NOOR ALBI 49
Mamuhgee 49_*
Kiran sunanta Anne tayi lokacinda tanjuya zata koma,
Cikin kalawa a natse tace”
Komawa Zakiyi ki kwanta ne? Jikinki zaiyi ciwo da kwanciya
Ba’a son Mai juna biyun da musamman yafara nisa da rashin motsa jiki kinji?
Zo ki zauna tare damu ba wata magana muke ba zance ne kawai
Halima tana shirya abinci a dining idan tagama saimuje muci tare duka harda Abbanki tunda nasan zuwa yanzu Na’ima kila ta kwanta..
Tafada hakan ne Dan kawar da rashin fahimtar zancen sbd tasani shima Turakin yasani harma da Laylan tunda itama ta wani fannin tasan mum Na’iman ko yunwa zata kashe Turakin yau bazaici abincin dazai fito daga garetaba dukda dama mafi akasari idan sunan gurin Annen ake Kai Masa abinci kokuma wasu lokutan tareda Annen yakeci anan bangarenta sbd rashin zaman Ms Na’iman dakuma rashin kusancinsu wancan lokacin Dan Haka ko yanzun bawani sauyi aka samun ba.
A sanyaye ta dawo ta zauna gurin Anne Dake binta da kallo cikin kulawa tana Mata sannu Kamar Mai ciwo harta zauna Kan qaramar sofar Dake gurin.
Murmushin karfin hali ta sake tana amsawa Annen sanmun datake Mata kafin ta Dan dago batareda ta juyo sosai ta kallesaba da Taushin murya tace”
Abba Ina wuni¿
Ahankali ya dauke idanuwansa daga kanta ya maida Kan wayarsa Dake hannunsa cikin nutsuwa ya amsa Kai tsaye duk da Idanuwansa akanta suke tun shigowarta,
Hakama irin kallon daya ringa jifanta dashi yasata duk kasa sakewa sbd ganin kaman Anne zata iya ganin abinda yake faruwa.
Fira Anne ke janta sama sama cikin kulawa tana tambayarta abubuwa dasuka shafi lafiyarta idan tanajin matsala.
Girgiza Kai tayi cikin nutsuwa tace”
banajin komai.
Kina zuwa asibiti ne acan USA din?
Kokuwa haryanzu bakya shan kowane magani?
Bakya Kan kulawan kowane likita kenan?
Gyada Kai tayi tana cewa”
Naje asibiti so daya acan.
Kallon Turaki Anne tayi Wanda yayi tamkar baya palon sbd gabaki daya ko inda suke Bai kallaba duk da hankalinsa na kanta Yana jiran yaji amsar dazata bawa Annen da kanta,
Da magana Annen zatai Masa sai taga yanda gabaki daya hankalinsa baya kansu saita qyalesa kawai sbd cikin Kam Dole itace zata tsaya gurin kulawa da wasu abubuwan na Laylah tunda batada uwa
Batada Mai fada Mata yanda komai yake,
Shi Kuma Turakin ba komai zai saniba sbd manyancin shekaru dakuma yanda yake a miskilance,
Gashi lokaci daya ta fahimci rabon ne kawai yazo Amma Babu shaquwa ko kusanci a tsakaninsu ko kadan.
Halima ce ta shigo ta sanarda sungama gyara komai a dining
Ta juya Takoma.
Anne ce da Laylan Suka fara fitowa suka nufa dining din har Saida suka zauna kafin shi yafito ya doso dining din idanuwansa akanta yanda lokaci daya kamarma ta rame sbd firgicin data shiga na wuni daya.
Jin idonsa akanta yasata dagowa a kasalance ta kalla hanyar tahowar tasa Suka hada Ido tayi wani iri da idonta Kamar zata sakar Masa kuka…
Kallon da yayi Mata na tabbas zata kwana gurinsa idan tana cikin damuwa yasata maida hawayenta tana dauke Kai daga kallonsa daidai qarasowarsa ya zauna a tsanake Yana ajiye wayarsa gefe.
Batareda da ya dagoba daga kallon dayake bin abincin Dake jere a dining din yacewa Ruky data kawo madarar Laylan da suna isowa A Abdoul yasiyo su yakawo yabawa halima aka Kai kitchen, ita Ruky tasan yanda zata dumamawa Laylan takawo Mata,
A kame cikin nutsuwa da sauti Mara qarfi yace”
Akawo fruits marasa sanyi sosai.
Yes sir.” Tafada cikin girmamawa ta juya bayan ta aje cup din madarar Mai dumi gaban Laylah Takoma kitchen.
Tana komawa kitchen ta sanarwa halima Dake jera kayan da aka gama aiki dasu gurin zamansu tace”
Shine zai Sha kokuwa Anne?
