
Duk da cikin dake jikinta sakewa tayi sukai abunda sukeso musamman dataga Abban yagama mutuwa a duniyarta Dan Haka ta sake Masa suka Gama hargitsa palon Kuma Suka koma daki suka qarasa sauran aikin.
Sai dare suka sauko cin abinci Yana riqeda hannunta Suka sauko stairs din tana sanye cikin guntuwar free doguwar Riga red Mai kyau sai slippers dinsa da sukai Mata yawa..
Shima sanye yake da Balenciaga shirt da wando sai slippers din.
Wannan karon taci abincin fiyeda fruits Tasha Madara shima yaci macaroni salad da Potato kababs.
Sama Suka koma madam sarat Bata Kuma ganinsuba ko Jin motsinsu sai washe gari,mamakin duniya yagama kasheta Amma ba damar nunawa tunda ba huruminta bane saidai ko daga kallo daya tasan Sir Turakin su a hannun wannan Yar qanqanuwar yarinyar yake.
Tunda tada iso qasar Bai Kuma fitaba sai dayayi kwana biyu cif a gidan sallah kawai ke fiddasa tukuna…
Wani mahimmin aiki ya taso Masa a Abujan Dan Haka badan yayi Shirin tafiyarsu a kusaba Dole Suka shirya A Abdoul ya siya musu tickets suka nufo Abujan.
Tunda Suka Shiga jirgi zuciyarta ke harbawa,
Takasa samun nutsuwar zuciya data ruhi,
Hannuwanta har Yar rawa sukeyi duk lokacinda ya riqo hannunta,
Sunan mum kawai idan ya fado ranta zuciyarta harbawa takeyi Dan kunyar Anne ma daga bayane zatazo idan sukai Karo da mum Na’ima idan ta Isa…
Duk dokinta da farin cikin zuwa Nigeria data Jima tana fata gushewa yayi sbd fargaba da rashin kwanciyar hankalin datake ciki.
Lura da yanda hankalinta ya tashi yasa yayi kokarin kwantar Mata da hankali Amma sam Bata ganewa Haka ya lallabata tayi bacci jikinsa saidai ba baccin tayiba kwanto kawai tayi sbd jikinta daya Gama mutuwa.
Suna sauka airport din Abuja motaci biyu sukazo daukansu sbd da ruky sukazo da zata ringa Mata komai.
Dan Haka suka shiga motocin Suka nufi gidan.