NOVELSUncategorized
RAINA KAMA (BOOK 1) 23&24

????????2⃣3⃣
…………..A saman sofa na iskeshi zaune, ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana waya. Idanu ya d’ago yad’an kalleni ya janye.
kunyace takamani saboda babu ko gyale ajikina, gashi kayan sket da rigane, kamar munafuka haka nawuce inda akwatina yake da aka kawo da safe, nima farkawa nayi kawai na gansa a d’akin.
Gyale na d’auka na yafa, sannan naje bakin gadon na zauna ina sauraren wayar dayakeyi, abinda na fara lura da halayensa shine, shi mutumne marason hayaniya, komai nasa zaka sameshi a nutse yakeyi, yanzu haka a d’aki d’aya muke zaune, amma ba komai nakeji ba a maganar dayakeyi, ga jan aji tamkar wani mace, jinin mulki dake yawo a jikinsa ne ke k’ara masa k’asaita da izza…….
Gyaran muryar da yayce yasakani d’agowa na kalleshi, idonsa a kaina, Dan haka muka had’a idanu, kowa janye nasa yayi cikeda basarwa.
Saina samu kaina da cemasa “ina kwana”.
Saida yaja wasu seconds sannan yace, “kin tashi lafiya?”.
“Alhmdllh” kawai nace masa nayi shiru.
Shiru mukayi babu Wanda yasake magana, yanata aikin latsa wayarsa, nikam ina satar kallonsa da mamakin wannan halayya tashi, shi koma takura bayayi? ina dad’i dan ALLAH kai kenan kullum baki 6am????.
Kusan mintuna 5 muna a haka, bakajin komai a d’akin sai k’arar AC, ni dukma sanyin ya isheni. batareda ya d’agoba yace “mikike buk’ata akawo miki break fast?”.
ALLAH shi k’yauta, nafad’a a raina kafin nace, “ko miyema”.
Idanunsa ya d’ago yana kallona, baice komaiba ya janye ya mada ga wayar. sai kuma yasaka a kunne, “mom ki basu su kawo abincin ta tashi”.
Bansan mitace masaba daga can, naga dai yayi murmushin gefen baki tareda yanke wayar.
Ya kalleni yana gyara zamansa, tareda kuma shan mur alamun maganar da zaiyi important ce, “ki kimtsa su mom zasu iya shigowa a kowanne time, dan zuwa anjima zasu tafi, duk yanda dai zaki nuna musu wani Abu yashiga tsakanina dake kiyi, dan banason su tafi dawani zargi a ransu OK?”.
Duk da na fahimci inda zancensa ya dosa, hakan bai hanani yimasa kallo mamakiba, nace, “kamar ya ban ganeba fa ni”.
Shima kallon mamakin yamin, kamar zaiyi magana saiya fasa kuma, yad’an furzo huci a bakinsa kafin ya cije lips nashi da d’an k’arfi. tsaye yamike yana zuba wayoyinsa cikin aljihun ash d’in wandonsa, sannan yafara tafiya, sai da yakusan fita sannan yace, “ki nuna musu tamkar wata mu’amullar aure tashiga tsakaninmu, wannan shine kawai mafita, idan kin gama kizo kiyi breakfast”. ficewarsa ya ida yi.
Yayinda nikuma na sauke ajiyar zuciya, danni maganganun nasa duk sunzomin a cirkud’e, to mom d’in nasa ba’a gidan takeba kome? Sannan kuma ai mu yakamata muje mu gaisheta bawai ita tazoba aganina, mi hakan ke nufi?. banida mai bani amsata, dan haka namik’e a gadon ina sauke numfashi, inason kiran Munubiya amma ina tsoron yaa marwan. wayar innarmu nakira, amma a kashe, idona yacika da k’walla, murya na rawa nace “wayyo innarmu I miss u wlhy”.
jinake tamkar nayi tsintsuwa naganni a gida, dama ashe akwai randa zatazo na kwana Na tashi ba’a gidanmu tareda munubiya taba? gaskiya masu cewa aure da dad’i basuda kai wlhy, dan ALLAH ina wani dad’i anan?.
Da Sauri Na goge hawayena saboda jin maganar Samha a kaina, jikinta a sanyaye ta zauna kusada ni, nima saina yunk’ura natashi zaune ina murmushi da share sauran hawayen fuskata.
“Samha yaushe kika shigo”.
Kanta ta langa6e gefe cikin damuwa tace, “Aunty yanzu na shigo, miya sakaki kuka? ko Uncle Sam…. ne?”.
Murmushi namata, danni dariya wannan shagwa6ar tata ke bani, ko kad’an bata d’aukar kanta ta girma, “A’a Samha, ba shi baneba, ina kika shigene haka?”.
“ina nan, tun d’azun naso zuwa Amma mummy ta hanani, yanzu ma tare muke dasu mom, suna falo kisaka Al’k’yabba muje”.
Kallon jikina nayi, nace “bara dai na saka hijjab, ALLAH Alk’yabba d’inan nauyi takemin”.
Dariya Samha tayi, “lallai aunty ai Indai kina gidannan dole saikin sakata, sai dai indan kun taho india, yanzu mafa dole ki saka”.
Badan nasoba na d’akko Samha ta tayani sakawa, sannan muka fita bayan nafesa turarrurruka na masu dad’in k’amshi.
A zatona suna falona, ashe suna nashi, Samha na rik’e da hannuna tamkar wata ‘yar jagora har sashensa, Wanda sai yanzune nake d’an kallon wasu abubuwan, dukda face d’ina arufe take da hular alk’yabba. Sallama mukayi a k’ofar falon akabamu izinin shiga, gabana na dukan tara-tara muka shiga, duk zatona irin sunada yawa d’innanne, saina gansu su 5 kawai, kuma duk manyane, mom kawai na gane acikinsu, sauran ban sansuba, saikuma shi boss d’in yana zaune a kujerar mai zaman mutum d’aya kamar ma yana wayane. ban zauna akujera ba sai a k’asa, mom tayi saurin fad’in “a’a d’iyata tashi ki zauna saman kujera mana”. kaina na girgiza muryata a raunane nace “a’a nanma ya isa” sannan a ladabce na gaishesu. cikeda fara’a da sha’awa suka amsa, shi kansa uban gayyar saida ya kalleni, yaji dad’in girmamawar dana bama k’annen mahaifiyarsa.
