NOOR AL HAYAT 61-70

Khadijah bata tanka sa ba yana rike da shureim har suka nufi gate, kasa daurewa tayi daga karshe tace “Me ya samu iklima haka?” Da kamar Aliyu baxai ce
komai ba sai kuma yace “She is suffering from Hiv” Khadijah ta xaro ido tana kallonsa a tsorace, yace “Yea, anjima dangin mahaifinta xa su xo su tafi da
ita…” Lkci daya hawaye ya cika idon Khadijah tace “Toh Anty khadijah fa?” Yace “Tana asibiti, tot kin san tayi hatsari?” Khadijah ta girgixa kai tana
kallonsa, yace “She had accident 2 weeks back” da damuwa tace “Toh ya jikin nata?” Yace “Ni tun lkcn da na kai su mumy ban san ke komawa ba so I don’t knw”
Khadijah tayi shiru duk jikinta a sanyaye, Aliyu yyi murmushi bai ce komai ba har suka fito waje, Khadijah ta bude back seat tana kallon khaleel da damuwa
tace “Don Allah kayi hakuri mun bata maka lkci” ya d’an yi murmushi yace “No problem” tun da Khalil ya kalli Aliyu sau daya bai sake kallonsa ba, Aliyu yace
“Barka da asuba” sai a sannan khaleel ya kara kallonsa yace “Good morning” Shureim ya shiga mota yana daga ma Aliyu hannu sannan khadijah ma ta shiga, suna
hada ido da Aliyu ta sunkuyar da kanta, Aliyu na kallonta yace “Allah ya tsare” Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace “Ameen” ya rufe masu motar, driver
ya tada motar suka bar layin, shureim ya fiddo bandir din Dari biyar a aljihunsa yana nuna ma Khadijah yace “Anty wannan Papa din nan ya sa min kudin a
aljihuna, I told him no but he didn’t even listen to me” Khadijah ta dinga kallon kudin, ya ciro wani kudin yana nuna mata yace “Uncle ma ya bani wannan”
Khaleel dake danna wayarsa bai dai ce komai ba, Khadijah ma ta rasa abinda xata ce.
Khaleel na rungume da Shureim suka sakko daga cikin jirgi hannunsa daya rike da trolley din yaron, Khadija na biye da su har suka iso gun da xa su hau taxi,
khaleel ya juya yana kallonta ganin yanda tayi laushi alamar ta gaji, murmushi yayi ya dauke kai, ta turo baki ta rungume hannayen ta, a Booth din taxin ya
ajiye trolleyn hannunsa, ta karaso a hankali ta ajiye nata jakar a ciki, ya xaga ya shiga back seat ita ma ta shiga ta rufe, sai a sannan yana kallon mai
taxin yace “Bridge street” har suka iso gida idon Khadija a lumshe suke, khaleel ya bude motar ya fito ya dau Shureim dake ta bacci, sai a sannan ta bude
idanuwanta yace “Ae da mai cab din ya wuce da ke” ta bude side dinta ta fito, Ya fito da jakunkunan sannan ya ba ma mai taxin kudi, na Shureim ya dauka ta
dau nata ta bi bayansa, suna isa bakin apartment dinsu, ya juya yana kallonta yace “Hope baki mance makulli ba” karamar jakar hanunta ta bude ta dubo
makulin, ya fara bude nasa sannan ya amshi nata makullin ya bude mata yana kallonta, hannu ta kai xata amshi Shureim dake bacci jikinsa yace “Hey, ai ba
gudu xan yi da shi ba hajiya” Wani kallo tayi masa ta wuce ciki ta rufe kofarta, duk yanda ta so ganin ta tsaftace ko ina kafin ta huta kasa yin hakan tayi
don wani bacci ta dinga ji, wanka kawai tayi ta sauya kaya tayi slh sannan ta cire bedsheet din kan gado ta shimfida wani sannan ta kwanta, nan da nan bacci
ya dauketa. Cikin bacci ta ji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Shureim kusa da ita yace “Anty, uncle yace in tashe ki kiyi sllh ki ci abinci” mikewa
xaune tayi tana kallon agogo taga bakwai na yamma ya wuce, ta kalli Shureim tace “Have you eaten?” Yace “Ehh uncle ya siya min, naki ma yana parlor” Shiru
tayi tana kallonsa sai kuma tace “Kayi wanka?” Gyada mata kai yayi, ta sauka daga kan gadon tace “Bari in yi alwala” Ko da ta fito daga bayin bata ga
Shureim ba, tayi sllh sannan ta fara gyare gyaren gidan tun daga dakin har parlorn, ta tsaftace ko ina tayi mopping sannan ta koma daki don dauko wayarta
sanin Umma xata yi ta kiranta, mis cals biyu ta ga nata da na Barrister sudais, Umma ta fara Kira bayan sun gaisa Umma tace “Kun sauka lafiya?” Tace
“Alhmdllh Umma” Umma tace “Ina Shureim din?” A hankali Khadija tace “Yana can wajen khaleel” Umma tace “Toh Ina gaishesa, ki kula kin ji ko daughter?”
