7⃣1⃣
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
*Dedicated to maman nour, soupnass, ikra rukayyat, maman 4H,hauwa lawal,kucigaba da comments*????
Jiki a mace ya shigo dakin tabishi da ido tanata kallonshi mamaki kawai yake bata yasha jibgarta amma bai taba yi mata wannan jina jinan ba, kenan itama watarana yakan iya yi mata haka,
Bakin gadon amira yaje yayi tsaye yanata kallon fuskarta da yadda take nishi zuciyarshi takara cunkushewa yanajin tsanar kanshi ,ya dade tsaye yana kallon amira Aisha batace mishi komi ba yajuya yafita daga dakin tabishi da ido,
Office din doctor ya shiga yaja kujera ya zauna yana yamutsa fuska yace “me ke damun amira? “
Doctor dake duba wani buk ya dago face yace “she’s very scared and shocked abun ya girmi brain dinta ,that force her to fainted ,amma she’ll be okay, “
Fahad yace “what about my wife? “
Doctor okato yakara gyara zama yace ” sakamakon dukan da akamata sosai tayi miscarriage sannan taji ciwuka sosai tana bukatar kulawa da lokaci kafin tasamu lpy “
Fahad ya daga kai ya hadiyi miyon bakin ciki,
Doctor yace “as ur family doctor I want to advise you, dukan mata baya taba kawo gyara sede yabata, mata wani lokaci they’re crazy se ana kai zuciya nesa ana kaucemusu amma duka bedace dasu ba saboda they’re weak , ina maka jajen rashi da kukayi Allah ya bata lpy”
(wani lokaci sekaga Christian da soft heart kuji yadda yake bawa fahad shawara)
Fahad yace “thanks you”
yatashi yafita yanajin duk duniyar tamishi zafi,
omer yakira abba yafada mashi suna asibity kuma ana bukatar jini ba bata lokaci segashi asibityn aka dibi nashi dana abul, aka cigaba da sawa faseelat dake kwance tana nishi,
Duk kansu hankalinsu tashe abba yakasa yadda da abun da yake gani,
ummi dataci kuka tagaji tacewa abba “wlh seya saketa yata bazata zauna da meduka ba, wannan shine karshen zamansu”
abba yace “kiyi hakuri asiya amma kidena rantsuwa cikin bacin rai, amma ni kaina bazanso takoma gidan shi ba”
ummi tace”hmmmmm”!
fahad dakin da akai admitting faseelat ya nufa ,akunyace ya tura kofar ya shiga wayam ba faseelat basu ummi yabi gadon da kallo zuwa jinin dake sargafe ,ya karasa ya tura kofar toilet nanma wayam hankalinshi tashe yakaiwa abunda ake dannawa for emergency bugu ya dauki kara, duk yaburkice ko 1mnt baaiba doctor yashigo da nurses biyu, sukaga gadon wayam se fahad dake tsaye kamar mahaukaci,
fahad jijiyoyi amike yace “where’s my wife? Ina matata where do you take her? “
Doctor da mamaki yagama cika shi yace “this is unbelievable, how will this happened in my hospital? “
Ya kalli fahad yace “I’m sorry sir bansan komai ke faruwa ba amma we have CCTV cameras all around the hospital zamu gano mike faruwa”
Fahad ya dafe goshi kanshi na mugun bugawa ,su ummi suka dauketa kokuwa? Yana ta tambayar kanshi,
Doctor yadafa shi yace “meet me in my office “
Yajuya yafita tareda nurses ,hawaye suka zubowa fahad yace “meyasa zaku dauketa? Ni yadace na kula daita”
Ya fita ya nufi office na likita,likita yanata duba computer abunda yafaru akofar dakin faseelat ya juya wa fahad computer yace “take a look at them do you know them or seen them before? “
fahad ya kalli computer omer ya fito dauke da faseelat ranshi yakara baci yace “he’s her brother, but saboda me zaabari sufitar min da mata a asibity su suka kawota ?yama akai suka san we are here? bazan kara kawo patient a asibitin nan ba tunda it’s not safety “
doctor yajawo computer gabanshi yayi rewinding lokacin da bello yakawosu kofar dakin ranshi ya baci yaja telephone ya kira number office dinsu bello ba dadewa sega shi ya shigo yanata hada zufa,
fuska tamke okato yanunawa bello computer yace “meyasa ka kira wadannan mutanen waya aike ka? meyasa ?”
bello yace “I’m sorry nasan yayanta ne banyi tunanin fadamishi ze zama matsala ba kuma nayi iya kokarina na tsayardasu basu tsaya ba “
fahad jiyake kamar yakaiwa bello naushi don haka ya tashi yafita ,
okato yace “meyasa baka fadawa securities ba? U r suspended kaje sena nemeka “
Bello ya fara begging “I’m sorry sir it’s a mistake wlh danasan haka zata faru da bazan kira shi ba dan Allah kayi hakuri “
okato ya nunashi da yatsa cikin nuna gargadi yace “next time idan haka tasake faruwa zaka bar nan harabada,now leave “
Bello yajuya yafita yana yamutsa fuska cikin ranshi yanata regretting kiran omer,
Fahad nafita yashiga mota ya nufi gidan umma don besan ya zaiyi ba, a mota hawaye yake tayi duk lokacin da ya tuno ihunta da jinin da ya zuba seyaji hawayen tausayinta Sun zubomishi,
ya samu yaisa gidan umma suna zaune suna kallon film din su bosho munafikin mata sunata dariyar yadda yake fadawa hafsa idris cewa jamila nagudu wari take seya toshe hanci yake bacci saboda tusa, kwasar dariyarsu kawai suke hankali kwance ,ya shigo main falon wuji wuji dashi riga duk jini, dukkansu faraar dake kan fuskarsu ta gushe yaje wurin umma ya zauna kasa tana kan kujera yadora fuska akan cinyar ta yasaki kuka,
Umma tadora hannu ta tallabo fuskarshi zuciyarta na harbawa dasauri tace “meyafaru fahad jinin minene ajikin ka haka? “
yana kuka yace “umma I cheated myself na doki faseelat har tayi miscarriage “
umma dasu lady suka dau salati “innalillahi wainna ilaihi rajiun!”
Umma kamar zatai kuka tace “me tamaka da zaka dauki wannan hukuncin? Faseelat ce fa ur love meyasa zakai haka? “
Muryarshi na rarrabuwa yace “naga pic dinta da wani awayarta I tried my best nakasa controlling kaina shine na doketa”
umma tai shiru hawaye suka zubomata na tausayin baiwar Allah,
ya cigaba da cewa “na kaita asibity ,wani doctor yakira yayanta yafadamishi ina komawa nasamu Sun dauketa Sun tafi daita, ya zanyi ne umma? “ya cigaba da kuka,
Su lady suna hawaye suka tashi sukabar main falon,
Umma tasamu ta goge hawayen fuskarta tace “sunyi dede kuma Sun kyauta konice abinda zanyi kenan, banji dadi ba da dana yakasance mahaukaci me dukan mata ba don duk namiji me hankali bazaya iya daukar hannu ya daki matarshi ba ,bare faseelat yarinya me ladabi da biyayya me sonka me addini amma har kaiya cutar daita kayiwa kanka ai don bazaka taba samun kamar ta ba “
yana hawaye yace “umma Dan Allah ki temakamin kije ki basu hakuri wlh inasonta kishinta ne yasa nai haka”
umma tace “yo kishi haukane ko kai kadai ne me kishi aduniya? Saad daya daga cikin mubashshirina bil janna yace dazan kama wani akan shimfidar iyali na dazan sare shi da adda kuma ta wurin kaifin zansa se sahabbai sukaita mamakin kishinsa manzon Allah (S. A. W) yace shin kuna mamakin kishin saad ne? yace wlh ni nafishi kishi kuma Allah yafimu kishi gabadaya,bakai kadaine me kishi ba fahad amma ai kishi bekamata ya rabaka da hankalinka da imaninka ba har kayi kisan kai ko agadon ta kasameshi? kasan yaya suke daita ne? Shin kai baka daukar pic dasu lady dasu ramlat? , wai duka ne har ze zubar da ciki wlh fahad bakayi ba ni banda temakon da zan maka sede zan baka shawara ka koma wurin malamai kakara neman ilimi saboda da kanada ilimi wadatacce da baka aikata haka ba “
ta dauke kanshi tatashi zata haye sama ya waiwaya fuskarsa gwanin tausayi yace” umma tafiya zakiyi? “
Batare da ta jiyo ba tace”eh tafiya zanyi ko zaunawa zanyi na tayaka kukan katashi kabarmin gida “ta haye sama ranta bace,
wasu zafafan hawaye suka zubowa fahad dama anan kadai yake tunanin samun sauki kuma itama ta hau ya dade zaune sannan ya tashi ya fita ya nufi gida,
Yana zuwa ya danne horn bako dagawa baba tsoho na toilet yaji odar tayi yawa ko tsarki besamu yayi ba yafito da gudu yaja gate din dayake sliding ne,
fahad da kanshi ke jikin sitiyari ya dago yaja motar cikin gida,
Yakai kusan 15mnt zaune sannan yafito yashiga cikin gidan, dakin faseelat ya nufa zuciyarshi na harbawa tuno jinin dake kwance adakin,
dakin a bude yake yana zuwa yayi tsaye ya dafe kofa yasa sabon kuka dakin duk jini bakyan gani, ya karasa ciki yanata kukan yayi zaman dirshan gaban gudan tsokokin dake a wurin yana ta kallonsu yana kuka, yake tuno maganar faseelat “amma kasani cikinnan shine farincikina shi nake burin gani ayanzu nabaka amanarshi karka bari wani abu yasameshi”
da kuma inda take cewa “zan haifarma baby boy kasamu freind”
Kamar dan maye yafara magana “meyasa zaka zube?inason naganka araye banyi don na cutar da kai ba, katafi kabarta she love you ur her happiness and joy why zaka gujeta? it’s just an accident meyasa bazaka hakura ba…” maganganun duk gasunan yadade yana sambatu, har yakai yayi kwance agun,
can zuwa yatashi yasamo leda ya sa hannu ya fara kwashe abinda zeiya kwasuwa yagama ya kulle ya ajiye gefe, ya cire shirt din jikinshi ya gogge abinda yasamu yafita ya dauko mofa yazo ya goge wurin sosai ya kuma sa fresheners duk da haka seda dakin yadauki kanni,
yafita yaje can garden yayi rami ya rufe ledan da rigar yadawo ya shiga toilet yasakarwa kanshi ruwa yanata meda numfashi, yana cikin cuda jikinshi ya tuno yadda yaja faseelat daga toilet din tana cikin cuda jikinta yakai wa bango naushi yanajin haushin kanshi, wayar faseelat ta fado mai arai yayi sauri yafito ya dauketa duk ta tarwatse baxata kara amfanuwa ba, ya budeta ya cire sim dinta wanda take chart ya dauko one of his phone yasa sim din, ya sake download wats app yayi restoring duk messages suka dawo ciki, yakoma cikin chart din ta da baffa beko bude pic dinba yawuce gaba don kar zuciyarshi ta tarwatse , faseelat da taga pic din tace “baffa kayi hakuri plss bansan yaakai nai missing contact dinka ba, ya gida yasu hjya da alhaji? ashe haryanzu kanada wannan pic din yayi kyau sosai “
Baffa yace “lpy lau suke ,badole kiyi missing no dina ba tunda kinyi aure ???? thank God ansamin rana jiya nima zan angwance “
faseelat ta tura laugh emoji ????tace “wai dagaske ?yaakai bansaniba “
Yayi dariya yace “young girl ,ai ummi dazakiji gunta batanan nasan kuma wannan miskilin baze kiraki yafada miki ba “
faseelat ta turamashi smiling face tace “namaka murna wacece ita takaini kyau ? ????“
yace “kedin me kyakkyawa ce ajin karshe”
faseelat tace “muganta in dagaske ne “
yayi dariya yace”banda sheri fa “
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
tace “Allah aa kawai inason ganinta “
seya turomata pic din wata black beauty jibgegiya kamata???? me dogon hanci da wawakeken baki tana da ido she’s cute de ????????,
Faseelat ta tura mishi “haba baffa wannan doshumar ina zaka ajiyeta ????“
baffa yace “kambuuuu matar tawa ce doshuma?”
faseelat tatura mai “sorry sorry ????“
yace “ke ni banason fararen mata ni fari ita fara abun will waste, nafison baka me kiba shiyasa seda na darje amma ai tanada kyau duba sosai inkuma Sheri ne sekitayi “
Faseelat takara kallon pic din itade awurinta batada kyau abun mamaki ma yabata yadda yake kyakkyawa amma wagga yakeso lalle so makaho ne,
Tace ” Allah yasa alheri, gaskiya tana da kyau ka gaidata kafin musan juna”
Yace “wannan is not a villager wayayyace degree gareta akan microbiology awani hospital ma take aiki kibari gobe innaje wurinta zan kiraki vedio call amma ta wats app seku gaisa daita ki kara ganinta sosai Allah tahadu kuma tanada hankali”
faseelat tace “ihmmmmm Allah yakaimu naganta “
Daganan se chart da yaturo mata yau wanda bata ganiba,
“aljanah ya kk tashi? gani wurin waseela “
“zan kiraki yanzu”
Se kiran,
fahad yasa hannu yaita bugun kanshi yana hawayen danasani “why ban tsaya ida karanta messages dinba? “
“meyasa zata dauki pic dashi? don yana cousin dinta ai zeiya aurenta donme zata sakarmishi jikina “
Yanajin wani malolon bakin ciki a makoshi yace “ya Allah ka ragemin kishinnan na zauna lpy kasamin hakuri akan dangin ta, don ban kaunar naga tana muamala da kowane namiji”niko nace insun barmaka ita ko?
