NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 2) 10&11

     *_RAINA KAMA……_*
              _{Kaga gayya}_
             *_Bilyn Abdull Ce_*
            _Duk marubucin daya kafa alk’alaminsa bisa takarda tabbas yagama tanadar yanda labarinsa zai kasance ne, amma

sai wasu wabubuwan mamaki kaga sun gaza k’arewa a social Media, ban saniba ko samunmu available ne yakesa a kullum kuke mana kallon marasa aikinyi?, ni dai nasan time d’in dana shirya labarin RAINA KAMA ban zauna tebirin shawara da kowaba a online, inkuwa hakane tayaya wasu har suke tunanin nafara sauka akan layin labarin?, to magana d’aya zanyi a wannan ga6ar, ban gina labarin Raina kama akan kwanciyar aure bane, dan haka masu maganar  munaya bata da aiki saima Galadima rashin kunya saisu jira saina kai k’arshen labarin kafin su k’alubalanceni, abin dariya, (wai aikina kenan daga nasa munaya ta murgud’a baki sai ta harari Galadima da masa k’unk’uni) tunda aikina kenan babu lallai wajen 6ata lokaci karantawa, haka Na tsara labarina tun farko kuma haka zanyi, duk wanda yaga bai masaba zai fara iya rubuta nashi shima kawai. wannan abun da kukema writer’s yana 6ata mana rai, bai kamata ku dinga k’alubalantar writer’s ba, bayan su suke da masaniyar yanda suka shirya labaransu, idanma zakuyi saiku ringa tanadar lokaci har zuwa bayan mun kammala, hakan zaifi tasiri fiyeda katsalandan a tsakkiyar labaran mu, akoda yaushe kuzama masu kula kafin Ku k’alubalanci mutum????????._

     *Ba akan kaina kawai nayi wannan bayaninba, harda sauran writers da yawa da akema makamancin hakan koma fiye da nawa.????????*
_____________________________
  ~Book 2~ ????????1011
         
  ……………….Koda motocin suka tsaya sarkin mota ya bud’e masa k’ofa yakai tsawon lokaci baiko motsaba, saboda tsantsar tunani da zuciyarsa ta lula, aduk sanda zuciya take cikin matsanancin matsi gangar jiki ma gazawar karfin ikon jini dana 6argo sukan mata k’aranci, shi kansa yasan yanada buk’atar mataimaki a kan wannan lamarin, amma k’arancin rik’on amana Na d’an Adam ne yake yawan gargad’arsa da taka masa birki, ba kowane zai fahimci ma’anar nok’ewar tasaba, sai mutum daya tsinci kansa a makamancin halin da yake ciki………
        “Ranka ya dad’e mun iso”. Sarkin mota yasake fad’a cikin taraddadi da taka tsantsan.
      A hankali Galadima ya bud’e idanunsa da suka koma launin jaa saboda damuwa a kan sarkin mota, batareda yace uffanba ya ziro k’afarsa k’asa yana cije lips da had’iye wani kududun damuwa a mak’oshi.
    Tunda ya fito ma’aikatan wajen suketa masa sannu da zuwa, dan tunda ya shigo k’asar sai yanzu ne zai shiga cikin plaza d’in.
    Hannu kawai yake iya d’aga musu, amma bakinsa yay masa nauyi, kallo d’aya kuma zaka masa ka nazarci damuwa da buk’atar hutun dake tartare da kuzarinsa.
      A cikin plaza d’in ma bata sauyaba, d’aga hannu agaresu shine yazama linzamin amsa gaisuwar dasuke masa.
    Da hannu yayma d’aya daga dogaransa nuni da amso masa key.
     Da sauri dogarin ya amsa yana mai nufar sashen da zai kaishi office d’in Saleem mai kula da CCTV camera’s.
    Sai dai kafinma yakai ga k’arasawar suka had’u da saleem, Wanda tun shigowar motocin Galadima ya gansa.
     Keys d’in ya damk’ama dogarin, sannan ya k’araso domin mik’a gaisuwa ga ogansa na wajen aiki kuma magajin garinsa.
    Shima d’in dai hannu Galadima ya d’aga masa, hakan kuma ya saka Saleem fahimtar akwai damuwa kenan.
