NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 61-70

kasa kallon idanuwansa da ya tsare ta da shi ga kamshin sa da ya cikata, A hankali yace “Fushin me kike yi da ni?” cikin rawar murya tace “Toh Fushin me xan 

yi da kai Dr, don Allah ka sakeni” d’aga kanta yayi tayi saurin runtse idanuwanta xuciyarta na bugawa, ya dinga kallon lips dinta, a hankali ya saketa yace 

“Where did you know Maryam from?” Ta shiga kokarin bude kofarta da sauri, ya rike handle din kofar yace “Au Ina maki magana xaki wuce?” Ta juyo kamar xata 

yi kuka tace “Ni ban santa ba sosai fah, kawai ina ganinta ne a schl kawar course mates dina ce” yace “Ohk, don’t frnd her for some reasons kin ji?” 

kallonsa tayi da sauri, lkci daya tayi saurin kauda kanta xuciyarta na bugawa, his eyes are always not encouraging, d’an murmushi yayi a hankali yace “Ki 

gaya min meye da idona Khadijah?” Ta hade rai tace “I don’t like them” wani murmushin yyi kamar me rada yace “Xan koya maki son su” murda kofar yayi ya bude 

ta juya da sauri ta shige kitchen din ta rufe kofar da makulli fuskarta daure. Shureim na cin abincin da ta xuba masa bayan magrib yace “Anty uncle yace 

gobe xan fara xuwa schl, we even went to the schl, uniform din na gidansa, in je in karbo?” Khadija dake ta kallonsa tace “I didn’t send you” yace “Ohk” 

sannan ya ci gaba da cin abincinsa. Washegari da asuba khaleel ya miko mata uniforms din Shureim ta kitchen, rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta karba 

tana kallonsa a hankali tace “Mun gode” ko kallonta bai yi ba ya wuce. Karfe takwas saura khaleel yayi dropping Shureim a makarantar da yayi enrolling 

dinsa, Khadija dake xaune bayan motar ta bi Shureim dake daga mata hannu da kallo har aka wuce da shi cikin makarantar, khaleel yayi parking in da ya saba 

ajiye ta a schl ya juya yana kallonta, ta bude motar a hankali ta fito,, bata ce komai ba ta kulle motar ya ja motarsa ya bar wajen, a sanyaye ta karasa 

department dinsu don saura few minutes a shiga lectures. Karfe sha biyu saura Khadija ta fito daga lectures, cafeteria ta tafi ita kadai ganin Maryam na 

tare da su Vanessa, tana xaune ita kadai a cafterian da lemonade a gabanta idonta a kan wayarta tana dannawa, kujerar dake kallon nata taga an ja ta daga 

kai da sauri, sosai gabanta yayi mugun faduwa bayan sun hada ido, tayi saurin dauke idonta, xaunawa yayi yana kallonta a hankali yace “Hi Iman” kasa cewa 

komai tayi ta kuma kasa dago kanta, bayan few seconds ta dago da kyar tana dubansa tace “Hello” Murmushi yayi yace “Ya boko?” Kasa amsawa tayi lkci daya 

little Sudais dinta ya fado mata, taji xuciyarta ya mata rauni, ganin tayi shiru ya fiddo wayarsa ya fara dannawa, a hankali tace “Ya su mumy” yace “Na baro 

su lafiya, how is Shureim?” Tace “Yana schl” yace “Har kinyi enrolling dinsa a nan?” Tace “Ehh” shiru ya d’an yi, kafin a hankali yace “How much did you 

spend Iman?” Ta kallesa lkci daya ta hade rai tace “What about it?” ya girgixa kai da sauri yace “Ohk, I am sorry I asked” bata ce komai ba, ya mike yana 

kallonta yace “Alryt, I will be on my way now Iman, my regards to Shureim” da ido ta bi sa, har ya tafi ya dawo da sauri ya sa hannu a aljihunsa yace “I 

think I’ve got something here” Chocolate guda daya ya fiddo ya duka yana kallonta ya mika mata yace “Ki ba Shureim plss” a hankali ta sauke idonta daga 

kallonsa ta karbi chocolate din tace “Ohk” yace “Thanks” daga haka ya mike ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya bace mata, kallon chocolate din hannunta 

tayi ta bude jakarta ta saka a ciki, tayi tagumi tana tunanin me yasa in dai ta ga Aliyu sai little Sudais dinta ya fado mata, or is it because of the 

resemblance, jin wayarta na ring ta sauke kai a hankali tana kallon mai kiran nata.