yatashi zuciyarshi na ciwo yasaka kaya ya tada salla har anyi laasar yayisu ahade, be taba adduar Allah yarage masa kishi ba segashi yau shine ke kuka yana rokon Allah yarage masa kishinsa,
yana gamawa ya tashi yafita direct gidan su faseelat ya nufa amma gidan akulle don duk suna asibity,
yadade yana kallon kofar sannan yajuya ya nufi asibity,
A asibity amira ta farko a firgice, Aisha ta riketa tana rarrashi amira tana kuka take cewa “ina anty? Ni kikai ni wurin anty “suna haka fahad ya shigo ya karasa bakin gadon dasauri yana fadin “sannu princess “
amira naganinshi ta rumtse ido tai gum zuciyarta na harbawa don matsanancin tsoronshi takeji,
Aisha dake hawaye ta kalleshi,
Ya riko hannun amira yace “princess open ur eyes it’s me ur dad “
gaf-gaf hannun amira ya dauki rawa, takara rumtse idonta yanzu in akwai abinda batasan gani befi daddinta ba,
Aisha ta zare hannunshi tana hawaye tace “katashi kafita bata son ganinka tsoron ka takeji karka karasa rikitamin ita”
Yayi kasake yana kallonta yace “u r lying “
Ya meda hannu ya riko amira yace “amira it’s me ur beloved dad”
amira tafasa kara idanunta a kulle wadda tasa seda fahad yasaki hannunta, amira na kuka tace “I don’t want to see you stay away from me”
ya fiddo ido waje “amira nine fa dad dinki bakison gani na inyi nesa dake? “
amira tace “mommy please take me to big mom house I’m scared here,”
Aisha tace “Dan Allah kafita kabarmu, badole taji tsoronka ba yadda kake dukan mu tana gani tanaji dan Allah kafita “
Fahad ya tashi yafita yanata tariyo maganganun umma da amira, wai his daughter da kullum take cewa she love him itace ke cewa yayi nesa daita ,ya shiga motar shi yayi zaune yakasa ma hawaye se zuciyarshi dake kuna,
yadade zaune sannan ya nufi gidan mommy dan yafada mata amira ba lpy,kokadan beda niyyar fadamata abunda yafaru amma yasan she must heard it,
har lokacin faseelat bata farfado ba daga baccin da take, dukkansu tun safe har yanzu bayan laasar ba wanda yakara sawa cikinshi komi,
itako jamila gidan siyama tawuce tana ta kuka tafadawa siyama abinda tayi tace dan Allah taje tabata hakuri,bataso su mama suji siyama shiru tayi kawai jin abinda hjy keyi da tsiyar da jamila tayi,
seda mijinta yayan mamar jamila yadawo cin abinci sannan siyama tafadamishi abinda jamila tayi tace anjima ze kaisu su bata hakuri,
Ranshi ya baci yakira jamila ya rufeta da fada “ke dan uwarki saboda yana kai dare be dawo ba shine zakije kiwa hjy wulakanci, ke wlh a aljanna kike in kikaji matsalolin uwayen mazan wasu sakarai shasha hakanan zaki rusa mana zumunci, kika ma kanki wlh in kuma so kike ki zama karamar jawara to tashi kiban wuri “jamila ta tashi tana kuka tafita,
Cikin kwantar da hankali siyama tace “kayi hakuri yarinya ce nangaba ko ance tayi bazata yi ba,Allah yasa hjyar ta hakura “
Tai shiru tana tunani don tasan hjyar ma bata kyauta ba kuma zatai mata magana koba yau ba ,
Motarsu khalil tayi nisa da tafiya sunkusa kai batsari tunda yashiga counter dinshi kawai yake latsawa yana lazimi dede gadar wani kauye kurmiyal wata mota ta kwacewa wani driver tazo tabanki motar su khalil karfen da yakare gadar ya balle duka motocin suka afka cikin gadar akife , suna fadawa suka kama da wuta gabadayansu,
Kafin mutane su taru mutanen ciki tuni sun kone koda mutane sukazo bakajin sautin komi se fasss! Dasss!! Tatasss!!! Jikin mutane na fashewa, mutane sunata zuba kasa da ruwa kafin motar kashe gobara tazo , daga katsina zuwa kurmiyal akwai yar tafiya don sunfi kusa da batsari,shiyasa abun yadauki mintoci
wutar bata mutu ba har yan kwana kwana sukazo aka kashe wutar ,
ranar yan kauyen kurmiyal sunga tashin hankali tsoron Allah yakara shigarsu wadanda suka manta da Allah ranar Sun tunadashi sun koma agunshi, ga warwakin sunyi baki kirin wasu Sun fashe wasu Sun kwarkwarje wasu hanji awaje, yara, jarirai, maza, mata, samari da yanmatasa,
kusan rai 15 don waccan motar j5 ce,
ba jimawa police suka zo aka daukesu zuwa matuary kafin asamu danginsu dukkansu sun mutu kurmusss,
dandanan gidajen radio suka fara baza labarin,
Hjya aminiyar radio tana zaune tana sauraren radion taji hadarin gabanta yayi mummunar faduwa, tai sauri takashe radion,
Ba arziki tana rawar duwawu ta shiga daki tana haki ta dauki waya takira mamar jamila,
Mamar jamila dabatasan abinda ke faruwa ba ta dauka da sallama hjy batako amsa ba tace “khalil yaiso nan? “
mamar jamila tace “a, a khalil bezo ba da yataho…. “bata ida magana ba wayar ta sullube daga hannun hjy,
Ta zame kasa zaune saboda kafafunta daketa rawa, ta dora hannu akai tafasa kara “nashiga ukku nabani na lalace wayyo Allah khalil dina ya mutu ya tafi yabarni”hawaye kamar famfo suke zubarmata ihun da take ta rafkawa yasa seda makwabtan ta suka shigo gidan suka rirriketa suna tambayar baasi,
Allah sarki rayuwa in Allah yaso cikin kiftawar ido se kaga duniyar ta zama empty , mutum ba abakin komi ba amma munsamu duniya mun shan take ko tunanin mutuwar ma bamayi kamar anan zamu dawwama,mun manta kiyama munata tsiya,ya Allah ka kyautata rayuwarmu kasa mucika da imani kasa muyi kyakkyawan karshe amin,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
*ya ubangiji ina rokon ka kajikan dukkan musulmai maza da mata ka musu rahma kajikansu domin kai mai rahma ne me jinkai*????????????
[8/20, 7:11 PM] SHALELE????: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍????✍???? *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍????✍????✍????
We are bearer’s of so golden a pen????
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen????
Be hold our words
A product of our pen????
Savour our words
For it will cause you no pain.✍????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣2⃣
*SHAFIN mommyn mufeeda da me dambu inajin dadi yadda kukasance daga cikin mabiyan buk dina ina kuma jin dadin comments naku thanks*
*yaruwa kinayin azkhar din safiya da marece kuwa? Koko aiki da son kwanciya barci ko saurin kunna data suna hanaki yi? Da kinsan falalar yinsu dako kina gudun ceton rai zaki rikayin su,in kuma kinsan falalarsu why kike sanya? Ko mantawa dasu? Azkhar suna haska rayuwa, yana sauya mummunan abu zuwa alheri, kariya ce daga sharrin kowane abu, yana kawo arziki dajin dadin rayuwa,yana gyara zuciya,yana kusantar da mutum ga ubangiji, yana kai mutum zuwa aljanna,shin me zesa kiyi sanya da yinsu? gasunan da yawa masu saukin karantawa se dumbin lada da falala, Dan Allah murika yin azkhar karmuyi sanya dasu don neman kusanci da kariya awurin ubangiji, duk abinda mukeyi mu daure murika yin azkhar dinnan koda muna kitchen ne, ko a mota going to office ko a school ko ina sau da dama Allah ya janyemiki sharri sanadin azkhar wanda ke baki sani ba, kinemi littafin azkhar a book shop’s ki kara samun wasu ki hardace kitayi insha Allah zakiji dadinsu kuma zaki samu natsuwa*
*yaruwa kinada riyadul janna fi azkharul kitabu was sunna kuwa?littafi ne da ya tattara azkhar da adduoi wanda baakawosu hakanan ba seda akafara rubuto hadissan da aka samosu da wadanda suka ruwaito, acikinshi akwai adduoi da yawa wadanda wlh zakiji dadinsu an tattara duk adduoin dake cikin alkurani a littafin da kuma sunayen Allah kyawawa wadanda idan an rokeshi dasu yana amsawa wanda sukazo a alkurani me girma wanda suka jerosu tun daga fatiha to nas, ga kuma manyan adduoi a bayansu wanda Allah yake amsa addua in akayi su , na rungumi riyadul janna naji dadinshi matuka,idan bakidashi ina me baki/ka shawara ki nemi riyadul janna zaki samu biyan bukata kuma zakisamu kusanci da Allah (S.W).zaki sameshi a kasuwanni wurin masu littattafai ko bookshops wallafar yusuf bin Ismael ,bangonshi da hoton lambu da flowers,nasan beda tsada ada bansaniba yanzu kiyi kokari ki mallakeshi don bukatarki, bakin cikinki,ko damuwarki zasu yaye,zaki godemin kede kinemi naki ki runguma*
Cikin gigicewa Hajiya take ce musu”nabani khalil dina ya mutu yayi accident ya mutu”
Matan suka dauki salati jikinsu yayi sanyi domin khalil mutum ne har mutum yana girmama mutane bazaka ce ga abokin fadanshi ba yana da hakuri uwa uba yawan ibada,
Hjy tace “hjya rabi Dan Allah kuce be mutu ba, be mutu bako? Nasan baze mutu yabar niba bandashi cikin motar wlh babu shi”
matar daakace ma hiya rabi ta kalli abokiyar zamanta tace “hjya zaliha ki kira alhaji kifada mishi yafada ma manu naji labarin accident din yanzu inajin radio se suje su dubo indashi se suanso gawar ai mishi sutura “
Zaliha ta juya dasauri ta shiga gida ta dauki waya ta kira mijinsu tafada mai yayi ta sallallami yace “yanzunnan naji labarin accident din bari nakira manun donni ina jibia amma yanzunnan zan kamo hanya “
ya kashe kiran ya kira manu, kawu manu ya girgiza ba bata lokaci ya tafi gidan kaninshi suka nufi matuary dauko gawa,
zaliha ba bata lokaci ta dannawa siyama kira ,siyama na kitchen wayar ta keta kara yaranta duk sun tafi islamiya jamila ta dauko wayar ta kawomata ta juya ,
siyama ta dauka takara kunne da sallama a bakinta,
Zaliha tace “siyama nice hjya zaliha ki taho gida khalil yayi accident ya rasu hjyar ku kuma bata lpy”diff takashe takoma gidan hjya dasauri,
Siyama zuciyarta ta rika harbawa dasauri hawaye suka rika zuba a fuskarta masu zafin gaske,
Tai cikin daki tana kuka, jamila dake zaune tayi tagumi taga siyamar tashigo tana kuka ta tashi tabita ciki siyama har tazira hijab jamila tana ta kallonta tace “anty lpy kike kuka? “
siyama tafashe da kuka tace “yaya khalil ne yayi accident ya rasu “
kamar saukar guduma jamila taji maganar ta yanke jiki tafadi,
Siyama tai kanta tana kuka tana kiran sunanta “jamila! Jamila kitashi Dan Allah “
Mijinta babban mutum ne idan ya dawo aiki a kofar gidanshi yake zama wurin har yazama majalisa cika yake da maza,
siyama ta tashi tafita waje dagudu bata tsaya koina ba se gaban mazan dake gun ta kalli mijinta tana kuka cikin tashin hankali tace “baban farida jamila ta fadi “
yace “subhanallahi ! “ya tashi yayi cikin gidan dasauri, siyama tabi bayanshi,
Yana shiga ya samu jamila a sume da sauri ya bude fridge ya dauko ruwa masu sanyi ya sheka mata su a fuska,
jamila tasaki ajiyar zuciya ta bude ido wuf tatashi zaune tafara hawaye” anty yaya na ya rasu? Ya khalil dina fa”?
siyama daketa kuka tace “ya rasu jamila “
Marar jamila da tunda tafarko take murdawa kadan, ta murda da karfi ,jamila ta dafe ciki da kugu tafara kuka tana nishi zufa tarika karyomata ta koina,
Baban farida yace “siyama me kike fada ne?”
siyama tace “yanzunnan aka kirani akace yayi accident ya rasu “
Baban farida yace “innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!! …
karar da jamila tayi ne ya katseshi,
“wayyo Allah marata zata balle wayyo kuguna “
dashi da siyama suka rirriketa baban farida yace ma siyama “dauko min keys dina mutafi asibity”
Siyama ta saketa tana kuka tatafi dauko keys, shima idonshi jawur ya dauko jamila suka fito siyama ta bude mai yasa jamila baya tashiga yajasu suka nufi asibity, tsakanin jamila da siyama bazaka gane wake nakudar ba don dukkansu kuka suke riris,
baban farida har kyarma yake wajen tuki dakyar suka isa Medical Center aka amshi jamila akashiga daita,
siyama ta cigaba da kuka zuciyarta kamar zata fito duka yaushe sukai rashin alhaji yanzu kuma khalil,
baban farida ya rungumota jikinshi yana rarrashi,
ba jimawa wata nurse tafito wurinsu tana sauri tace “patient da kuka kawo labour take ayi sauri akawo kayan haihuwa “tajuya takoma dakin,
baban farida ya zaunar da siyama akan seat ya fita anan bakin asibitin yasiyi kayan haihuwar ya koma ciki dasauri,
Ba jimawa nurse tafito ta amshi kayan hankali tashe yace “ta haihu ne?”
