NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 1) 21&22

????????21
     …….Har safiyar yau jikina sai k’amshin turaren Galadima yakeyi, feena dake kwance kusa dani tace, “Mrs Galadima!

k’amshin nan nakufa yayi over”.

     Harara Na dalla mata, tareda kai mata bugu ta kauce tana dariya, Bilkeesu ma dariyar takeyi, ta jawo wayarta tana fad’in “jama’a kunma tunamin, bara na duba comments d’in jama’a akan pictures d’in jiya”.
      Zumbur natashi zaune ina kallon Bilkeesu, “Bilkeesu kinada kai kuwa? yanzu nan hotunanmu kika mik’ama duniya?”.
      Da sauri Ameera tace, “to miye aciki, ai gamma mak’iya masu yad’a hotunan wancan 6atacin har 6utiyarsu Na rawa sugani yanzu kin zama halalinsa, ai wlhy jiya kusan kwana nayi karanta comments d’in jama’a akan pictures d’in, idanma mu bamu turaba wlhy abokansa sun yad’a a kowacce kafar yanar gizo, kuma yarinya harma a news wlhy an nuna, idanma baki saniba live aka nuna komai awasu gidajen tv”.
      Hannu na d’ora aka kawai nafashe da kuka saboda bak’inciki, nace “dan ALLAH harda abinda yaymin?”.
        “sosaima kuwa”. ‘cewar Ameera’.
      Kukana yakuma k’arfi sukuma suka saka dariya harda rik’e ciki sukeyi, nikam wlhy kukan gaske nakeyi basu saniba.
    Munubiya ce ta fahimci hakan, saita rungumeni tana k’ok’arin rik’e dariyarta data kasa rik’uwa.
     Ahaka aunty salamah tashigo tasamemu, “kai lafiyarku kuna dariya kuma ita tana kuka?.”
       Labari suka bata, ita kanta dariyar tayi, “yo miye abin kuka anan, koba komai ai  ya nunama duniya yana k’aunarki, ‘yan bak’in ciki kuma yasaka musu ciwon zuciya”.
       Kallonta nayi ina shar6ar hawaye, “yanzu nan aunty salamah kema haka zakice? mutum yamin wannan iskancin a bazama duniya sannan kuringa d’aukarsa abin kirki? yanzu dan ALLAH idan su Abba suka ganifa? tunda ance harma gidajen TV aka nuna”.
      “kajimin yarinya, yo ina kuma ruwan su Abba, mijinki nefa yanzun, to ai su inna ma duk sun gani agida, haka suma su abban”.
        Zumbur nayo tsalle tsakar d’akin hannuna bisa kai nace “galadima ka kasheni wlhy, ka cuceni ALLAH ya isana”.
      Dariyarsu k’aruwa tayi, suka shiga yi harda hawaye. yanda kukasan Na bibbigesu haka nakeji.
    Aikam yinin ranar ban yarda Na had’a ido da kowaba agidanmu, har lokacin da innarmu suka kiramu sukai mana fad’a itada mama Rabi’a da inna lami.
    Munci kuka tamkar zamu k’arar da hawayenmu.
     Zuwa la’asar fa anfara shirin kaimu gidajenmu, saifa lokacin hankalina dana Munubiya yakuma tashi sosai, domin abinda ake gudun yazo (rabuwa????, sabo turken wawa).
       Muna d’aki nida munubiya kowa zazza6i ya rufeta, yayinda iyayenmu keta k’imtse-kimtse, ita kanta innarmu jikinta yayi sanyi lakwas, saboda ganin abinfa da gaske ake, tafiyar zamuyi mu barta.
         Suma sauran amaren kowacce Na d’akin uwarta, wasunsu kam ko’a jikinsu, hankalinu kwance Dan d’okin auren sukeyi su.
     
       Anayin sallar magriba inna lami tazo tasakamu mukayi wanka, ana shiryamu muna kuka, bayan mun saka atanfa iri d’aya da aka bamu da gyale aunty Salamah tafara zazzage mana turarurruka ajiki.
        Duk wasu tarkace an had’a manashi kowa a handbag d’insa, sannan aka tarkatamu dukkan mu amaren zuwa falon Abbanmu, dukkan iyayenmu mata suma suka shigo, harda innaro da gwaggo Safiyya.
      Nasiha aka shiga mana mai ratsa jiki, mukam sai shar6ar kuka mukeyi mu dukanmu, hakama iyayenmu mata bakowa ya iya yimana nasihar ba. tun ana mana fad’an naji ana rad’e rad’in isowar wasu daga cikin angunan, wani kukan bak’in cikine Yakuma tahomin saboda tuna ni nawa Auren nanda shekara 1 ya k’are.
      Rungume innarmu mukayi yayinda akace mufito masu d’aukar amare duk sun iso.
     Innarmu Itama kukan takeyi, da gyar aka ciremu daga jikinta, an fara fita dasu fiddausi saboda motocin d’aukarsu duk sungama isowa, nice dai basu isoba.
     Suna kuka da komai aka fita dasu, yayinda dangin iyayensu mata kowa tabi tawagar mortar tasu amaryar, danginsu abbanmu kuwa rarrabuwa  sukayi, domin su sami zuwa kowanne 6angare suma.
       Motocinsu Na fita daga anguwar na gayyar abokan Galadima suka shigo, mitocine a Jere kuma masu yawa, abokan yaa marwan ma dama su suke jira, dan ance dole sai Munubiya tamin rakkiya sannan tunda nice k’arama.
   
      Bushe-bushen algaita yafara tashi anguwar tamu, dukda darene hakan bai hanasu busa kayarsu ba, hakan ya tabbatarma da ‘yan anguwa tawagar gidan sarauta sun iso kenan.
        Mata hud’u sun shigo gidanmu tareda kuyangi, Alk’yabba mai azabar k’yau da suka kawo aka sakamin, sannan aunty salamah takuma fesheni da tirare dagani har Munubiya.
         Da k’yar aka 6an6aremu daga jikin innarmu, tana kuka munayi, haka aka fita damu k’ofar gida wajen motoci.
      Motar datafi kowace tsari da k’yau aka sakamu nida munubiya, sannan inna lami da gwaggo Safiyya suka zauna a gefenmu.
       Kuka muke rik’e da hannun juna, har aka Isa damu cikin masarauta.