Khadija ta gyada mata kai tace “In Sha Allah Umma” Umma tace “Toh Allah maku Albarka” Khadija ta amsa da “Ameen” daga haka suka yi sallama da Umma, Sudais
ta shiga kira, bayan wani lkci ya katse ya kirata, A hankali tayi masa sallama bayan ta daga,ya amsa yace “Ina kika shiga Amira?” Ta langwabar da kai tace
“Bacci nayi” yace “Ohk, ya hanya?” Tace “Alhmdllh ya takwarata?” Yace “She’s good, where is my son?” D’an murmushi tayi tace “Yana waje” yace “Waje kuma,
babu sanyi ne?” Tace “Akwai amma it’s not much” yace “Ohk try and get him a lot of sweaters, the cold won’t be funny from next week I guess” tace “Haka ne”
yace “Xan tura maki kudi sai ki siya masa very thick one’s, kema ki siya” murmushi tayi bata ce komai ba, yace “Alryt then, sleep tight dear” tace “Toh
nagode ka gaida min Amira” yace “Xata ji” daga haka ya katse wayar, kwanta tayi a hankali ta lumshe ido tana tuna moment dinsu da Barrister sudais, tashi
tayi daga karshe duk a sanyaye ta fita parlor, abincin da khaleel ya siyo mata dake kan center table ta bude don ganin wani iri ne, ta d’an tabe baki ta
rufe ta mike ta shiga kitchen ta kunna wuta, noodles ta fiddo xata dafa, jin motsi a waje ta leka window a hankali, xaune ta gansa kan kujera yana sanye da
glass idanuwansa kan wani babban textbook yana rubutu, babban sweater ne jikinsa da neck warmer, Shureim ma dake sanye da sweater da head and neck warmer na
tsaye daga bayansa ya jingina jikinsa yana kallon abinda yake yi, a hankali khaleel ya juyo ganin ta kunna wutan kitchen suka hada ido tayi saurin dauke
kanta, mayar da dubansa yyi kan littafin gabansa yace “Xa ki fara koh?” Ta hararesa tace “Xan fara me?” Yace “Kin fi ni sani ai” Bata tanka sa ba ta bar
wajen ta shiga yin abinda ya kawo ta kitchen din. Tana gama dafa indomien ta dauka ta fita ta koma parlor. Tana xaune parlor Idonta na kan wani material din
karatun ta misalin karfe goma saura aka danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta tsaya, a hankali tace “Yes?” Muryar khaleel taji yace “Hmm koh?” Bude kofar
tayi ya shigar da Shureim parlorn ta yace “Alryt good nyt” tace “Allah ya tashe mu lafiya” juyawa yayi ya koma apartment dinsa, ta rufe kofarta ta kama
hannun Shureim ta kashe wutan parlorn ta wuce daki tana rike da shi tace “Me yasa baka yi bacci can ba” yace “I said I want to come to you” bata ce komai ba
ta rufe kofar dakin bayan sun shiga ciki. Washegari da safe Shureim na bacci ta fita xuwa supermarket, har ta dawo bai tashi ba ta ajiye duk abubuwan da ta
siyo ta fara hada breakfast, muryar khaleel taji daga waje yace “Good morning” ta yi still don bata san yana gun ba, can dai tace “Ina kwana?” Yace “Hamdan,
Ina kika je da sassafe cikin sanyin nan?” Ta d’an bude ido tace “Gadi na kake yi kuma?” D’an murmushi yyi jin bai ce komai ba ta leka window a hankali, 3qtr
ne jikinsa da sweater mai hula yana tsaye bata dai ga abinda yake ba, kallonsa kawai take, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, takowa yyi har gun
windown yana kallonta yace “Ina kika je?” Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta Sauke idonta kasa a hankali tace “Market” yace “What did you get?” Ta hade