nurse din tace “a, a dasauran lokaci kumata addua “takoma ciki dasauri,
wayar baban farida tadau kara yana dubawa yaga mamar jamila ce, kamar kar yadauka ya dauka ya kanga akunne ,
acan bangaren tace “yaya kuna lpy kuwa dazun maman siyama ta kirani tana tambayar khalil ko yazonan bamu gama waya ba takashe wayar yanzu naji labarin accident da akayi ahanya shine hankalina ya tashi nace bari nakira “
Murya dishe yace “harda Khalil acikin accident din, yanzuma muna asibity jamila labour take “
maman jamila dake zaune ta mike tsaye tana salati tace “Allah yajikanshi, Allah yabata lpy nan bada jimawa ba zamu taho “takashe kiran tafara neman layin mijinta yana dauka tafada mishi ba jimawa yazo gida suka kama hanyar kt,
Shiru shiru jamila bata haihu ba, hankalinshi duk da baa kwance yake ba yayi ta maza yacewa siyama tajira zeje yadawo,
yanufi gidan hjy,
Hjya tabi ta rude tayi sambatu har muryarta ta shake dole tai shiru tana ta kuka batsayawa, matan dake wurinta sunata bata hakuri, hjy rabi tafara mata nata waazi “haba hjy kinaso kinuna Allah be kyauta ba komi? kituna fa Allah ne yabaki shi kuma ya amshi kayansa meyasa bazaki hakuri ba? Kiyi hakuri kita innalillahi wainna ilaihi rajiun ki kuma cigaba da mishi addua ita yake bukata a yanzu ,insha Allah yanzu khalil ba abinda yakeso fiyeda akaishi makwancinsa inamishi kyakkyawan zato kiyi hakuri Allah seyabaki ladar hakurinki, ko kuma kita kuka da surutan har Allah yayi fushi dake, hjy bayau akafara miki mutuwa ba ina iyayenki ina mijinki? duk kin hakura donmi yanzu bazaki hakuri ba? kuka dole ne amma ba irin yadda kike ba kiyi hakuri Allah yamishi rahma “
hjya ta cigaba da kukanta danbata jin wani waazi yanzu,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
kawu manu sunje matuary mutane da yawa wadanda abun ya rutsa da yanuwansu ,har akazo kan su kawu manu aka tambayi sunan khalil suka fadi acikin list na fasinja harda khalil a motar su shidda ne ,
dandanan aka shiga dasu ciki akafara zaro maza daga lokokinsu ba kyangani abun, basuga khalil ba, abun yabasu mamaki ga sunanshi amma babushi dan sandan da kenan yace “to gaskiya kila babushi a motar don motocin duk sunyi ragaraga kaida ka gansu kasan ba ran daze fita daga ciki kuma ba gawar da tazama toka donba kasusuwa kuma wurin ba wasu gawarwaki awaje munyi screening sosai kuje kukara bincikawa ko kafin accident sun saukeshi wani gari “
su kawu manu suka fita suka nufi gidan hjya,
hjya na zaune tayi lakwas ko mutuwar alhaji bata girgizata haka ba, suka shigo suka zauna,
ta dago tace “manu ina gawar khalil? Ko gawar tashi ma bazan samu gani ba? “
manu yace “se hakuri hjy, Allah kadai yasan komi munje acikin gawarwakin ba khalil kuma dasunanshi acikin list na passengers ,kila babu shi cikin motar”
Hjya tafashe da kuka da shakakkar muryarta tace “khalil ya zama toka ya zaai aganshi,ashe kallon bankwana nayi mishi ayau, naso ya mutu yanajin dadi ba cikin kunci ba “
baban farida yayi sallama yashiga ciki,
kawu manu yace “ance ba gawar da ta kone, kode har yaisa batsarin shi?”
baban farida yace “a, a beje ba saboda yanzu mukayi waya da zulai tace beje ba “
hjya tace “khalil fa ya rasu shikenan banda kowa yanzu se siyama ba alhaji ba khalil “
Sukace “hakuri zakiyi hjya Allah yajikansu ya musu rahma “
Hjy ta kalli baban farida tace “ina siyamar? “
baban farida yace “suna asibity da jamila taji mutuwar se labour tataso mata “
hawaye suka zuboma hjy jin wadda ma yatafi biko tana cikin garin, se tausayin jamilar yakamata tanason khalil sosai, se hjyar taji yanzu ba abunda takeson gani se dan ko yar khalil ,
Tana share hawaye tacewa baban farida “mutafi asibitin “
Ta tashi ta dauko abayarta, ta fita su kawu manu da baban farida suka biyo bayanta, su hjya rabi ko suna zaune jingum jingum,
Baban farida ya budemata mota tashiga suka nufi asibity,
Suna zuwa siyama ta rungume hjy tana ta kuka se yazama hjyarce ke rarrashin siyamar, suna tsaye ba abinda sukeji se kukan jamila dake fitowa daga cikin labour room,
Fahad na isa gidan mommy yashiga jiki sabule ,ya fada kan kujera yayi zaune yanata tunani yanzu wane hali faseelat take ciki? zuciyarshi zafi kawai take for minutes sannan mommy tafito taganshi yanayinshi wani iri tace “lpy son naganka haka? “
yace “mommy amira bata lpy suna asibity tundazu “
mommy tace “subhanallahi tun yaushe? “
yace “tunda safe “
tace “shine se yanzu zakafadamin? “
Yayi shiru taja tsoki ta haye sama segata tafito da gyale da car key da jaka tazo zata wuceshi tafita,
Yace “mommy kitafin musu da abinci don haryanzu Aisha bataci komi ba “
mommy ta harareshi tace “tunda safe ace haryanzu bataci komi ba kai miye amfaninka ne dabazaka zo kafadamin ba in ita hankalinta ya dauku wurin jinya? Mtsswww “taja tsoki tafara kwadawa jummai kira, jummai tazo dagudu mommy tace “kingama dinner? “
Jummai tace “a, a amma akwai abincin rana kuma cikin warmer yake “
Mommy tace “daukomunshi dasauri”
jummai takoma tadawo da kula mommy ta amsa ta fita tashiga mota tai asibity,
Fahad nanan zaune dafe da kai yarasa yazayayi neman mafita yaketayi daga karshe yatashi yakoma kofar gidansu faseelat har lokacin kulle gidan yake yaja tsoki yanajin kamar yayi kuka ya bar unguwar,
mommy nashiga wurinsu Aisha amira ta rungumeta tana hawaye tace “mommy kitafi dani gidanki banison gidan daddy “
mommy tace “yi hakuri princess dake zan tafi kinji ko? Ki kwantar da hankalinki “ta kwantar da amira jikinta,
ta kalli Aisha dake koje koje tace “meya sameta?”
Aisha ta girgiza kai tace “zamuyi maganar after”
Mommy tace “okay kidaure kici abinci ko kadanne fahad yace bakici komi ba “
Aisha tace “banajin yunwa ruwa kawai nakeso “
Mommy tace “kibude jug gashinan ki zuba tea kisha amira nasa aka hadomashi itama ki zubamata “
Aisha tace “baride na zuba mata kibata ni zanfita nasamo mana drinks a reception “
Ta zuba tamikawa mommy ta dauki kudi ajakar mommy tafita,
Mommy tayi tayi amira tasha amira taki sema tafara rigimar ita anty “mommy ni anty nakeson gani ki kaini wurin anty”mommy tai shiru tana tunani dan tagano akwai abinda ke faruwa,
Su hjy na zaune sukaji kukan jariri yanata inyarrrr inyarrrr, hawaye suka zubowa hjya, dukda jamila ta haihu bata bar kuka ba nurses sukace ko ciwo takeji wani wuri batace musu komi ba tacigaba da kuka sunata fada itako bata fasa kukanta ba, suka shirya baby nurse tafito wurin su hjya dauke dashi,
duk suka tashi tsaye hjya hannunta har rawa yake wurin son ta amshi yaron, ta amsheshi ta bude fuskarshi yaron sakkkkk khalil lokacin da yana jariri, hjy se kuka ita kuka siyama kuka, Allah assamad khalil yatafi khalil yadawo, nurse tai tsaye tana kallonsu ganin suduka suna kuka ta juya takoma ciki,
Baban farida na tsaye ya rike hannu,
bayan mintoci aka fito da jamila aka medata rest room, su hjya sukabi zuwa dakin,
Jamila na kwance tana ta kuka suka shigo hjya ta mikawa baban farida jaririn ta matsa tariko hannun jamila tace “kiyi hakuri jamila, Allah yafimu san khalil shiyasa yadauki abunsa, “
fuska jage jage da majina da hawaye jamila ta kalli hjya tace “hjy kema kin yarda ya mutu? Wlh be mutu ba yana raye yananan zuwa baze tafi yabarni ba “
Hjya ta share hawaye tace “kiyi hakuri jamila kowa seya tafi can”
jamila takara fashewa da kuka, ko sanin me ta haifa ma batayi ba, hjy tasa hannu tana share mata hawaye tana rarrashinta,
Baban farida besan lokacin da hawaye suka zubomishita gefen ido ba, duniya kenan gashide wanda suke fada kanshi ya rasu dukansu suna kukan rashi yasa hannu ya share,
ana haka mamanta suka iso ,jamila takara wage baki tana kuka, duk dauriyar zulai seda tayi kuka,
gaf Maghreb faseelat ta farfado tana nishi ,idonta arufe ta tuno abinda yafaru tabude ido dasauri hawaye na zubarmata ta dafa cikinta dake ciwo, hawaye masu zafi suka kara zubomata,
ummi ta dafata tace “sannu faseelat ya kikeji?”
Se sannan faseelat tasan su ummi na wurin ta juyar dakai ga ummi abba,omer abul ishak da Mubarak harda baaba matar baba babba,
hawaye na cigaba da zubomata murya dishe tace “ummi cikin ya zube ko? “
ummi tace “kiyi hakuri haka Allah yakaddara”
Faseelat ta juyar da kai tana hawaye ,tana tuno yadda fahad ya rikice yarika dukanta kamar ba mutum ba, yanzu shikenan cikin ya tafi,
Ummi takatse mata tunani tace “bari na temaka miki kisha tea kokadanne “
faseelat ta girgiza kai tace “nakoshi ummi bazan iya cin komi ba”
Ummi tace”kidaure ko kinsamu karfi “
faseelat ta girgiza kai, dukkansu suka matso suna mata sannu ta rumtse ido bata amsa suba,
she wonder yaakai takenan ina fahad yaakai baya nan se su ummi kawai mike faruwa ne? Karde……..zuciyarta tabuga da karfi, ta bude ido tace “ummi ina fahad? “
ya omer dake gefe zuciyarshi nacigaba da tafasa saboda halin da take ciki jin tana nemenshi yasa yaja dogon tsoki ya fita daga dakin,
Ummi rai bace tace”wane fahad kuma ke yanzu dan kina dakikiya ya nakada maki shegen duka daga farkowarki kifara tambayarshi wlh sunan fahad yafita daga bakinki ko natashi nai tafiya ta “
faseelat na hawaye tace “ummi waya kawoni nan?dan Allah kufadamin yana ina “
Ummi taja tsoki zatai magana abba yace “Dan Allah kibarta zafin ciwo ne bawani abu ba, kibari tadawo hankalinta sannan “
ummi ta tabe baki, faseelat ta cigaba da hawaye zuciyarta na harbawa tarasa gane meke faruwa,
Maghreb tayi musa da yazo duba gonarshi daga babbar riga, besamu yaje gonar bama seda aka kusa Maghreb don ya samu hadarin da yafaru, yagama abunda yake ya na cikin tafiya zuwa wurin da yayi parking motarshi yaga mutum sheme sanbal straight akwance acikin ciyayi,
Ya matsa wurin khalil ba alamun ko rauni jikinshi ya zukunna ya fara duba shi,
kamar wanda yayi bacci khalil ya tashi zaune, yana salati ya jujjuya kai gabas da yamma kudu da arewa ,sannan yadafe goshi yana jin kuwwar mutane da salati da mutane sukai tayi lokacin accident din,
musa ya dafashi yace “bawan Allah mekake anan yanzu da daddare? “
khalil idanunshi jawur zuciyarshi sanyaye yace “bansan yaakai nazo nan ba, nide nasan muna cikin mota, wata mota tahawo tamu daganan bazan iya tuna komi ba”
Musa yaja kabbara “Allahu akbar ,Allah me yadda yaso dama akwai ran da yafita a motocin can abun alajabi, bawan Allah lalle Allah nasonka daya barka da rai har zuwa yanzu domin acikin motocin bawanda ya fita duk sun kone “
khalil ya dago arazane, mutumen yace “eh duk sun mutu kaima ina mamakin ganin ka anan tunda yayi nisa da inda hadarin yafaru “
khalil yace “jinake kamar nayi bacci na farka amma nasan bakomi ne yasa Allah yatsareni ba se don yawan ambatonshi da nake kuma nakasance me kiyaye dokokinshi “
Musa yace “hakika wannan ba abun mamaki bane don ikon Allah yawuce mamaki azamanin manzon Allah (S. A. W) wata unguwa takama da wuta duk gidajen suka kone daakazo akafada ma sahabin daya daga cikin mutanen unguwar se ya karyata yace wlh banda gidana saboda bana fitowa gida harse nayi adduar da manzo ya koyar damu (fans namanta adduar) kuma ana zuwa akaga gidanshi lpya lau amma duk nakusa dashi akone,”
Ya cigaba da cewa” nan kusa akwai wani abokin mahaifina shide yakasance kullum baya manta karanta ayoyin karshen suratul tauba, lakadjaakum sau 7 koda yana tafiya yakan karanta ta koda besamu yin kowane azkhar ba yanayin wannan, se wani amininshi ya kawo mashi ziyara daga sudan shikuma abokin mahaifin nawa yana zaune a kaduna, bayan ya kwana se suka shirya suka nufi abuja don ziyarar abukkansu, tareda driver suke amma se abokin mahaifina yaamshi driving, kasancewar beiya dogon driving yake fara bacci suna cikin tafiya yafara gyangyadi dole yadawo gidan baya ya kwanta amininshi da driver suna gaba, baadade ba bacci ya daukeshi,yana bacci sukai accident koda yafarka sede yaganshi yashe a gefen titi mutane suna zagaye dashi bako kwarzane jikinshi, seyafada musu suna tare da yanuwanshi a mota, daaka bi daji ashe motar yankar daji tai taita tafiya tayi raga raga driver ya mutu yana ciki yayi jina jina, hankalinshi yatashi aka dukufa neman amininshi baagano amininshi ba se da akai tafiyar kilometers 25 sannan akaganshi kwance a mace cikin kungurmin daji, ya kidima sosai abun yabawa mutane mamaki, a kd akai janaizar amininshi da driver ana zaman gaisuwa wanda ina daga cikin wadanda ke gun anata jajanta lamarin sewani malami yake tambayar shi wace addua yayi ayau seyace “wlh ban karanta komi ba se lakadjaakum kafa 7 wanda kuma a riyadul janna nasamu falalarta hadisin da yakawota a rauda ta 18 ankarbo hadisin ne daga Muhammad bn abubakar cewa wanda ya lazimci karanta lakadjaakum ila akirul sura lam ya mut hadman wala garqan wala harkan wala darban hadid,shine na lazimceta kowane lokaci “
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
,malamin yace”hakika karshen suratul tauba kariya ce daga dukkan abun ki, nima zankara dukufa wurin yinta “
Musa ya cigaba dacewa daganan sena rike ta inayi danaji falalarta ,ban wata biyu da riketa ba zanje Lagos motar mu ta kife karamar macapolo ce amma bawanda ya fita seni nima cikin jini nake domin naji ciwo sosai “ya bude kafarshi zuwa bakin gwiwa wani katon tabo ya bayyana harda rami ajiki yace “kaga tabon da yakasa bacewa daga cikin tabunnan danayi a kalla anyi shekara biyar amma har yanzu be cike ba sede ina tafiya da kafata lpy lau duk dan temakon Allah “(it’s true life story ya faru dagaske)
khalil yace”ina yawan karantata domin tana daga cikin jerin azkhar dake cikin littafi na sede bansan falalarta ba, hakika nagode ma Allah daya kareni domin koda mutuwa hutuce aguna zanso nakara rayuwa dan nakara aikata aikin alheri ,inada mahaifiya ita kadai ta ragemin inason na rayu har zuwa tsufanta zuwa lokacin da zata kasa yiwa kanta komi yazama nine me mata hidima don samun rahmar ubangiji da albarkarta dafatan Allah yabani wanda zemin haka nima”
musa yace “Allah ya yarda wane gari kake zan temaka maka nakaika duk da dare yayi “
khalil yace “cikin katsina nake idan har zaka temaka mun ba gida nakeso kakaini ba, don ina samun matsala da matata da mahaifiyata nasan in sukaji labarin mutuwa ta zasu saduda mahaifiyata zata sauko domin tana sona sonda takemin ne yayi yawa haryake kawo mana matsala take kishi da matata kamar kishiyarta, inso samu ne zanso na zama bakonka nawani lokaci sannan zan koma garinmu “
Musa yace “ba matsala nima zanso nasamu ladar bakuntarka, na tausaya maka Allah ya ganar da mahaifiyarka”
Khalil yace “amin nagode Allah ya baka ladar “
musa yace”amin ni sunana musa ina zaune babbar riga da matata da yara na uku “
khalil yace “ni sunana khalil ina zaune a layout matata yarinya ce aurenmu beyi shekara ba”
musa yace “masha Allah Allah yabada zuria dayyiba zamu iya tafiya “
khalil yatashi suka nufi motar musa suka shiga suka kama hanyar babbar ruga batareda kowa yasan khalil na raye ba.