Samha ta gwargwad’ama mom magana a kunne, wai ta iskeni ina kuka. murmushi kawai mom tayi, tasan kukan bai wuce na shiga kwaryar manyaba, ga d’an nasu dagani jarumine (aikam mom ragone tunda ba abinda kike tunanin bane????????).
Kallon Galadima tayi dake harar Samha, “gulmammiya mikike fad’a? tashi kibar falon nan”.
Tashi tayi tana tunzura baki, “wlhy Uncle Sam ni Vance wani abuba, Mom dan ALLAH wani Abu nace?”.
Murmushi mom tayi, tace “a’a bakice komaiba”.
Batareda ya kalleta ba yace, “naji, tunda kin rakosu wuce ki tafi”.
Fita tayi tana daddaga k’afafu, yaja guntun tsuka, yayinda su mom suke mata dariya da tsokana irinta kakanni, nidai kaina na k’asa nima ina murmushin rigimar ‘ya da Uba, duk dama har yanzu bansan yasukeba, naji dai tana Uncle kawai.
Bayan fitar Samha d’aya acikin matan ta kalleni, d’iyarmu cire hular kisha iska kinji, mu nan duk iyayenki ne, daina jin kunyarmu.
Babu yanda na iya, dole na zame hular Alk’yabba d’in, amma kaina na duk’e sosai yanda bazasuga fuskataba, nasiha mai ratsa jiki da 6argo suka Shiga mana daga ni har harshi, duk jikinmu sai yayi sanyi k’alau, nikam kukama nakeyi, Dan dama kad’an nake jira a ta6ani na fashe. sun dad’e sosai sannan suka ajiye min k’yaututtuka suka tafi harda shi domin musu rakkiya.
Bayan fitarsu saina shiga rera sabon kuka, saida nayi mai isata sannan natashi da nufin tafiya nawa d’akin, kallon falon nashiga yi, masha ALLAH, komai yayi a falonnan, kujerun Navy blue ne, sai labuloli da Carpet sun kasance Silver da kwalliyar k’ananun flowers blue, babu wani tarkace sosai, wani hotonsa ne yay masifar d’aukar hankalina, gaskiya hoton ya d’auku, yana sanye cikin kayan sarauta akan dokin dashima yasha kwalliya, murmushin dake d’auke a face nashi shine Yakuma k’awata tsarin hoto, ga hoton irin k’aton nanne kamar kamasa magana ya amsa maka.
Na juya na kalli d’ayan dake bangon kudu, shikam sanye yake cikin farin wando k’al da farar riga itama, ya tsuke k’ugunsa da bak’in belt, takalmansa da hularsa duk bak’ake, yana awani k’aton filine daya k’awatu da korayen ciyayi, hannunsa rik’e da wani k’arfe ga k’aramar boll a gabansa, nan ma fuskarsa washe da murmushi, har hakwaransa sun fito waje, a raina nace dama d’an wasan Golf???????? ne? kokuwa yasaka kayanne kawai?.????
Da sauri na juyo jin motsi a bayana, sai kunya ta kamani ganinsa tsaye hard’e da hannayensa a k’irji yana kallona, gudun karya zaci kallon hoton nake sainayi saurin cewa “dama kana buga Golf? ”.
Murmushin gefen baki yayi, yatako a hankali ya zauna a kujerar dake kallon hoton, shima idonsa na kan hoton, ya d’ora k’afarsa d’aya kan d’aya….
Jin yayi shiru yasani juyowa na kalleshi, a tunanina kobai ji baneba, ido muka had’a, kowa ya janye cikeda basarwa, saiya lumshe nasa tareda jingina da kujerar, tamkar anmasa dole yace “kinason wasanne?”.
Nace, “kusan haka, duk da bansan kan wasanba har yanzun”.
Murmushi naga yayi kawai amma baice komaiba.
Nima saiban sake cewa komanba na juya zan fita. idanu ya bud’e yabini da kallo harna fice.
Yana mamakin yanda bata da tsoro, zai iya cewa itace yarinya ta farko budurwa dakan iya masa magana kanta tsaye bada wani shakkuba atare da ita.
Tabbas a wannan fagen ya yaba mata, domin takafa tarihin da manyan ‘yan mata masuji da mulki da Kansu suka kasayi, akwai ‘ya’yan sarakuna da yawa dakesonsa amma sukan kasa fad’a masa, sunsha shan alwashi akansa amma da zarar sun had’u dashi sai alwashin nasu ya gudu, hakama ‘ya’yan manyan attajirai, kuma baisan abinda yasa sukejin shakkar tasaba, shidai kawai abinda yasani baya sakar musu fuska, to ita wannan tatsitsiyar yarinyar koda fuskar tasa takai hadarin gabas murtukewa bata Shankar masa magana, ya cige lips nashi yana ta6e bakinsa wanda shiyasan dalilin yin hakan.
★★★★★★
Mama Fulani tagama cika tayi fam da rainin wayon Galadima, ba’a ta6a angon dayay abinda Galadima yayiba a masarautar, duk randa ango zai shiga d’akin amarya za’a kai farin k’yallen dasuke kira (yankin mutuntaka) a shinfid’a agado, washe gari za’a aika a d’ako domin kowa yaga mutuncin da yarinyar takawo, sannan dolene kuma kakawota da safe ta gaida matan Sarki da Sarki kafin yafita fada, saikuma sauran jama’ar gida wad’anda suka kasance iyaye.
Amma saboda rashin mutuncin fand’ararren yaron can anje d’aukar k’yallen yace zai kawo da Kansu saboda shine shugaban marasa kunya na duniya, ta aika bayi masu hidima damata CID ya korosu wai zai nemesu, gashi ana neman k’arfe uku na yamma amma har yanzu baizo gaisuwa ba shida matarsa, sai bayintane ke sanar mata sunga yarako dangin uwarsa lokacin dazasu tafi, amma ita tunda yazi bikinnan bama ta sakashi a idonta ba sai ranar da akayi Mother’s and tarbar amarya event ta gansa awajen. yaron nanfa yana shigar mata hanci da yawa fa, bari taga iya gudun ruwansa da k’arshen wutsiyar iskancinsa, ai ko ubansa bai Isa mata abinda gagararren yaronnan ke mata ba a gidannan.
★★★
Shi baima San tanayiba, Dan tun bayan fitar Munaya daga sashensa yatashi zuwa masallaci sallar azhur, ana idarwa ko yarda su had’u da Sarki baiyiba ya shiga gida, shigewarsa yay bedroom, yayi kwanciyarsa domin yasamu yad’an huta, jikinsa duk ciwo yake masa, saboda ainan-ainan na al’adar biki, dukda yasan ko Rabin hidimar da harun yayi shi baiyiba, saima ka rantse Harun shine angon wlhy.
