Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 21

Mamuhgee 21
Jiki amatuqar mace ta tattaro kanta ta fito toilet bayan ta zare kayanta dake jiqe acan ta dauro towel
Tana fitowa a darare ta samo Riga da wando masu kauri na bacci cikin kayanta ta Sanya ta Haye gado Bayan takira Cindy takawo Mata maganin zazzabi dataji yana saukar Mata da koinama ajikinta,
Shigewa Tai cikin bargo tareda to rintse idanuwanta dasukai jajir zuciyarta da jikinta ba Dadi.

Daqyar ta hadiye maganin zazzabin da Cindy takawo Mata sbd radadin da maqoshinta keyi
Tana Gama Shan Takoma takuma shigewa bargo tareda zura hannu ta kashe sidelamp tana rufe idanuwanta da Dan qarfi cikin azaba.

Washe gari da zazzabi Mai qarfi ta tashi Dan Haka ko breakfast Bata iya fitowa shima Kai tsaye yau din Bai tsaya breakfast a gida ba ya fice office Dan Haka breakfast din Haka taqaraci zamansa Kan dining Dole aka daukar Mata Wanda zataci aka Kai Mata daki saidai zazzabinta Mai qarfi ne Dan Haka Bata samu cin komaiba sbd tsananin zafi da ciwon da maqoshinta keyi gashi ya Dan kumbura.

Wuni tayi batareda ta iya cin komaiba sai ruwa datake Sha daqyar
Ahaka dare yazauna cin abinci Wanda Dole Cindy ce tayi serving dinsa Kai tsaye yaci abincinsa batareda ya tambaya Laylan dabai ganiba Yana gamawa ya fice ya Haye sama.

Da dadadden yunwa da azabar ciwo suka taso Mata sosai Haka ta ringa kuka tana juyi cikin mummunan yanayi
Daga qarshe wayarta ta iya dagawa daqyar ta saka Kiran Cindy
Tana dagawa taji kukan Laylan sai hankalinta yayi mummanan tashi ta taso ta nufo dakin Laylan a rude.

Ganinta cikin halinda take yasa Cindy Jin tsoro sbd kukane da Laylan Tasha farar fuskarta tayi jajir hakama fararen idanuwanta sun kumbura gabaki daya dai fuskarta ta sauya gata akwancen takasa tashi sbd sosai maqoshinta ke Mata azabar ciwo ga kumbura da yayi.

Kasa tabata Cindy tayi ta juya da sauri ta nufi main hall ta dauka wayar landline Dake hall din tayi dialling Numbers din dazasu Kai kiranta direct dakin Turaki.

Saida tasake Kira kafin ya daga cikin nutsuwa Kai tsaye furta kalmar “yes”

Cikin sauri da nutsuwa ta sanar dashi halinda Laylan take ciki tunda Ms Na’ima Bata Nan shine kawai zasu iya sanarwa Kai tsaye Dole.

Aje wayar yayi bayan yaji abinda tace tareda miqewa tsaye ya nufi closet ya sauya pyjamas Dake jikinsa zuwa milk jallabiya ya zuro slippers ya fito.

Yana saukowa hanyar dakin nata ya nufa direct Yana Dan sake saka Kiran Dr Noah Bata Shiga kafin ya kashe ya saka Kiran A Abdoul yace yaje yazo da Dr Noah.

Kai tsaye dakin ya bude yashiga sbd sanin Cindy na ciki tareda ita.

Amai tagamo a galabaice Cindy ta taimaka Mata Ta Watson ruwan zafi ta fito daure da brown towel a sulale daqyar tana bin bango sbd rashin qarfin jikin Cindy tabar dakin taje kawo Mata wani tea din Mai zafi,
Kai tsaye bakin gado Takoma tana kokoarin zaunawa aka turo kofar dakin Bata dagoba sbd sanin Cindy ce saigashi qamshunsa ya fallasar Mata da waye a matuqar wahalce ta dago daidai Yana sanyo Kai dakin idanuwansa akanta bai tsammanin samunta ahakanba,

Idanuwansa dasuka sauka Kan fararen cinyoyinta Dake bayyane ya daukesu da Yana dakatawa daga kofar.

Da Dan sauran qarfinta tayi saurin miqewa tsaye har towel din na Dan subucewa daga sama da sauri Takoma cikin toilet tana dafe bango batama Gama ankarewa sbd tsananin rudewa da firgitar datai sai wani Aman Mai karfi yakuma kufce mata tafara kelayawa da qarfin gaske Dan babu komai acikin nata.

Cindy ce data kawo tea din tayi saurin ajewa tana qarasawa cikin toilet din ta nufeta lokacin tuni jikinta yasaki agurin ta zube jikin Cindy gaba daya Bata wani motsi.

Ihu Cindy tasaki tana Kiran sunanta da qarfin gaske cikin rudewa ganin Kamar Laylan Bata numfashi….

