NOOR AL HAYAT 61-70

gama jawabinsa yana danna waya amma fuska a murtuke, Ummu ta d’an yi murmushi a hankali tace “Ni na isa khaleel? What am saying in here is that, ina laifin
bayan anyi bikin naku da Jawahir sai ka auri Khadijahr babu mai hanaka yin hakan ae, hakan ma xai fi” Washegari Khadijah ta gama hada few abubuwan da xata
bukata domin komawa UK, umma kuma ta hada ma Shureim nasa kayan cike da jin kewan yaron gashi khaleel ya rabasu da shi tun rasuwar sudais, karfe takwas
saura khaleel ya taho gidan tare da shureim, Khadijah tana bedroom ta gama daukar masa kadan daga takalmansa, ganin na sudais a gun yasa lkci daya mood
dinta ya canxa ta koma ta xauna a sanyaye, tun bayan rasuwarsa dama Umma ta bada komai nasa a gidan saboda Khadijah xata fi samun nutsuwa, takalman ma
mancewa tayi bata bayar ba, Nanny ce ta shigo dakin tace “Khadijah jiran ki fa suke” a sanyaye Khadijah ta mike ta fito rike da takalman Shureim, driver ne
daga gidansu Khaleel xai kai su airport din, Shureim dake jikin Umma ya sakko da sauri ya rungume Khadijah yace “I missed you Anty” ta shafa kansa tace “I
missed you same” Umma tace “Toh kuyi maxa yana jiran ku a mota” Khadijah tace “Yanxu Shureim din ya shigo?” Umma tace “Yanxu ya shigo” Khadijah ta karasa
gun umma ta rungume ta tace “Ummata sai mun dawo” Umma tayi kokarin ganin bata fara hawaye ba a hankali tace “Toh Allah maku albarka daughter, Allah ya
tsare min ku, sannan ki kula da kanki plss” murya can kasa Khadijah tace “Nagode Umma” Nanny na rike da shureim cike da kewarsa xata rakasu bakin motar,
Khadijah na isa bakin kofa ta juyo a hankali tana kallon Umma tace “Toh Umma ba a kai sa yayi ma Mumy sallamar ba kuma, I mean shureim” Umma tace “Lah kin
ga ni har na manta, to ki yi ma Khaleel din magana sai ku fara biyawa can a gurguje ki kai sa kafin ku wuce airport” Khadijah ta gyada mata kai ta fita
parlorn, Shureim ne ya bude back seat Khadijah ta dinga kallon khaleel dake xaune sanye da glasses a idonsa yana operating wayarsa, Shureim ya shiga motar
sannan ta shiga tana daga ma Nanny hannu, gaishe da Nanny khaleel yayi ta amsa da fara’a ta masu Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ta koma ciki. Sai da
suka dau hanya sannan khadijah ta kalli khaleel a hankali tace “Good morning” yace “Morning how was ur nyt?” Ta sauke idonta tace “Alhmdlh” Wayarsa dake
ring ya daga ya kai kunne, sai bayan da ya gama wayar Khadijah tace “Umma tace plss kafin mu tafi in kai shureim wajen mum din Aliyu su yi sallama, idan
suka yi waya tana yawan tambayar ta shi….” Khaleel yace “Ohk then” daga haka ya fadi ma driver anguwar da xai fara kai su, tafiyar kusan minti ashirin
suka yi suka iso gidansu Aliyu, Bayan drivern yayi parking a inda Khaleel ya nuna masa, khaleel ya juya yana kallonta yace “Ku shiga toh” tace “Kai baxa ka
shiga ba” da sauri yace “A’a, am waiting for you two a nan” a hankali khadijah tace “Ohk,” daga haka ta bude motar ta sauka tana kallon Shureim tace “Come
down” daga mata hannu yyi yace “Anty ki dauke ni” ta hade rai tace “Sakko my friend” khaleel yace “Ki daukesa mana ko baxa ki iya bane?” murmushi kawai tayi
ta dauki yaron nata ta shiga cikin gidansu Aliyu yana daga ma khaleel da ya bi su da ido hannunsa, A hankali khadijah ta murda kofar taji a bude ta shiga,
babu kowa parlorn, tana jin Shureim na ce mata gidansu wannan uncle din nan nasa ne, tana kokarin sauke sa kasa sai ga Aliyu yana sakkowa stairs, jallabiya
ce baki jikinsa tayi saurin dauke kanta bayan sun hada ido, tana ta tsaye har ya iso inda suke tsaye, ya mika hannu ya karbi shureim komawa baya tayi da
