Noor AlbiNOVELS

NOOR ALBI 43

Cikin gajiya da wannan masifa itama Zinat din tace”

Ki nutsu Na’ima tunda kema kingano Cinna Miki hauka al’amarin Turaki zaiyi,
Tashin hankali bazai Bari musan abinda mukeson saniba…
Turaki yagama bamu mamakin duniya tunda yayi aure bare yanzu Dan yayiwa wata Mai rubutacciyar qaddara a hannunmu ciki,
Fatan dai kin gano wani Abu akanta ba haukar banza kikayoba Kika dawo?

Kasa magana Ms Na’ima tayi sbd batama San Mai zataceba,
Da alama gwara shaanin Sa’adah shi data san komai akan wannan da batamasan ta Ina zata faraba saidai Abban abin data sani shine koma yayane itace ta Los Angeles da khairat ta fada Mata Dan Haka sake tattarawa zatai Takoma Dan sai tana Atlanta zatafi Gano wani abun Dan idan zata mutu tadawo duniya Turaki bazaice Mata komaiba akan lamarin Koda ta tambaya kuwa sai lokacinda yaga Dama yaso fada.

Cikin takaici Haj Zinat tace”

Koma meyene Anne tasani Amma dayake batada adalci shine tayi shiru tabarsa ya rufeki a baibai saidai kawai akawo miji jaririn ‘da ace Miki gashi na Turaki ne tsabar a nuna bakida wani amfani bayan tun farko shi tukarin ai shine Mara amfanin,
Tunda ya warke yanzu Dole zai ringa tsalle tsallen zuwa gurin Mata bazai iya tsayawa akan wadda ta zauna shekaru dashiba…. Mtsss Ni ke kanki Na’ima wani lokacin kayan takaicine Dake,
Ki tattare dukiyar ki rabu dashi yaje ya nema matan duniya idan zai iya Amma kin tsaya ke acikin bacin Rai Nima aciki…

Zinat wallahi bazan iya rabuwa da Turaki ba tun wuri daina maganar rabuwar Nan,
Zaunawa zanyi naringa cin uban duk wadda tayi gangancin shigowa rayuwarmu nidashi tunda kwadayin abun duniyar kowa a zuba Masa a zuciya.

Haj Zinat tafi Jin zafin Anne Akan Turaki sbd Babu kalar asirin da basuyiwa matarnan ba Amma yaqi ci,
Idan suka mallaketa tamkar sun mallaki Turaki ne sbd a duniya ba maganarta dayake tsallakewa saidai tsohuwar tamkar wadda take kwana rungume da Qur’an Dan kudin dasuke narkawa bokaye da malamai bama gaskia bane Amma a banza Dole Suka watsar sbd basa Wasa da lissafi, bazasu iya cigaba da hasararda Babu riba acikiba.

Cikin son Kai qarshen matsalarsu kowa ya huta Haj Zinat tace”

Zan Kira khairat mugun bincike za’ai Mana asan koma wacece daga Nan sai asan matakin dauka…

Cikin zafin Zuciya Na’ima tace”

Bazan iyaba kasheta zanyi har ita har cikin..

Idan kin kasheta acan saikiyi bankwana da Turakin da kikai kisar dominsa Dan kina gidan yari ko lahira zai aura wata Matar.

Zinat meyasa bakya fadar alkhairi yanzu koyaushe muguwar data kikemun,Wai ko mun fara samun matsala ne?”” Tafada ranta na baci Sosai akan baqin datake ciki.

Cikin takaici itama Zinat din tace”

Aiki da hankalinkine bakyayi koyaushe irin Haka ta taso kedai maganarki kisa,
Kinsan hukuncin kisane?
Kin aikata Abu Dan wani Amma kinaji kina gani za’a rabaki da duniyar Kuma Babu abunda zaiyi miki,
Ni bana komai ba lissafi kin sani,
Inada ‘yaya idan Ina rufe Ido Ina biye Miki gurin yin komai da tuni mun Jima da zama Yan gari a lahira,
Dan Haka bazan biye Miki mu hau jirginda ba saukaba sai filin Danasani da lahiraba Dan hake kema ki nutsu cikin ruwan sanyi zamu zuba rashin arzikinmu batareda mun barwa kanmu abun fada ba.

Naji zancen ya Isa Haka sbd Zinat yanzu kin daina gane ciwona,
Kedai idan magana Bata fitowar kudi bace batada babban mahimmanci agurinki,

Yanzu kisa Fahad yamun komai cikin gaggawa inason komawa,
Tunda Turaki ya fara fadar I love you kinsan Yana gap da gane mace ciki da wajenta da halayensu da kyau Wanda kema kinsan hakan nada barazana agun mu daga lokacinda yafara karantar son dukiyarsa a jinina yake.

Zamuji da wannan idan mungama da wannan babbar matsalar dake gabanmu Dan Nima ko a mafarki bana Mana fatan wata macen da haifawa Turaki ‘yaya idan bakeba to kowama bazai masaba a zauna ahakan yafi tunda kunada ‘yar riqo.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button