NOOR AL HAYAT 61-70

yace “Noo thanks son, cinye abun, ko Anty kar ka ba” dariya yaron yayi bai ce komai ba, can ya kalli Khadija, alama yayi mata da ta bude bakinta, tayi
murmushi ta bude masa bakin ya sa mata chocolate din a hankali yana satan kallon Khaleel. Suna isa gida bayan khaleel yyi parking khadijah ta bude motar ta
fito tare da Shureim tana kallonsa murya can kasa tace “Thank you” fitowa yayi yana mimicking din muryarta yace “Thank you” daga haka ya rufe motarsa,
hararansa ta fara yi sai kuma tayi murmushi ta wuce apartment dinta rike da hannun Shureim, ya jingina da mota ya rungume hannayensa ya bi su da kallo. Tun
da Khadijah ta fito daga lectures yau take xaune cafteria ta rasa dalili, har lkcn lectures din karfe biyu yyi tana xaune gun bata tashi ba, Maryam ce ta
shigo cafterian tare da wata kana ganinta kasa yar Nigeria ce, Maryam na ganin Khadijah tayi murmushi tace “Khadijah kina nan ashe, ya lectures?” Khadija
tace “Alhmdllh ya naki?” Maryam tace “Alhmdllh” Maryam ta kalli yarinyar dake gefenta tace “Deejah meet ur namesake Khadija, tana studying pharmacy ne a
nan, she is also a Nigerian from kaduna” Warce Maryam ta Kira da Deejah tayi murmushi tace “Its nyc meeting you namesake” Khadija tayi murmushi sosai tace
“Nyc meeting you too” gun Khadija suka xauna su biyun, Maryam tace “Sun xo hutu ne nan da kanwarta shine na shigo da ita taga Cambridge” Deejah na kallon
Maryam tace “Khadijah tana min kama da Safeenah, ko ke baki gani ba” Maryam ta kalli Khadijah da kyau, sai kuma tayi dariya tace “Suna dai yanayi ba kama
ba, and the nose…” Deejah tace “Exactly, dama Ammi xata ganta cewa xata yi Safeenah ce” ita dai Khadijah bata ce komai ba banda murmushin da take yi, haka
kawai taji tana son Deejah…. drinks da snack Maryam ta sa a kawo masu su uku, Maryam na shan drink din gabanta tace “Deejah wai me yasa jawahir ta ki biyo
mu?” Khadijah ta daga kai tana kallonsu, Deejah ta tabe baki tace “Kilan kar su hadu da Dr Ayman” Maryam tace “Tab, Ayman sau biyu yake shigowa makarantar
nan a sati, Mondays and Thursdays, I think ranakun yake nasa karatun” Maryam ta kalli Khadijah tace “Kingakiwa neighbor dinsa ce Khadijah fa” Deejah ta
kalli Khadijah da sauri tace “Haba dai” Maryam tayi dariya tace “Wlh, ranan da naje gidanta tare da frnds dinmu na gan sa, yace min nan yake” Deejah tace
“Wani anguwa kenan?” Maryam ta fada mata anguwar tana cin snack din hannunta, Deejah tace “Ayya, daxu dai naji da suka yi waya jawahir ta bashi address yace
xai je anjima da yamma” Maryam tace “Gidan mu?” Deejah tace “Sure” Maryam tace “Ohk ai gwara dai ya je” Khadijah ta mike tana murmushi tace “Maryam xan
shiga lectures yanxu” Maryam tace “Haba to baki dau snack din ba ai da drink” Khadija ta kirkiri murmushi ta dauka tace “Toh nagode” daga haka ta bar
cafteria din bayan tayi ma Deejah ma sallama, Deejah ta bi ga da ido, kafin ta kalli Maryam tace “Maryam joke apart wllh kamar Safeenah, idan kin lura har
da Maimoon ma suna yanayi, Maryam tace “A coincident” wani gun Khadija ta tafi ta xauna don sun cika mata kunne da surutu ne gaskiyar magana. Tana ta xaune
nan har khaleel ya kirata bayan kusan awa daya, tana ta kallon Kiran kafin ta daga yace “Are you done with lectures Khadijah?” Girgixa kai tayi tace “No,
idan na gama xan taho gida, kawai ka tafi” yace “Karfe nawa xa ku gama?” Turo baki tayi da kamar baxa tace komai ba sai kuma tace “Anjima” yace “Toh Ina
jiran ki” daga haka ya katse wayar. Karfe hudu saura Khadijah ta isa gun da Khaleel ke jiran ta, fuskarta daure ta bude motar a hankali ta shiga, yana