ya Allah kajikan musulmai maza da mata ka musu rahma ????????
*zakuji inata yiwa mamatanmu addua wata falala naji daga bakin sheikh daurawa cewa duk wanda ya nemawa muminai gafara zaarubuta masa lada adadin musulman da suka mutun , dukda de inayi akowace sallata domin nikan tuno da yanuwana da abokaina da suka rasu, to jiya kuma hatsarin nan yakara tadamin hankali har natuno garabasar nan shine nace bari nafada maku nasan akwai wadanda basu sani ba se sufarayi, Allah kakaramana ilimi*
[8/21, 5:33 PM] SHALELE????: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍????✍???? *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍????✍????✍????
We are bearer’s of so golden a pen????
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen????
Be hold our words
A product of our pen????
Savour our words
For it will cause you no pain.✍????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣3⃣
*shafin nakine AISHA ALTO writer of SANA’ACE,da begenki arai na nayi typing inafatan zakiji dadin page dinnan nakine ke kadai uwargidan fahad????*
Har suka isa babbar ruga bawanda yace uffan dukkansu suna tunani daban, a kofar wani karamin gida suka tsaya duk suka fito waje, musa ya kalli khalil yace “nan shine gida na,muna zaune ne tareda mahaifiya ta “
Khalil yayi shiru yana tsaye musa ya shiga gida ba dadewa ya fito bakin gidan akwai kofar wani daki yasa key ya bude dakin yashiga few minutes yafito yacewa khalil “bismillah”
Khalil ya karasa ciki dakine karami da toilet aciki bakomai ciki se katifa da praying mat musa yace “nan shine masaukinka duk abinda kake bukata kamin magana “
Khalil yace “nagode sosai Allah yabaka ladar”
Musa yace “amin “ya juya ya fita,
Da fitarshi khalil yashiga toilet yayo alwala ya dawo ya shimfida carpet ya tada sallar laasar da Maghreb ,yana sallar yana hawaye yana tuno mutanen da suke tare a mota dukda shi yana gaba amma a bayanshi yanajin wata mata na waya tanafadin Sun kusa karasowa abata minty 10 kawai, da danta ahannu yanata kuka,sanda yagama sallar addua yayi ta masu akan Allah yajikansu ya musu rahma ,
Aisha ta dawo da drinks a leda tazauna tabude kwalin happy hour tadansha ta aje sauran, har lokacin amira tana ta kiran anty,
Mommy ta kalli Aisha tace “wai ina antin tata ita bazata zo dubata bane? “
Aisha ta yamutsa fuska tace “itama bata lpy tananan asibitin akwance “
Mommy tace “mtswww meyasa meta ne ita kuma? “
Aisha tace “I don’t know me tamishi yayita jibgar ta ina shiga dakin na ganta cikin jini inaga tayi miscarriage abinda ya tsorata amira kenan har ta suma “
Mommy tace “amma naji dadi shegiya Allah yakara
Aisha ta girgiza kai ta nunamata amira da ido, mommy tai shiru,
amira tace “nide kukaini wurin anty inason naganta “
mommy tace “to zan kaiki wurinta kisha tea nikuma sena kaiki “ta dorawa amira cup,
Amira ta dan sha ta janye fuska,
mommy ta kalli Aisha tace “bari naje naga likitan inda yiwuwa se mukoma gida seya cigaba da zuwa yana dubata acan kamin ta warware “
Aisha tace “to “
Mommy ta dauki amira suka tafi office din doctor, ta zauna ta mishi magana yace ba matsala zasuiya tafiya mommy tai payment suka koma dakin, Aisha ta tashi suka shiga mota suka nufi gidan mommy,
Kafin su isa amira tai bacci suna zuwa mommy ta kwantar daita Aisha kuma tashiga toilet ta watsa ruwa,
Hawaye faseelat taketa yi don ma batada karfin yin kuka ,
ummi tagaji tace “shin ce miki akai ya mutu komi?”
faseelat tace “toyana ina?”
ummi tace “yananan zuwa ki kwantar da hankalinki “
Sannan tai shiru tana ta son taganshi don tsoro take karde sakinta yayi ,
Suna haka omer yashigo dakin faseelat tai sauri ta kulle ido, badan yadena jin takaici ba yace “faseelat ya jikinki? “
tai shiru saboda kunya dama he warned her amma bataji ba ga abinda yake gujewar yazo yana faruwa,haka akai ga auren khalil bata dauki shawararshi ba abinda yazatan kuma shi yafaru,
Ummi tace mishi “jiki kam aiba sauki kana ganin yadda take a kumbure, sonake jinin nan yakare in kamata in dan gasa mata jikin kotaji dama “
Omer yace “Allah ya sawwake “
Gidan sabeer fahad ya nufa yana parking yafito ya nufi gun sabeer dake waya da fatouma, sabeer naganinshi yace wa fatouma “pretty ga kanenki nan yazo bari nayi attending dinshi I will call you back”
yakashe kiran ya kalli fahad da yazauna a seat ya dafe kai ,sabeer yace “lpy de fahad naganka haka Very tensed? “
Fahad ya dago fuskarshi da tayi jawur yace “ina cikin tashin hankali sabeer kabani shawara plss “
sabeer yace “inajinka”
Fahad ya furzar da iska shikanshi haushin kanshi yakeji yace “something bad happened, kishi ya rufemin ido na doki faseelat hartayi miscarriage after I took her to hospital…”
sabeer yakatse shi yana fada “kana cikin hankalin ka kuwa? wane irin kishi ne da zesa ka bugi matarka har tayi bari? haba dude sekace baka waye ba ga hanyoyi nan birjik da zakai punishing nata seka tsaya ga duka saboda kajawa kanka raini agunta da iyayenta?”
Fahad ya dagamai hannu yace “please karka ce zakamin fada banzo wurinka don ka karamin tension ba nazo ne kafadamin mafita,in kuma fada zakamin sena tashi nai tafiya ta kobari bakai ba nakai numfashina ba “
sabeer yaja tsoki yace “badole nai masifa ba karika abu like mad person yanzu inajinka “
Shima fahad yaja tsokin bacin yana neman mafita da tafiyarshi zeyi, ya cigaba da cewa “after na kaita asibity nafita in duba princess dabata lpy se dawowa nai na tarar batanan yanuwanta sun dauketa naje gidansu many times a kulle “
sabeer yace”wow sunyi dede dasuka dauke diyarsu, kai kana tunanin kamar Aisha ce da kake jibga son rai dan tana kanwar ka? to yanzu de kaga da banbanci, seka jira hukuncin da zasu yanke “
fahad da tundazu yake kallon sabeer kamar ya kaimishi naushi, ya hadiye miyon bakin ciki yace “u r very stupid da kake tunanin ina hada Aisha da faseelat kowace da matsayinta in Kana bani shawara kabani in bazaka bayarba senai tafiya ta “
Sabeer ya janye hannunshi da yadora kan fuska yarage murya yace “gaskiya baka kyauta ba duk son da yarinyar nan ta nuna maka amma har kaiya mata haka “
fahad yace “I known, ya zanyi yanzu they took her bansan ina suka kaita ba nikuma inason ganinta inason sanin halin da take ciki “
Sabeer yace “dole kayi hakuri kaita zuwa har kasamu ganin mahaifinta kabashi hakuri sosai kila su hakura , don inajin tsoron kar su rabaku, saboda diyarsu tana da komai dahar wanda yafika zata iya aura “
Fahad ya dafe goshi yace “bazan iya rayuwa babu ita ba, she’s my life, I’m regretting bazan iya bacci ba batare da nasan halinda take ciki ba ,ina son sanin halin da take ciki “se hawaye sharr sharrr
sabeer ya dafashi yace “kayi hakuri kabi komai asannu faseelat takace,ka kwantar da hankalinka kacigaba da zuwa gidannasu har kasamu ganin abban nasu sede sekayi hakuri bazan boyemaka ba duk mutuncin da suke ganinka dashi yanzu babushi “
fahad yayi shiru yana tunanin yadda ze tunkari abban nasu,
sabeer yace “amma dan Allah ka rika kiyayewa,karage kishinnan karika hadiye shi don gudun nadama “
Fahad ya share hawayenshi yace “thank you, nagode “ya tashi ya shiga motarshi yabar gidan,
Sabeer yabi bayanshi da kallo ya girgiza kai,
har bayan isha seda fahad yaje gidan har lokacin yana rufe, yajuya yanufi asibity yanaganin basanan yayi tunanin an sallame su ya nufi gida,
faseelat na nan tazuba ido jiran hero shiru babushi,hankalinta duk yatashi ,jinin na karewa ummi ta jona heater ta kamata suka shiga toilet, ta temaka mata ta tube se lokacin ummi taga tashin hankali jikinta duk bakin tabo ne ga kumburi da tayi, ummi takara hawa fiyeda baya, ta gasa ta tai mata wanka ta sauya mata kaya sannan takamata suka fito,
faseelat ta kwanta tana meda numfashi, ba dadewa abba yashigo da maltina da madara aka hadamata ,ummi ta tadata tabata don dole tasha sannan ummi ta kwantar daita ,
ummi ta kalli su abul da tundazu suna asibitin kamar masu azumi tace “yakamata ku tafi gida hakanan har tara tawuce”
Suka fita jikinsu a mace, ya omer ma ya masu seda safe yafita,
Ummi ta kalli baaba tace “baaba yakamata kitafi gida kihuta kema “
baaba tace “to Allah yakara lpy bari natafi “
ummi tace “a, a kijira alhaji ya kaiki “
abba yace “to inde ana bukatar wani abu ki kirani”
ummi tace “to insha Allah “
Abba yafita baaba tabi bayanshi yana cikin tafiya baba babba yakira ya dauka bayan sun gaisa,baba babba yace”ya me jikin?”
