NOOR AL HAYAT 61-70

rai tace “Ina ruwanka” yyi murmushin sa mai kyau ya sauke hular kansa yace “Ohk then” daga haka ya juya ya bar wajen, Irish ta soya da kwai sai ruwan Lipton
da ta dafa da kayan kamshi, har xata fita kitchen din ta dawo, ta fi minti biyu a tsaye kamar mai contemplating abinda xata yi, kawai daga karshe ta dau
wani warmer ta debi Irish din da kwai ta xuba ruwan Lipton din a wani karamin flask ta ajiye su a gefe ta fita kitchen din, Bedroom dinta ta wuce ta tada
Shureim dake bacci ta wuce bathroom da shi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta sa yayi alwala suka fito, sai da ta gama shiryasa sannan ta shimfida
masa darduma tace “Idan ka gama sllhn meet me at the parlor” daga haka ta fita, ba a dau lkci ba ya fito yace “Anty na gama, good morning” tace “Morning
dear” kitchen ta tafi ta dauko flask din Lipton din ta mika masa tace “Ka kai ma uncle sai ka dawo ka karbi dayan” yace “Toh” ta bude masa kofa ya fita, ta
danna bell din apartment din khaleel sannan ta juya ta koma ciki da sauri, Shureim na tsaye bakin apartment din khaleel ya bude kofar, dukawa yyi yana
kallon yaron murmushi dauke fuskarsa yace “Good morning handsome” Shureim yace “Good morning uncle, Antyna tace in kawo maka” karba yyi yana kallon flask
din sannan ya jawo yaron ciki, Shureim yace “Uncle tace it’s remaining one” rufe kofar yayi yace “Kyaleta xata kawo da kanta” Khadija tayi ta jiran dawowan
Shureim amma shiru, mikewa tayi ta bude kofa ta leka waje a hankali taga kofar apartment din nasa a rufe, kiran Shureim ta shiga yi, Shureim dake xaune yana
cin bread and butter da khaleel ya basa da shayi ya mike da sauri yace “Uncle Anty is calling me” xaunar da shi yyi yace “Don’t worry she will come in now”
Khadija ta gaji da tsayuwa amma Shureim bai fito ba, komawa ciki tayi ta rasa yanda xata yi da Irish da ta dibar ma khaleel, daga karshe ta wuce kitchen ta
dauko ta sa hijab ta fito waje, tsaye tayi tana kallon baturiyar dake bakin apartment dinsa, baturiyar ta mata murmushi tace “Good morning” dauke kai
Khadija tayi kamar ana tilastata tace “Morning” xata koma ciki sai gashi ya bude kofar, Kallon Khadija yayi kafin ya dubi baturiyar dake masa murmushi tace
“Good morning Dr Ayman….” Juyawa Khadija tayi ta shige apartment dinta ta rufe, Khaleel na kallon baturiyar yace “Morning Lydia, hw did u knw I am back?”
Tace “I just met with Dr Ahmad, he told me you are back” shafa kai khaleel yayi a hankali yace “Ohk, we will meet later in the day, I am about going out
now” tace “Ohk do you mind dropped me?” Ya girgixa kai yace “You get a taxi” daga haka ya rufe kofarsa, yana ta tsaye bakin kofa bayan kusan minti biyar ya
bude kofarsa ya ga ta wuce, fitowa yayi yana kallon kofar Khadija, a hankali ya murda ya ji a bude ya shiga parlorn.