Sorry for the short chappy kilan in kara post around one na dare????

A hankali khadijah tayi picking wayar ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren ya amsa yace “Ya kike Amira?” Khadija tace “Alhmdllh ya aiki?” Yace 

“Lafiya lau, account number ki xa ki turo min yanxu” shiru ta yi na wani lkci kafin tace “Barrister…. Shureim fa yana da kayan sanyi, wllh you shouldn’t 

bother….” Katse ta yayi yace “I am not asking for you opinion Khadijah” a hankali tace “Toh shkkn, ya Amira fah?” Sudais yace “Tana gun ummanta” bai 

karasa maganar ba ya ga jiddah tsaye kusa da dinning din da yake xaune tana kallonsa, ya dauke kansa  yace “I will call you later Amira” katse wayar yayi ya 

ajiye, jiddah tayi dariya tana tafe hannu tana masa wani kallo tace “Cin amanar har cikin gidana Aliyu?” Sudais bai kalleta ba balle ya tanka ta, lkci daya 

idanuwanta suka kankance tace “Toh ko ma wace yar iskar ka samu wlh wlh sai tayi da ta sanin sanin ka a rayuwar ta, sai na nuna mata tayi kadan tayi kishi 

da ni, ba ma xai yiwu bane, mu xuba da ita sai dai idan ba mijina take cusa ma kanta ba” mikewa yayi yana kallonta yace “Wannan da kike gani wllh ta fi ki 

k’ima a idanuwana Jiddah, kuma kina nan xaki ga ta shigo gidan nan ta koya maki yanda ake kula da miji” bai sake sauraranta ba ya bar parlorn, jiddah ta 

kasa tsaye gu daya, ta ja kujera ta xauna da kyar xuciyarta na tafarfasa, lkci daya tayi wani murmushi tace “Babu boka babu malam, amma kai xaka bata 

shawarar ta rabu da kai, mu dai je xuwa, da kuluwa take xancen” Har khadijah ta iso gun motar khaleel idonta na kansa, shi kuma yana jingine jikin motar 

yana danna waya, bai san ta iso ba kawai kamshin ta ya ji, ya daga kai yana kallonta, a hankali tace “Good evening” ya mayar da wayar aljihunsa yace “Ya 

lectures?” Tace “Alhmdllh, karfe nawa su Shureim ke tashi?” Ya buda ido yace “Ke fa yarinyar nan baki da kara” turo baki tayi tace “Toh me nayi, am just 

asking” yyi murmushi yace “Daga nan xa mu dauko sa, yanxu suke tashi su ma” ta karasa ta bude front seat ta shiga, shi ma ya shiga motar ya tada suka bar 

wajen, har suka iso makarantar shureim khaleel bai ce komai ba ita ma haka, ya bude motar ya fita, ba a dau lkci ba suka dawo tare da Shureim, xagayowa 

Shureim yayi ya bude inda khadijah take xaune ya rungumeta yace “Anty good afternoon” ta shigo da shi cikin motar ta xaunar da shi kusa da ita tana kallonsa 

da murmushi tace “How you sweetheart?” Yace “Fyn Anty, I love the schl, I wish Sudais will come here also, am really missing him” Khadija bata ce komai ba, 

inda sabo ta saba, don bbu ranar da xai wuce Shureim baxai mata xancen Dan uwansa ba, he is always wishing Sudais is with him, lkci daya chocolate da Aliyu 

ya bata ya fado mata, ta bude jakarta a hankali ta fiddo chocolate din ta mika masa, karba yyi cike da jin dadi yace “Waow, Anty ke kika siya min?” Girgixa 

masa kai tayi tace “No” ya wara ido ya juya yana kallon Khaleel dake driving yace “Uncle kai ka siya min?” Khaleel ya kallesa yyi murmushi yace “No bani 

bane” Shureim ya mayar da dubansa kan Khadija yace “Toh Anty waye ya siya min” Khadijah tace “Idan baxa ka ci ba bani in cinye” Shureim ya bude chocolates 

din yace “Noo Anty ina so, ai irin wanda kind uncle din nan yake ba mu a gidansu maman nan ne, he told me his name is Dr Aliyu, Anty ina son a kai ni 

gidansu a Nigeria” Ita dai khadijah kallon yaron kawai take, ya gutsura ma khaleel ya mika masa yace “Uncle taste it” khaleel yyi murmushi yana girgixa kai 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button