    Mom itace zaune a matsayin Momma uwar Ango kenan, Dan haka aka kaini sashenda take tareda dangin Momma.
     Tarba ta mutunci aka mana, irin wadda kowad’anne iyaye suka kai ‘yarsu gidan wani aka mata wannan tarbar hankalinsu zai kwanta sosai.
      Su inna lami basu wani dad’eba suka fara mik’ewa, saboda suna son mik’a Munubiya itama.
        K’ak’a rak’a k’aka, yanzufa akeyinta, danni da Munubiya mun rik’e hannun juna gamma munk’i saki, anyi lallashin da ban magana amma munk’i, da k’yar aka rabamu muna kuka tamkar ranmu zai Fifa. mun burge jama’a da basu tausayi sosai, sai hotuna ake zuba mana kuwa a wayoyi, (yo gidanne kwanyar da lantarki ko ina????????).
           Mom tasakani a jikinta tana lallashina da bani hak’uri, bayan fitarsu aka kaini wani d’aki, har lokacin ina shashshekar kuka, su Ayusher duk suna tare dani, basubi Munubiya ba, dan sunsan ita yau yaa Marwan zai shiga daga ciki????????????.
        Har lokacin mom Na tare dani, zazza6ine mai zafi yarufeni kuwa, amma dukda haka saiga wata mata wai tazo shiryani, Ashe za’ayi Mother’s event ne acikin gidan dakuma wanu Abu dasuke kira wai tarbar amarya a masarautar.
    Babu yanda zanyi, haka Na zauna tamin kwalliya Na shirya cikin less lemon green, aka sakamin alk’yabba mai k’yau itama, yanzuma har hular aka sakamin, Dan haka fuskata arufe take, saina sami damar yin kukana hankali a kwance.
      Mom da kanta tazo ta kama hannuna muka fita, yayinda kuyangi ke binmu abaya.
      Filine aka k’awata da haske, anmasa decoration da kayan sarauta Na kwalliyar gida, anutse kowa yake zaune, babu wata hayaniya sosai, (abinka da lamarin manya to????).
         Yaukam Galadima cikin ainahin basarakensa yafito, domin komai Na jikinsa Na sarautane, yasha alk’yabba kalar tawa, sai dai tasa ta maza ce, hard’e yake a zaune bisa wata kujera 2sita, wlhy wanda baima saniba saiya d’auka sarkinne gaba bad’aya, yaci mur fuskarnan d’inke, yasha rawani abin zak’k’yau kamar nabama (gwaurayen group d’ina shi????????).
         Gefensa mom ta zaunar dani, tunda aka shigi wajen dani suka d’auki tafi, fuskata a rufe take, ba kallon kowa nakeba, saima hawaye dake cigaba da zirara har yanzun.
      Mom tad’an ja hancin Galadima ya murmusa, sannan takamo hannuna tasaka cikin nashi tabar wajen.
    K’amshin turarena da nasa ya had’e yabada wani kalar k’amshin Na musamman.
       Dukda kukana a hankali nakeyi mara sauti hakan bai hanashi jin ajiyar zuciyar danake saukewa ba, yad’an matsa hannuna dake cikin nasa amma baiyi magana ba, nima sai bance komaiba nacigaba da kukana.
 
     An fara gudanar da addu’oin fatan alkairi da zaman lafiya agaremu, sannan akamin barka da zuwa cikin wannan masarauta mai d’unbin tarihi, Mom takar6a tayi jawabi irina uwar kwarai mai tarin mutunci da kamala. aka shiga tafa mata, saboda taburge kowa.
      Hakama aunty Mimi tayi jawabi mai birgewa, sannan mama Fulani tafito cikin tsantsar izzarta da k’asaita tayi welcoming d’ina a wannan family, hakama matan Sarki, saikuma k’annen galadima mata da yayunsa, yayun momma da k’annenta, komai yana tafiyane cikin nutsuwa, nidai ba ganin kowa nakeba, amma ina sarrarensu, har lokacin kuma hannuna yana cikin Na Galadima, yakan d’an murzashi time to time.
     Duk Na k’agara a tashi wlhy, dan jikina yayi masifar zafi saboda zazza6i,  shikansa Galadima yanajin zafin a hannuna, ganin kamarma ina rawar sanyi saiya kwantoni jikinsa.
    Ban musaba, saboda babu abinda nake buk’ata a lokacin kamar kwanciya, ga barci ga ciwo da gajiya.
     Bayan angama jawabai da k’yaututtuka da kowa kan bani wad’anda aketa zuwa ana jibgewa a gabanmu aka fara gudanar da liyafar cin abinci kamar yanda komai yake a tsari, sai abinda kakeso za’a kawo maka.
    Muma ankawo fruits salad da gasashen kaza da snacks sai drinks da wani abinci dabansan miyeba an ajiye agabanmu.
     Da hannu Galadima yayi kiran aunty Mimi, ta k’araso inda muke.
     “my k’ani lafiya dai? Ko abincin bai matabane?”.
      “no aunty bama abinci baneba, batada lafiya fa, ta6a jikinta kiji”.
     Hannu aunty Mimi tasaka a wuyana, tausayi nabata saboda zafin  da jikina ya d’auka, “to yaza’ayi yanzu? ko tad’an k’ara hak’uri kad’an tunda naga ankusa tashi, kasan halin mama Fulani, kuna tashi yanzu zata d’aukeshi wani Abu daban, dama wannan d’an kwantar da itan dakayi ajikinka inaji tana maganar bakada kunya wai”.
     Guntun tsaki yaja yace “canta matse mata, indan tagadama tacika masarautarnan da surutu, nanda minti 30 inba’a gamaba zamu tashi kawai”.
      “karka damu zama’a gama insha ALLAH”.
     duk maganar dasukeyi ina jinsu, sai naji tausayin kaina ya kamani, domin nafahimci nanma akwai mai irin halin innaro kenan. Wasu hawaye suka silalomin a kumatu, sauk’i nama auren 1year ne Na kama gabana.
         Daga ni har shi babu Wanda yaci wani Abu har aka tashi a taron, lokacin 12pm, yanzuma mom ce takama hannuna muka koma 6angaren da aka fara kaini, muna shiga kwanciya nayi, bayan mom tasakani cire alk’yabbar jikina, duk kunya ta rufeni, ganin haka yasata ajiyemin kayan barci masu kauri ta  fita, a hanzarce na shirya na saka hijjab sannan na kwanta, saida ta kintaci time sannan suka shigo itada aunty Mimi da Galadima sai wani ba’indiye, Ashe abokinsa ne dayazo biki, kuma doctor ne.