abba yace “dasauki zaace”
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
baba babba yace “Allah yabata lpy, da Allah ko mijinta yazo karka saurare shi ,ya saketa kawai “
abba yace “to Allah yasa haka shine mafi alheri”
Baba babba yace “amin”sukai sallama,
abba na ajiye baaba ya wuce gida,
fahad na zuwa gida besamu su Aisha ba yajuya ya nufi gidan mommy, yana zuwa ya zauna a kujera ya kwantar da kai jiki kanshi na mugun ciwo,
mommy tafito daga kitchen taganshi tabata rai tazo ta zauna, tace “yanzu fahad rayuwar da kazabar wa kanka kenan? matanka kamedasu kamar jakkai kaita bugunsu kamar dabbobi? “
Fahad hannunshi akanshi yace “mommy it’s a mistake baason raina nayi ba “
mommy tace “idan de zakai hankali kayi idan kana dukan Aisha nayi shiru ita wagga iyayenta ba shiru zasu yi ba “
tatashi zata haye sama murya sanyaye yace “ina Aisha? “
mommy tace “tayi bacci katafi kawai gobe kazo ka dauketa, ita kuma amira anan zata zauna tunda kagama tsorata ta”
Ta juya ta hayewarta,
Fahad ya tashi yabar gidan, yakoma gida ruwa kadai ya iya sha ya shiga dakin faseelat yayi kwance kan bed dinta yanajin kewarta sosai, ya tashi ya bude wardrobe dinta ya dauko sleeping dress dinta ya rungume a kirji yana hawaye,
gidansu umma ma duk basu cikin walwala har 10 tayi umma taji bata iya bacci ta tashi ta nufi dakin lady, Lady na waya da Hussein dasuke matukar son juna yanzu, umma ta shigo lady takashe kiran ta meda hankalinta kan umma,
Murya sanyaye Umma tace”waikinsan gidansu faseelat ne? “
lady tace “eh nasani”
umma taji dadi tace “yawwa kitashi kisa hijab can zamuje yanzu bari naje na dauko mayafi na”
ta juya tabar dakin, Lady ta tashi ta dora after akan kayan baccinta tafito, umma tafadawa daddy suka tafi gidansu faseelat,
suna zuwa sukai parking suka fito suka tsaya bakin kofa sunata knocking, can zuwa abulkhair ya bude gidan unguwar dun dum dan babu nepa, sede hasken farin wata,yagade mata ne yayi tunanin kawayen ummi ne,
abul yace “inawuni “
Umma tace “lpy lau ya me jiki an sallamosu ne”
yace “dasauki suna asibity “
umma tace “wace asibity suke room nawa? “
Yace “turai, aminity ward room 9”
umma tace “to nagode sosai “ta kalli lady tace “mutafi asibitin “
suka juya suka tafi abul yameda gida ya rufe,
akan hanya suka sai kaza me dawafi da drinks suka tafi asibitin,
Bawani wahala suka gane dakin suka tura suka shiga da sallama bakinsu, ummi kadaice ta rage itama tana salla, da lady da umma hankalinsu bakaramin tashi yayi ba ganin halin da faseelat ke ciki,
idon faseelat akulle umma takarasa kan bed din dasauri tana kara ganin barnar da danta yayi,
jin kamshi na daban faseelat ta bude ido taga umma, tafara hawaye,
Umma tace “sannu faseelat Allah yabaki lpy”
Faseelat tariko hannun umma murya shake tace “umma! ya sakeni ko? “
umma tace”me kike cewa ne? Yazaai fahad ya iya sakinki yana sonki sosai baze iya rabuwa dake ba “
Tace “ban ganshi ba har yanzu bezo wurina ba, Dan Allah umma kikiramin shi inason ganinshi “
Umma tace “ki kwantar da hankalinki yananan zezo “tasa hannu tana share mata hawaye,
ummi da tundazu ta sallame tai shiru tana kallon gadon da faseelat ke kwance tanajin takaici kamar me,
lady ta matsa tace “sannu anty “
faseelat ta daga mata kai tana cigaba da hawaye,
ummi ta tashi tana linke carpet tace “sannunku da zuwa “
umma ta juya wurinta tace “ina wuni yame jiki Allah yabata lpy”
ummi tace “amin “
Itama lady ta gaida ummi, shiru dakin nawani lokaci sannan umma tace “Dan Allah ummi kuyi hakuri akan abinda fahad yayi baa cikin hayyacin shi yayi haka ba, shi kanshi yana cikin tashin hankali don koda yazomun da labarin kuka yakeyi ,nasan yanacan cikin tashin hankali, kuyi hakuri Dan Allah wlh ni kaina abun yabatamin rai sosai don faseelat kamar diyata na dauketa, yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba”
ummi tace “ihhhm bakomi”
umma tace “kuma wlh naji dadi sosai da kuka dauketa, sede ina rokon da kuyi hakuri kubarmishi ita karku rabasu, don ita haske ce arayuwar dana, tana duk wani kokari na gyara mishi rayuwarshi badan ita ba da yanzu bama tare dashi, ina rokon da kuyi hakuri akan abinda yafaru kubarmishi ita Dan Allah “tahade hannayenta biyu,
umma ta bawa ummi tausayi tace ” da nasa araina dole ya saketa saboda wannan abunda yayi kuma ba yaune yafara dukanta ba, amma na hakura saboda ke kuma zanyi iya kokarina naganin takoma dakinta, sede bazan bashi ita hakanan ba se yagane kuskurenshi “
Umma tace “nagode sosai ummi kuma naji dadin hakan don ko dauketan da kukayi yau kadai ma ya razana shi na tabbata wannan zesa yagane kuskurenshi nagode da kika min wannan alfarmar “
ummi tace “bakomi “
su faseelat najin abinda suke fada sede ita abun be mata dadi ba ashe dauketa sukayi, yanzu se yaushe zata ganshi? jin datayi umma tace yana ta kuka yasa taji tausayin shi ta riga tasan fahad na sonta sosai wannan dukan da yamata Har cikinta yafita kokadan besa ta rage digon son da takema shi ba,
Faseelat tace “umma dan Allah kikiraminshi inason ganinshi “
umma tace “kiyi hakuri kinji ,kibarshi yakara gane kuranshi, hakan zesa kobaya cikin hankalinshi baze iya dukanki ba, kuma ze kara sanin darajarki “
faseelat tai shiru,
ganin har 11:30 yasa umma tacewa ummi zasu tafi ta fiddo kudi boundles na 1k ta aje musu,
Ta shafi fuskar faseelat tace “kiyi hakuri kinji yata gobe inanan zuwa me kkso nazo miki dashi? “
faseelat ta girgizakai,
umma tace “kifada min me kkson ci ni da kaina zan girka miki “
Faseelat ta yamutsa fuska ahankali tace “komai inaso “
umma tai murmushi tace “to ki kwantar da hankalinki kiyi bacci “
taiwa ummmi bankwana ummi nata godiya suka fita daga dakin,
ummi ta kalli faseelat tace “shasha ashe duk sunsan kin mutu sonshi,mutum ya nakada maki duka amma kinata nemanshi har uwarshi taji haushi amma ke ko ajikinki marar zuciya”
faseelat ta juyar da fuskarta ummi tace “Allah yakawomaki sauki”
khalil ko abinci kala kala aka kawomishi wanda sede ya tsakura yabarsu saboda bejin dadin komi hankalinshi kuma yakoma ga hjya yasan iyanzu tana cikin tashin hankali, musa yazo sukai ta fira sama sama se 9 sannan ya shiga gida,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
suma su hjy sunanan har 10 ganin ba yau zaa sallamesu ba yasa mamar jamila tace wa su hjya sutafi gida, hjya tace ita zaabari akai akai tatafi taki dole suka hakura suka tafi sukabarta rungume da lil khalil ,
da khalil da fahad da hjya da jamila, duk bawanda ya rumtsa,
Baccin asuba ne ya dauke fahad sede bewani dade ba yafarka ,
karfe 7 aka sallami su hjy suka dawo gida,
Karfe takwas fahad ya fita daga gida wanka kadai yayi ya sauya kaya ya nufi gidan su faseelat sede ya makara don har sunbar gidan yana kulle kamar jiya, ya bata fuska yanajin kamar yayi kuka ya cize lips ya juya ya tafi gidan umma,
umma na kitchen don sotake karfe tara tabar gidan,
ya shiga yayi kwance kan kujera don gabadaya bejin dadin jikinshi,
umma tagama komi ta fito da niyyar hawa sama tai wanka ta ganshi kwance hannunshi saman kai,
ta dawo tai tsaye kanshi tace “lpy me kazo yimin nan? “
fahad ya tashi zaune kanshi na sara mishi kamar ze kuka yace “Dan Allah umma kiyi hakuri wlh nayi nadamar abinda na aikata,”
umma tace “to ni aiba fushi nai ba, don kai kaiwa kanka ,don haka katashi katafi wadanda kawa laifi yakamata kabawa hakuri bani ba”
yace “umma nayi zarya gidansu akulle narasa yadda zanyi “
Ta tabe baki tace “to dama ya zaai ka iskesu tunda kaja musu jinya hakuri zakai har tasamu lpy insun barmaka ita to ,katashi katafi fita zanyi akwai inda nikeson zuwa “ta tafi tabarshi dafe da kai fahad ya rasa yadda zeyi kwana guda jinshi yayi kamar shekara,
umma nagama shiryawa ta sa me aikinta ta kaimata girkin da tayi da lemun da tahada a mota sannan tafita ta nufi asibitin,
abul da omer basunan suna school ,dakin daga ummi se Mubarak da ishak,
umma ta shiga tana ta faraa lokacin har ummi takama faseelat tayi wanka ta sauya mata kaya,
Bayan ta zauna suka gaisa ,
umma taiwa faseelat ya jiki sannan ta tambaya kotaci abinci, ummi tafada mata bata ciba, ta zuba farfesun kayan ciki da tayomata ta tada ta zaune tasa hannu ta rika bata abaki,
agidan hjy kau anata zaman gaisuwa dan ta tabbatar khalil ya mutu don beje batsari ba kuma baya kt hakan ya tabbatar da ya mutu tunda safe su kawu manu sunje inda akai accident din sunga yadda motocin sukai hakan yasa sukadawo suka zauna ansar gaisuwa,
mata anata zuwa yiwa hjya gaisuwa da barka lokaci daya,
Anata kiran fahad da wayoyin Suka isheshi da kara seya kashesu gabadaya donshi bata wani aiki yake yanzu ba,
yana zuwa gidan mommy ya tarar da Aisha main palo tana zaune tana kallo ga amira da tai kukan anty har tagaji kwance kan cinyarta,
amira na ganinshi ta tashi ta haye sama da gudu,
Aisha tabishi da kallo duk ya fita hayacinshi,
Fahad ya zauna gefen Aisha ya kwantar da kanshi akan cinyarta yasaki kuka me taba zuciya,
Aisha ta rungumo kanshi tana share mishi hawaye idonta tafff da kwalla tace “kayi hakuri yaya kadena kuka “duk atunaninta gudunshi da amira keyi yakewa kuka,
Yana kuka yace “meyasa zasumin haka? meyasa zasu dauketa daga gareni ina tsananin sonta bazan iya jure rashinta akusa gare niba “
Aisha ta tsaya da share mai hawayen tace “…..
[8/22, 2:56 PM] SHALELE????: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍????✍???? *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍????✍????✍????
We are bearer’s of so golden a pen????
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen????
Be hold our words
A product of our pen????
Savour our words
For it will cause you no pain.✍????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣4⃣
*ban manta daku ba,kuna raina,lady ,maman zainab, Aisha habib, Firdausi,sede kundena comments why?*????
*soupnas* comment dinki nasani farin ciki keda *maman nour* comments dinku yana kayatarwa kucigaba da gashi ????????, *maman nour* wai ina kawalliyarki *earmeenatuwa*????