Bai wani dad’e da kwanciyar ba barci ya kwasheshi hankalinsa kwance.
★★★★
A gidanmu ma dai bak’i kowa yakama gabansa, an barsu daga su sai su, da daddare Abba yace ashirya da safe kowacce abita da akwatunanta, shi baiga dalilin ajiya ba.
Duk sun amsa da to, amma kowacce burinta ace da ita aka kai nawa, Dan sunason suyo kallon kwaf, basu gamsu da labarin da ‘yan kai amarya suka fad’aba akan gidana Dana munubiya, su a tunaninsu ma an aurenine domin a maisheni baiwa, yaushe nakai matsayin da har d’an Sarki guda mai sarautar Galadima zai gani yace yanaso, bayan lungu da sak’on hotunan mun gama zagaye duniya ni da shi.
K’ilama da gaske yagama lalatani d’in.
Haka dai sukaita gutsiri tsomarsu da kushe irinta masu hassada, duk da wasu abubuwan suna dawo kunnen innarmu batako damuba, ita dai babu abinda zatace ma ALLAH sai godiya, tunda ‘ya’yanta kowanne yasamu matsugunni, yanzu saita maida hankalinta ga ibadar ALLAH da tarbiyar yaranta biyu maza dasuka rage, sune basu gajiba indai tozarcine.
★★★★★
Zuwa la’asar mama Fulani tafara k’ananun magana akan rashin nuna shaidar Munaya takawo budurcinta, dakuma rashin fitowarsu gaida mutane.
ALLAH Sarki Aunty Mimi sai abin ya dameta ganin yanda aketa k’ananun magana a masarautar, hakkane yasata nufar sashen Galadima, babu zancen jiran a mata iso, sarkin k’ofa yabata hanyar tashiga.
Tun’a falon farko daya raba sashina da nasa tace bayinta su jirata.
Babu kowa a falonsa, Dan haka ta zauna tad’au waya ta kirasa, dan batasan halin dayake acikiba, baikuma kamata tashiga kai tsayeba, balle yanzu yanada mata.
Fitowarsa kenan daga wanka saboda tashin dayayi a makare baisamu sallar la’asar ba, sai anan d’aki yayita sannan yashiga wanka. Wayar ya kalla yayinda yake goge ruwan fuskarsa, ganin aunty Mimi yasashi picking call d’in, saiya saka a Hans free yana cigaba da hidimarsa.
“my aunty kin 6uya fa”.
“na 6uya ko ka 6uya my k’ani, gani zaune ai a falonka”.
“kai haba dai? to bani kamar 5minutes na shirya nafito”.
“ok babu damuwa”.
Bai wani dad’eba yafito sanye cikin farin boyal mai shara-shara, yayi k’au sosai, sai zabga k’amshin turarensa yakeyi na koyaushe. daga shi har Aunty Mimi suka sakarma juna murmushi, ya zauna kujerar dake kallonta yana fad’in “sweet aunty na ni kad’ai”.
“anya kuwa yanzu bamu raba da Munaya ba my k’ani?”.
Murmushi yayi wadda har hak’waransa na bayyana, ya d’ora k’afafunsa d’aya kan d’aya yana gyara zama, “in haka kikeso my Aunty saiku raba ai”.
dariya tayi tace, “nama bar mata. wai kasan mike faruwa a gidannan kuwa?”.
“A’a saikin fad’a”.
“tun kafin tafiyar su mom aka fara k’ananun magana a masarautar nan, wai anzo kar6ar yankin mutuntaka ka hana”.
“mtsoww!” yaja tsaki yana jingina da kujerar da lumshe idanunsa, “Aunty Mimi dan ALLAH karki biyema wannan jahilcin kema” yabud’e idonsa akanta, ransa a d’an 6ace yacigaba da fad’in “kawai da Wanda yakai sanin sirrinka da Wanda ma baikaiba wai duk sai sun sani?, a wace ayar alkur’ani ko hadisi akace dan ka tare da matarka a daren farko sai duniya ta sani?. ita mai aiko a d’auki k’yallen ince agaban kowa na gidannan lokacin da abunnan yafaru take fad’in bakinta bazai iya maimaita k’azantar danayiba?, to kuma tunda tariga da tasan nayi k’azantar abaya miye na aiko da wani k’yallen banza da wofi? wlhy fa suka kaini k’arshe zan shuka rashin mutunci kinji na rantse”.
Shiru Aunty Mimi tayi tana kallonsa, tasan ransa yakai k’ololuwar 6aci, dan Galadima yanada hak’uri sosai, gudun kar matsala ta biyo saboda ciwonsa saita kwantar da murya, “haba my k’ani kwantar da hankalinka mana, ai abun bana 6acin rai baneba kaji, haba my habibi”.
“Aunty Mimi nagaji ne wlhy, rashin mutuncin masarautar nan yafara isata, nifa komai zan iya kawoshi karshe a wannan karon”.
Tasowa tayi ta zauna kujerar gefensa, ta kama hannunsa “please cool down mana my man, kaci gaba da hak’uri tamkar yanda kakeyi abaya, ALLAH yana tare da masu hak’uri, Momma bazataji dad’in wani Abu yabiyo bayaba, hakama Abie duk da yana a kwance zuciyarsa zatayi kunci, kansu ai sukema wa, yanzu ina k’yallen? ”.
Iska ya furzar daga bakinsa, sannan ya nuna mata bedroom d’insa da hannu.
Tashi tayi tashiga, a saman sofa taga k’yallen dan haka ta d’akko ta fito. zama takuma yi a kusa da shi, “my K’ani ina zamu samu syringe?”.
Idonsa yabud’e ya kalleta, “syringe kuma? mizakiyi dashi?”.
“Sameer duk abinda zamuyi mu kare mutuncin mahaifanmu da lafiyarka muyishi mu zauna lafiya. yanzu dai kasa wani ya kawo mana”.
Baice komaiba yajawo wayarsa yakira Muftahu, buk’atarsa ya fad’a masa sannan ya yanke wayar batareda yajira cewar Muftahun ba.
Wata hirar Aunty Mimi ta d’akko masa, tun yana basar da ita, har ya fara tanka ta, daga nan suka cigaba da hira.
Knocking d’in k’ofar akayi, Galadima yace, “waye”.
Sarkin k’ofa yace, “ranka ya dad’e yalla6ai Muftahu ne yazo yace amasa iso”.
