Noor Albi

NOOR ALBI 49

Ba damuwa ai yanzu sai aduba komai a dorata Kan magani da sauran Abubuwan,
Allah dai ya raba lafiya yasakawa rabon albarka.

Amin” Anne tace tana kallon cikin.

Massage tayiwa Abba dayayi Musu booking appointment na ganin wani babban hamshaqin likita.

Jin Anne takira likita tazo dubata din yasa ya soke maganar fitar tasu duk da yaso su fitan yaganta dakyau da lafiyan cikinta sbd jiyan data Bari hawayenta sun sauko agaban Annen bazai iya Hana kansa share Mata suba.

Duk wasu checkups Dr Meenah tayi Mata su scanning ne kawai ya rage Wanda sai da zata tafi Suka tafi da ita harda Anne a asibiti cikin office din babban gynecology consultant dinsu akai Mata.

Cikin harya fita wata biyar Yana cikin na shida Dan Haka sosai Anne ta bayyanarda nutsuwarta da farin cikinta akan cikin sbd tabbas ta jinjinawa dauriyar Laylan data raina cikin batareda taimako ko tallafawar kowaba ita kadai abunta.

A hanyarsu ta dawowa gida suka biya sukai siyayyar dogayen rigunan marasa nauyi amma sai tsada wainda Laylan zatafi Jin dadin sakewa acikinsu sosai.

Harda Yan wash siyayyan abubuwan buqata Laylan ta sissiyo sbd kusan komai na abun buqatan amfaninta debowa tayi batazo dasu da yawaba shiyasa.

Sai yamma suka dawo gida lokacin Haj Zinat itama zuwanta kenan ta Parker motarta tana kallo Suka fito lafiyayyar motar dasuka dawo ciki Suka wuce gaban motarta,

Ciki dai gashinan ajikin Laylah tsaf a zaunensa cikin koshin lafiya….

Tabbas akwai babban bala’i Dan wlh idan ya tabbata cikin Turaki ne jikin Laylah ko ita bazata taushi Na’ima saisun koyawa kowa darasin wannan Cin Amanar Mai laminated ticket,

Wannan karon Kam akwai rikici Dan wlh sai anyi abinda kowa zaiji ajikinsa bazasu yarda ba,

Na’iman ta raini yarinya agabanta Amma ace a bayanta tana kwanar Mata da mijin da Bata Gama morewa lafiyarsaba..
Dan ko ita zata fada saduwarsa da Na’iman kirgagge ne duk da rashin zama ne Amma ai Bata Gama cire kwadayintaba na kwanciya dashi.

Saida Suka shige ta bude motarta ta fito tana bin Anne da tsinuwa tafi dari Dan kuwa duk itace takawo musu wannan masifar suna zaman zamansu cikin cin Arziki.

Wanka tayi tayi sallar la’asar da magriba da akai tana gurin wankan,
Sai data zauna tayi waya da abbanta daya kirata harma yabata Abdullahi Suka gaisa dashi shima ya karba numbernta.

Sai data Yi sallar isha tafito sanyeda dogon wandon da rigar bacci masu santsi kanta sanyeda hula Mara nauyi datai Mata kyau tana qamshinta ta nufi dining taga abincin da akai tuwon semolina da miyar kubewa Mai kifi da Naman rago da ganda aciki harma da zallan tsokan Naman kaza wadatacce dayaji aciki,
Sai fruits dinta dasukai sanyi sosai Dan Haka ta zauna sbd Anne dama idan karfe Takwas zuwa tara ta wuce batacin abinci Mai nauyi Dan Haka ita kadai tazauna taci abincin tana gamawa ta koma bedroom dinta tana cewa Ruky ta biyota ta gyara Mata closet dinta data yamutsa gurin Ciro kayan baccin da batasan inda aja jera matasu ba da farko.

Da kewar abbanta da zaiyi tafiya washe garin ranar ta kwana Dan Haka ma da safe Bata fito da wuri ba sbd yanayin sanyin jiki datake taredashi sai guraren 10 tafito tayi breakfast ta zauna Palo tasaka Ruky ta zauna da ita suna fira sama sama sbd ta Saba Haka takeyi da Cindy dinta.

Kewar Cindy dinma yasa ta dauki wayarta takirata Suka Jima suna magana akan itama Cindy din tana kewan Laylah tadawo Amma Kuma ba Hali sai ta haihu.

Bayan Cindy sofia Suka Jima suna waya itama kafin Anne tafito ta zauna tana Taya Laylah debe kewan.

Haj Zinat ranar datazo din ta dauke Ms Na’ima daga gidan sbd Tafara dawowa daidai komai zai iya faruwa ta Bata musu tsarinsu Dan Haka Dole ta tilastata Kiran Turaki da yayita Kiran wayarta kusan so uku Bata dauka sbd jinsa take badan tanasonsa ba Kuma yanada amfani agurinta da shi kawai zata qarawa gudu ta huta da abunda yake sakata ciwon Rai da masifa.

Sanar dashi tayi zata kaduna bikin Yar yayar Haj Zinat Bai hanataba kaman yanda aka Saba yace Mata Allah ya kiyaye,
Dayake yasan irin hakan duk tayi tambayar tafiya saita tambaya kudi masu yawa Dan Haka bayan sun Gama Wayar ya Sanya A Abdoul saka Mata kudi a account dinta
Tana gani Amma hakanan taji sun qara Mata takaicinsa Dan Haka ta qudurta wargaza duk wani tanadinsa akan macen dayakeso.

Barin gidan sukai batareda ko Anne sun sanarwaba sukai gidan Haj zinat da itama nata mijin Baya Nan Suka zuba Dora sabon shiri akan shaanin.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button