       Galadima ya zauna a bakin gadon kusada kaina, dayake na juya musu bayane, bargon Dana rufa har fuskata yad’an janye, Idan Akash yay tambaya saishi ya d’an rankwafo Dan yaji amsar da zan bada, saiya maimaita masa abinda na fad’a.
    Bayan gama tambayoyin Akash yace damuwa ce da gajiya kawai, ya rubuta maganin daza’a sayo min, (duk cikin harshen ingilishi suke maganar).
    Kar6a Galadima yayi ya d’auki waya yakira Harun, sunan maganin ya Sanar masa sannan ya yanke wayar, mintuna 10 saiga Samha takawo maganin.
       Ya kalli mom yace, “amma bataci abinciba ai”.
     Kallon Samha mom yayi, tace “taje ta had’o min tea.
    Samha na kawowa duk sai suka fice suka barni dagani sai shi, shima Akash fita yayi.
      Bargon jikina ya yaye gaba d’aya, muryarsa a dake yace “tashi kisha”.
     Shiru na masa, hakkane yasakashi kausasa muryarsa, “wai bak’ya jinane?”.
     Yun k’urawa nayi na tashi da k’yar, kad’an na saci kallonsa, harya cice kayansa na d’azu, yana sanye da dogon bak’in wando da T-shirt mai gajeren hannu, gefen wandon anmasa zane layi 2 da farin zare. fuskarshi babu walwala kamar kulum.
      Mug d’in tea n ya mik’omin bayan na gyara zamana na jingina da gado, ALLAH ma ya soni sanye nake da hijjab.
    Kar6a nayi dan nima nasan harda yunwa ke cina, inaga rabona dawani abincin kirki tun ana jibi d’aurin aurenmu, (ranar kamu).
     Nasha rabin cup d’in na mik’a masa, bai kar6aba yashiga hararata, cikeda k’asaitarsa yace “cup d’in kawai nake buk’atar gani, kina 6atamin lokaci zanje na kwantane”.
     Tamkar na makeshi haka naji, na harareshi nima a k’asan ido, muryata na rawa nace “wlhy na k’oshi, zanyi amaine”.
    Bai tanka minba kuma bai k’ar6i mug d’inba, hakan ya nunamin dole dai saina shaye kenan, haka na rumtse idanu na shanye na mik’a masa mug d’in.
    Kar6a yayi ya ajiye saman table glass d’in dake gabansa, sannan yad’auki magungunan ya 6alla min, bana tsoron Magani sai allura, dan haka babu musu na kar6a nasha tareda ruwan daya bani a cup.
     Ina gamawa na zame na kwanta, mik’ewa yayi yaja bargon ya lullu6a min sannan ya fice batareda ya tanka minba.
     Babu dad’ewa barci ya kwasheni, bamma San su Ayusher sun shigo sun kwantaba suma. da yake gadon babbane duk sai ya d’aukemu.
     Washe gari natashi dad’an sauk’i, sai dai kewar munubiya data innarmu, harma data gayyar tsiyar ‘yan gidanmu, sauk’i nama d’aya ina ganin su Feena.
       Break fast mai rai da lafiya aka kawo mana, su Ameera sai zuba santi sukeyi, nidai uffan bance da suba, nad’an tsakura kad’an na turo, maganin jiya na d’auka nasha na safe, dan har lokacin kaina na ciwo kad’an-kad’an, babu dad’ewa barci yay awon gaba dani.
       Ban farkaba sai 12, shima tadani akayi, wai za’ayi ko hawan mi, nidai wannan bidi’a ta isheni hakanan wlhy.
        Shiri akamin yanzuma cikin farin less, sanan aka samin alk’yabba, yanzun ma fuskar tawa a rufe take.
    Gaskiya gidan sarauta akwai girma, dan shimafa dole akirasa da suna wani gari guda kam.
        A mota aka sakamu zuwa inda za’a gudanar da hawan, dukda kuwa acikin gidanne fa, nida Samha ne kawai a mortar, tana ta zubamin surutu har muka isa.
     Wata daban santa bace ta fitar dani daga motar, tana rik’e da hannuna har gurin da aka tanada domin zamana, yanzun fuskata a bud’e take, ba’a sakamin hular alk’yabba d’inba, dan muna zama awajen matar data fidoni ta ciremin, sai dai kunya tasani kasa kallon kowa, duk tsiwata inada tsananin kunya da rashin son zama wajen da mutane suka cika yawa.
       Aunty Mimi ce a gefena na haggu.
     Ban iya kallonba saida ta min magana tana kamo hannuna, dole babu yanda na iya na kallesu, su Galadima ne a saman dokuna shida samari kusan biyar duk da irin shigarsa ta sarauta, dokunan suna a tsaitsaye, da alama umarni suke jiran abasu, dan kamar gasace zasuyi.
     Caraf muka had’a ido dashi, murmushin gefen baki ya sakarmin, cikeda mamaki na janye idona daga kallonsa.
        Ana busa wani k’aho kowa yabama dokinsa k’aimi suka rera da gudu, nanfa hankalin kowa yakoma kansu ana zufa tafi, babu wata hayaniya dan bawani yawane damuba, kusan ma wajen duk ‘yan matane sai abokan Galadima dasuke son ganin al’adar dabasu saniba. Saikuma yayunsa mata irinsu aunty Mimi, amma babu manya kamar su mom awajen.
     Ni ban saniba Ashe wannan tafiya saisun zagaye masarautar su dawo, Wanda yafara zuwa shine na d’aya.
     Muna nan kusan mintuna 30 saigasu aguje suna tada k’ura, ko ganin fuskarsu ma ba’ayi sosai bare kagane wanene a gaba.
      Jinai kawai ansaki tafi kowa na ambatar Galadima! Galadima!!, wai Ashe shine yafara isowa. ya diro akan dokin yana murmushi da goge hannunasa da handkerchief d’insa daya zaro aljihu, sannan yagoge fuskarsa.