“kace ya shigo”.
Da sallama Muftahu ya shigo, ya rissina ya gaida Aunty Mimi sannan yabama Galadima hannu suka gaisa cikin musabaha.
Ledar hannunsa ya mik’ama Galadima, “no kabama aunty mimi”.
Aunty Mimi ta kar6a ta fiddo da Syringe ta 6are daga ledar, had’awa tayi tare da Allurar sannan ta janyo charger ta d’aure tsintsiyar hannunta, Galadima da Muftahu dai kallonta sukeyi, allurar zata tsira Galadima ya rik’e “mizakiyi hakane Aunty Mimi?”.
“Sameer! wannan itace kawai mafita, kabari kawai na d’iba a saka musu, da safe saika basu”.
lips d’insa ya cije da k’arfi, yashiga kwance charger data d’aure hannunta, “ki barsa zan saka musu nawa, yanzu ma koda an saka zai bushene, dan yayi wuri ai”.
“karfa kazo ka shukani”.
“karki damu zanyi, kema kin sani ai, tunda na amsa to zanyin”.
Mik’ewa tayi tana fad’in “shikenan to, bara na duba k’anwata itama”.
Kansa kawai ya jinjina mata, yayinda muftahu yamata sallama ta fice.
“wai mike faruwa? ranka ya dad’e”.
Tsaki Galadima yaja, yay shiru kusan minti 2, har Muftahu ya yanke tsammani da samun amsa. labarin komai yabashi.
Shima Muftahu tsuka yaja, “wai dan ALLAH yaushe za’a daina jahillar al’adarnan a masarautar nan? abinda ba addini ya wajabtaba sun kama sun rik’e, kuma duk matsalar tsohuwar nan ce wlhy, masarautu nawa ne suka daina wannan abun, amma mu takafa ta tsare, ALLAH lokacin da akayi na Uncle Hayatudden, kunya abinnan yabani saboda shi kawai nata6a gani, sashe-sashefa haka akaita nuniyar abinnan a masarautar nan wlhy”.
Wani mugun tsuka Galadima yaja saboda haushi da abin yakuma bashi, fitarma da yay niya saiyaji yafasa.
★★★
Ni bansan mike faruwa ba ma, ina d’aki kwance duk kewa da kad’aici sun gallabeni, ga wayata babu caji saboda na manto cajan a gida.
Nayi zurfi a tunani naji ana sallama. firgigit nayi sannan na amsa, hijjab d’ina najawo na saka, ina k’ok’arin tashi tashigo. da Sauri na mik’e ina mata sannu da zuwa, dan nariga da na shaidata itace aunty Mimi. rissinawa nayi na gaidata, ta amsa cikeda fara’a sannan ta zauna. mik’ewa nayi na nufi freight domin bata ruwan amma saita dakatar dani ta hanyar kamo hannuna.
“no k’anwata barshi kinji, yi zaman ki, ya zaman kad’aici da bak’unta?”.
Kaina a k’asa nayi murmushi kawai, sannan nace “Alhmdllh aunty”.
“masha ALLAHU k’anwata, babu dai wata matsala ko?”.
Kai na na d’aga mata alamar babu, daga nan mukayi shiru saboda rashin sabo.
Zuwa can nace, “ina Samha?, tun d’azu tace zata dawo amma har yanzu?”.
Murmushi tayi, tace, “sun fitane itada Sauban tun d’azun, amma nasan suna hanyar dawowa kam”.
“Ayya ALLAH ya dawo dasu lafiya”.
Ta amsa da amin tana mik’ewa. har falona namata rakiya, inajin dad’in yanda take nuna tana sona.
*******
A can kuwa bayan Muftahu yafito daga wajen Galadima sai yayi murmushi, tabbas yasamu hanyar dazata zame masa tsanin *CIKAR BURINSA*, da wannan kawai zai iya cin galaba akan Galadima.
Da wannan tunanin ya hau mota yabar masarautar gaba d’aya.
Mikake k’ullawa ne Muftahu?????
★★★★★★
Bayan sallar isha’i ina zaune ina karatun Alkur’ani Galadima ya shigo, ban daina ba saida na kai aya sannan, na d’ago domin gaidashi sainaga idonsa a kai na.
Janyewa nayi nace “barka da dare”.
Bai amsaba cewa kawai yayi “tashi ki shirya zamuje gaisuwa cikin gida”.
Nima sai ban amsa shiba namik’e kawai na maida Alkur’anin inda na gansa. tashi yayi yafita danya bani damar shiryawa. banja wani lokacin mai tsayiba nafito cikin Alk’yabba, tsaye na iskeshi a falona, batareda yace uffanba yafara k’ok’arin fita, nima sai nabi bayansa batareda na tanka d’inba……………..✍????
????mun tafi sashen mama Fulani, maison jin yanda zata kaya saiya biyoni.
⛹????♀⛹????♀⛹????♀
Barka da juma’a????????????
*_YA ALLAHA KA GAFARTAMA IYAYENMU_*????????????
*_Typing????_*
*_HASKE WRITERS ASSO…????_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_
*_♦RAINA KAMA……!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
????????2⃣4⃣
………… Tunda muka fito masu hidimar sashensa suketa zubewa suna gaishemu, hannu kawai yake d’aga musu, nikam ma ba amsawa nakeba.
Wata mota aka bud’e mana muka shiga, mamaki ya kamani, shin ba’a cikin gidan bane?. banida mai bani amsa dan haka nayi gum.
Duk da darene muna ganin bayi dake yawo tsilli-tsilli, ga ko’ina kwanyar da haske, a k’ofar wani sashi ya tsaya da motar.
Kallona ya juyo yayi, cikin muryar nan tasa ta k’asaita yace, “basai na fad’a mikiba, kinsan yanda ya kamata ace kowa ya ganmu, nan sashen kakarmu ne mai suna mama Fulani ”.
Kai na na gyad’a masa, sannan muka fito saboda anbud’e mana dama tuni.
Tunda muka fito ake kwasar gaisuwa, nikam sai binsu da kallon tausayi nakeyi, su shikenan a bautama wasu zasu k’are, basu da wani ‘yancin Kansu……
Tunanina ya kakare, lokacin danaji tattausan hannunsa cikin nawa, kowannen mu saida yaji shock, nad’an rumtse idanuna, yayinda shikuma ya cije lips.
Saida aka mana iso sannan muka shiga. kata faren falone na alfarma, iyakar k’yau da tsaruwa yayi, saikace ba falon tsohuwa ba, ga k’amshin turare na musamman na tashi,.