Aisha tace “bangane ba yaya? “
Yana cigaba da kuka yace “iyayen faseelat Sun daukemun ita sun tafi daita”
Aisha farin ciki ya mamaye zuciyarta batasan lokacin da tasaki murmushi ba tace “Allah yasa daga can ai can”
Jin abinda tace Fahad ya tashi zaune yana mata kallon mamaki yace “me kk cewa ne Aisha? kina farin ciki da abinda yafaru ko? “
Aisha ta zumburo baki tace “to da so kake nace Allah yasa su medo maka ita? Saboda ita kamanta duk wata soyayyata idonka ya rufe akanta se kuma nakijin dadin tafiyarta, wlh naji dadi Allah yasa susa dole ka saketa ,hakanan batasan ya zaman mu yake ba tayi duk yadda tayi taja hankalinka har ka aurota ni ba abinda zance sede nace Allah yaraka taki gona “
Ranshi ya baci sosai da dane da seya mazge bakin amma ya dau alwashin barin dukan matanshi ya ciza lips yace “toko Allah baze amshi adduar ki ba saboda bame kyau bace, faseelat tananan dawowa gareni nida ita mutu karaba, don we love each other insha Allah we will die together”
Aisha dake jin haushin maganar shi kamar me ta turo baki gaba ,
Yaja tsoki yace “stupid bansan time din da zaki dena kishin hauka akan faseelat ba, ita kullum tana girmamaki tana sonki ke kuma ba wacce kika tsana kamarta”
ya tashi tsaye ze fita Aisha tace “bazaka jira ni mutafi tare ba? “
Beko waigo ba yace “batare mukazo ba kinsan hanyar gidan inkinso zuwa “
Yajuya ya bar gidan,
Aisha taja tsoki tace “so yake nayi addua sumedota kome?wlh yaya ya raina ni da yawa wai yagama cemin yanason ta har kuma yayi tunanin zanyi wata kyakkyawar addua can”
Mommy da tundazu tana kan dining tana jinsu tafito da cup ahannu tana kyalkyata dariya,
Tace “ke kuma dan ubanki waya ce kice mishi haka keda yazo ki rarrasheshi “
Aisha tace “mommy ba abin dariya bane wannan yazaai yazo yana fadamin wai he love her inba raini ba”
Mommy tace “to seme dan yace yanason ta tuntuni ina fadamiki kidena fiddo mai kiyyyar ta a fili kirika nuna kinasonta”
Aisha ta mike kafarta akan kujera tace”bazan iyaba niba wacce natsana kamarta Allah nagani da nasota kafin nagane hainta ta take ita ,ni wlh har mamakin zuciya ta nayi duk yadda natsaneta ranar da ya nakada mata duka seda naji tausayinta “
Mommy ta zauna ta kurbi tea tana murmushi tace “kin shirya zaman gida ko? Tunda kinsan ba zuwa zeyi daukar ki ba “
Aisha tace “hmm zezo ai Wadda ake makalewar batanan kinanan zaki ganshi “
mommy tai dariyar manya tace “amma kinyi kuskure karki kara irin wannan “
Aisha tace “to”
Fahad gida yakoma yayi kwance zuciyar shi na kuna yarasa ina zesa kanshi ba arziki da yunwa ta cishi ya tashi ya hada tea yasha,
akai akai yakan leka unguwarsu faseelat amma gida kulle, har dare yagaji yakoma gida,
Aisha taci wanka tana jiran yazo daukarta har 9:30 shiru bezo ba ta tashi ta dauko gyale mommy ta kalleta tace “ina zaki? Bakince ze dawo ba kijira shi “
Aisha ta yafa gyale akafada tace “mommy baze zo ba tunda har aka kai wannan time din bezo ba tafiya zanyi maybe yanacan ko abinci beci ba “
mommy tace “aiko baki isa ba ki samu wuri ki zauna, har se randa yaga dama yazo da kanshi daukarki “
Aisha ta turo baki gaba tace “Dan Allah mommy kibarni in tafi wlh hankalina duk baa kwance yake ba, yaya yana bukata ta yanzu “
mommy tace “yanzu kikasan haka ai, kicire gyalen nan “
Aisha ta turo baki ta tafita daga dakin mommy nata kiranta taki amsawa, daga karshe mommy tace “zakizo kisameni ne “
Aisha ta fita tasamu napep ta haye yakaita bakin gidansu, ta kwanwasa baba tsoho ya bude ta shiga ciki,
Ta kitchen tabiyo ta shigo gidan, fahad na kwance akan gadon faseelat rungume da kayanta ta shigo dakin,
Dukda yaji kamshinta amma be nuna ba, tana sanye da riga da wando na Sari ta haye gadon idanunshi a lumshe ta riko hannunshi tana cewa “yaya kaci abinci kau? “
yayi banza ya kyaleta tace “yaya kayi hakuri da abunda yafaru plsss katashi kaci abinci kar ciwo yakama munkai”
Fahad ya bude ido yana kallonta ,ta langabe kai tace “plsss katashi kaci abinci? “
ya yamutsa fuska yace “Aisha plss leave me alone ba ruwanki da naci abinci ko banci ba just go to ur room “
kamar zatai kuka tace “yaya da ruwana mana yanzu in wani abu yasameka fa?bansan ganinka cikin wannan halin na damuwa kayi hakuri katashi kaci wani abu “
Yace “bazan ci ba ko dole ne, kitashi kibani wuri, damuwa kuma zan cigaba da zama acikinta har lokacin da farin cikin rayuwata zata dawo gareni “
Aisha ta tashi tafita daga dakin tana kuka, fahad yaja tsoki yace “u don’t love me da kina sona da kinso faseelat”
Aisha tafada kan bed ta cigaba da rusar kuka, ita ba maganganun nashi ba suka fi kona mata rai aa yadda yabi ya rude harda sukin cin abinci saboda mace, ta sha kuka har tagaji, har 2 takasa yin bacci shima ba baccin yake ba idonshi biyu,
Kanta na ciwo Ta tashi ta shiga kitchen ta hado mishi tea me kauri ta dawo dakinshi, yana kwance yanata kallon silin tazo ta zauna akan gadon murya dishe tace “Dan Allah yaya katashi kasha ko da tea ne ba don ni ba “
yayi mata banza tai ta magiya hardasu kuka sannan ya tashi zaune ko kallon fuskarta be ba ya mika hannu ze amshi cup din, taki bashi ta kai cup din bakinshi seda yashanye shi tasss sanan ta dauke cup din,
Tai murmushi ta share hawayenta tace “nagode da ka daure kasha “ta ajiye cup din a bedside table ta tashi zata bar dakin ya riko hannunta yace “anan zamu kwana”
Ta dawo ta kwanta gefenshi ta rungumeshi ba dadewa bacci ya dauketa,shiko yakasa koda rumtsawa sema kukan faseelat da yayita masa yawo akunne kamar lokacin yake dukanta duk da AC dake dakin yayita zufa,
Da safe,
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
tun 7 ya isa kofar gidansu faseelat lokacin har abba yafita yana tsaye bakin kofa omer yafito cikin shirin shi ze tafi school, fahad ya mika mai hannu ya mishi sallama fuska murtuke omer ya mika mai hannu ya amsa gaisuwar, ya zare hannunshi tun kafin fahad yace komi omer yawuce ya shiga mota yayi tafiyarshi,
fahad yayi tsaye zuciyarshi na kara zafi,can sega abul yafito shima ze tafi school ko kallon fahad beba yawuce warshi, sega su ishak da Mubarak sunfito suma zasu tafi school kasancewar yau Monday abun yabashi mamaki suma basuko kalleshiba ishak ya garkame gida suka juya suka tafi abun su,
dana sani yakara cika zuciyar fahad yara kananu ma Sun dena ganin girmanshi ,ya dade tsaye sannan ya shiga mota ya nufi gida time to time seya share hawaye bakin ciki da suke fitowa ta gefen idonshi,
Ya koma gida yayi kwance, Aisha tayi rarrashin yakasa koda shan ruwa ne har tagaji se yanzu takara gane faseelat ta mata nisa azuciyar fahad gatade zaune dashi amma zuciyarshi tana wurin faseelat seta karajin tsanar ta aranta ,damuwar shi yasa itama tashiga damuwa, yakasa komi se aikin tunani, itama faseelat na can tana fama da ciwo da damuwa amira ma nacan tana kukan anty, fahad akewa punishment amma su duka suke azabtuwa, har Aisha taji gwara faseelat din ta dawo kota samu fahad dinta yasamu natsuwa,
Wansafe tunda asuba fahad yafita da mota a masallacin unguwarsu faseelat yayi salla ana sallamewa yafito yakoma bakin kofar gidansu ya tsaya yasan de dole abba yafita sallar asuba, yana nan tsaye yara yaran sukai tawuceshi suna shiga gida, can zuwa sega yaya omer yana zuwa ya daga mishi hannu yace “assalamu alaikum” yawuce abunshi, fahad bewani damu sosai ba shide burinshi yaga abba, yana tsaye sega abba yazo ze wuce yashiga gida, yayi sauri ya duka yafara gaishe shi memakon ya amsa seya mika masa hannu suka gaisa fahad na zukunne be tashi ba,cikin ladabi yace “abba Dan Allah ina neman yafiyarku kuyi hakuri akan abinda na aikata, nasan ban kyauta ba kuma nayi nadama Dan Allah kuyi hakuri “
abba yace “banji dadi ba yadda ka wulakanta min diya raina ya baci amma ni na yafe maka sede ina bukatar ka rubuta mata takardarta saboda zamanku atare akwai cutarwa “
Fahad da kanshi ke Duke ya dago arazane besan lokacin da ya mike tsaye ba, sannan yakoma kasan yana magiya “Dan Allah abba kuyi hakuri inason ta sosai bazan iya rayuwa batare daita ba, wlh nayi alkawari bazan kara dukanta ba Dan Allah kuyi hakuri wlh itace rayuwa ta zan kiyaye duk wani abunda ze bata mata rai koya taba lpyarta”
Jin abinda yake cewa cikin ran abba yace “nan wurin ba lpy “????
Yace “nide nafada maka Dan Allah kakawomin takardanta in kuma bahaka ba zamu shiga kotu “yana gama fadar haka ya shige gida,
fahad yaida yin zaman dirshan awurin yana hawaye da kukan zuci seda gari yayi fayau sanann yatashi ya nufi gidan umma,
umma ko kullum setaje asibity suna zaune a dining sun hallara don yin breakfast yashigo gidan duk sukabishi da kallo umma ko kallonshi batai ba bare ma yabata tausayi,
yazo yaja kujera ta kusa da daddy ya zauna murya na rawa yabawa daddy labarin abinda abban faseelat yace,
yace “Dan Allah daddy kaje kabashi hakuri wlh nayi nadamar dukanta tun daga lokacin da abun yafaru “
umma tai karaf tace “alhaji dan Allah ka kyaleshi karka shiga wannan maganar kaje kaji kunya kaima kasan sunada gaskiya gwara ya saketan yafi tunda beda hali “
Fahad idonshi cike da hawaye yake kallonta,
daddy yace “a, a bahaka yakamata ba, zanje nasamu abban nasu in roki yafiyarsu, ka kwantar da hankalinka kaji “
fahad de bece komi ba ya tashi yafita tun kafin yakai gida zazzabi ya rufeshi yana zuwa ya shiga wurin Aisha ya kwanta ya kudundune jikinshi na mazari, Aisha ta rude tai ta kuka ta kira doctor ba dadewa okaton yazo ya dubashi jinin shi yahau yabashi drugs da shawarwari ya fita, dakyar Aisha tasamu yasha maganin da aka rubuta mishi badadewa bacci ya dauke shi dan cikin magungunan akwai na bacci acikinsu kwananshi ukku ba bacci saboda rashin faseelat, Aisha na zaune gefenshi tai tagumi tana kallon fuskarshi duk yabi ya rame har baki ma yayi ba wata kwanciyar hankali duk harijan cin nan ya tafi ????yau kwana ukku ba tabi ????,
awurin aikinshi anyi neman wayoyinshi amma switch off ba karamar asara suke yiba mutane sunyi zarya gidanshi sede baba tsoho yace bayanan, don fahad yabashi umarnin fadin hakan,
Yau akayi sadakar ukkun khalil su hjya suna cikin tashin hankali har yau, jamila duk tabi ta zube ta rame duk kibarnan ta tafi hartafi lokacin da take budurwa rama, hjy ma ta kanjame don bata bacci rashin ganin gawar nema yakara tada mata hankali, zakuyi mamaki innacemaku hjy ce kebawa jamila abinci abaki don mugun tausayinta takeji tana ganin kamar itace takashe mata miji, kullum lil khalil yana hannunta ,
bayan yan gaisuwa Sun wuce da marece sosai mamar jamila sun hadu falon hjy tafadawa hjy yau zasu koma gida kuma tareda jamila zasu tafi,
Hjya tafashe da kuka tace”dan Allah zulai kubarmin yarinyar nan awurina wlh yanzu ba abunda nake kallo naji dadi se ita da danta, ina rokon kubarmin ita tazauna anan nawani lokaci ,zuwa lokacin da zansamu natsuwa nida kaina zan medo muku ita na rokeku “
Maman jamila tace “hjy zamu tafi daita ne don amata wanka, kuma anan zata karamiki damuwa tunda har yanzu taki dena kuka ga danta dabata damu dashiba,dawainiya zata miki yawa ki kula daita ki kula da danta, gwara mutafi daita can “
hjy tace “wlh bata karamun damuwa, wanka kuma zansamu unguwar zoman da zata mata wanka, kula daita da danta bawani abu bane wurina, nide ina rokonku wannan alfarmar”
dakin yayi shiru na wani lokaci jamila na kuryan hjy kan dadduma tanajin komai hawaye suka kara zubomata wai hjy ce kuka tana rokon abar mata ita inama ace lokacin da khalil yana raye ta nuna mata wannan soyayyar ba yanzu ba,
Baban jamila yace “toshikenan hjy ga jamila nan zata cigaba da zama anan kamar yadda kika bukata, Allah yakara mamu hakurin rashin khalil “
Maman jamila tai shiru dan taso tatafi da yarta takula daita sosai ,
hjy tafara godiya “nagode sosai Allah yabar zumunci”
sukace “amin “
Maman jamila ta tashi tashiga ciki tasamu jamila dake zaune ta zauna tace “jamila zaki zauna nan din? “
jamila ta daga kai tana matse baki,itakanta jamilar tausayin hjy takeji saboda Halinda tashiga, lalle mutuwa waazi ce gasu ba sulhu sun dedeta,
maman jamila tace “to amma ki kula da kanki sosai don dinkin jikinki ya warke kuma ki daure kiyi hakuri jamila khalil de yatafi baze dawo ba addua kawai zaki rika masa “
jamila tace “to mama”
maman jamila ta tashi tafita hjya nata godiya suka tafi garinsu,
Unguwar zomar dake dora musu ruwa itace ta cigaba da yiwa jamila wanka kuma tana bakin kokarinta,
Khalil ko yanacan yana daukar darasi musa ya girme shi dan yayi 45 amma yanayin yadda yake tafiyar da rayuwa ya burge khalil, yana aiki ne a babbar ruga shima likitan fata ne, bayada wani hali sosai amma kullum dasafe se anfita da Kula da bokitai na kunu wanda ake kaiwa asibity ana rabawa patients marassashi, da yadawo daga asibity yake sauya kaya bayasa kananan kaya, kuma kayansa duk ba tazarce suna da dan shape Iya gwiwa yaiya dressing sosai anan khalil yakara daukar cause din saka hula ashe ba bakin ido ake kaita ba ????tsakiyar goshi ake dedeta ta,
Shima musa ya karu da khalil dan yalura khalil kosu na magana yana dannar counter dinshi in suka tsagaita wani lokaci yana ganin bakinshi na motsi ,shima yanzu ya dage rikon counter yana tasbihi kuma yakara kula da mahifiyarshi akan baya don yayi mamakin dukda khalil bejin dadin mahaifiyarsa amma burinshi ya rayu dan ya kara kyautata mata bare shi tashi da yakejin dadinta ,
da drugs suka saki fahad ya farka tsakar dare dakyar Aisha tasamu yasha tea tayi iyayinta yakara shan magani yaki wai beso yayi bacci ,idanshi biyu har asuba yakara komawa gun abba,
abba beji wani tausayin shi ba yakara memeta mishi abinda yafada jiya don umarnin alhaji babba ne kuma shi bemasan su ummi sunyi wata magana da mahaifiyar fahad ba yade san tana zuwa amma besan komi daganan ba,
fahad ya koma gida ya dukunkune dan zazzabin da yakara rufeshi fiyeda jiya,
sabeer ya kira wayar fahad many times besameshi ba, tun karfe 7 yayi parking kofar gidanshi yafara knocking gate, baba tsoho ya bude mishi yaganshi tsaye baba tsoho da yasaba ganin shi yana faraa yace “barka da zuwa alhaji “
Sabeer yace “ina kwana baba, mutumen yana ciki kau? “
baba tsoho yace “eh yana ciki sede yace duk wanda yazo ace bayanan”
Sabeer ya girgiza kai yace “OK Allah yasa lpy nizanshiga naganshi”
baba tsoho yace “afito lpy “
sabeer yawuce ciki yatsaya bakin kofa ya danna door bell shiru yadade tsaye yanata dannawa sannan Aisha taji tazo tabude mishi,
idanunta jawur dan tana shan kuka akai akai ta yadda fahad be damu daita ba, ga kuma damuwa da halin da yake ciki “tana ganin sabeer taji dadi ,
sabeer ya kalleta tayi wani kala abun tausayi yace “Aisha lpy kuke “?