            Koda aka bud’e ya shiga saiyayma dogaransa nuni da suje kawai, sannan ya maida idanunsa ya lumshe tareda kwanciya jikin kujerar yana lilawa a hankali.
     Shi kansa baisan tsawon lokacin daya d’auka a hakanba, amma tabbas yasan yashiga kudin nazari mai zurfin gaske. Knocking d’in k’ofar da akayi yasakashi bud’ar baki da k’yar ya bada izin a shigo.
    Nuren daya shigo ya maida k’ofar ya kulle, kafin ya ida takowa cikin office d’in, idonsa nakan d’an uwannasa.
    Zama yay a d’aya daga kujerun dake fuskantar Galadima,  “brother what happen?”.
      “Northing”. Galadima ya fad’a batare da ya bud’e idonsa ba.
    Shiru kawai Nuren yayi shima, ya d’akko laptop a briefcase d’in daya shigo da ita, kunnawa yay, kusan mintuna biyu ya d’ago ya kalli Galadima, sai kuma ya maida kansa ga laptop d’in. “Sameer nasan kaga cigiyar da akeyi takowacce kafar yad’a labarai ta k’asarnan akan d’iyar minister, sannan jami’an tsaro tsaye suke akan binciken inda take. yakamata musan abinyi kafin lokaci ya k’ure mana”.
     Guntun murmushi Galadima yayi, batareda ya bud’e idanunsa ba yace “Nuren indai har babu wata waya datake aiki inda kakai yarinyarnan, kuma ka cire sim card d’in phone nata a lokacin daka d’auketa, to babu wata hanya dawani jami’in tsaro zai ganota, dama hanya d’ayace da kuskure zai basu damar bibiyarta, na d’aya lokacin daka d’auketa yazam wayarta na aiki, tabbas zasubi ta wannan hanyar su gano har iya inda ka kashe wayar, hanya ta biyu itace ka kashe wayarta baka cire sim card d’in ta ba daga phone nata, koda wayar a kashe take zasu bibiyeta ta hanyar ???? su ganota” ya tashi zaune sosai yana bud’e idanunsa akan Nuren, “wannan hanyoyin biyu kawai ke garesu saikuma idan da camera tare da ita, idan duk babu wannan basuda wata hanya, ka kwantar da hankalinka my brother, komaina da tsarinsa right?”.
       Murmushi Nuren yayi, kafin ya salute d’in Galadima yana fad’in “I thrust to you my dear broth”.
       Shima galadima salute d’in Nuren d’in yayi yana murmushi.
    Komawa yay ya sake kwanciya jikin kujerar, “yanzu inaga time d’in turama minister Massage yayi?”.
     Cikin zaro idanu Nuren yace “baka kallon hakan a matsayin ganganci kuwa?”.
     Baki Galadima yad’an ta6e yana crossing k’afarsa, cikeda izzarsa yace “sai idan nabama wani damar hakan ai”.
      Nuren baice komaiba, dan yagama sanin hatsabibancin Galadima wajen iya sarrafa Computer, dan haka ya bar wannan zancen ya d’akko wani. “yauwa to maganar Malam Saminu fa? Kasan yana hannunmu fa har yanzu?”.
      “wannan barsa saiya kuma magantuwa, dan da alama yasan wani Abu, saidai akwai abinda ya sakashi za6ar 6oyewa. ni yanzu damuwar 6atan Muftahu yafi damuna, nasaka camera’s jikin mutane 10 danake iya zargi a masarauta amma banga alamun da hannun koda mutum d’aya ba, hakan ya tabbatar min da gaske Muftahu na bibiyar lamarina, sai dai bansan dalilinsa ba, ko kuma waye sakashi?”.
         Nuren ya jinjina kansa, “brother aini da Harun dama mun dad’e da zargin Muftahu, Kaine kawai kake masa kallon mutumin kirki daman”.
     Lips kawai Galadima ya cije, amma baice uffanba, Nuren yaci gaba da ‘yan danne dannensa a laptop d’in, zuwa wasu mintuna batareda ya d’agoba yace, “maganar Sirikinka fa?”.