Bafulatanar tsohuwace mai jikin fulanin asali, dankuwa akwai k’yawu iya k’yawu, tabbas wannan a zamanin k’uruciya anyi asalin k’yak’yk’awa, sai dai gajarta tamata tsiya kam????????.
A kishin gid’e take, yayinda hadimai ke zagaye da ita, kowanne da aikin dayakeyi. Shigowar mu tasakasu kowa tasaki tanemi hanyar fita kamar yanda tabasu umarni. Bai saki hannuna ba har muka k’arisa gabanta, yayinda ita kuma idonta ke akan hannayenmu dake sark’e dana juna ko k’yaftawa batayi.
Saida ya taimaka min na zauna bisa tattausan carpet d’in dake falon, gaf da mama Fulani kad’an, sannan shima ya zauna kusa dani.
“Ranki ya dad’e barka da hutawa”. Nima sai bayi saurin gaisheta.
Cikeda izza da tak’ama ta d’ago idanu tana kallonmu, a raina nace (ga wadda tafi Galadima izza ashe, ko dai itace sarkin?????)..
Kamarma bazata amsaba, saikuma naga ta gyara zamanta, idonta a kaina tana k’aremin kallo, “sai yanzu ka gadamar zuwa gaida mutanen saboda giyar amarci na kwasarka?”.
Wani k’asaitaccen murmushi Galadima yasaki, Wanda ban ta6a Sanin ya iya shiba, “kusan haka ranki ya dad’e, kinsan masu iya magana kance amarya kota buzuzu???? ce d’okinta akeyi, bare ni kuma mai wannan dirarriyar macen doguwa k’yak’yk’yawa abun buk’atar kowanne namiji”.
Idanu na zaro domin mamakin maganarsa, kakarsa yake fad’ama hakan?. maganarta Ce yaja hankalina itama……..
Saida ta yamutsa fuska tana guntun murmushi, duk da maganar Galadima ta daki zuciyarta kwarai da gaske, ta kalleni da k’yau, “to ke dirarriyar mace abinda mijin naki yafad’a gaskiyane kuwa? dan mu bamu gani a k’asa ba”.
Gabana yashiga fad’uwa, dan bansan mizan Ce mataba, 6oyayyiyar ajiyar zuciya na sauke saboda jin Galadima na bata amsa, dukda kuma amsar tashi itama tazomin a rud’ani.
“to ranki ya dad’e miye amfanin gani a k’asan?, tunda nida ALLAH ya halattama ganin naga kayana”.
Yanzu kam a kufule tace, “a titi ko?”.
Ya murmusa yana kallona, “tunda Nina gani ai babu damuwa ranki ya dad’e, koda a titinne kuwa, bawai dole bane saike kin gani a gida ba”.
Rasama mizata cemasa tayi, sai can tace inbanga na matarka ba ai naga na Uwarka da yayar uwarka ko?”.
“well hakanefa ranki ya dad’e, amma nasan kafin kiga nasu, kema anga naki, so banga laifin hakanba ai”.
Kutt, tsantsar 6acin rai na hanga a fuskar mama Fulani kuwa, nidai kam sun d’aure kai na da wannan zantuka nasu masu kama da gugar zana, wannan dai baza’a kirashi wasan jika da kaka ba, dan baimayi kama da wasanba, nataso gidanmu na yawa da tun ina k’aramata nagama sanin miye habaici miye gugar zana ko shagu6e. tabbas naji a raina akwai lauje cikin nad’i gameda wannan masarautar, dan tundaga zuwana zuwa yanzu naci karo da abubuwan mamaki bila adadin, ashe ba’a rabu da bukarba an haifi habu kenan, nabaro guguwar gidanmu na fad’a tarnak’in gidan sarauta mai wahalar zama, ni dai ALLAH ka taimakeni komai yafita filima kafin shekara d’ayarnan na kama gabana, bazan iya da kitimurmurar wannan gidan sarautar ba gaskiya.
Mun mata sallama muka fito tana jifan Galadima da kalmar “fand’arrare mara mutunci, wlhy zanyi maganin kane, amma zan kira uwar taka naji idan itace ta baka wannan sak’on kabani”.
Baice uffanba sai murmushi daya saki yakamani na tashi, munje bakin k’ofar zamu fita yajuyo yana kallonta, salute nata yayi sannan yace, “da safe za’a kawo miki jinin budurcin matata OK?”.
Gaba nane yafad’i, da mamakin yanda yay furucin babu ko kunya bare shakka. nidai kam narasa yanda zan fassara wannan lamari, har muka shiga motar ina juya zantuttukansu a raina.
Mun isa sashen dayafi kowanne sashe girma a gidan, sannan ya had’u iya had’uwa shima, Hadimai sunfi yawa anan fiye da ko ina, anan d’inma dai gaisuwar ce aketa mana.
Mun isa wani k’ofar mai azabar k’yau, matar dake zaune a k’aramin falon farko ta rissinar da kanta tana fad’in “lale marhabin da Galadima, Gimbiya barkanki da zuwa fadar masarautar gagara badau”.
Murmushi nayi na jinjina mata kai, amma gogan naku fuska a d’inke yace “Amana iso ga mai martaba idan bai kwantaba jakadiya”.
“angama ranka ya dad’e, 6auna mai tafiyar k’asaita, bajimin zaki sa d’auka sa yak’i, magajin masarautar gagara badau……..
Hannu ya d’aga mata alamar ya isheshi haka..
Ruf tarufe bakinta sannan tashige wata k’ofar, kusan mintuna 5 saigata yafito tana fad’in mu shigo.
Jama’a karkuce nayi k’auyanci, tabbas ni Munaya yau naga daular duniya, dolene sarakuna suringa tunanin kamarma bazasu mutuba, yo irin wannan daular inbakayi yak’i da shaid’anba ai bautar ALLAH ma saika bari, dole suke halaka juna akan sarauta kam lallai.
Wanda nakeda tabbacin shine sarki yana kishingid’e a kilisarsa, idonsa bisa TV yana kallon labarai, sai wata hamshak’iyar mace dake cikin ado na kece raini da alfarma zaune a gefensa, koba a fad’a makaba kasan matar sarkice.
Yanzu ma har gabansu muka isa hannun na cikin nasa, dukda mutsu-mutsun kwata danakeyi yak’i saki, saima k’ara damk’ewa da yayi, nesa dasu k’ad’an muka zauna, cikeda girmama Galadima yace “barka da dare Abba?”.