sauri don wani shock ta ji ta dalilin hannunsa da ya taba jikinta, shi kam sai kallonta yake ya maxa ya kawar da memoryn da bai son tunawa a ransa, Murmushi
Shureim yake yana kallonsa yace “Uncle good morning” Aliyu ya shafa kansa shi ma yana murmushin a hankali yace “Morning how are you sweetheart” yace “Am
fine” Kallon khadijah yayi suka kara hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yace “Good morning Iman” kame kame ta fara yi, can tayi saurin cewa “Ina kwana,
wajen mumy muka xo” yace “Ohk tana Bedroom” taki yarda ta sake kallonsa tace “Toh kayi mata magana muna sauri ne” yace “mu je up stairs” daga haka ya fara
tafiya ta bi bayansa xuciyarta na bugawa wannan tunanin da yake ita ma shi take a lkcn. A hankali ya bude kofar dakin mumy ya shiga da sallama, tana xaune
da aminyarta, ta daga kai tana kallon Aliyu, ya sauke yaron hannunsa ya tafi da gudu ya hau kanta yace “Mama good morning” lkci daya bakin cikin dake
tattare da fuskar Mumy yayi fading ta rungume yaron tana murmushi sosai tace “Kai da waye Shureim, wa ya kawo ka” Yace “Ni da Anty na” Aliyu ya juya yana
kallon khadijah da ke tsaye bayansa ta ki shigowa ya koma gefe ya tsaya, Mumy na kallon ta tace “Maa sha Allah ashe tare ku ke, toh ki karaso mana Khadijah”
kanta a kasa ta karaso ciki a sanyaye ta xauna tace “Ina kwana mumy” da fara’a mumy tace “Lafiya lau Khadijah ya gidan, ya su ummar ki?” A hankali khadijah
tace “Suna lafiya Mumy” gaishe da kawar mumy tayi sannan tana kallon mumy tace “Mumy dama xan koma karatu ne kuma xa mu je da shureim shine Umma tace in
kawo sa yayi ma ki sallama” Mumy tace “Allah sarki, amma naji dadi sosai wllh, Allah ya kai ku lafiya, ya bada abinda aka je nema” kallonta Kawai Aliyu yake
jin abinda ta ce, Mumy ta mike tace “Bari in kai sa su gaisa da Abba yana nan” daga haka ta fita, Hajiya Salma dake ta kallon khadijah cike da tausayinta
tace “Allah ya bada nasara kin ji Khadijah, sai a kula sosai” Khadijah ta sunkuyar da kai kasa tace “In sha Allah Mum na gode” Bayan kusan minti goma Mumy
ta dawo, duk khadijah ta damu saboda khaleel da ta bari a mota, Mumy tace “Toh mu je kema ku gaisa da Abban koh” khadijah ta kasa dago kanta ta mike da kyar
ta bi bayanta har xuwa side din Abba, da fara’a ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mutanen gidansu, ba su dau lkci a parlorn ba suka fito tare da mumy, Lkci
daya mood din mumy ya canxa a hankali tace “Mu shiga ki gaida iklima” Khadijah tace “Toh” daga haka ta bi mumy suka shiga dakin. Kallon iklima kawai
khadijah take ganin yanda ta rame kamar warce ta shekara tana ciwo, cike da karfin hali tace “Sannu iklima Allah ya sauwake” kallonta kawai Iklima take ita
ma ta kasa cewa komai, Mumy na kallon khadijah tace “Mu je” Khadijah ta bi bayan mumy a sanyaye, Mumy tace “Babu daman in baki turarruka tunda flight xa ku
bi Khadijah, amma kar ki damu xan tura ma Maryam kudi a can ta siya ma ki, sai tayi ma Shureim ma shopping” murmushi kawai khadijah tayi tace “Ba komai mumy
na gode” Har downstairs mumy ta rakata, Aliyu dake xaune parlorn tare da shureim ya mike ganin sun sakko, mumy tace “Toh Allah ya tsare, nagode Khadijah”
Khadijah tace “Ameen mumy” daga haka ta bi bayan Aliyu da shureim don har sun nufi kofa, a tsakar compound din Aliyu ya jira Khadijah ta iso inda suke, bata
yarda ta kalle sa ba xata wuce su ya riko mayafinta, juyawa tayi amma ta kasa kallon idonsa, murya can kasa yace “Baxa mu yi sallama ba?” Still ba tare da
ta kallesa ba tace “Mumy na xo yi ma sallama ba kai ba” yayi murmushi yace “Ohk, Allah ya kiyaye hanya, sai mun hadu a can, cos am also leaving tomorrow”