        Ruwa wani dogari ya mik’a masa, ya d’auka daga saman tired’in da aka d’oro yabud’e Goran, batareda ya saka kofiba ya hau shan kayansa, tas ya shanye ya jefar da robar, suma sauran duk ruwan suke sha.
      Daga nan hotuna akayi, sannan yazo har inda muke ya kama hannuna, wai Ashe nima yanzu dole saina hau dokin, ahakane zamuje sashe-sashe, dan kowa yanacan yafito waje yana jiran zuwanmu.
      Banta6a hawa dokiba sai yau, dan haka jikina yakama rawa. Muryarsa can k’asan mak’oshi yace “k bak’auya ki nutsu”.
      Maganarsa saida tabani haushi amma ya zanyi, da taimakonsa na hau dokin bayan dogarai sun baza rigunansu yanda baza’a ga hawa naba.
     Saida na hau da k’yau sannan shima yaje ya hau nasa, kuyangine a gabanmu suna zuba flowers, a bayanmu kuma dogarai, gefe da gefenmu ma dogaraine, wasu suna busa algaita wasu suna kid’an taushi, sai gayyar abokansa biye damu abaya dasu Ayusher da ‘yammatan masarautar.
     Ahaka muka dinga zuwa sashe -sashe inda duk sun firfito, duk muna akan dokin bamu saukaba, sai dai mukan risina alamar gaisuwa. fuskata kuma tana abud’e yanzun kowa Na ganina, saida muka zagaye ko ina a masarautar sannan aka maidani wajensu mom. Lokacin la’asar tayi.
        Dukna damu saboda kiran munubiya danaketa yi  wayar akashe, tsakin danakeyine ya saka Ayusher tambayata, na fad’a mata.
    Dariya tayi, “yo banda abunki ina zakiji munubiya kuwa, yaa marwan nacan nashan amarci kema kin sani ai, kema zuwa gobe wazai kiraki ya samu, Galadima nacan yana kwa…..”.
    Filo na d’auka Na jefa mata a fusaka, suka sanyamin dariya kuwa.
★★★★
    Nasha kuka yayin tafiyarsu Ayusher, inaji ina gani suka tafi suka barni nikad’ai cikin wad’anda ban saniba.
       Tun magriba aka shiryani tsaf cikin wata tattausar atanfa, sannan aka d’oramin alk’yabba, wlhy nagaji da saka alk’yabba r nan, saboda nauyi sukemin, har mamaki nakeyi yanda su basu damuba.
       Zan iya cemuku nidai yau wanka akamin da turare dan kowane lungu da sak’o na jikina saida yasha ruwan turare, ruwan danayi wanka dashi kansa na musamman ne, nayi k’yau harna gaji.
         An fiddoni aka sakani cikin mota, sannan aka nufi sashen Galadima dani. Dukda nasan auren Contract nayi, hakan bai hana zuciyata luguden dakaba, tunda bamuyi wata yarjejeniya dashiba ta zaman da zamuyi, addu’a natayi a zuciyata ina tunano innarmu da munubiyata da kewarta ta gallabeni, jinake tamkar mun shekara 5 bamuga junaba, bamu ta6a yini ba’a tareba, saigashi yau munyi kwana da yinima, ko’a waya bamuji muryar junaba.
     Duk da fuskata a rufe take hakan bai hanani shaida 6angaren Galadima ya had’uba, dan k’amshinsa ma da banne.
     Muryar wata na tsinkayo a cikinsu tana fad’in wai falon Galadima za’a kaini, gabana yakuma fad’uwa.
         Nidai naji mun iso inda turaren Galadima yafi ko ina yawa, inaga nanne falon nasa, gawani lallausan Abu danake takawa a k’afata, sun zaunar dani akan wani laushin dayafi Wanda nake takawar, sannan sukayi addu’a suka fice.
    Tunda suka fita ban iya d’ago kainaba, dukda falon tsitt yake alamar babu kowa cikinsa, sai k’arar AC kawai da ni’im taccen k’amshin dake tashi, a falon, sai TV dake magana can k’asa an rage k’arar sosai, hawayen danaketa rik’ewa tun d’azun suka shiga ziraro min a kumatu. a hankali nakejin takun takalmi na tunkaro falon………????
Muhad’u tomorrow idan munkai da rai da lafiya, yau kaina namin ciyo kuyi manage da wannan please????????.
Ko Galadima zai angwance oho mar????????.
????♀⛹????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
*_Typing????_*
  *_HASKE WRITERS ASSO…????_*
       _(Home of expert and perfect writer’s)_
       *_RAINA KAMA……!!_*
               _{Kaga gayya}_
         *_Bilyn Abdull ce????????_*
????????22
     ……….Takun takalminsa yana bada sautine dai-dai da kowacce dak’ik’a na bugawar zuciyata, gaba d’aya saina nemi jarumtata na rasa, musamman da firarsu a Ayusher tashiga dawomin a zuciya.
     Zuciyata tashiga tsitstsinkewa, saikace ba Munaya mai tsiwarnan ba da rashin barin kota kwana, kululu cikina yabada sauti lokacin da aka murd’a handle d’in k’ofar. kamshinsa ne ya buso min har cikin hancina.
    Shikam cak yatsaya yana kallona da mamaki, yasan wannan aikin aunty Mimi ne ko mom, yakuma tamke face saboda tsaro ba tsoroba????.
    Oho ni bamma san yanayiba, nima tawa ta isheni a zuciya, dan wani tsoronsa ALLAH ya dasamin lokaci d’aya. kusan mintuna 2 yana a tsaye tamkar bak’on falon, yayinda k’amshin turarena ke dukan hancinsa, yau da ace auren soyayya yayi da wadda yakeso, babu abinda zai hanasa sauke nauyin daya damesa tsawon shekaru. a hankali yacigaba da takowa har cikin falon, ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu cikeda izza, k’afarsa d’aya a kan d’aya yana wani kallona a k’asan idanu, shiru kakeji tamkar bama a cikin falon…….
       Muryata a sanyaye nace “ina yini”.
      tamkar bazai amsaba, saikuma yace “lafiya”.
     Daga nan kowa yay shiru.
      Knocking d’in k’ofar da akayine yasakashi sauke 6oyayyar ajiyar zuciya, cikin muryarsa mai kama da anmasa dole ya tambayi wanene?.
