake ko kiftawa babu, ta gyara tsayuwarta tana masa wani kallo tace “Barrister Aliyu… Sunan sa ya ci” daga 

haka ta juya ta fara tafiya fuskarta daure, murmushi Aliyu yyi ya bi ta da kallo, can yace “Ohk, wait Iman, nagane barrister Aliyu ne ba ni Aliyun ba” 

tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa inda take yace “Toh yana ina yanxu, I haven’t seen him since yesterday” tace “Yana gidansu Dr khaleel” shiru yyi 

bai ce komai ba, can a hankali yace “Ohk good nyt” daga haka ta juya ta wuce ciki ta rufe kofa. Washegari aka yi sadakan ukun sudais, tun da sassafe Mumy ta 

taho da su Siyama da frnds dinta biyu, sadakar wainan shinkafa da Kayan flour ta kawo gidan, Ummun khaleel ma ta xo da jikokinta tare da shureim wajajen 

karfe tara, ita ma wainar ta kawo sai lafiyayyen rice and stew da ta kawo ma khadijah da soyayyen kaji a warmer daban, Karfe sha daya Barrister sudais ya 

bar gidan kasancewar yana da wani case, ya tura ma khadijah text cewa xai dawo da yamma, karfe sha biyu ummun khaleel ta koma gida tare da su Shureim da 

yanxu ya saba da yaran sisters din khaleel amma har Ummu ta gaji da amsa tambayar da yake mata na cewa yaushe sudais xai dawo, shi dai a kai sa wajensa, 

tausayi yaron yake bata don tsakaninsa da Allah yake son ganin dan uwan nasa, a ko da yaushe dai ce masa take soon xai dawo, sai kusan azahar Mumy suka bar 

gidan, Khadijah ta raka su har gate tayi mata godiya a sanyaye, Mumy ta sa mata albarka sannan suka wuce da yaran nata, kafin dare frnds din Umma suka fara 

watsewa gidan, Shaheedah ma suka koma Abuja tare da Sadeeq, gidan ya rage daga Khadijah, sai Nanny da Umma da Wata aminiyarta. Bayan magrib khadijah bna 

xaune kan darduma tana azkar kira ya shigo wayarta, a hankali ta daga ta kai kunne ganin barrister sudais ne, yace “Amira xa ki iya fitowa yanxu plss, am 

outside” tace “Toh” daga haka ta mike ta fita, sai da ta fara gaya ma Umma sannan ta tafi kofar gida, fitowa yayi daga mota ganinta, yana rike da 3 years 

old daughter dinsa, Khadijah ta wara ido tana kallon kyakkyawar yarinyar ta xaga inda yake ta karbeta tace “Waow ya sunanta?” Sudais ya jingina da motar 

yace “Ur namesake, ita ma Amira ake kiranta,  na kawo ta ne ta gaida Antyn ta” Khadijah tayi murmushi a sanyaye tuno kiran ta da mahaifiyar yarinyar tayi 

mata ranan da sudais xai rasu, tana taba dogon gashin yarinyar tace “Naji dadi sosai” Yace “Sure?” Ta kallesa da sauri tace “Eh mana, ko xaka bar min ita” 

yar dariya yayi yace “In dai kika shigo gidan ubanta ai taki ce ita” Wani murmushin Khadijah tayi bata dai ce komai ba, yana kallonta a hankali yace “Baxa 

ki shigo ba kenan, xaro ido tayi tace ” Ka ji na fada haka?” Yace “Uhmn dont forget who is standing before you” ta dauke kai tana ci gaba da murmushi tace 

“A barrister” ya shafa kansa yana kallonta a hankali yace “Toh ya k’arin hakurin mu dear?” Tace “Mun gode Allah” yace “Har yanxu shureim din bai dawo gida 

ba?” Ta gyada masa kai tace “Bai dawo ba” yace “Ohk, ya su umma?” Tace “Suna ciki” kamar warce ta tuna da sauri tace “Sorry na bar ka tsaye mu shiga ciki” 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button