Aisha tace “sabeer yaya yadena kula dani baya bacci baya cin abinci baya zuwa aiki baya komi se tunanin faseelat, tun jiya baya lpy har yau nayi iya kokarina yaki shan magani doctor ma yace jinin shi ya hau sosai, yarage damuwa amma yaki,dan Allah kaje kamishi magana koyaji ya rage yiwa kanshi wannan horon”
ta matukar bashi tausayi yace “kiyi hakuri insha Allah ze dawo dede muje naganshi “
Aisha tawuce tahaye step sabeer na bayanta har cikin dakin faseelat da fahad ke kwance cikin duvet,
Aisha na tsaye sabeer yaje ya zauna kan bedside ya dan yaye duvet zuwa kan fuskar fahad yaganshi duk yayi wani wuriwuri dashi,
be wani mamaki ba don yasan yana matukar son faseelat ,sede yaji haushi yadda ita Aisha ke azabtuwa saboda da damuwarshi
Fahad ya bude ido ya kalli sabeer, sabeer yace”yanzu fahad dan an dauke faseelat shikenan Kagama rayuwa, kazauna kana wahalar da kanka da matarka, ka ki yin aiki kaki zuwa office kasan asarar da akeyi kuwa kuma kasan kamfani baze dauki asara ba “?
Fahad da muryarshi ta Marassa lpy yace “I know and I don’t care ,idan har basu barmin faseelat ba mutuwa zanyi she’s my life bazan iya dena tunaninta ba kona second “
sabeer yadan saci kallon Aisha don shi kanshi yaji haushin maganar yaga tana ta kallon fahad tana hawaye,
Yace ma fahad “to cewa sukai bazasu baka itaba kome? “
fahad yace “naje 2times wurin mahaifinta he’s asking for her divorce later nabashi hakuri amma beyiba “
Sabeer yace “Dan Allah friend karika hakuri da yadda rayuwa tazo maka, yanzu kaga Aisha daita dakai bazaa gane marar lpyar ba, ka daure karika shan magani ko kasamu lpy “
“yanzu ka kwantar da hankalinka kabani address na gidansu zanje nasamu mahaifinta nakara bashi hakuri zan kuma nemi alfarmar yafadamin asibitin da suka kaita, kaje kadubota koka dawo dede “
fahad yafada mishi adress din ,
sabeer yace “zanje nasameshi insha Allah zanyi bakin kokarina wurin shawo kanshi amma katashi kasha magani”
fahad yace “magani baze yimin wani amfani ba faseelat itace maganin rashin lpy ta “
Sabeer ya tabe baki yace “Allah yasawwake to, bari natafi gidan nasu “ya mike tsaye,
fahad ya meda kanshi cikin duvet, da hannu sabeer yayiwa Aisha dake tsaye tana hadiyar zuciya magana akan ta biyoshi, ta bishi suna fita kofar dakin, sabeer ya juyo yace “kiyi hakuri Aisha da yanayin shi, karki bari suratan shi su dameki naga kamar baya cikin hayyacin shi, kiyi hakuri ki sa masa ido “
Aisha tai murmushin da yafi kuka ciwo aranta tace aiba yanxu nafara jin irin wadannan daga bakinshi ba, afili tace “Tom nagode Dan Allah kayi bakin kokarinka wurin samo mishi address na gidan nima zanso yaganta koya dan samu sauki “
sabeer ya lumshe ido ya bude yanajin matsanancin tausayinta yace “I will do my best “
ya juya yatafi ita kuma takoma dakin ta kwanta gefen fahad don hakanan take kokari amma zuciyarta matsanancin ciwo take,
sabeer na cikin mota yana tuki hannunshi daya akan bakinshi yana tunanin maganganun fahad,yace”kammmm amma wlh Aisha na hakuri, wannan irin so haka to ko ya zaman nasu yake? nide insha Allah bazan bari matana sugane wacce nafiso ba,”
har yaisa unguwarsu faseelat gidannasu a kulle dayake komi acikin natsuwa yafi hankali seya nufi wasu samari dake zaune can gaba da gidan bayan ya musu sallama yatambaye su kosun san inda zesa mu alhaji maaruf,suka fada mishi ai shagon shi nanan kofar keke, ya musu godiya ya kama hanyar kofar keke don ganawa da abba,
gaskiya duk group din da baa comments zandena turawa aciki kunsamu awani wuri, yan groups dina kuma zanfara removing marassa magana wasu ma tunda suka shigo basuyi magana ba kar in cire mutum yaji badadi shiyasa nafada kurika comments please,
shalele novels group
Shalele value group
shalele boost group
raggon miji fans 123
duk wace batason ganinta awaje tarika comment.
[8/23, 2:42 PM] SHALELE????: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍????✍???? *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍????✍????✍????
We are bearer’s of so golden a pen????
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen????
Be hold our words
A product of our pen????
Savour our words
For it will cause you no pain.✍????
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
7⃣5⃣
*page dinkune yan group dina shalele novels group, kai jiya kun matukar burgeni wannan ruwan comments haka, naji dadi sosai Allah yasa ku dore ????*
Ba wuya ya gane shagon shi ya shiga ciki da sallama bakinshi,
Shagon ba kowa ciki don safiya ce mutane basu fito ba, abba ya amsa sallamar yana kallon sabeer,
Sabeeer yaja bench ya zauna acikin ladabi yace “abba ina kwana ya mejiki? “
Se sannan abba ya gane ba siyayya yazo ba yace ” lpy lau dasauki “
Sabeer ya kara sunkuyar da kai yace “abba ni abokin fahad ne aminina ne sosai, nazo ne nakara baku hakuri akan abinda yayi wlh yayi nadama sosai yana cikin tashin hankali yanzu haka ma baya lafiya, Dan Allah abba amishi hakuri kar a rabasu domin yana sonta sosai kishi ne ya rufe mai ido har ya mata haka “
Abba yayi murmushinsu na manya yace “u only know about ur friend, yayanta da kannenta suna nan suma duk basajin dadi atare suke jinyar, kishi ai bahauka bane daze mata irin wannan dukan haka, don kishin ma nada kyau manzon Allah (S. A. W)cewa yayi wanda baya kishin matar sa baze shiga aljanna ba, amma shi nashi yawuce akira shi kishi gaskiya “
Sabeer yace “Dan Allah abba kuyi hakuri kudauki wannan abunda yafaru a matsayin kaddara “
Abba yace “mun dauki kaddara kam amma seya saketa “
Sabeer yace “kuyi hakuri dan Allah wlh duk gidannashi ya birkice rashin faseelat, shiba lpy matarshi ma yarshi ma, Dan Allah kuyi hakuri tunda yagane kuransa nasan nan gaba baze sake ba “
Abba yayi shiru sabeer ya cigaba da bada hakuri,
Jim kadan abba yace “nifa nadade da yafemasa tunda ya sameni batun saki kuma bani zebawa hakuri ba seyabari idan alhaji yadawo daga Niger yaje yasameshi idan ya yafemishi shikenan danni haifuwar yara na kawai nayi amma alhaji yafini son su yafini kula dasu danhaka nabar masa ragamarsu seyajira shi har yadawo nanda kwana goma “
Cikin ran sabeer yace “tirkashi yo shi yana kai kwana goman ma “
Afili yace “to nagode sosai abba Dan Allah ina rokon alfarma abani address na asibitin da faseelat take ,wlh yar shi ma kullum kuka takeyi tanason ganin antin ta atemaka Dan Allah “yayi kamar maroki,
Abba ya yamutsa fuska yace “nan ne asibitin turai room 9”
sabeer yace ” nagode sosai abba ina kuma kara baku hakuri akan abinda abokina yayi “
abba yace “bakomi “
Sabeer ya mishi bankwana ya tafi,
direct gidan fahad yawuce, Aisha ta budemai yashiga yana shiga dakin da fahad yake ya zauna gefen shi ya furzar da iska ya dan bugi fahad yace “katashi muyi magana “
fahad ya yamutsa fuska jikinshi na fidda wani irin suraci yace “komi zaka fada kafada inajinka kaje baka samesu ba ko? Bashi ne maganar ba “
Sabeer yaja tsoki yace “to wlh zanyi tafiya ta in baka tashi ba nasameshi har shagonshi nabishi amma zan tafiya ta “
fahad ya tashi yana yamutsa fuska yace “inajin ka “
sabeer ya kalleshi duk yadda ya koma yace “look at you hmm, na sameshi nabashi hakuri sosai yace shide ya yafe amma seka saketa da nai ta bashi hakuri yace shi yahakura sede kajira yayanshi da yatafi Niger har yadawo kabashi hakuri in ya hakura shikenan yacemin nanda kwana goma ze dawo “
fahad ya tabe baki yace “kafin kwana goman na mutu ai ,wlh ina cikin hali zuciyata ciwo takemin kamar zata buga”
sabeer yace “kai kasani ai kana mutuwa ni kuma nasamu mata “
fahad ya wurga mai harara sabeer yayi karamin murmushi yace “eh mana ko haramunne?”
fahad ya koma ze kwanta sabeer yace “jira mana inada good news bayan bad one’s nasamo maka asibitin da take da room number “
fahad yafasa kwanciyar yace “wace asibity room nawa? “
sabeer yace”turai room 9″
fahad naji ya yaye duvet din yatashi tsaye Aisha na gefe na kallon ikon Allah,
ba bata lokaci ya bude wardrobe ya dauko jallabiya ya zira ya dauki key din mota yayi hanyar fita ,
sabeer yace ” kai malam bazaka tsaya muida maganar ba? ko godiya aikatsaya kamin “
fahad ya juyo yace “thanks ,kuma kafitomin daga dakin mata “ya juya ya bude kofa yafita yana sauri,
Sabeer yayi murmushi ya girgiza kai ya tashi tsaye, ya kalli Aisha yace “Allah yabashi lpy ni natafi aita hakuri lokacine “
Aisha batace komi ba, ya fita,
Koda yafita har fahad yabar gidan ya shiga motarshi ya nufi office,
fahad yayi ta sharara gudu cikin mintuna kalilan yaisa turai yana tafiya ahankali jikinshi ba kwari har yaisa kofar dakin,
nan kuma gabanshi yarika faduwa yayi knocking so biyu omer da tunda yazo duba faseelat yakasa tafiya saboda yadda ya ganta yana zaune yana bata abinci yace “turo “
Jiki mace fahad ya tura kofar dakin yana shiga yaga faseelat jikin omer ,zuciyarshi tayi mummunar bugawa, (ana nanfa me hali…..) dasauri yafara a’uziya yana korar shedan aranshi
Faseelat idonta a lumshe suke itakadai tasan yadda takeji abubuwa Sun jagule mata ba ciki ba fahad ga ciwo, kamshin fahad daya kewaye dakin yasa faseelat ta bude ido ta ganshi tsaye kamar bashi ba duk ya rame ya jeme yayi wani iri, tausayin kansu yakamata ta meda ido ta lumshe,
kallo daya omer ya mishi ya daure fuska tamau,
fahad yasamu yakara dedeta kanshi ya karasa ciki,
Ya mikawa omer hannu, omer yabashi sukai musabaha kowa ya zare nashi,
Omer ya dauki spoon yakara kaiwa setin bakin faseelat ,ta kauda kai idonta lumshe,
Omer ya kwantar da ita ya ajiye cup din yafita don in yatsaya bazaa kwashe lpy ba,
Bakowa dakin domin ummi tafita,
fahad yakarasa bakin gadon da faseelat take kwance yana kallonta tayi muguwar rama tayi fayau,
Faseelat kam taji dama da taganshi amma bataji dadin yadda taganshi duk yafita hayyacin shi ba,
Fahad Ya zauna kan bed din yanajin matsanancin tausayin ta ya dora hannu akan cikinta , yace “I’m sorry honey I hurt you, na rabaki da farin cikin ki I’m very sorry kiyafemin ” hawaye suka zubomai ,
faseelat bata bude ido ba tai shiru se takara jin kewar cikinta don tunda yana 3wks yafara mata motsi,
Fahad ya riko hannunta ya rungume a kirji ya saki kuka, tabude ido tana kallonshi ba tayi shiru dan tanajin haushin shiba ne tayi shiru ne don kartai magana tayi kuka don inde tabude baki kuka zatai, ganin yana kuka yasa tafara hawaye,
irin muryar marassa lpy tana hadiye kukanta tace “hero kadena kuka,bakamin komi ba, nasani acikin tunaninka bazaka yimin haka ba,kayi hakuri kashare hawayenka banajin dadin ganinsu”
fahad yanata kallonta da jikakkun eye lashes dinsa tunda tafara magana ,yace “we lose our baby “
faseelat ta lumshe ido ta bude tace “Allah ze bamu wani, kadena damuwa “
Fahad be dena hawaye ba na tausayi da kaunar faseelat yariga yasan tana sonshi sosai yanzu dabata yi fushi dashi ba sonta yakara ninkuwa a ruhinshi,
faseelat tace “stop shedding ur tears pls, har yanzu inasonka mijina nayi kewar ka sosai, kewarka tafi ciwon jikina zafi amma na samu lpya da naganka “tasakar mishi murmushi,
Ya share hawayenshi ya duka ya mata kiss a wuya yace “I miss you too kidubeni yadda sonki ya medani ina wahala honey “
faseelat tai murmushi tace “I’m very sorry ina Princess?ina anty I hope suna lpy “
Yakai hannunta dayake rungume dashi abaki ya mishi kisss yana karajin sonta yace “Aisha tana nan lpy, princess bata lpy, yanzu haka bata gida don tsoro na takeji saboda halin da ta ganki aciki, kiyi hakuri honey wlh bansan nayi ba bansan meke faruwa ba sede naganki cikin jini “
faseelat ta lumshe ido tana tunanin yadda yashigo toilet din ya fincikota, tace”i known kadena damuwa na yafe maka since,yakamata ka kawomin amira naganta kona ida warwarewa ina kewarta da surutun ta “
Yace “zan kawomiki ita meyasa baki fushi dani ba ?”