     Shiru Galadima ya masa, saida ya mula dan kansa sannan ya murmusa tareda maida idonsa ya lumshe, “a daren jiya nagama da wannan matsalar, sim card d’insa 3, akwai Contact 300 da 38, mtn yanada mutum 172, ya fara saka credit a layin shekaru 15 kenan, ranar 3/6/2005, glo 107, ya fara amfani dashi shekaru 8 kenan, wad’annan sune Sim card d’insa da yake mu’amulla da kowa a ciki, kuma anfi saninsa da su, akwai 6oyayyen layinsa Na mtn shima, yafara aiki dashi shekaru 13 kenan, kuma mutane 59 ne kawai acikinsa, sannan ba kowane yasan layinba, dan dukkan family nashi basu San da zamansa ba,  ita kanta mahaifiyar su Munaya batasan anyi saving number a phone nata ba, suma da suka kirata basusan da number a wayarta ba, dan baita6a kiranta da shiba, akwai matakan tsaro dake tattare da Layin, hakanne ya tabbatar min da akwai abinda yake 6oyewa a Sim card d’in, dan sai time to time yake amfani da shi, kiran matarsa da sukayi da layin wannan shine kuskuren farko da suka tafka da Sameer ya samu hanyar musu takun sauro. zan fara aiki akan layin na shigesu ta hanyar da basu zataba”.
      Jinjina kai kawai Nuren yakeyi dan mamaki, Galadima da banne, kamar yanda basirarsa take daban, ya sauke ajiyar zuciya yana kama hannun Galadima da idonsa ke a lumshe har yanzun, cikin karsashi yace “lallai kai RAINA KAMA ne Sameer”.
      Murmushi kawai Galadima yayi, amma baice uffanba.
      Knocking akayi, Nuren ya kalli k’ofar yana bada izinin a shigo, Sauban ya shigo da sallama, su duka idonsu a kansa, Nuren yace “lafiya kuwa?”.
     Zama Sauban yayi yana sauke Numfashi da k’yar, cikin magana d’ai-d’ai da alamar a birkice yake yace, “wlhy Yaya binmu aka ringayi da wata bak’ar Jeep, da k’yar mukasha wlhy, ni dai yau zanbar k’asarnan gaskiya”. Sauban ya fad’a tamkar zaiyi kuka’.
       Gani kawai sukai Galadima yana dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya tsagaita.
     Nuren da Sauban suka tsaya kawai suna kallonsa.
     Tashi yayi tsaye yana takawa cikin izzar k’asaita, ya dafa bango yana lek’en waje ta window d’in office d’in, yakai wasu adadin lokuta a wajen, sai kuma ya juyo yana kallon Nuren d’in da Sauban da suma suka zuba masa idanu.
      “my dear brother! daka tsaya sun kamaka ai, tabbas da wannan shine kuskuren da zasuyi Wanda bazasu ta6a mantawa da waye Muhammad Sameer Saifudden ba a tarihin rayuwarsu. Waya gaya maka kana yawo cikin 9ja ne batareda idon Sameer ba a kanka?”.
     Sauban ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin daya jik’a fuskarsa, “wlhy yaa Sam daka fad’amin da bazan tsorata ba”.
     Daga Galadima har Nuren dariya suka kwashe da shi, Nuren ya dafa kafad’ar Sauban yana fad’in “matsoracin banza”.
      “uhm-uhm yaa Nuren bazaka ganeba wlhy, tsoro halak ne fa”..  
      Galadima dai baice komaiba ya koma ya zauna yana murmushi.
)))*((()))*((()))*((()))*(((
        Ganin har anyi sallar Magriba babu baba k’arami balle Dady ya saka Innaro d’aukar gyale ta fito, lokacin gwaggo Safiyya tana salla, shiyyasa batasan innaro ta fitaba, habiba da Naja’atu dake tsakar gida suna tattare kaya saboda hadari na farkon damina dayake nuna alamar zai zubda ruwa. suka kalli juna, Naja’atu tace “yaya habiba tsohuwarnan fa bata da dama wlhy”.
     Dariya habiba tayi, “ai kad’anma kika gani Naja’atu, yanzu dai zataje ta tadama baiwar ALLAH hankali”.
      “to ALLAH ya k’yauta”. ‘cewar Naja’atu tana rik’e ha6a’.
      Lokacin da Innaro ta shigo gidan d’akin Innarsu Munaya ta nufa kai tsaye, sai dai ta iskeshi rufe, kwala kiran sunanta ta shigayi cikin masifa, “Ai’sha!! Ai’sha!! Nasan kina jina, wlhy ki fito kafin yau d’innan igiyar aurenki ta tsinke”.
