NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 61-70

yayi murmushi yace “Aa bari in yi ta tsayuwa ta” ta turo baki tace “Allah na manta ne kayi hakuri, mu shiga ciki” daga haka ta nufi gate rike da Little 

Amira, ya bi ta da ido kafin ya bi bayanta, kan fararen kujerun dake compound din Sudais ya xauna duk yanda tayi da shi ya shiga ya gaida umma ya ki yarda 

wai sai gobe, tace “Toh bari in kai mata Little Amira ta gani” yace “Toh sai ki bar ta a can ki dawo ke kadai kar in yi rashin kunya gaban daughter na” 

dariya kawai khadijah tayi ta tafi tare da Amira dake ta waigo Abbanta ya daga mata hannu yana murmushi. umma ta xaunar da ita kan kafarta tace “Maa sha 

Allah, daughter na mai kyau da ita, Allah ya albarkace ki” khadijah tace “Naga kamar bata magana” Umma tace “A’a don dai bata san mu bane amma wannan ai ta 

isa tayi magana” fridge khadijah ta nufa ta bude ta dau ruwa da lemo ta daura kan tray ta sa glass cup sannan tace “Umma ina xuwa” Umma tace “Toh sai kin 

dawo” Har khadijah ta iso gun sudais idonsa na kanta, ta ajiye karamin tray din hannunta ta bude drink din ta xuba masa sai dai bata masa ba tace “Ya aiki?” 

Ya langwabar da kai yace “Ba dadi, Amira har yanxu you didn’t answer my questions…” Ya lumshe ido ya bude yace “Ohk let me leave it this way, you don’t 

want to answer my question” shiru khadijah tayi tana kallonsa, a hankali yace “A lot of things happened after I left you and the boys Amira, na koma 

damaturu gidanmu tare da Mamina amma gaba daya na rasa kwanciyar hankali, i was always sad then, thinking about you and the twins, hankalin Mami ya tashi a 

lkcn ta dinga cewa kilan asiri kika min ko kuma aljana ce ke, gashi nan abun na affecting dina, nan tasa aka tayi min rokan Allah, gradually dai na fara 

kokarin ganin na mance ku, na cire ku a rai na dinga harkokin gabana… saboda ku ko da ina da aiki a Abuja to baxan je ba, gaba daya na daina xuwa Abuja, 

daga Lagos, kano sai Kaduna and other States nake xuwa amma banda abj, dama ni din ba wai ina da time na yan mata bane, jiddah dai ce ita ma a Holland muka 

hadu lkcn ina karatu ita kuma tana tare da yayarta dake kasar tare da mijin ta, I never knew ma ashe Mami ta san mum dinta sun yi makaranta daya though it’s 

not as if they are frnds, to dai a haka na fara neman jiddah har aka sa aurenmu ana saura few months bikin mu na hadu da ke ranan na fito daga gida, Amira 

saboda ke nasa aka daga bikin nan har na kusan watanni shiddah, a kwana a tashi kuma na kara neman a daga cos kin kusa haihuwa lkcn, let me make things 

brief, at the end fasa auren nayi gaba daya, suka maido min da lefen da na kai all because of you, and happily then Abbana supported me, but bayan rabuwar 

ki sai gashi na koma mata cos I don’t have any option again, at first kamar baxata yarda ba daga karshe dai a cikin wata daya aka daura mana aure, 2 years 

da aurenmu da jiddah Allah yayi ma Mamina rasuwa bayan tayi fama da kidney problem, though before then duk na mata bayanin yanda aka yi na hadu dake, ban 

boye mata komai ba, kuma hankalinta ya tashi a lkcn but kawai sai ta maki fatan Allah ya hada ki da dangin mahaifiyar ki, daga nan kuma bata ce min komai 

ba, and gaskiya a lkcn kusan na ma cire ku a rai na daina damuwa cox I knw surely Allah na tare da ku, amma kullum sai na maku addu’a every blessed day, ba 

tonan asiri ba Amira ni ba wani jin dadin aure nake da jiddah ba, fitinar ta yayi yawa she is always pestering my life, ko kadan bana son hayaniya yana daga 

min hankali, bani da rest of mind idan ina gidana, ko irin weekend din nan ma ni na gwammace in tafi office in yi kallo, Amira I need a woman that i will 

find peace in, I need a better life partner, ina raga ma jiddah ne kawai saboda yarinyar nan dake tsakaninmu, and divorce is totally out if it baya cikin 

tsarin rayuwata, I need you plss Amira” Khadijah taji kanta ya mata nauyi sosai ta rasa abinda xata ce masa, bata san lkcn da hawaye ya dinga sakko mata ba 

tana kallonsa, deep down her kuma ta rasa me yasa khaleel ya fado mata.

