Uncategorized

THE GOVERNOR’S WIFE 3

 *THE GOVERNOR’S WIFE*

…… MATAR  GWAMNA….

 *©Azizat Hamza*

 wattpad Azi_zat 

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

03

“Aseey we are dead”  CY ya faɗa lokacin da suka shiga mota za su koma office.

“Ni fa ka ganni nan ba na tsoron ta ɓaci wallahi. Gaskiya ce zan faɗa ko da ba za ta yiwa wasu daɗi ba. Idan ban faɗi gaskiya ba miye amfanin aikin jaridan da na ke yi”

“Dama kin fi kusa da MD ai”

“Kai ka san wannan”

Lokacin da su ka isa office Asiya ta ɗauka MD zai ma ta faɗa amma bai ce komai ba. Ta yi mamaki kam dan indai MD da ta sani ne to da tuni ya fara diri akan ta sako maganar albashi a rahoton da ta kawo.

Awa ɗaya bayan SSK ya kalli rahoton Asiya, ya saka hannu aka sakewa ma’aikata albashin su, zuwa yammaci kusan fiye da rabin ma’aikata kowa ya ji alert ɗin albashinsa.

Mintuna kaɗan bayan SSK ya sake albashi kiran Gwamna Saminu Bacchi ya shigo wayarsa.

Duk da Gwamna Saminu ya girme shi da shekarun da ba za su wuce biyar zuwa shida ba, SSK bai chanchanci irin tsawan da Gwamnan ya masa ba akan ya sake albashi kafin ya dawo.

Bayan ya ajiye wayar ne ya fara tunanin anya kuwa zai iya cigaba da irin wannan tozarcin..

***

Daf an kusa tashi aka kawowa Asiya Shahida letter daga office ɗin MD. Tana gama karantawa ta wuce office ɗin sa da sauri.

“Sir yanzu aka kawo min wannan letter, ban gane  ba. Two weeks suspension sannan ka maida ni copy editor”

“Kafin ki tafi ki je ki reporting a wajen News Director”

“Sir???”

“Ba za ki sake airing komai ba har sai kin iya banbanta professional da personal affairs”

Sai yanzu ta gane ashe shirunsa ɗazu ba yana nufin cewa ransa bai ɓaci da abinda ta yi ba ne.

“Idan kuma ba ki gyara ba, Hill TV za ta iya ɗaukan mataki mai tsauri akan ki”

Haƙuri ya ke so ta bashi ta sani kuma ba zata bayarba.

“Shikenan Sir, nagode”  daga haka ta fice daga office ɗin tana dunƙunƙune takardar da ke hannunta. 

Ko jira lokacin tashi ba ta yi ba ta ɗau jakarta ta bar station ɗin…

Asiya na zaune akan stool a ƙofar ɗakinsu tana yiwa Ummanta kitso Ubayd ya shigo gidan da sallama. Da sauri Umma ta jawo hijabinta da ke gefe ta saka ta bar Shahidah da buɗe baki. Umma ba dai kunya ba. Ta faɗa a zuciyarta.  Wai dan ma ba ayi aurenta da Ubayd ba kenan.

Ubayd ya tsugunna ya gaishe da Umma. Ya iya gaisuwa kam amma har yanzu bai fahimtar yaren kurame sosai kodan bai taso a gidan ba ne?

Ya ajiyewa Umma wata ƙatuwar leda tareda kuɗi acikin envelop.

Umma ta shiga yi ma sa godiya, ta zunguri ƙafar Asiya alamar ta tayata yiwa Ubayd  godiya.

“Ya Ubayd yaushe aka yi albashi?”

“Ai inaga ke ce dalilin wannan albashin, da safe da ki ka yi maganan albashin nan zuwa ƙarfe ɗayan rana mutane sun fara ganin alert. Ni nawa ya shigo ƙarfe uku da rabi ne lokacin ina Alwala a masallaci”

“Mugu ba. Yana tsoron kar ubangidan sa ya dawo ya samu bai biya albashi ba ya haushi da faɗa”

“Ikon Allah, yanzu ya biya albashin ma bai miki ba”

“Dama ya so yin kasuwanci da albashin mutane ne, Allah ya kamashi”

Ubayd ya girgiza kai kawai ya wuce ɗakin Inna Yaha dan ya kai mata nata kayan.

***

Yau Gwamna ya dawo daga tafiyar da yai, kusan ya ƙara kwanaki biyu bisa ranan daya ɗiba zai dawo. A ranan ne kuma abubuwa da dama suka faru.

A chan gidan Yallaɓai Alhaji Kachallah ne zaune a falon gidan yana jiran fitowar Yallaɓai. Kusan minti ishirin da biyar yai yana zaman jiran sa kafin ya fito yana dogara sandar ƙarfe wacce ta ke ta ado ba wai dan yanada matsalar ƙafa ba.

 Minti biyar ya ɗauka yana yiwa Yallaɓai bayanin abinda ke tafe da shi.