        Mamansu yaa Hameed da gwaggon Haleematu ne suka fito, mamansu yaa hameed tace “aiko tafita fa inna, dan gab da magribar nan naga Fadeel ya shigo sun fita, bansan mike faruwa ba dai”.
      “yaza’ayi kusan mike faruwa tunda anyi k’ulle-k’ullen munafunci, lallai jafaru, wai yau da kaine za’a muzantani hannun mak’iyana, to nikuma naga ta yanda Ai’sha zataje wata k’asa jiyyar Auwalu da raina”…….. haka taita zuba banbamin masifa matan gida na saurarenta, daga daddy har baba k’arami suna gidan amma sukak’i fitowa. Jarabar Innaro ta saka kowa na gidan fahimtar mi ake ciki, nanfa hassada da bak’in ciki suka kume zukatansu, dukda kuwa sunsan tafiyar bata dad’i baceba, maman fauziyyace kawai hakan yamata dad’i, koba komai inna ta huta da cin zarafin Innaro koyayane.
       Sai da Gwaggo Safiyya ta shigo tama Innaro magana sannan ta tafi gida, su matan gidanma sai yanzu suka San da zuwa gwaggo Safiyya d’in.
     Amma sunso ace innarsu munaya na gida Innaro tayi wannan rashin mutuncin.
   
    Hummm????.
****************************
        Bayan fitowar su Galadima daga birnin gayu, sun wuce gidane, Nuren kuma yakoma hotel d’in daya sauka.
         Galadima kawai ne ya shiga sashensu, amma Sauban 6angaren mai martaba ya nufa neman yarima Mahfuz.
      
     Munaya na zaune a falon farko tareda sabbin kuyanginta guda uku, (dan bata amince su shiga falonta ba, saita gama tantance su sannan) ba wani hira sukeyiba, d’ayace a cikinsu ke sak’a shine abin ya birge Munaya take kallo, tana kwance cikin doguwar kujera ne, yayinda su kuma su ke zaune a k’asan lallausan carpet d’in falon.
      Dogarai biyune suka fara shigowa hannunsu d’auke da ledoji, sai kuma mai gayya mai aiki Galadima.
     Da sauri bayin suka mik’e tsaye, saida ya ida shigowa sannan suka d’urk’ushe a k’asa suna kwasar gaisuwa.
    A la66ansa ya amsa yana d’aga musu hannu, yayinda idanunsa ke kan munaya da itama ke satar kallonsa
       Duk d’insu kowa janyewa yayi, yayinda bayin da dogaran suka fice bayan sunkai ledojin falon Galadima.
     Baice da ita uffanba yafara takawa zai shige, tamkar mai tsoron fad’a tace, “sannu da zuwa”.
    Ysayawa yayi cak, sannan ya juyo da kansa tamkar mai ciwon wuya ya kalleta, bata yarda sun kuma had’a idoba takuma fad’in “nagode sosai”.
     “for what?”. ‘ya fad’a cikin isa’.
      Shiru munaya tayi, ta kasa cewa komai.
    Shima bai sake cewa komai ba ya taka ya shige abinsa.
      Harara munaya ta raka bayansa da shi, sai kuma ta sauke numfashi tana tashi itama, bedroom d’inta ta koma, a saman sofa ta zauna tana dafe kai, sosai take buk’atar zuwa sake duba mahaifinta, amma ta kula Galadima bashida niyyar cemata taje, kai itako wannan wane irin abune haka? shi dama gidan Sarautar haka yake bakada ‘yancin kanka?, komai saida k’a’ida. tun d’azu kuma take kiran number inna bata d’agaba, tadai kira baba k’arami da daddy sun gaisa ta tambayi jikin Abba, shine ma har suke kuma sanar mata k’ok’arin da galadiman keyi. tabbas hakan da yayi yasata jin farin ciki, koba komai tasan shi adaline, ko anan gaba ragamar shugabanci ta riskesa zaiyima na k’asa da shi adalci.