Not edited.????????♀
Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta inda xata fito amma bata fito ba, karasawa yayi kan kujera a hankali ya xauna ya jinginar da
kansa jikin kujerar ya lumshe manyan idanuwansa, bayan wani lkci sai ga ta ta fito daga daki da hijab a jikinta, mikewa yyi yana kallonta amma bai ce komai
ba, Babu yabo babu fallasa tace “How may I help you?” Yana shafa lallausan gashin kansa a hankali ce “Where is…. the food?” Tace “Wani abincin? I didn’t
cook with you ai” ya d’an kalleta na few seconds sai kuma ya nufi kitchen cikin takunsa na kasaita ta bi sa da ido, rike da warmer din Irish din ya dawo
yana dubanta yace “This” daga haka ya bude kofa ya fita ta bi sa da harara ta ja tsaki. Khadijah na ji suka fita gidan da Shureim wajen karfe goma, kafin
sha daya ta gama duk abinda xata yi a gidan ta kwanta duk da ta so tafiya makaranta amma ta bari gobe kawai, ganin bacci ya ki xuwa mata ta dauko kayan
karatun ta ta shiga yi, tana ta xaune har azahar yayi, ta mike daga karshe ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta kwanta, lkci daya
bacci ya dauketa. A hankali khadijah ta bude idonta bayan wasu awanni ta mike xaune cikin sanyin jiki tana tunanin mafarkin da tayi, bell taji an danna
wanda hakan sai da ya d’an tsorata ta, bayan wasu yan dakiku ta mike tsaye da kyar har lkcn mafarkin ya kasa fita a xuciyarta, jin an kara danna bell din ta
sa hijab ta fita kamar mai counting steps dinta, tana isa gun kofar ta bude a hankali, Vanessa da Angela sai Maryam ta gani bakin kofar, sosai gaban Khadija
ya fadi ganin Maryam bakin kofar, da farko kallonta ta dinga yi, sai kuma ta kirkiri murmushi tana masu sannu da xuwa ta basu hanya suka shigo parlorn,
mamaki ta dinga yi a ranta, me ya kawo Maryam gidanta, after all she isn’t her course mate nor her frnd, bayan sun gaisa suka mata gaisuwar Sudais, khadijah
ta mike ta wuce kitchen don kawo masu ruwa da cakes din da ta siyo daxu da safe da ta fita, Maryam na kallonta tace “Mumy tace da daya twin din kika taho
koh?” Ba tare da Khadija ta kalleta ba tace “Ehh tare muka xo” Maryam tace “Yana Ina?” Khadija tace “Ya fita ne” Maryam bata sake cewa komai ba, Khadija
suka dinga hira da su Vanessa, sai dai hirar duk ta makaranta ce bayan kusan minti talatin suka ce mata xa su koma, har waje ta rakasu inda xa su samu cab,
wani cab ne yyi parking dai dai su, aka bude cab din khaleel ya fito tare da Shureim da wani leda hannunsa, kallonsa kawai Maryam take, ya wara ido ganinta
yace “Isn’t this Maryam?” Yar dariya tayi tace “A nan anguwar kake dama Dr khaleel?” Yace “Sure, me kika xo yi nan?” Ta nuna masa Khadija tace “My frnd, mun
xo mata gaisuwa ne yaron ta ya rasu” ya kalli khadijah yace “Ohh that’s nyc, a schl kika santa kenan” Maryam tace “Eh a schl na santa” yace “Good” Maryam ta
karasa gun Shureim tana kallonsa a hankali tace “Hello boy” gaisheta yayi, ta amsa tana murmushi jin muryarsa kamar na Aliyu, Su Vanessa ma suka taho gunsa
duk ya gaishe su da turanci, ita dai Khadijah na tsaye, Khaleel na kallon Maryam yace “Alryt bari in shiga ciki Maryam, sai anjima” tace “Yauwa Dr, ya
mutuniyar fa?” Har ya fara tafiya ya tsaya yace “Wai jawahir?” Tace “Ehh” yace “Haba ai ke ya kamata in tambaya, kun fi kusa” Maryam tace “Au haka ma xaka
ce” Yace “Yes, nasan yau ma baxa ku rasa waya ba ni kam bata kira ni ba” Maryam tace “Lallai ma, ita ce ma xata kira ka kenan, soon ma xa su xo hutu nan da
yayarta ar” Khaleel ya d’an kalleta yace “Really?” Girgixa kai Maryam tayi tace “Dad dina naji ya fadi haka nima” Ya dauke kai ya nufi cikin gida yana rike
da Shureim yace “Allah ya kawo su lafiya” Taxin da Khaleel ya sauka suka hau Khadija ta daga masu hannu tace “We’ll meet in school tomorrow, thank ya all”
daga haka ta wuce ciki. Khadija na kitchen tana girkin lunch khaleel ya taho ya tsaya gun window yana kallonta yace “Ya kike?” Dauke idonta tayi daga
kallonsa tace “Lafiya lau” Shureim dake kusa da shi a tsaye yace “Anty I am missing you” Khaleel yace “Bude masa ya shiga” kallon Shureim tayi sannan ta
ajiye wukar hannunta ta isa gun kofar ta bude, Khaleel ya shigar da Shureim ciki sannan ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, ya jawo kofar ya rufe gam, ya
jinginar da ita jiki yana mata wani kallo murya can kasa yace “Ni kike daga ma hanci” A tsorace tace “Kaga bana son haka ka bari, ka kyaleni plss” Duk ta