Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 21

Rasa sanin abin Yi tayi ta daga wayarta da sauri ta saka Kiran Anne tana dauka Bata jira me Annen zatace ba tace”

Ba’a bude ba..

Laylah kishiga ki duba
Bari kawai nakira Abdoul ya hawo ya duba..

Komawa gefe tayi tana jiran tahowar Abdoul din sai gashi ya hayo da sauri ya qarasa dakin tareda knocking so daya ya Murda kofar yashige.

Sosai hankalinsa ya tashi da ganin yanayinda turakin yake Dake nuni da rashin lafiya sosai ataredashi saidai Kuma qarfin halinsa yasa Yana zaune Kan sofa tarin magungunansa birjik agabansa wainda yaketa faman Sha Amma erection dinsa yaqi sauka shiyasa ya nesanta kansa da fita ko Ina sbd kallo daya zakai Masa ka iya gano wani abin.

Ahankali ya dago idanuwansa dasukai wani iri yayiwa A Abdoul din daya shigo kallo daya ya dauke Kai yana bude Baki cikin dauriya yace”

Akwai damuwa ne?

Cikin tsananin kulawa da damuwa A Abdoul yace”

Hankalinmu ya tashi da rashin fitowarta Anne tabada izinin nashigo na duba,
Wayarsa yafara laluba Yana cewa”

Zankira Dr Allen yanzu na sanar dashi halinda kake ciki.
Juyawa yayi da sauri yafice Yana Nemo Numbern DR Allen.

Qasa ya sauko Laylah na biye dashi cikin sauri yace”

Ahada Black tea Mai zafi akai Masa Kar asanya sugar likita zaizo ya dubawa yanzu ba jimawa.

Gyada Kai kawai tayi jiki a Sanyaye
Ta nufi kitchen din da kanta ta Dora Masa tea din tana cewa siddika ta gasa Mata bread uku da kwai.

Tana gamawa ta hada a tray ta fito dasu ta nufi saman da tuni har A Abdoul yaje da gudun masifa yazo da Dr Noah duk da bashine likitansa na asalin lalurarsa ba Amma zai iya taimakawa.

Allurar da Dr Allen ya rubuto musu yanzu yanzun itace Dr Noah yayiwa Turakin tareda kallonsa cikin kulawa da nutsuwa yace”

Baka buqatan riqe kanka Haka sosai you have to let it out sbd zakaiwa kanka illa sosai tunda desire din tafara zuwane gadan gadan control nata zai fara wuya saidai Kuma saika lura sosai gurin having first sex din zai iya zuwa da tangarda.,
Amma dai for now Dole zaka daina kokarin dannewa lokacine yazo Dole zaka Bari abinda kakeji ya fita.

Dr Noah na fitowa tareda A Abdoul Dake Palo Yana jiransa Dan Bai shigaba tana shigowa daukeda tray din harma da fresh milk Mai sanyi kadan ta hado duk ta kawo.

Kallonta A Abdoul yayi Yana cewa”

Ki Kai Masa bedroom…

Ficewa sukai ganin dakin bude Kuma ganin Suma duk ciki Suka fito ya sanyata nufar dakin Kai tsaye tareda sallama Mai sauti Bata dagoba ta kutsa Kai dakin qamshin Bois elite na tashi tako Ina Yana rikita kanta da qafafunta Dake Dan rawa ta nufi table Dake dakin tafara kokarin ajiyewa.

Tunda tashigo Yana zaune a sofa Bai motsa ba bayan idanuwansa dasukai taushi Babu abinda ya zuba Mata Yana kallon yanda qafafuwanta ke hardewa
Tana dososhi ya dauke kallonsa daga gefenta gaba daya musamman qamshinta na Creed Dake tashi daga jikinta ahankali ahankali.

Tana ajewa cikin nutsuwa tace”

ALLAH yasauwaka yakawo afuwa.

Juyawa tayi ta fice tabar dakin da qamshinta dabaiyi qarfi da yawan nasa ba Amma hancinsa na Jin natan na shigarsa.

Da sanyin jiki tayi bacci hakama da safen da sanyin jiki ta tashi batareda tasan meya kawo Mata hakan ba Haka ta shirya ta tafi makaranta tagamo wuninta tadawo har lokacin batajin dadin ranta Sam.

Ms Na’ima lokacinda saqon Turaki na ticket da akai Mata booking na dowowarta yashigo wayarta tayi mamaki sosai saidai koda Laylah takirata ta sanar da ita bayada lafiya kwana biyu saita fasa dawowa Dan Bata Gama abinda takeba tunda ba wani abin zatai Masa idan tadawoba.

Kwana biyun sosai ciwonsa ya damu Laylah dake daukan hakan amatsayin kaga Wanda ya kyautata rayuwarta data mahaifinta dama ta Yar uwarta tagansa cikin Hali na ciwo.

Sam baya saukowa cin abinci yanzu saidai Cindy da A Abdoul yace anbawa damar Hawa Kai Masa abinci acan sbd har lokacin Ms Na’ima Bata dawoba.

Da wannan gidan yakoma kamar rayuwar kadaici takeyi sbd yanzu kowa Bata gani daga ita sai masu aiki take rayuwar gidan,
Kwata kwata ta daina ganin Turakin sbd ya yankewa kansa nesantarta sbd yanayin lafiyarsa ga Na’ima Bata dawoba Dan Haka yasaka kansa zama busy Sosai Sosai ko gidan Baya dawowa sai dare daya shigo Babu Mai sake ganinsa a qasa sai zai fita Kuma.

Ganin Haka ta maida hankalinta Kan karatunta itama ta rage zama gida sosai koyaushe tana makaranta ko gidansu Sofia.

Ahaka Ms Na’ima ta shanye kusan sati hudu kafin tadawo lokacin Turakin baya gari yayi tafiya Dan Haka sai gidan yadan dawo Mata daidai Amma hakanan takejin kewar su Anty Sa’adah.

Washe gari tana dawowa daga makaranta tana shigowa gida sai ganin Anne tayi A Palo zaune batasan lokacinda tasaki wata dariyar farin ciki ba tana qarasawa da sauri ta rungume Annen tana cewa”

Anty Sa’adah fa???

Da ido Annen ta nuna Mata bedroom dinta tana cewa”

Tana jiranki a dakinki hutawa takeyi.

Sakin Anne tayi ta nufi dakin ta tadda anty Sa’adah kwance kan gadonta tana bacci tayi wanka da alama Dan rigar jikinta bamai nauyi bace.

Kasa tada ita tayi ta aje handbag dinta tareda wayarta tana fadawa toilet da sauri tayo alwala tazo tayi sallah har lokacin anty Sa’adah Bata farka ba Dan Haka ta fito Takoma gurin Anne tana sake bayyanarda farin cikin zuwansu dayake Ms Na’ima Bata Nan tafita Koda suka iso.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button