Murmushi sarki yayi, yace, “Galadima sai yanzu ake ganinka?”.
Murmushi yayi yana shafa gefen wuya alamar jin kunya, ya kalli matar yace “barka da hutawa ranki ya dad’e”.
Fuskarta d’auke da fara’a ta amsa masa..
Nima na rissina na gaidasu cikin tsantsar ladabi.
Sun kar6amin fiye da yanda nayi zato, matar tamik’amin hannu alamar na matso gareta, banyi musuba na matsa, hannuna takama tana murmushi, “yaya bak’unta gimbiyarmu?”.
Muryata a kunyace na amsa da “Alhmdllh ranki ya dad’e”.
Murmushi sarki dake kallonmu yayi, ya maida kallonsa ga Galadima da shima idonsa na kanmu. “yarona babu dai wata matsala ko? ”.
“Alhmdllh Abba babu komai”.
“to Alhmdllh ai haka muke fata mu dama, ALLAH yayi muku albarka, yabamu zaman lafiya na har abada da zuri’a d’ayyiba, wadda musulunci da Muslims zasu alfahari da ita…………” Nan yashiga mana nasiha mai ratsa jiki da 6argo, har lokacin hannuna na rik’e ga matar sarki, wadda k’amshin turarenta kemin dad’i sosai a hanci.
Mun dad’e anan, dan sai kusan 9pm muka fito, tare da gagarumar k’yauta ta mukullin mota da sarki ya bani, matar kuma tace zata aikomin da tata insha ALLAH.
daga ni har Galadima munyi godiya sannan muka fito, sai juya keys d’in nake ahannu inajin wani makahon dad’i, wai nice da mota har biyu, yanzu Abbana da Dady sun samu kenan, saura baba k’arami, dan nikam babu abinda zanyi dasu, iyayena zan baiwa.
Daga nan munje 6angaren sauran Matan sarki, sai kuma na k’annen babansu Galadima d’in, mune har sashen da aunty Mimi ta sauka,, k’yaututtuka dai nasamesu sosai, harda masu sark’ok’i da sauransu, mun dad’e annan fiyema da ko ina, dan har 12 muna can, sunata hira tsakaninsu, danni dai ban iya cewa komai, sai sun sakoni ne nakanyi murmushi, musamman Sauban sarkin tsokana da Samha sarkin surutu, galadima kam ba komai yake tankasuba, shida aunty Mimi ke maganarsu jefi-jefi, khaleel ma sanda mukaje yayi barci. saida aunty Mimi tace mutashi muje sannan muka dawo namu 6angaren.
Sai da yarakani har d’akina sannan ya juya yafita batareda yace uffanba.
Binsa kawai nayi da kallo ina sauke ajiyar zuciya. Ni ban ta6a ganin murd’ad’d’en mutum irin wannan mutuminan ba, wlhy miskili yafishi dad’in zama, danshi na lura ba muskili baneba, tsabar jin kai ne kwai ke d’awainiya dashi.
★★★
Shikam har yayi shirin barci yagama yay shafa’i da wutiri maganar Mama Fulani na caccakar masa rai, ya murmusa kawai saboda takaici, ya zauna saman kujera d’akin, Syringe d’in d’azu ya d’akko da k’yallen yana jujjuyawa a hannu, wani sashe na zuciyarsa na cewa kawai yayi dabaran Aunty Mimi, wata kuma nacewa kar yayi tunda ba addini baneba, koma Dan ya k’ular da zuciyar mama Fulani, to amma kuma ita yarinyar za ana kallonta wani iri ai kuma a masarautar, harma sudunga tunanin ta zubar da mutuncinta a wajene kamar yanda mama Fulani tace, gara yayi kawai dabarar Dan fatansa harsu rabu baya son wani abu na family d’insa ya shafeta. Wannan shawarar da zuciyarsa ta yanke masa yasashi jawo charger ya d’aure hannunsa, jijiya ta bayyana, ya rintse idonsa yayinda ya tsira allurar, cikin cije lips yaja jinin kad’an sannan ya zare ya danne da auduga yanajan tsaki, charger d’in ya kwance yay wurgi da ita saikace itace tamasa laifin????????.
d’aukar gyallen yayi ya yamutsashi da hannu duk yayi Squeezing sosai sannan ya matse jinin ajikinsa yad’an yayyarfa bayan yazuba shi awaje d’aya da yawa. sai wani yamutse fuska yakeyi tamkar yaga kashi, kokuma jinin ba daga jikinsa yafito ba. ya ajiyeshi gefe sannan yamik’e yafito, a duzben d’in falo ya saka syringe d’in da kad’ar yakoma ciki, saida ya wanke hannunsa sannan ya haye gadonsa ya kwanta yana wani 6ata rai.
Nima can bayan na kammala hidimata kwanciyar nayi cikeda kewar ‘Yar uwata, yauma nadad’e banyi barciba, sai daga baya ya saceni.
Washe gari bansan miya faruba naji busar algaita na tashi a k’ofar sashenmu, yayinda aketa cillara gud’e-gud’e dake tashi, ina niyar fitowa domin ganin abinda ke faruwa Galadima yashigo da d’an hanzarinsa, hannunsa d’auke da k’aramin tire da kofin shayi akai. “hau gado ki kwanta” yay maganar yana ajiye kofin a table d’in gaban gadon.
“miya farune?”. na tambaya cikin binsa da kallo.
“ok zauna tambayata har su shigo ciki, oya malama ki hau”.
Nidai duk mamaki ya isheni, kamar wadda aka make haka na hau gadon na zauna, kallon face d’ina yayi yaga babu wata alamar dawani zaiga nashiga wani hali, dolene ya canja yanayina kenan idan har yanason ya tsira daga kwakwaf d’in wannan shirmen kafin su shigo.
Kawai sainaga ya hayo gadon shima, kuma kaina yayo gadan-gadan, na bud’e baki da nufin tambayarsa dalili, kawai naji bakinsa cikin nawa. tsorone ya kamani da fargaba, sai kawai nahau dukan bayansa da k’ok’arin turesa, haka dama yakeso, yazam nayi yunk’urin kwatar kaina har nad’an jigata yanda kowa zai d’auka wahalar daren jiyanne. kuma rikicewa nayi saboda wasa daya fara da wasu 6angare na jikina,, so kawai nake na kwaci kaina awajensa, tun ina iya yunk’urin turesa harna kasa, dama nima nasan ganganne na iya da wannan basamuden mutumin???????? (munaya tafad’a ba niba????⛹????♀).