       Galadima daya shiga tun a falo yafara k’ok’arin cire navy blue d’in jacket d’insa, ya wullata saman kujera, sassauta belt d’in yayi shima amma bai cireba, ya zauna cikin tsantsar nuna gajiya yana furzo iskar bakinsa, remote ya d’auka ya kunna tv, tamkar ya saita lokaci saiga hoton d’iyar minister mai amsa sunan Farhat ana nunawa, an saka 2.5 millions ga dukkan wanda ya kawota koya bada bayanan sirri akan wanda yasan wani Abu akan 6atanta.
    Wani mugun tsaki Galadima yaja a zuciyarsa yana fad’in wawaye, saiku k’ara yakai 100millions ba 2 ba, idan ubanta ya shirya kawo kansa gareni nima a shirye nake nabashi shashashar ‘yarsa mai zubin ta6arya, ya kashe TV d’in kawai ya mik’e ya shige ciki.
    Ko ina fes da shi, yasan baida Matsala da Sauban a 6angaren tsafta dama. kayan jikinsa ya ida cirewa ya shiga wanka.
     Bayan ya fito samu yay yad’an kwanta, dan ya samu Hutu kona 2hours ne, dan yanzu akayi sallar zuhur. aiko kwanciyarsa babu dad’ewa barci yay gaba dashi.
     Munaya ta jawo wayarta da nufin kuma kiran inna, amma sai taga Ashe credit d’inta yama k’are, kanta ta dafe dan haushi, zuwa can tamik’e domin bin shawarar zuciyarta. turare ta kuma fesama jikinta ta d’auki gyale ta yafa.
         Ta d’an dad’e a k’ofar d’akin tana tunanin idan kuma ta shiga hasashenta bai zama gaskiyaba  ya kenan?, wata zuciya tace kije abinki k’ilama wanka yake.
    Da sand’a na ida shiga tamkar wata 6arauniya, sai kuma na tuna ai yanada CCTV camera, nutsuwa nayi na daidaita kaina, na koma normal saboda tsaro. Ganin babu abinda naje nema d’in a falo saina zarce bedroom ina wani ciccijewa.
    Mamaki ya kamani ganinsa kwance a kan gado yana shak’ar barci hankali kwance, hakan yamin dad’i kam.
     Saida nabi ko’ina na bedroom d’in da kallo, ganin babu alamar akwai camera a nan saina ida shiga, wayoyinsa biyu na ajiye gefen filon dayake kwance, rabin hannun damarsa ma nakan d’aya ya d’ora cikin barci halan?.
       Dole saina hau saman gadon, dan haka na tsaya tunanin yanda zanyi, banida wata mafita dan haka nahau a hankali, kai kace wata hawainiya ce.
      Cikin rintse ido da cije la66a nakai hannu zan d’auki wayar d’aya.
     Caraf aka rik’emin hannu, babu Shiri na bud’e idona zuciyata nawani tsitstsinkewa.
     Fisgoni yayi na fad’o jikinsa, zafin danaji ya sakani sakin k’aramar k’ara.
          Ya matseni a jikinsa batare da ya kula miya aikata ba. nikam jikina sai rawa yakeyi, tsorona karya d’auka ko cutar da shi zanyi ma…….. maganarsa cikin yanayin barci ta Sani kallonsa.
     Kad’an ya bud’e idonsa dake jajir, alamar da gaske barci yakeyi, muryarsa a sark’e irinta barci yace, “sata kika koma?”.
     Baki na tunzuro ina marmar da idanu da suka cika da kwalla, nace “ALLAH ya kiyaye, arafa zanyi”.
      Kuma matseni yayi har saida na rik’e hannunsa,, yace “wannan ba aro bane sata ce yalla6iya, dan haka dolene ki kar6i punishment”.
     Jin ya ambaci punishment saina kuma rikicewa, nahau k’yarma ina rantse-rantae da matso kwallan idona.
     Bai wani saurareni ba ya hau sumbatar wuyana, tureshi nafarayi amma saina gaza, dan haka na koma mintsini, shima a banza man kare????.
       Dukna d’auka wasa yakeyi kawai farfaganda Ce danna tsorata, amma saina tsinci ya fara sakin layi, iya yina da rok’o, yakushi, mintsini, ban samu ku6uta ba, saima salonsa yafara tasiri a kaina, nima nai luf harda k’ok’arin maida murtani. saida naji zai kama wata tashar nai azamar tsaidashi ta hanyar fad’in “please yalla6ai camera”.