Kai tsaye shigowa yayi toilet din ya dauketa gabaki dayanta Yana cewa Cindy ta dauko Mata Kaya ta Sanya Mata.

A gado ya kwantarda ita ya juya ya bar dakin Cindy da duka jikinta ke rawa ta dauko wata doguwar Rigar bacci bataredama tasan abinda takeba ta Sanya Mata tafito ta fada Masa.

Dan shiru yayi Kamar Bai jiba Yana nazarin lafiyarsa idan yakuma hada jikinsa da natan Dan bayan fitowarsa Saida yaje yasha magani ya dawo.

Kallon A Abdoul daya iso Yana jiransa yayi Dan Dr Noah baya gari Dole asibiti za’a kaita.

Dakin yashiga ya daukota da kansa yakaita mota batareda ya lura da kayan da Cindyn tasanya mata Saida Suka Isa asibitin bayan an dauketa anyi ciki da ita A Abdoul ne ya kalli Cindy cikin Dan fada yace”

What was that??

Sauke Kai tayi saboda itama Saida Suka iso asibitin ta lura da abinda tasanyawa Laylan
Cikin damuwa da ban hankuri ta saci kallon inda Turaki ke zaune kamar baisan da tsayuwarsu agurinba murya na rawa tace”

I’m sorry sir I….

Abdoul kaita gida takawo wani kayan.

Daga Haka Bai qaraba ya duba agogon hannunsa Dan koma menene bayason su kwana a asibitin data farfado gida zasu koma.

Kaya kala uku ta dauko sbd gudun wani shirmen suka dawo asibitin lokacin har Laylan ta farko tana bacci Dan Haka drugs kawai suka karbo suka dawo gida.

Yana kwantar da ita ya bar qasan gabaki daya ya Haye sama Bai Kuma saukowaba har washe gari Babu Wanda yaga ya sauko breakfast Haka ya wuni Bai fito ba saidai A Abdoul daya damu sosai yayita kiransa karshe dayake Babu Wanda yake shiga samansa bayan A Abdoul shima tunda su Ms Na’ima Suka dawo qasar Bai qara bin hanyar saman ba Dan Haka hankalinsa ya tashi Sosai yayita Kiran wayar Ms Na’ima Bata dauka ba Dan Haka baida zabi bayan Kiran Anne.

Washe gari har dare ba Turakin ga wayayinsa a kashe Dole yanda Anne tace hakan zaiyi duk da yasan ran Turakin Zai baci Idan aka tura Masa Laylah dakinsa,
daddare yashigo babban palon qasa ya tambaya Cindy jikin Laylah ta tabbatar Masa da taji sauki sosai harma yau ta Dan fita taje makaranta.

Kira Masa ita yace Cindyn tayi
Ba jimawa sai gata tafito sanyeda doguwar jacket data Dora Kan kayan baccinta Dan tuni Tai Shirin bacci harma ta kwanta.

Cikin nutsuwa ya sanar da ita kwana biyu Turaki Bai fito ba wayoyinsa akashe shine Anne tace taje tadubosa tunda masu aikin gidan kaf basa zuwa   gurin.

Shiru tayi tareda sauke kallonta daga kansa zuciyarta na harbawa da fargaban haduwarta dashi sbd abinda ya faru kwana biyu Wanda haramun ne gareta faruwar hakan,
Mijin yayarta Abokin mahaifinta duk da tsautsayine na ciwo da zuwan Abu Amma hakan ya tsaya Mata arai harta fara Jin kamar zamanta anan Bai kyautu ba duk da riqontane ake Amma sai tanajin tsoron zamanta nan Yana shigarta.

Kiran Anne ne yashigo wayarta tana dauka Kai tsaye Annen tace”

Laylah kije kidubo Mana Turakin ko lafiya hankalinmu duk ya tashi ga ba Wanda zai dubaso maza jeki kidubo Mana tun kafin Abu yayi nisa.

Jin hakan yasa gabanta faduwa ta dago ta kalli A Abdoul da duk yayi wani iri lokaci daya na rashin sanin halinda uban gidansa yake ciki Jin yake kamar yayi tsalle yagano lafiyar Turakin.

Da sauri ta juya ta nufi hanyar saman ta Haye gabanta na tsananta faduwa da sauri,
Bata taba ko kallon hanyar Master bedroom dinsaba sbd iyakacinta palon shima sai babban dalili idan ankirata kokuma taje Kai wani abin Dan Haka Bata taba kallon hanyar bedroom din nasa ba…

Tsayawa Tai bakin kofar tana Dan knocking kofar hannuwanta na Dan rawa,
Sake knocking takeyi tafara tsorata da Shirun itama Dan Haka taci gaba da bugawa tana jiran Jin motsi Amma shiru.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button