Sai da yaga nayi lakwas ina hawayene kawai na daina tureshi sannan ya d’agani yana sauke numfashi, nikam saina kuma fashewa da sabon kuka, (kai jama’a Galadima akwai bariki????????) yanajin takun isowar su Fulani da kirarin kuyanginta sai yayi saurin jan bargo ya rufamin zuwa cikina, yawani kwantar da murya yana fad’in “please my jannat kiyi hak’uri hakanan, kukan ya isa kinji, tun daren jiya kike Abu d’aya, haka ai kowacce mace tayi sannan tazama uwa, ALLAH dai yayi miki albarka, kifad’amin wace kauta kikeso saboda tukuycin budurcinki daki kawomin har gidana”.
Idanu nad’an zaro saboda tsorata, mi wannan gayen yake nufi? wai ko dai Galadima yana shaye-shayene ban saniba, abunda yazo yamin daban sannan yakuma d’akkomin wani zancen daban………
Gyaran muryar da akayice yasamu waigawa ni da shi, kakarsa ce ta jiya a atsaye dawasu mutane biyu, gabana ya fad’i da matsananciyar kunyar su, Dan inada tabbacin sunji ko sunga abinda yamin, ko dai saboda su yake wannan abun? da sauri naja bargon na rufe fuskata saboda kunya.
Yayinda shikuma ya kalli mama Fulani yana wani susar gefen wuya kamar gaske, “o ranki ya dad’e kune? bar kanku da zuwa Ku shigo mana, saima Ku tayani lallashi ai”.
Matannan buyu gud’a suka callara a tare, yayinda mama Fulani ta kafama Galadima idanu, alamun tuhuma. kansa ya d’ago shima suka kalli juna ya sakar mata wani lallausan murmushi, kafin ya janye idonsa ya maida a kaina danake k’udundune cikin bargo.
d’aya cikin matan ta rissinar da kanta, cikin girmamawa tace, “Ranka ya dad’e ko zaka bamu waje mu k’imtsa ta?”.
Kallonta yayi, fuskarsa d’auke da murmushin Dana sakama suna na rainin hankali, cike da k’asaitarsa yace, “na hutasheku jakadiya, danni tun a daren jiya na gyara matata”.
Mama Fulani dake kallonsa a zuciyarta tace amma dai yaronnan d’an rainin wayone wlhy, gaba d’aya ya shirya komansa dai-dai ta yanda babu wanda koda ta k’aryata zai yarda da ita, Dan tabbas tasan duk k’arya yakeyi gameda wannan k’yallen, gashi lungu da sak’o na gidan angama nuna k’yallen, saboda ma ya raina mata wayo ba 6angarenta aka kaiba, sashen matan sarki ya aika da k’yallen, zancennan ma da akeyi ita bataga k’yallen ba har yanzun, Dan ba’a kai mataba, kowa ya d’auka daga sashenta ya fito, tunda ita ake fara kaimawa tagani sannan Matan sarki.
Had’a ido sukayi da Galadima, bakin ya ta6e mata, tareda d’age gira sannan yasaki murmushin Dake k’ular da mama Fulani aduk lokacin da yayisa.
Ta had’iye wani yawun bak’in ciki tareda kauda kanta gefe, su jakadiya kam tuni sun yi nisa wajen kar6o k’yaututtukan da kuyangin kowane sashe ke kawowa daga Matan gidan da iyaye, duk abama Munaya.
Dole mama Fulani ta k’arasa gaban gadon tasakama munaya turare da Sanya mata albarka tamkar yanda al’adar gidan ta tanadar, sannan takama hannunta ta saka mata bangles na goal masu k’yau da d’aukar idanu. Ta shafa kan munaya tana murmushin yak’e. sannan tadawo gaban Galadima shima takama hannunsa ta d’aura masa agogon Azurfa mai k’yau.
Salute nata yayi yana fad’in thanks my sweet Granny ”.
Uffan batace masaba tajuya tafice daga d’akin. yayinda su jakadiya suka take mata baya.
Suna fita ya sauke ajiyar zuciya tareda dafe kansa yana jan tsaki, nima kaina na bud’e amma nakasa tashi saboda kunyarsa data dabaibayeni.
Kusan mintuna 5 muna a haka, ni inata hawaye da jamasa ALLAH ya isa a zuciya, ga la66ana sai zugi sukemin saboda Sumbata d’inma na mugunta yamin. shikam yana dafe da kansa har yanzun yana sauraren kukan danake rairawa.
Zamansa ya gyara ya juyo yana kallona, fuskarsa a matuk’ar d’aure yace “tashi ki zauna muyi magana”.
Yanda yay maganar yasani tashi zaune batare da na musaba.
Yad’an kalleni ya janye idonsa sannan ya mik’amin Handkerchief d’insa daketa tashin k’amshi alamar na goge hawayena. Kamar bazan kar6aba dai saikuma na kar6a na goge fuskata.
Nanma shiru mukai nawasu mintuna da basufi 2 ba, nakula magana yakeson min amma yanata mulmulata a zuciya saboda jin kai, kuma d’agowa yayi ya kalleni saikuma yay gyaran murya kad’an, “em kiyi hak’uri, bamuda wata mafita sai wannan, munada wata kidahumar al’adane a masarautarnan, dolene randa katare da matarka sai kowa yasani ta hanyar ganin jini ajikin k’yallen da aka shinfid’a muku a gado. mukuma namu auren yasha banban dana saura, banida niyyar zalintarki na maidaki bazawara sannan na sakeki, inason idan mun rabu duk mijin daya aureki yasameki cikin mutuncinki, shiyyasa bazan aikata abinda suke buk’atar ba. ajiya anta surutu saboda bamu bada wannan shaidar ba, shiyyasa a Daren jiya nayi wata dabarar daban, fitowata kenan daga wanka najiyo busar algaita da gud’a alamun k’yallen yagama zaga masarautar, shiyyasa nayi azamar d’akko coffee d’in da aka had’amin zansha nanufo nan dashi, Dan Muftahu yakirani ya sanarmin zafa azo har sashena domin sanyamiki albarka da k’yaututtuka dakika samu saboda kin kawo mutuncinki, yanayin dana ganki nasan zasu gane shirina, shine dalilin yimiki wannan abun dan fidda zuciyarsu daga zargi, karki d’auka nayi mikine da niyya koki kalleni cikin mutane masu sa6a alk’awari”.
yana gama fad’a yamik’e zai yafice, nidai kaina ak’asa jinake tamkar namasa masifa amma kwarjininsa ya hanani, saida yaje bakin k’ofar zai fita sannan ya kuma furta “kiyi hak’uri, Sameer baya zalunci”. ya ida ficewarsa kawai.