    Cikeda girmamawa sarkin k’ofar yace, “nime ranka ya dad’e, dama an kawo sak’one”.
       Kansa ya jingina da kujera, sannan yace “su shigo”.
        Kuyangi kusan biyarne suka shiga falon da sallama, duk muka amsa akan la66a, suka dire kayan hannunsu sannan suka zube suna kwasar gaisuwa agaremu, hannu kawai ya d’aga musu, nidai koma motsi banyiba, dan nima kunyama nakeji idan naga sun durk’usa suna gaidani, danfa wasuma sun girmeni sosai wlhy, wasuma sun haifeni, kai sarauta dabance gaskiya, al’amuransu sunada wahalar gaske, nidai harma yanzu ban fahim ci komaiba wlhy.
     Bayan fitarsu da kusan mintuna 4 naji alamar mik’ewarsa, yanzu ma baice dani uffan ba yashige wani d’aki danake k’yautata zaton bedroom d’in sane a wajen.
      Guntun tsaki naja, a raina nace ALLAH ka rabamu da girman kai dai wlhy.
     Ban damu da cire hular alk’yabba d’inba, dan sanyin Ac yasa ban takura ba, sai zamana dana gyara sosai yanda zanji dad’i da k’yau a saman lallausar kujerar, duk da har yanzun a tsoracen nake kuwa. dan wannan d’an jinkan yafi k’arfina, zai iya amfani da k’arfinsa ya cutamin batareda yayi la’akari da matsayin auren namuba.
      Shikam yana shiga d’akin nasa yafara k’ok’arin cire bottom d’in rigarsa, idon sane ya sauka akan gadonsa dake lailaye da zanin gado blue, dan komai nasa na nan white and blue ne, sa6anin na India dasuke White and Golden, kuma matsawa yayi sosai saboda ganin farin k’yalle dake saman bedsheets d’in.
     Tsaki yaja yana fad’in “waisu wad’annan mi suke nufi da shinfid’amin wannan farin abun a saman gado? samazo su d’auki kayansu yanda suka ajiye, motsww”. Yakuma jan tsaki sannan ya shige bathroom.
      Acanma yana wankan yana jera tagwayen tsoki, bai wani dad’eba yafito sanye da bathrobe milk, hannunsa rik’eda k’aramin towel yana goge fuskarsa zuwa kansa.
       Bai shafa maiba, wando yasaka da t-shirt duk milk color marasa nauyi, da alama yayi shirin barci kenan, ya d’auki turarensa na barci mai sanyin k’amshin ya faffeshe jikinsa, sannan ya saka silifas bak’ak’e a k’afarsa yakuma fitowa.. 
         Kallona yayi da mamaki ganin ko fuskarta na kasa bud’ewa, ya ta6e baki da cije lips nashi saman  ya zauna bisa tattausan carpet d’in tsakkiyar falon inda kuyangin suka ajiye kayan d’azun.
      Tankwashe kafafunsa yayi yashiga bud’e kwanikan domin duba abinda ke ciki. “halan kekam bak’ya jin zafi?”.
      Yayi maganar yana zuba fruits salad a k’aramin bowl na tangaran mai k’yau.
      Shiru nayi tamkar ban jishiba, shima saiya shareni yaja bowl d’in gabansa yafara sha a hankali tamkar bayaso.
    Duk abinda yakeyi ina kallonsa ta k’asan ido, saboda kaina Dana jingina da kujera.
      Kusan mintuna 5 yana shan fruits salad d’in tamkar wani k’aramin yaro, dan ko Rabin Wanda yazuba baiyiba, araina nace abincinma sai an masa sarauta kenan.
     Idanunsa ya d’ago yana kallona, “k wai bakijin ana Miki maganane? bazaki bud’e face nakiba?”.
        Saida naja kusan seconds 20 sannan na janye hular alk’yabba d’in.
    Janye idonsa yayi yacigaba da shan kayansa, nikuwa saima na zame na kwanta a kujera, dama 3setter ce, idanuna na maida na lumshe saboda ciwon da kaina yakeyi kad’an-kad’an, ga kewar innarmu da munubiya dasu Aryaan na damuna, ga wannan auren na fargaba na addabar zuciyata.
     Dukda yaga kwanciyar danayi bai tankaba, ya kammala shan fruits salad d’in yamik’e, saman kujera yakoma ya zauna, ya d’auki wayarsa yana latsawa, saikuma ya ajiye ya d’auki remote ya canja tasha zuwa labarai.
      Haka muka zauna tamkar kurame, shi yana kallon labarai yayinda nikuma barci 6arawo ya saceni batareda na shirya ba, to gajiya na nuk’urk’usata.
         Shi duk bai farga barci nakeba harya kammala kallon labaransa ya kashe tvn, kallona yayi da nufin min magana saiyaga kamarma nayi barci a haka.
      Yay d’an jim yana tunanin tayaya zai tasheni, danshi soyake ya shige yayi shafa’i da wutiri ya kwanta, a ganinsa kuma bai kamata ya barni a wajenba.
     Matsowa yayi kusada kujerar, ya d’an bubbuga hannun kujerar, dama barcin nawa baiyi nisaba, na bud’e idanuna dasukayi d’an jaa a hankali, saboda barcin dana fara.
      “tashi muje ki kwanta”.
     Gabana ya fad’i, amma saina yunk’ura da k’yar natashi zaune.
     Ganin ya nufi k’ofar futa sainaji d’an sanyi, tashi nayi nabi bayansa muka fita, bakowa falon alamun duk suntafi makwanci. Wani falon muka shiga daban kuma, gaskiya shima ya had’u, komai na cikinsa lemon green ne da milk, sai tashin k’amshin turaren wuta da air fresheners masu dad’i yake. bai tsaya ananba yay gaba, nidai ina binsa abaya kawai, munshiga k’aton bedroom tamkar nasa, saidaifa aganina nasan yafi had’uwa duk da ban ganiba, nanma komai lemon green ne acikinsa, sai labuloli milk kamar falon, shima yanata tashin k’amshin.
      Juyowa yayi ya kalleni “nan shine d’akinki”. ‘yayi maganar tamkar an masa tilas’.