Tai murmushi tce”yazaai na iya fushi dakai, kaine rayuwata hero ina tsananin sonka bazan iya rayuwa in babu kai ba “
Yana tausayin kansu yace “gashi zasu rabamu abba is asking for ur divorce paper ,yan uwanki duk basu son kici gaba da zama dani “
faseelat ta dan bata fuska jin abinda ke faruwa tace”bazasu rabamu ba don inasonka sosai ka kwantar da hankalin ka ni takace, taka kai kadai my hero,u r my everything we will be together forever “
fahad yayi shiru yana aika mata da wani kallo me kashe jiki, itama ta rika aika masa da nata sihirtaccen kallon da murmushi kan fuskarta dukkansu Sun manta aina suke,
ahankali fahad yake kasa da fuskarshi zuwa tata, har fuskokin su suka hade suka rika kissing juna passionately, dukansu sunajin matsanancin dadi,
Ummi da taje dubo diyar wata kawarta data haihu ta dawo omer har ya tafiyarshi yabar asibitin gabadaya, batare da tasan abinda ke faruwa ba ta tura kofar dakin tashiga, abinda tagani ne yasa ta fiddo ido waje, faseelat na kwance fahad agefenta azaune ya sunkuya har yadan danne ta sunata kissing bakunan juna a dimauce faseelat hardasa hannu tarike mai kai don duk sunyi kewar juna,
ummi batasan lokacin da bakinta yafara hailala ba “Lailaha illal lah Muhammadur rasulillah (S. A. W)
tun kan takarasa faseelat ta Saki kan fahad, ya tashi zaune ya sadda kai yana sosa keya, itako faseelat ta rumtse ido,
kafin ummi tai magana umma ta turo dakin da faraa da sallama bakinta,
Taga fahad zaune gefen faseelat ga ummi tsaye hannunta kan bakinta da alama yanzu tashigo,
Umma tabata fuska tace “kai me kakeyi a nan? “
fahad ya dago ya kalli umma ya kara sadda kai kasa,
tace “tambayarka nake me kk anan da ba kasheta kaso kayi ba “
fahad yayi fuskar tausayi yace “umma nazo dubata ne, bawani abu ba “
tace “to tashi kafita tunda kagantan”
Fahad ya kalli faseelat da har lokacin idonta ke kulle tanajin matsanan ciyar kunya ya tashi ya fita yanajin kamar yayi kuka, faseelat jitayi kamar tajawo shi ya dawo ya zauna dan zamannan nashi setaji har karfin jiki tasamu,
yana fita umma taja tsoki, har lokacin ummi na tsaye da hannu abaki, umma ta kalleta tace “se hakuri yaran zamani basu da kunya kokadan”batasan ma abinda sukayiba zaman shin agadon kadai ma taga bedace ba,
Aran ummi tace “aini naga dahirrr”
umma takarasa ta ajiye kulas dake hannunta da ledoji ta zauna gefen faseelat tana kallon fuskarta, datake kamar meyin bacci,
ta juya ta kalli ummi tace “bacci ma take ko? “
ummi tace “ihmmm idonta biyu “
umma ta riko hannunta tace “daughter yau bakison ganina ne? “
Faseelat ta bude ido badan taso ba, bata kalli gun ummi ba tace “sannu da zuwa umma “
Umma tace “yawwa ya jikin? “
faseelat tace “naji sauki”
ummi tace “kwarai kau taji sauki azoma a sallame mu mutafi gida haka ta karasa warwarewa acan”
Umma tai dariya tace “zaman asibiti akwai cin rai dama amma tunda ta samu lpy gwara ku koma gidan “
ummi tace “ai dole saboda banga amfanin zaman da muke ba “
umma tai dariya ta meda hankalinta gun faseelat tace “yau tuwon shinkafa miyar shuwaka na miki danta temaka jinin da yarage ya ida wankowa, inafatan zakiiya ci? “
faseelat ta daga kai, umma tafara zuba abincin faseelat ta saci kallon ummi taga har lokacin ita take kallo takara lumshe ido sosai,
Umma nagama zubawa ta tadata zaune ta rika bata batajin yunwa bataci sosai ba tace takoshi,
Umma na nan zaune zuwa sha biyu da 30 lady da safiyya suka zo sannan suka tafi tare,
Suna fita kamar ummi najira tace “kede anyi jarababbar banza daga zuwanshi kin sakar mai jiki yakara dura miki wani cikin yakara zubardashi shasha wadda batasan ciwon kanta ba”
maganar ummi tabawa faseelat dariya aiko tadora hannu abaki tafara dariya ummi tace “dariya nabaki ko zata koma maki kuka don alhaji babba yace dole seya sakeki bazaki komaba kuma kinsan shi in abu yabata mai rai yana dadewa be sauko ba “
faseelat ta tashi zaune idonta taff da hawaye tace “ummi dan Allah kuyi hakuri kutemaka mana wlh kuskurene kuma bazaya kara faruwa ba “
ummi tace “seki bari seyazo seki fadamai nide ba ruwana aciki”
faseelat ta koma ta langwabe,ciwo yadawo ummi tace “kima tashi alhaji kawai nake jira yazo a sallame mu nagama wahala dake kuma “
Faseelat Tai shiru gabanta nata faduwa,
Tunda fahad yafita Aisha take kuka, tayi danasani tayi danasanin sanin faseelat a rayuwarta tanata karajin mugun tsanarta a ranta,
fahad ya nemi fever din jikinshi ya rasa yana cikin mota se lasar lips yake yana sakin murmushi shikadai, gsskiya he’s missing he’s messing soft and sweet hq na faseelat
yana zuwa gida ya shiga yasamu Aisha kwance taci kuka tagaji, yaje wurinta ya zauna ya medo kanta jikinshi yace “meke damunki ne Aisha?”
Aisha ta kalleshi cikin ranta tace shifa har ya warke, tace “zuciyata ke ciwo sosai”
Ya bata fuska yanajin tausayinta yace “sannu heart beat bari nakawo miki abinci da magani dan Allah kikara hakuri dani “ya aje kanta ya nufi kitchen,
Aisha tabi bayanshi da kallo tanajin takaici tace “ga heart beat dinka can ni I’m only a sister kuma kasan baka kyautamin kenan har kake bani hakuri”
shima yunwa yakeji ya dafa musu indomi da kwai yadauko mata magungunanta itama yunwa takeji ta bude baki tadanci yabata magani sannan yaci nashi yana gamawa ya dauketa yanata mata sannu taita kallonshi kawai,
ya sakarmata murmushi yace “I love you heart beat ina tsananin sonki”
aisha tai murmushi me ciwo tace “I love you yaya more than everything in this world “
Yace “thanks you so much dear ya kaimata kisss a head”
Akan bed yaajeta yashiga toilet ya watsa ruwan dumi don yakara jin karfin jikinshi yadawo har lokacin bacci be dauketa ba tana ta kallon shi kamar bashi ne ke kwance dazun ba, yazo ya haye bisa gadon ya matseta yafara aika mata da kisses,
Bata hana shi ba don itama tayi kewar dumin jikinshi sambatunshi and his sweet words after sex,
bayan komi yagama wakana ya rungumeta yana fada mata sweet words da kullum yake fadin sabbi kuma tanajin dadinsu ,har bacci ya dauketa yana rungume daita ya dade yana kallon fuskarta duk ta rame ya shafi gashinta ya tashi yayo wanka yasaka kaya ya nufi gidan mommy dauko amira yakaita wurin faseelat,
koda yaje yasamu amira kwance tana bacci ya Daukota beko gaisa da mommy ba ya nufi asibity,
Tun kafin yakai amira tafarka tana ganinshi tafara kuka yace “princess wurin anty zan kaiki kiyi shiru kinji “
amira tace “aika kasheta ni kamedani wurin mommy “
yanajin zafin maganganunta yace “antinki bata mutu ba kiyi hakuri mutafi wurinta tanason ganinki, kinji?”
Tai ta kuka yanata rarrashi har suka isa ya fito ya dauketa suna Zuwa bakin kofar dakin ya tura yace tashiga, amira tashiga dakin wayam bakowa don an sallamesu,
yana tsaye bakin kofa tafito tana kuka, ya riketa yace “me akamiki? “
tace “u lied to me bata ciki “
Ya tashi ya tura kofar wayam ba kowa, ya dafe kai yace “nashiga ukku”
amira ta kama hanya zatai tafiyarta yabita ya dauketa tana ta harbe harbe, har suka isa bakin mota ya dorata saman motar ya zaro mata ido rai bace yace “Dan ubanki natsu kimun gumm wlh kona zane ki “
amira tai gum tana ta hadiyar kukan, don betaba mata haka ba
Idonshi jawur yace “in kara jin kin min kuka sena miki dan banzan duka “
ya dauketa yasata motar suka tafi gidansu faseelat gidan kau a bude yake,
Ya fito ya dauketa yakaita har bakin kofa yace “she’s inside enter “
a tsorace ta shiga cikin gidan, ummi nata yan aikace aikace amira ta shigo tana share hawaye
Ummi tace “a, a amira kedawa? “
amira tace “daddy ne yace anty tananan in shigo “
ummi tajawo hannunta tace “antinki nanan kuwa”ta shigar daita dakin faseelat
faseelat na kwance bacci ya dauketa, amira ta tafi ta rungumeta tana kuka,
faseelat ta bude ido taga amira ta riko fuskarta tace “princess yaakai me kikewa kuka? “
amira tace “inata nemanki banganki ba anty karki dawo gidanmu daddy yakara dukanki”
ummi tace “kwarai ko fadamata gaskiya tunda ita kwakwalwarta ta toshe”tajuya tafita tana surutai
Faseelat ta sa hannu tana sharewa faseelat hawaye tace”bakiso na dawo mu cigaba da cin abinci tare, karatu, wasa, bakiso? “
Amira tace “inaso amma daddy na dukanki bana so ya cigaba da dukanki”
Faseelat tajawota ta rungumeta tace “baze kara ba it was a mistake kuma it won’t happen again kinji? Kidena jin tsoron daddynki he loves you baze miki komai ba”
Amira tace”he don’t love me anymore, yanzu ma yafadamin ze zane ni”
faseelat tace “kidena tsoronshi baze miki komai ba, kinji ko maybe kin bata masa rai kuma I have told you baa batawa iyaye rai “
amira ta daga kai, sunanan kwance sunata dan labari amira nabata labarin abinda yafaru bayan batanan,
fahad yana cikin mota zaune se tunani yake shifa he want to see her me yasa aka sallamesu acan zesamu damar ganinta anan ko baze samu ba “
omer yadawo daga aiki har yazo yashiga gida fahad be lura dashi ba yanata tunani,
omer nashiga ummi na tsakar gida yace “lpy ummi naje asibitin naga bakwanan kuma naga har yanzu dasauran jikinta “
ummi tace “kai ke ganin haka amma ita ta samu sauki ,ina dawowa dakin nasamu mijinta yazo ya danneta sunata tsotsar juna, shiyasa nace a sallame mu takarasa warware wa anan karma yadura mata wani cikin tun muna asibitin tunda de ita sakarai ce”
Omer ranshi ya baci yaja tsoki yace “yanzu ma nabaro shi kofar gida kome yake anan shima yasan baze samu ganin taba “
Ummi tace “yarshi yakawo tana ciki wurin ta”
omer yaja tsoki ya nufi dakin faseelat suna kwance ya janye amira, yace “kede anyi wawuya wadda batasan ciwon kanta ba, wato wannan karan ma bakiga laifinshi ba ko? To inke bakisan ciwon kanki ba mu munsan ciwon kanmu”
Yaja amira suka fita waje har bakin motar fahad da kofar ke bude ya tafi dogon tunani gwam gwam omer ya kwankwasa motar, fahad ya dago yana kallonshi,
Omer ya tura amira wurinshi yace “take ur daughter and go karka sake dawowa kofar gidannan, I warned you kar nakara ganin ka anan idan kuma kazo to zaka sha mamaki”
Fuuuu yajuya cikin gida,
Fahad yayi kasake yana ta kallon bayan shi, ya girmi omer amma gashi yanata datsa mishi magana, amira dake ta kuka tace “daddy ni awurin anty zan zauna”
Zuciyarshi na zafi ya dauketa yasata cikin motar suka nufi gida ita tana ta kuka shi kuma yanata tunani tunkafin suyi nisa zazzabin yadawo mishi,
Itama faseelat tana can tana kuka.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
comments, comment’s nikuma in rika antayo maku long page ko mungama.