Duk da na yarda da abinda ya fad’a, hakan bai hanani rushewa da sabon kuka ba, nace mugu kawai ALLAH ya isana wlhy, na shafa la66ana da da haryanzu zugi sukemin suda k’irjina wlhy, dan tsabar mugunta shine yama tsaya iya bakin amma harda wani wajen, ALLAH ya isana nidai.
????????kujifa, mutum da sadakinsa Munaya ke kiransa da mugu da jamasa ALLAH ya isa????, yau munga auren Contract readers????⛹????♀⛹????♀.
Tunda abunnan yafaru bamu sake had’uwa da shiba a ranar da yinin washe gari , kullum dai Samha kan kawomin abinci tareda kuyangin Aunty Mimi.
★★★★
Bayan sallar isha’i damuwa da rashin jin innarmu da Munubiya ya gallabi zuciyata, jinai bazan iya daurewa ba, dan haka na yanke shawarar zuwa na rok’esa ya aramin charger kona samu nayi charge wayata, duk da ma banida isashen credit aciki. na d’au turare nad’an fesa kad’an sannan nazura dogon hijjabi nafita zuciyata na d’ar-d’ar.
Na dad’e k’ofar falon tsaye ina tunanin yanda zan shiga, daurewa nayi nai Knocking, wata murya naji ta amsa sa6anin tasa, akace “waye?”.
Saida gabana yad’an fad’i, cikin rumtse idanu nace “nice”.
Galadima dake kwance cikin kujera idonsa a lumshe yana sauraren Muftahu yabud’e idonsa da sauri.
Shikam muftahu cewa yayi “bismillah ranki ya dad’e, ki shigo”.
Na tura k’ofar ahankali na shigo da wata sabuwar sallamar, Muftahu ne kawai ya amsa cikin washe baki, (yayinda k’asan zuciyarsa ke wata iriyar murna ganin shirinsa zai tafi dai-dai kenan). Galadima kam idanu kawai ya zubamin cikeda mamakin miya kawoni?.
Gaisawa mukayi da Muftahu cikin mutunci. saiya mik’e yana fad’in “ranka ya dad’e nikam na wuce, zuwa Safiya zamu k’arasa maganar kawai”.
Kansa kawai ya d’agama Muftahu n.
Muftahu ya kalleni yace “gimbiya mu kwana lafiya”.
Na murmusa sannan na amsa da “to ALLAH ya tashemu lafiya”.
Koda Muftahu yafita sainayi tsaye nakasa magana ganin ya zubamin idanu, ganin banida niyyar magana saiya nunamin kujera alamar na zauna. shima yana tashi zaune sosai.
Ban musaba na zauna.
“miya faru?”. ‘yafad’a yana zuba Hollandia fresh milk a glass cup d’in gabansa”.
d’agowa nayi nad’an kallesa, dai-dai yasaka kofin a bakinsa zai sha, janye idanuna nayi ina kuma had’e fuska. aransa yace kai wannan yarinya akwai jan ajin tsiya.
Saida naja wasu seconds sannan nace charger zaka aramin please, nabaro tawa a gida, gashi inason waya da munubiya da innarmu.
Crossing kafarsa yayi yana cigaba da shan free milk nashi tamkar bai jini ba, harna fidda tsammanin zai tanka min, sainaji yace, “ina wayar?”. yay maganar da mik’omin hannu alamar na bashi
Mik’ewa nayi na kai masa wayar ina tunanin mizaiyi da ita?.
Koda ya kar6a saiya mik’omin cup d’in hannunsa bayan yak’ara fresh milk d’in a ciki.
Na girgiza masa kai alamar na k’oshi.
wani kallo ya watsamin daya sani kar6ar dole. nadawo mazaunina na zauna, inata rik’on cup d’in amma nakasa sha, haka kawai naji hankalina bai kwanta da fresh milk d’in ba, bawai zargin yazuba wani Abu nakeba, haka kawai dai banjin sha.
Shikuma ya basar dani yanata juya wayar kawai a hannusa, basan miyake kalloba ajikinta.
Kallona yayi yace, “kin rik’e Number su?”.
“eh” nafad’a batareda na kallesa ba.
Wayarsa ya d’auka guda d’aya ya had’omin da tawan ya mik’omin, “kije kuyi wayar kawai, da safe sai a nemo miki charger d’in”.
Na tashi naje na kar6o tareda cewa “nagode” najuya nafice da cup d’in fresh milk d’in a hannu na.
Bina yayi da kallo harna fice, ya sauke ajiyar zuciyata kafin ya cije lips nashi domin jin mararsa tad’an rik’e masa kad’an.
Koda naje d’akina saina kasa ajiye fresh milk d’in, haka kawai naji kuma sha’awar nasha, nako d’aga cup d’in na shanye tas sannan na zauna ina juya wayar tasa datamin k’yau, saina tuno wayarsa daya barmin ranar idi, na ta6e bakina kawai nafara saka number innarmu…………..✍????
Hummm mi zai biyo baya bayan shan fresh milk kuma?. da zuwan muftahu?.????
Wannan amsar sai ranar Monday????. naso yimuku wannan weekend d’in amma munada biki gsky.????????????
*_hhhh naji k’orafinku sister’s, ammafa ko pages biyu nakeyi ba isarku zaiyiba????, wlhy bama nida time d’in yin typing 2pages a rana, saboda inada aure, akwai nauye-nauye a kaina nima, masu kuma so nagama kafin azumi suma ina basu hak’uri, bazai yuwu nagama kafin azuminba, dan azumin kad’an ya rage, kuma banason datse labarin nan kamar yanda nayi a SIYASA KO KABILANCI, zanbi a hankali na gama, wlhy nafiku son nagama nima Na huta, Dan dana fara buk zai fara cizona a zuciya nima, so kawai nake naga nagama????, karku manta ko tarihin masarautar su Galadima sameer har yanzu bamu saniba, Dan haka zamuyi, iya inda muka tsaya saimu cigaba bayan salla idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya, Dan kamar yaune ai.????????????._*
Ngd sosai da soyayyar dakuke nunama buk d’innan, ina sonku nima har cikin raina, ina fata zaku fahimceni????????????.
❤❤❤❤❤❤❤
⛹????♀