      Uffan bance masaba, sai d’aga masa kai nayi alamar naji, shima bai sake cewa komaiba ya fice abinsa.
      d’akin na shiga bi da kallo, yamin k’yau sosai, na cire alk’yabba jikina ina sauke numfashi, sanan na cire sark’a da ‘yankunne da bangles d’in duk na zube saman madubi. Suma kayan na hau cirewa dan bazan iya barci da suba, sai kuma na shiga tunanin inda zan samu kayan barci? tunda lefena suna gidanmu ba’a kawoba, akwatin da’a kawoni dashi kuma jiya ban Ganshi a d’akinba, zuciyatace tabani shawarar duba wardrobe d’in dake d’akin, banyi musuba naje na bud’e, a mamakina saina ganta da kaya, sai dai duk k’ananune, kayan barcinma babu na mutunci, tamkar zan fasa kuka haka naji, da k’yar nasamu wasu Riga da wando masu sauk’in fidda tsiraici, duk da suma d’in dai sai a slow.
     Gadon na hau amma saina kasa barci, kewar ‘Yar uwata yadawomin sabuwa, na tashi zaune na fashe da kuka.
        Ina zaune ina kukana sai kawai naga mutum yashigo min da sallama ciki-ciki.
    Da Sauri na jawo gyalen dana ajiye gefe na yafama jikina, plate d’in hannunsa ya ajiye a table d’in dake jikin gadon, dan harya kwanta yatuna banci komaiba, gani yayi bai dace ya barni da yunwa ba, danni bak’uwace yanzu a gidan, dole sai an bani zanci.
    Tamkar bazai tankaba saikuma ya kalleni, “mike faruwa kike kuka?”.
       Wasu kwallanne masu zafi suka sake kwararomin, na sharesu da gefen gyalena nace, “wlhy ni tsoro nakeji, ban ta6a kwana ni kad’aiba, dan ALLAH ka kiramin Samha ta tayani”.
      Shiru yay ya tsaya kawai yana kallona, azuciyarsa yace kajifa wannan yarinyar dawani batu, kawai saina tafi kiran Samha ta tayata kwana?. guntun tsoki yaja, Wanda yasakani d’agowa na kallesa. Ya cije lips d’insa sannan ya juyo yakuma kallona “mikike nufi da bazaki iya kwana ke kad’aiba? kin san dai babu wanda yasan manufar aurenmu, daga ni sai ke sai muftahu, dolene ki koya ma kanki iya kwana ke kad’ai d’in, sannan inason kisanfa dolene ki dinga canja behavior naki agaban mutane, domin su agaresu aurene mukayi kamar kowa, sannan ta wannan hanyarne kawai zamu iya samun wani avoidance a kan case d’inan, nasan kinada wayo dan haka saiki bud’e idanunki dan kema zaki iya zama security d’in kanki da kanki, game da zaman gidannan kam za’a samu mai koyar dake komai, dan komai a tsare yake, sauran bayani zamuyishi daga baya, kisa a ranki zaman da zamuyi dake zamane na taimakon juna irinna abota, bayan aiki ya kammala zan baki sakinki kamar yanda nayi alk’awari”.
       Duk da hawayen dake neman zubo mini haka na had’iyesu, cikin aro jarumta nace, “insha ALLAH komai zai tafi yanda yakamata, kuma zaka sameni mai tsare gaskiya da amana, ALLAH yabamu nasara, ina fata da lokaci yacika komai ya bayyana zaka cika alk’awarin sakina?”.
       Batare da ya kalleniba yace, “zaki sameni mai cike alk’awari insha ALLAH koda ace bamu cika shekararba komai ya bayyana zan sakeki, idan kuma ashekara 1 bamu samu yanda Muke soba zamuyi 2 ne kamar yanda nafad’a miki tun farko, amma inama addu’ar kafin shekara  komai yazama done OK?, ga abinci nan kici, kiyi addu’a ki kwanta, zakiyi barci insha ALLAH”.
     Batareda ya jira cewata ba yay ficewarsa, kusan mintuna biyu idona na kallon k’ofar, saikace zanga dawowarsane, mamaki yabani sosai, dama yana magana mai yawa irin haka? Kuma cikin kwantar da murya. na sauke ajiyar zuciya tareda bud’e plate d’in daya ajiye, gasashen namane mai rai da lafiya, yawu nane ya tsinke, gashi dama inajin yunwa, na mik’e na bud’e fright d’in dana gani ad’akin, ruwane kawai aciki aka zuba, guda d’aya na d’auka na dawo saman gadon na zauna, inacin naman ina hawaye, gaba d’aya kewar ‘yan uwana ta gallabeni, musamman Munubiya, waya na d’auka na kuma gwada kiranta, amma still akashe, wasu hawaye masu zafi suka kuma kwararowa a kumatuna, naman na ture gefe naciga da kukana, saida nayi mai isata sannan natashi nashiga toilet d’in d’akin na wanko fuskata da bakina na d’auro alwala, a fright d’in na saka naman da sauran ruwan na kwanta kamar yanda yabani shawara, addu’ar barci nayi sannan narufe ido. tunani yace salamu alaikum, haka naita juye-juye a gadon, barci 6arawo bai saceni ba sai around 3. daga nan ban sake sanin inda nakeba saida naji ana bubbuga gefen filon danake kwance.
    Da k’yar na bud’e idanuna dasuka kumbura saboda kuka da rashin isashen barci. Galadima ne tsaye a kaina, sanye cikin jallabiya ruwan hanta, tamasa k’yau dukda kallon fisha na masa.
    Agogon d’akin ya kalla sannan ya juya zai fita yana fad’in “kitashi kiyi salla”.
      Da k’yar na iya sauka, dan jikina duk ciwo yakemin, ga barci danake masifar ji. daurewa nayi nafara wanka da ruwa mai d’an zafi sannan nayo alwala nafito, salla na gabatar ta asuba nayi addu’oina sannan namik’e na koma gadon, dan danan barci ya kuma kwasheni.
★★★★★★★
     A gidanmu bayan kwashemu dukkan amare washe gari ‘yan biki suka fara kama gabansu, sai makusanta ne kawai aka bari.
    Lokacin da su Ayusher suka koma sun iske innaro na zuba tijara a tsakar gida, wai an munafunceta ba ace ta fitoba lokacin da akazo d’aukata, dama tasan innarmu bak’in ciki take mata karta dangwali arzik’i, to kuwa ita k’adangaren bakin tuluce, babu yanda aka iya da ita, duk wani makirci da innarmu zata shirya mana akan karmu taimaka mata dolene tanan matsayin uwar ubanmu.
