LabaraiYarinya

Subuhanallahi Cuta Ta Sa ’Yar Shekara 19 Ta Koma Karamar Yarinya

Wata cuta da ta sauya halittar wata budurwa mai suna Aboli Jarit, ’yar garin Najapur a kasar Indiya inda za a iya daukar cewa yarinya ce da ba ta wuce shekara shida ba, duk da cewa ta kai shekara 19 Aminiya ta rawaito.

Aboli, wacce take da tsawon kafa 3 da inci 4, labarinta ya dauki hankalin jama’a a shafukan intanet bayan ta wallafa shi.

A lokacin da take jaririya, an gano Aboli tana da ciwon da ke kankantar da jiki (renal rickets), wani yanayi da ba kasafai ake samun sa ba, wanda ya hada da ciwon koda da nakasar kashi.

Abu mafi muni shi ne, an haife ta da wata matsalar da dole ta sa nafkin a kowane lokaci, saboda fitsari yana zuba a-kai-a-kai.

Kasusuwan yarinyar sun ci gaba da yin rauni yayin da lokaci ya wuce, kuma daga bisani ta kasa tafiya.

Bayanai sun ce a kowace rana tana harkokinta a matsayin mai shekara 19, amma ko ta yaya ta samu karfin hali don yin kyakkyawan fata ga rayuwarta nan gaba?

Aboli Jarit ta shaida wa jaridar Jam Press cewa, “Ba mutane da yawa ne ke dauke da irin wannan cuta ba, abin da yake da kyau shi ne har yanzu ina raye kuma yawancin mutane ba za su iya rayuwa da wannan cuta ba.

“Ina so in zama mawakiya da kuma jaruma a masana’antar shirin fim ta Bollywood da Hollywood, ina fata zan iya yin hakan nan ba da jimawa ba,” inji ta.

Mafarkin Aboli shi ne ta zama sananniya, ba saboda halittar yarinta da ba a saba gani ba; Tana son mutane su gane ta don basirarta da kyanta.

An yi sa’a, tana da dangi masu goyo mata baya kuma suna karfafa wa fasaharta don taimaka mata ta cika burinta.

Duk da mutane da yawa za su yi mamaki ko da alamun rashin lafiya don ganin ta kai sama da shekara 15, ga Aboli, jin cewa tana kama da karamar yarinya ba shi ne burgewa ba.

A gaskiya ma, ba ta son yanayinta a hakan, kuma ta yi kira ga wadanda suke hada kamanninta da na wada su daina yin haka.

Yanayin budurwa Aboli Jarit ba sabon abu ba ne, kuma ba ita ce ta farko da ke da irin wannan halitta ba.

A shekarun baya, mun yi rahoto a kan wani mai suna Denis Vashurin, mai shekara 32, wanda ake kallo kamar bai cika shekara 14 ba, da kuma wani Zhu Shengkai, wani dan kasar China mai shekara 34, wanda ya daina tsawo bayan samun rauni a kai.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button