       Maganinki ai baby????, su Galadima akwai bak’in wayo dai????????, idan ta gaskiya za’abi ni banga abin punishment anan ba????, dama yadawo ‘Yar matsalarsa dai tsautsayi ya kawo mai karanbani dason banza ta fad’a tarko????????????.
******************
     Koda inna ta dawo saita had’ama su Aryaan kayansu, da nufin su koma wajen mamansu yaa hameed harta dawo.
     Amma suka tibire akan bazasu jeba, su Uncle yace zaizo ya kaisu wajen Auntynsu.
    Tun inna na lallashinsu harta kai ga mammakesu suka fara kuka, daga nan sukai barcin dole.
    Bata fasa had’a kayanba, tagama tsaf ta d’auki akwatin zuwa d’akin mamansu yaa hameed.
    Su Bintu kawai ta iske a falo suna kallo, Aminu ne yace “innar ‘yan 2 ina zaki da daddare?”.
    Murmushi inna tamasa tana fad’in “kayansu Aryaan ne Aminu……..”
    Bata gama rufe bakiba mamansu yaa hameed ta fito. ganin innarsu munubiya da kaya saita had’e fuska. Inna bata damuba tace “ga kayansu Aiyaan, saisu dawo nan da zama kafin na dawo”.
    “to”. Kawai mamansu yaa hameed tace tana kauda kai gefe.
   Ran inna ya sosu, amma sai batace komai ba ta ajiye ta fice jiki a sanyaye.
    Da murnar Haneeff ya tashi zai d’au jakar yakai d’akinsu, amma sai Maman ta watsa masa harara. babu shiri ya koma ya zauna. Jakkar dai sai anan ta kwana, bata d’auka ba, bata bar ‘ya’yanta sun d’auka ba saboda bak’incikin inna zataje jiyyar Abba ba itaba.
   ALLAH ya k’yauta????.
****************************
     Dakatawa yay daga abinda yakeyi, ya bud’e idanu a hankali akan fuskata, murya k’asa-k’asa ya furta “camera?”.
      Kaina na d’aga masa batareda na bud’e idoba.
    Bai kuma cewa komai ba ya koma ya kwanta yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips yana gyara kwanciya da sake rungumeni kawai.
    Idona na bud’e a tsorace, azatona zai cigaba ne, sainaga ba haka bane.
    A cikin kunnene ya furta “barci please”.
    Kallonsa nayi ta gefen ido sai naga idonsa a rufe, nima banida za6in daya wuce na rufe nawan, dan haka na lumshe kawai.
       Ni sai barcin ya d’aukeni, amma shi ya k’auracema idonsa, mamakin furicina ya dami zuciyarsa, dama yadad’e yana zargin akwai camera a d’akin nan nasa, sai dai bawai ya tabbatar bane, kuma bai ta6a yunk’urin dubawa ba. da wad’annan tunanin ya cinye lokacin barcinsa har aka kwala kiran sallar la’asar.
    Bud’e idanunsa yayi akan fuskata, yad’an tsuramin ido nawasu time’s, sai yaga barcin yamin k’yau, kauda idonsa yayi cikeda basarwa, saikuma ya janyeni daga jikinsa yana yunk’urin tashi, hakanne ya sakani farkawar nima, na tashi da hanzarina ina gyara rigata, sai kuma na sauka na fice batareda nako waiwayoshi ba.
    Bina yay da kallo harna fice sannan ya janye yana ta6e baki.
       Ban kuma jin labarin Galadima ba har dare yayi, nafito wanka ina shirin barci ya shigo, yau dai babu laptop d’in kaddara, dagashi sai phone guda d’aya ma, yana sanye da kayan barci kalar gwaiduwar kwai masu duhu.
      Zama yay a kujerar dake cikin d’akin, yayinda ni kuma na k’arasa saka hijjab d’in dana jawo, babu walwala ko alamar wasa kwata-kwata a face nashi, dan haka nima saina kama kaina.
       cikin k’asaitarsa yace  “muyi magana mana”.
     Kallonsa na d’anyi, saikuma na amsa da “ina jinka”.
    d’ago ido yay muka kalli juna, da ido yay min nuni da bakin gadon.
   Ban musaba nazo na zauna, amma sai nayi k’asa da kaina ina wasa da zoben hannuna.