       ‘Yan gidanmu fa abin nema yasamu, saifa aka hau dariyar gatsa-gatsa suda sauran bak’in su.
   Innarmu kam murmushi kawai tayi, zuwa yanzun ita ta wuce k’aramar yarinya, dama sarai tasan bawai nadamar gaskiya innaro tayiba, kawai dai wani abu dake a ranta kawai. Ko lek’owa batayi tsakar gidanba, barema tanuna tasan da ita takeyi.
       Shigowar su Ayusher da kaya nik’i-nik’i na biki da mom tabasu yasa innaro waryar leda d’aya tana fad’in munafukai, Ashe kune aka tura domin Ku tattaro komai, to ALLAH ya fiku, kafin mai biri yaga mai gona mai gona yaga biri”.
     Ayusher zatayi magana mama Rabi’a ta hanata, haka suka shige da sauran kayan suna k’unk’uni.
   Innaro na bud’ewa taga duk drinks ne aciki saita biyo bayansu, ledar ta dangwarar a k’ofar falon tana kunfar baki, “bazansha kayan ruwan ba kayan fitsari, yanzu-yanzu a canjamin kokuma na kwashe komai babu yanda za ayi dani dangin tsiya dangin rashin asali, kai ALLAH yarabamu da bak’ar zuciya mai cike da nunkufurci dai wlhy”.
       Babu wanda ya tanka mata, Mama Rabi’a ta bud’e komai ta d’iba mata,  tanuna ledar datafi kowacce girma da mama Rabi’a bata bud’eba, “to uwar iya, ita waccan ledar miye aciki?”.
     Da sauri Bilkeesu ta d’auke tana murgud’a baki, “wlhy babu mai baki wannan, domin a lissafe suke, kuma mu aka bamawa bawaniba, zannuwane”.
       “to ‘Yar karoro, kekuma asuwa gand’oki muje biki? Aiba uban wani ya Haifa min Auwalun ba daya haifi munaya, saiki bari sai ALLAH yabaki farin jinin auren koda kansilan anguwarkune sannan kimana iyayi, kujimin bak’ar banza kawai”.
    Baki Bilkeesu ta ta6e, suka ja ledar itada feena suka shige tsohon d’akinmu, yayinda su Ayusher da Ameera suka take musu baya.
    Daga mama Rabi’a har innarmu babu wanda ya dakatar dasu.
    Aiko sai innaro ta saka kuka wai su Ayusher sun zageta agaban innarmu batace komaiba.
       Duk abinda ke faruwa ‘yan gidanmu na tsaye cirko-cirko suna dariya.
       Yaa Hameed daya shigo gidanne yazo har inda innaro ke tsaye a k’ofar fallon innarmu yana tambayarta lafiya?.
    Cikin kuka da shar6e majina ta kora masa bayani, Kansa kawai ya girgiza, danshi lamarin innaro baya burgesa. Da lallashinsa tahak’ura tafita yarakata har gidanta da ledar da mama Rabi’a ta zuba mata kayan bikin.
       Acanma zage-zage taitayi tana aibanta innarmu, kunya dukta ishi gwaggo Safiyya ga sauran ‘yan biki suna saurarenta, gwaggo Safiyya fitowa tayi ta baro gidan, gidanmu tashigo tazo tana bama innarmu hak’uri.
     Murmushi innarmu tayi, tace, “wlhy babu komai gwaggonsu, ai inna nima mahaifiya tace, mizaisa dantamin Abu yazama ya 6atamin rai, ai ta Isa danine shiyyasa”.
     Innarmu ta bama gwaggo Safiyya tausayi, tana k’ara jinjina hak’urin innarmu a ranta, tabbas da acikin sauran matan gidanne da innaro ta magantu, dan ba raga mata zasuyiba, danma suna Shankar mazajen gidan su Abbanmu.
★★★★**•°•°•°•**★★★★
       
     Su Munubiya amaryar yaa marwan, ????baiwar ALLAH taban tausayi, dan kallo d’aya namata nasan yaa Marwan ya ajiye muskilamci ya kashe arna????.
    Duk takuma zama wata silent, tana kwance a falonta dayayi k’yau da tsari, hannunta dafe da kanta, idonta arufe tamkar nai barci, tunanin innarsu da kewar ‘Yar uwarta ya gallabeta, gashi tun shekaran jiya yaa Marwan ya kar6e phone nata ya kashe, tayi rok’on duniya yabata takira Munaya da innarsu amma k’ememe ya hana, yadai kira mata innar sun gaisa jiya da daddare, amma munaya yace ba yanzun ba. hawayene suka ziraro ta gefen idonta.
       Tun d’azun yashigo yake kanta tsaye bata saniba, tsigunnawa yayi saitin fuskarta yafara share mata hawayen, da sauri ta bud’e idonta, ganinsa yasata tashi zaune tana k’ak’aro murmushi damasa sannu da zuwa.
     Bai amsaba, sai zama dayayi kusada ita yajawota jikinsa ya rungume, “haba my baby yanzu kukannan bazai k’areba? ko har yanzu wajen yana ciwonne nasake had’a miki ruwan zafin ki shiga?”.
     Kanta ta girgiza masa tana kuma matso hawaye, murya na rawa tace “ina kewar Munaya”.
         Tausayi ta bashi, tareda mamakin tsantsar k’aunar da sukema juna itada ‘Yar uwar tagwaicinta, shikuma wlhy bayason kiran Munayar ne saboda karsu shiga hak’in Galadima, amma yanzu kam bashida mafita, yakai dubansa ga agogon falon, 11:49am, maybe zuwa yanzu sun tashi, wayarsa ya d’auka ya lalubo number Munaya yafara kira. cikin sa’a kuwa sai gata tashiga.
    Mik’ama Munubiya yayi, cike da d’oki ta kar6a tana murmushi tana hawaye, shi saima abin yaso bashi dariya.
  
     Ina cikin barci naji ringin d’in wayata, da k’yar na lalubota batareda na dubaba nayi picking kawai, a kunne na kara cikin muryar barci nayi sallama.
      Daga can Munubiya ta amsa mani.
     Ai zumbur namik’e zaune danjin muryar gudan jinina, “Sweetheart kece? Wlhy I Miss u so much ”. ‘nafad’a ina share hawayen dasuka ziraromin’.