No Madam ne zataci.
Tanacinsu tareda dinner ne kokuma lunch.
Ok, ki bude fridge ki dauko ki hada a guri ki Kai bangama wannan aikinba tukuna.
To” tace tana juyawa ta nufa fridge din.
Ko da Ruky takawo fruits din Laylan Bata fara cin abinci ba Amma dai ta zuba white pasta da kidney veggies souse.
Ana aje Mata fruits din tafara cinsu a natse sbd Jin tasamu yar nutsuwa da kwanciyar hankali ganinta tareda su biyu din,
Duk tsanani tasan Anne bazata Bari mum ta iya yimata wani abuba duk da shima tasan bazai Bari din ba Amma Kuma mum din matarsace bazai tauyeta da yawaba tunda ko yayyane anyi Mata ba daidaiba.
Babu Mai magana a dining din har suka gama,
Shine yafara kammalawa ya miqe tsaye bayan ya goge Baki da tissue ya kalli Anne yayi Mata Saida safe yabar gurin bayan yayiwa Laylan kallo daya.
Itama tana gamawa daki ta nufa bayan tayiwa Anne Saida safe.
Sallar isha tayi ta sauya Kaya zuwa kayan bacci ta zauna ta Jima tana waya da Anty Sa’adah kafin ta kashe ta kwanta da tunanin Turaki cikin ranta bayan ta duba saqon ” Take care Baby ” daya Aiko Mata.
Bata saka ran zata samu bacci Mai nutsuwa ba sbd Abin dayake gabanta na fuskantar mum Amma wayarta da anty Sa’adah a Daren kafin kwantarta yasa tasamu nutsuwa da kwanciyar hankali daidai gwargwado sbd shiga tashin hankali da damuwa bashine zai kawo Mata sauki ba Dan fuskantar fushin mum Dole ne tunda anriga an aikata laifin koma menene lafiyar babynta ne agabanta fiyeda saka damuwar.
Da wannan ta tashi fresh abinta tafara daukan wayarta da Abban yayi Mata massage tun asuba data tashi sallah Bata budeba sai lokacin…
I love you kawai ta rubuta Masa bayan duba sakonsa na sanar da ita da yayi akan ta shirya yau zataje asibiti za’a duba lafiyanta Dana babynsa.
Toilet ta nufa tashige hankali kwance tayo wanka ta fito daureda towel Mai Dan girma sbd cikinta rabe qaramin towel yake.
Ruky ce take gyaran dakin ko data fito Dan Haka Kai tsaye gaban mirror da aka gama jere Mata komai nata na turarukanta da Mayukanta ta zauna ahankali Kan kujera tana kallon kanta cikin madubin.
Augustinus Bader body oil ta shafawa jikinta kafin ta fesa Erbaviva relax body spray ta gyara kanta dayake Dan hargitse.
Doguwar Riga ta Sanya sbd kusan yanzu sune kayanta ta daina saka Riga da wando irin sosai dinnan Amma bawai ta daina sakawan bane kwata kwata..
Rigarta Mara nauyice red Mai tsadar gaske da Abban yasiya Mata su Tun tafiyansu Athens.
Qaramar hula da slippers ta saka ta fito ta nufi palon dakin Anne.
Annen na palonta zaune tana waya Laylan tashigo cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta qaraso a ladabce tace”
Anne Ina kwana¿
Kashe wayar tayi tana kallonta cikeda kulawa tace”
Lafiya kalau Laylah,
Yaya jikinki?
Ya yanayinki badai damuwa ko?
Eh” kawai ta iya fada a taqaice sbd nauyin zancen cikin takeji matuqa.
Daga ita sai anne sukai breakfast dinsu hankali kwance
Kuma taci abinci sosai sbd akwai pancakes cikin abincin Kuma tana sonsa sosai hakama taci Doyan da aka soya fara da liver sauce sosai.
Bayan sungama suka dawo Palo saiga Dr Meenah tazo gidan
Kallo daya tayiwa Laylah ta saki murmushin farin ciki mai tsanani tana cewa”
Masha Allah patient Dina is going to be a mum soon…
Cikin kunya Laylan take Mata sannu da shigowa tana cewa”
Barka da zuwa Dr Meenah.
Zama tayi tana cewa”
Sannu Laylah,
Anne Ina wuni?
Ya gida?ya fama da masu nauyi?
Lfy kalau Dr Amina,
Masu nauyi Kuma gasunan
Dama ita za’a duba da komai na yanayinta sbd yarinta Bata taba zuwa ganin likitaba ko acan gashi yanayin nata yafara nisa tunda ita da kanta batasan watanninsa nawa ba.
Dariya Dr tayi tana kallon Laylah daketa Jin wani iri zancen tace”