Shiru Umma tayi tana kallon khadijah, a hankali tace “Ko saboda me?” Khadijah ta langwabar da kai cikin sanyi tace “Umma I will be lonely all alone, I want 

him to be by my side” Umma tace “Life with him there won’t be esay Khadijah, karatun ki na bukatar natsuwa sosai kin sani, shureim will ba a distraction, 

baxai yiwu ba Khadijah” da damuwa Khadijah tace “Umma ai shi ma makarantar fa xai dinga xuwa, plss ummata” Umma tayi shiru alamar bata san me xata ce ba 

kuma, can tana ci gaba da linke kayan da take tace “Rabani da shi dai kike son yi koh?” Murmushi Khadijah tayi kunya ya kamata tace “A’a wllh ummata” Umma 

tace “Gaskiya ne mana, ke gashi baki kusa da ni, grandson din ma kina son daukesa” Khadijah ta xaro ido, da damuwa tace “Allah sarki Ummata ba haka bane ba 

fa” Murmushi Umma tayi tace “Toh shkkn tunda kina son tafiya da shi sai ku je, Allah ya tsare” Sosai Khadijah taji dadi, Umma ta xauna gefen gadon tace 

“Yanxu ya xa mu yi da maganar sudais Khadijah, kin ga samu na yayi ya min magana….”  khadijah tace “Umma ya san xan koma makaranta ai, daxu ma mun yi 

magana da ya xo, kuma kinga 100k da ya bani ai saboda xan tafi makaranta ne” Umma tace “Toh ai ban ce bai sani ba, kin san dai dole sai an je katsina koh?” 

Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, bata son jin sunan garin ita kam, Umma ta mike ta ci gaba da abinda take tace “Shi kuma Aliyu ai ya kamata ki sanar 

masa xa ki tafi da Shureim din koh, ko kuma kije ma da yaron yayi sallama da mahaifiyar Aliyun” Khadijah dai bata ce komai ba idonta a kan wayarta. Can 

gidansu Khaleel kuwa Ummu ta sa driver yyi ma Shureim siyayya da taji tare xa su tafi UK da uwar sa, Khaleel dake xaune bedroom dinta yana duba kayan yace 

“Sun gode Ummu” Ummu tace “Khaleel ina son mu yi magana fa da kai, gashi gobe da sassafe xa ku wuce” ya maida hankalinsa gaba daya kanta kamar baxai ce 

komai ba, sai kuma yace “Ina ji Ummu” sure ya san kwanan xancen amma yayi pretending bai sani ba, Ummu ta kwantar da murya tana kallonsa tace “Abuu kasan fa 

saura wata daya kachal bikin ku da jawahir kuma naji ko magana baka yi” Khaleel ya shafa kansa yace “Ina sane Ummu” tace “Toh Alhmdllh tun da kana sane, 

amma ba wani shiri da xa ku yi ne?” Shiru yyi bai ce komai ba, can ya dago ya kalleta yace “Ummu tun da ba laifi bane ina son hada su da mahaifiyar yaron 

nan na aura….ina da interest a kanta” Ummu ta dinga masa wani kallo tace “Kana da hankali ma kuwa khaleel???” hade rai yayi, kan kace me ya juya xuwa 

Arabiya… toh nan fa ake yin ta, don Mai typing dai ba jin yaren take ba ina laifin ma yayi turanci, tun tana d’an tsintar daddaya har ya kai ya kawo ta 

ajiye takardar da Biro kawai ta dafe kai, ganin khaleel fa sai xuba larabci yake a fusace ga ummu sai kallonsa take ta kasa cewa komai mai typing tasan abun 

babba ne, ba fans ba, har ita tana son jin abinda khaleel ke cewa don haka ta juya da sauri don nemo kanwarta Ilham ta mata translating, can ita ma ta 

sameta xaune tana halinta wato nukurci, ashe dai ba xancen translating din larabci, rai ba dadi mai typing ta kwashi legs ta koma, nan ta ga har khaleel ya 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button