       Itama Munubiya hawayen takeyi, muryarta na zuga tace “miss u 2 sweetheart, I love you I love you for ever”. sai kawai ta rushe da kuka tareda fad’awa jikin yaa Marwan dake kallonta tana rera kukanta.
     Hannu yasaka yana bubbuga bayanta yana murmushi, yayinda nima naketa maimaita mata kalmar I love you ina kuka.
         Wayar yaa marwan ya kar6a, muryarsa kawai naji yana fad’in “to kukan ya Isa haka kema, kar Galadima yagani ya d’auka munyi miki wani abune, sai anjima idan kin nutsu masake kiranki”.
      d’if ya yanke, batareda yajira amsa taba.
     Sai kawai nakuma ruahewa da kuka na fad’a saman filoluwan da suke zube a saman gadon.
     Galadima dake tsaye bakin k’ofar yazo dubani saboda  dangin mom da zasuzo mana sallama, saiya koma da baya bai bari na gansaba, zuciyarsa tana masa tunanin dawa nake waya? har nake jera masa kalaman I love u?.
       Ya d’an ta6e bakinsa, tareda kauda tunanin a zuciyarsa, to shi inama ruwansa, kwana nawane zai bani takardata na kama gabana.
         Falonsa yakoma ya zauna yana jan tsakin Aiken mama Fulani na d’azun data tuna.
    Yakuma jan tsakin yana gyara zamansa, dolene ya takama tsohuwarnan birki da wuri, inba hakaba tana neman Shiga masa hanci.
     Abinda yafaru d’azunne da safe kusan around 7:30, yadawo daga masallaci bayan yaje ya tadani yadawo d’akinsa, zaune yake a doguwar kujera a falonsa yana azkar kamar yanda yasaba a kowacce Safiya ta duniya. sarkin k’ofane yamasa knocking.
     “waye?” yayi tambayar batareda ya bud’e idanunsa dasuke a rufe ba.
     Sarkin k’ofar ya amsa da “nine ranka ya dad’e, dama Amintacciyar kuyangar Fulani Ce ke Neman iso”.
        Saida yaja guntun tsuka sannan yace tashigo.
       Babu dad’ewa saigata kuwa, saida tayi sallama a k’ofar yabata izinin Shiga sannan ta shigo, risinawa tayi (dan ya hanata durk’usa masa saboda ta manyanta sosai) tana fad’in “barka da Safiya ranka ya dad’e”.
    Idonsa yabud’e a kanta yace “kin tashi lafiya”.
      “lafiya lau ranka ya dad’e, dama Fulani ce tace azo a d’auki yankin jiya”.
      Bai fahimceta ba, dan haka yace “miyene hakan?”.
       “ka gafarceni ranka ya dad’e, yankin farin k’yallen mutuntaka da aka shinfid’a a gadonka jiya”.
          Bakinsa ya ta6e, ya maida kansa ya jingina tareda maida idonsa yanda suke, kusan minti 1 harma ta fidda ran zai amsa, saitaji yace “kije kawai, zan kawo mata da kaina”.
         Idanu tad’an zaro waje saboda mamakin zancensa, amma babu yanda ta iya, kowa a masarautar yasan murd’ad’d’en hali irinna Galadima, saidai akwaishi da kirki da yawan k’yauta. ta risinar da kai, “na barka lafiya ranka ya dad’e, afito lafiya”.
      Uffan baice mataba harta fice tarufo k’ofar.
      Azkar d’insa yacigaba dayi batareda ya maida hankaliba.
       Mom ce takirasa a waya, bayan ya gaidata cikin mutunci ta sanar masa gasunan zuwa sashensa suyi sallama, dan jirgin 1pm zasubi ya maidasu tasu masarauta.
     Wannan dalilinne yasakashi zuwa Sanar min, amma saiya Tatar ina Waya da fad’in I love you ina kuka kuma, shine yajuya batareda yayi maganaba.
           Kamar na sani natashi na gyara gadon fes, nad’anyi shara dukda babu wani datti, toilet nashige nayo wanka.
        Ina tsaka da shiri najiwo sallamar da wata murya ketayi tun d’azun, a gurguje na shirya naje na bud’e k’ofar.
         Yarane matasa a durk’ushe can gefe a falona, sai wad’anda suka d’an girme musu su biyu.
    Ina fitowa suka zube suna gaidani, abinda baka saba ganiba to, duk sai kunya ta kamani, nace “please Ku tashi minene ya faru?”.
       “d’aya acikinsu tace “ gimbiya ranki ya dad’e, ki gafarcemu mune masu miki hidima. ni sunana Alawiyya nice mai gyara miki makwancinki kawai da shiryaki, sukuma wad’annan zasu cigaba da sauran hidimominki, irinsu gyaran falo, girki, wanki, baki labari, da sauransu”.
       Babbar jaka uba, shirinma sai anmin kamar wata ‘Yar baby, nidai naga idi gaskiya, wannan wace iriyar rayuwacw haka?.
       “ranki ya dad’a zamu iya fara aikinmu?”.   Alawuyya takuma maimaitawa a aladabce.
      Kafin nabata amsa muka jiyo gyaran murya a abayanmu. dandanan naga sun juya suna kwasar gaisuwa, jikinsu har 6ari yakeyi.
      Hannu kawai ya d’aga musu, kafin yabud’e baki da k’yar yace, “miya faru ne?”.
       Alawuyya takuma rissinar dakai tace, “ranka ya dad’e mune masuma gimbiya hidima”.
      Shiru tamkar bazai amsaba, yad’an yamutsa fusaka yana gyara tsayuwa “wanene ya turoku?”.
          “ranka ya dad’e mama fulani ne”.
     Baice komaiba ya ra6a ta gefena zai wuce ciki, harya kusa shiga sannan yace, “zaku iya tafiya zan nemeku”.
       Atare suke fad’in godiya muke ranka yadad’e, ALLAH ya kiyayeka, yatsare bayanka da gabanka.
      To tunima yariga yashige, nikam tausayi suke bani wannan abun dasukeyi, nace “please kutashi kuje kawai”.
        “to ranki ya dad’e, godiya mukeyi……..
    Nidai juyawa nayi nashiga d’akin nima, dan banason wannan kirarin wlhy……………..????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button