Ya ƙara da cewa ” ina fata idan lokaci yayi ba za a juya min baya ba”

Yallaɓai yai murmushi ya ce “Alhaji Kachallah ka sani sarai bana magana biyu. Abu ɗaya ne zai sa na chanja maganata, idan har shi ya karya dokar wannan tafiya”

“Ina tsoron kada Mr Paul ya idda mugun nufinsa. Idan har kujerar mataimakin Gwamna ta kuɓuce mani, Yallaɓai za a samu matsala a wannan tafiya”

“Ka kwantar da hankalinka ba abinda Mr Paul zai iya yi”

Alhaji Kachallah ya miƙe ya ce “ni zan wuce”

Bayan tafiyar Alhaji Kachallah Yallaɓai ya dubi kujerar da Alhaji Kachallan ya tashi akai, itace dai kujeran da Mr Paul ya zauna akai jiya yana kawo ƙorafinsa akan a dakatar da tafiyar Alhaji Kachallah saboda akwai giɓi sosai a tafiyar ta sa.

“Ba shi da experience ko kaɗan a wannan harka Yallaɓai. Yanada sanyin zuciya idan aka ɗaura shi akan kujera zamu samu matsala da shi. Ya kamata a datse…”

Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu. Mr Paul yai tsit yana zazzare idanu.

Yallaɓai yai murmushin gefen baki, yana son irin wannan wasan…

***

Cikin shiga ta alfarma shiga ta ƙasaitattun mata Hajiya Bilkisu ta fito daga ɗakinta. Wani tsadadden leshi fari ta saka ɗinkin buba da zani, ta saka takalmi mai tsini kalar ja wanda yai dai-dai da kalar clutch bag ɗinta, ɗan kunne da awarwaro da kuma sarƙa, 

Tana takunta ɗaiɗai har ta sauko ƙasa.

“Hajjaju Makkatun, Hajjan Gwamna, Hajjan mu” ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya tana ɗan tafa hannu.

“Hansa’u kenan”

“Hajja idan na girma ina son zama kaman ki”

Wani lokaci takan ɗan tausayawa Hansa’u. Wacce ta kawota ta gaya mata cewa auren wuri aka mata tana shekara  goma shauku, ta wahala sosai a wajen Kishiyarta. Tana shekaru shabiyar mijin ya rasu. Ba a jima ba ta haihu ɗan bai zo da rai ba wannan psychological trauma ɗin shine ya taɓa ma ta ƙwaƙwalwa. Anyita magani ana tunanin Aljanu ne ko sammu amma shiru. Bayan shekaru ana jinya shine wata Gwoggonta ta kawota Birni dan ta koyi sana’a tunda ta ƙi auruwa. Hansa’u akwai aiki kam amma akwai shirme da shiririta dan har yanzu hankalin ta kaman na budurwar ƙauye ce ‘yar shekaru shabiyar. Kusan ko da Hajiya Bilkisu ta girmeta to abinda za ta bata ba zai wuce shekaru biyu ba.

“Hansa’u Malamin Junior ya zo ko?”

“Eh Juno yana karatu da malamin sa a waje”

“Good, idan ya gama lesson ki tabbatar yayi wanka kafin ya ci abinci. Ni zan fita”

“Hajjan mu a kawo mana tsaraba”

Hajiya Bilkisu ta ɗan yi dariya sannan ta fita daga gidan ta nufi motarta inda driver ke jiranta.

Kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da ita. Ba wannan ne farkon zuwanta gidan ba amma abin mamaki ba a bari ta ƙarisa falon First lady ba kamar yadda ta saba yi idan ta zo. Mai aikin gidan ta ce ma  ta First lady na da manyan baƙi dan haka ta jira a falon baƙi kafin su tafi.

Da farko abin ya yiwa Hajiya Bilkisu banbaraƙwai saboda irin haka bai taɓa faruwa ba amma daga baya sai ta yi tunanin ko dai first lady na tare da surkuwanta ce. Ba abu ne ɓoyayye ba a wajenta irin takun saƙa da ke tsakanin First lady da Maman Gwamna. Rabuwa su ka yi da matarsa ta farko wacce sun yi kusan shekaru ashirin da biyu tare kafin su ka rabun, hakan kuma ba ƙaramin ƙona ran mahaifiyar Saminu Bacchi yai ba, Murjanatu itace uwar ‘ya’yan sa guda shida amma haka ya rufe ido ya shure ya saketa ya auro Hajiya Sha’awanatu. Kusan shekaran su bakwai da aure amma har yanzun tsakaninta da Mahaifiyar Saminu Bacchi ba sa ga maciji.

Zaman jiran da ta ke gani ba zai wuce minti ishirin zuwa talatin ba shine ya zamana har ya wuce awa biyu. 

Sau biyu tana turawa a duba ma ta first lady amma sai a ce tana tareda baƙi.

Tun Bilkisu na ɗaukan abun ba komai ba har ya zo ya fara ba ta haushi. 

Awa uku da zamanta a falon ta miƙe tsaye dan ta wuce gida zuciyarta cike da ƙuna. Barka da dawowa ta zo yiwa First lady ba wai zaman walaƙanci ba. Ko bakin ƙofa ba ta kai ba ta jiyo shewar first lady da wasu mata. Ta juya a fusace dan ganin su waye su ka fita mutunci a wajen first lady ɗin, lokacin da ta juya first lady ce ke saukowa ƙasa biye da ita kuma Hajiya Hadiza matar Senator da Hajiya Kaltume matar Commisioner.

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button