kallonta yace “Ya lectures?” Kamar ana tilastata tace “Fyn” sai bayan da suka bar cikin makarantar yace “Wa ya bata maki rai?” Shiru tayi bata ce komai ba,
bai sake cewa komai ba har ya isa schl din Shureim ya fita ya daukosa ya dawo sannan suka dau hanyar gida, a waje yyi parking yana kallon Khadijah da ta
bude motar ta fita, Shureim ma ya fito, yace “Am going somewhere now, sai na dawo” Khadija ta d’an buda ido tana kallonsa tace “Gun jawahir din ne
somewhere??” Kallonta ya dinga yi da mamaki, ta tabe baki tace “Wai somewhere….” daga haka ta kama hannun Shureim suka wuce ciki, shafa kansa yayi ya tada
motar yayi reverse ya bar wajen. Da daddare Khadijah na parlor aka danna bell, ta mike ta isa gun kofar tace “who is there” yace “Somebody” bude kofar tayi
tana kallonsa ya mika mata ledan hannunsa yace “Ki ba Shureim?” Bata karbi ledan ba tace “Yayi Bacci” yace “Toh ki ajiye masa” Bata yarda ta kallesa ba ta
amshi ledan daga haka ta rufe kofarta. Washegari da sassafe Khadija ta fito apartment dinta tare da Shureim da tayi ma Shirin makaranta, ganin waje xa su
fita Shureim yace “Anty baxa mu jira uncle ba yau” hararansa tayi bata ce komai ba har suka fita ta tsayar masu da cab, sai da ta fara dropping dinsa schl
sannan ta wuce nata makarantar. Tare da su Vanessa suka fito daga lectures misalin karfe sha biyu, tun daga nesa ta hangosa da wani bature suna tahowa, har
ya iso inda suke xaune bai gansu ba yana magana da baturen Khadijah ta dinga kallonsa har suka wuce, still ta bi sa da ido, muryar Vanessa ne ya dawo da ita
tana cewa su je su ci abinci, mikewa tayi a hankali suka bar wajen xuwa cafterian da suka saba xuwa, xaune ta ga Aliyu da Baturen a ciki, suna shigowa kuma
ya ganta, ta dauke idonta daga kallonsa bayan sun hada ido, waje daya suka xauna tare da su Vanessa, Vanessa tayi masu ordering abinda xa su ci, drink kawai
Khadija ta sa aka kawo mata, duk suka gama cin abincin Vanessa ta biya bill sannan suka mike, Khadijah dai na xaune bata tashi ba, Vanessa tace “Ain’t you
attending the next lecture?” Khadijah tace “I will be going home soon” Tana kallon su Vanessa suka wuce, dai dai lkcn da Baturen dake tare da Aliyu ya mike
shi ma ya fita, tasowa Aliyu yyi ya dawo inda take ya ja kujera ya xauna yana kallonta yace “Good afternoon” ba tare da ta kallesa ba tace “Same….” Ya
shafa kansa yace “Ya Shureim?” Tace “Yana schl” yace “Ohk kin gama lectures yau ne?” Girgixa kai tayi tace “Aa xan wuce gida ne” yace “Ohk, yanxu?” Sai a
sannan ta kallesa tace “Soon” yace “Alryt if you are ready mu je sai in yi dropping din ki” tace “I prefer cab” yace “Ohk then,” wayarsa ya mika mata yace
“Sa min digit din ki anjima da yamma xan kawo maki sakon Shureim or I give Dr.. Ayman, Maryam tace min same house ku ke da shi, and I saw him a gidanmu
jiya” Khadijah bata ce komai ba da farko, can dai tace “Sakon me?” Yace “Shine xan bada a kai maki ai” Ta Girgixa kai ta karbi wayarsa ta na sa number ta
tace “You call me instead” daga haka ta mayar masa da wayarsa, ita ta fara mikewa kafin shi, ya bi bayanta suka
fita cafterian, sai da suka isa gun motarsa ya kalleta yace “Let me drop you Iman”
Bude mata motar Aliyu yayi yana kallonta, ta ki kallonsa tana dai tsaye kamar me contemplating ta shiga ko kar ya shiga, a hankali ta karasa gun motar daga
karshe ta shiga ya rufe, sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar. Sai da suka hau saman titi yace “Wani anguwar kike?” Ba tare da ta kallesa
ba tace “Tun da Maryam ta gaya maka gidanmu daya da Dr Ayman nasan ai baxata rasa gaya maka address da house number ba” Murmushi kawai Aliyu yyi yana ci