      Maida kallonsa yayi ga zoben danake jujjuyawa, kusan mintuna 4 harna d’auka ya ma fasa maganar, na d’ago na kalleshi.
       Ya kauda kai gefe yana fad’in, “waya fad’a miki da CCTV camera a d’akina?”.
       Nima ban kalleshi ba na bashi amsa a tak’aice, “bakai ka saka kayarka ba danni?”.
    Da mamaki ya kalleni, sai kuma ya kausasa muryarsa, “Munaayaa seriously nake miki magana!”.
       nad’an razana, amma saina dake, nace “kana nufin bakasan da itaba?”.
     “idan nasan da ita mizai sani aikata wani Abu na sirrina  a d’akin”.
     da mamaki na kalleshi domin tabbatarwa, tsantsar gaskiya na hanga a idonsa, dan haka na danna yatsun hannuna da k’arfi suka bada sautin “k’asss!, k’asan zuciyata na tunanin minene sirrin nasa?”.
      Idonsa a kaina ko k’yaftawa bayayi, nima na d’ago mukaima juna kallon ido cikin ido, dukda tsorata danai da hango masifa cikinsu ban janyeba, nafara fad’in “tabbas naga camera a falonka, tana nan saitin hotonku kaidasu momma, inda flower d’in nan take, hakanne yasani zargin kai ka saka kayarka saboda tsaro”.
      “hummm”. kawai yafad’a yana janye idanunsa, sai kuma ya taso ya dawo inda nake zaune, ganinai kawai ya rungumoni jikinsa, na waro idanu dan mamaki, shikuma ya lumshe nasa tareda sumbatar goshina a hankali, shigar sumbarce tasakani lumshe nawa idanun nima tareda k’ank’ameshi.
      Cikin kunnena ya furta “i’m proud of you my friend”.
      Da sauri na waro idanu ina kallonsa, saiya d’agamin gira d’aya yana wani miskilin murmushi, sannan ya tadani zaune shima ya tashi ya fita.
       Baki da idanu da hanci duk na saki ina binsa da kallo, a k’asan raina ina tambayar mike damun guy d’innan ne wai?.
      Banida mai bani amsa, dan haka na mik’e na cire hijjab d’in nai kwanciyata.
       d’akinsa ya koma ya d’akko wani Abu kamar k’aramar ball???? ya ajiye saman table d’in gaban gadon, sannan ya manna wani dogon Abu a jikin ‘Yar ball d’in, ya d’akko laptop d’insa ya kunna. shiru na kusan mintuna uku ya k’urama abinnan ido, zuwa can yafara wata k’aramar k’ara d’i! d’i! d’i!, sai kuma k’aramar danja ajikin abinda ya manna d’in shima tana kawo haske  jaa da d’aukewa.
     Murmushin takaici kawai yayi, a zuciyarsa yanama ALLAH godiya dabai ta6a kusantar Munaya a d’akin nanba. dan tabbas ga CCTV camera ya gani a d’akin, an sakatane can ta saman wardrobe, yanda ko alama hankalinsa bazai kaiba, baiyi yunk’urin cirewa ba, ya d’auki kayan aikinsa ya koma parlour, dan yaga itakuma tanan a ina take?. yanama shigowa tun’a k’ofar tsakanin bedroom da falon ya gani, baima k’arasaba ya koma ciki, kashe laptop d’in yayi ya d’auke k’aramar ball d’in ya 6oye.
   Duk wannan hidimar da Galadima keyi Sauban na kwance bisa gadonsa yayi d’ai-d’ai yana kwasar barci.
      Gyara masa bargo yayi saboda tasowar hadarin farkon damina da iska tafara kad’awa sanyi ya busa. daga nan ya kashe masa fitila ya fita zuwa d’akin Munaya.
      Ita harma tayi barci, tana k’ank’ame da fillo saboda sanyin hadarin dake busawa, gadon ya hau tareda warware bargon ya lullu6a musu. dai-dai iska ta taso mai azabar k’arfi, a rikice Munaya ta juyo ta k’ank’amesa saboda tsorata.
      Rik’eta yay sosai yana fad’in “uchh! Karki karyani”.
     Babu shiri munaya ta bud’e idonta, tana k’ank’ame da shi tace, “wai miyasa bazaka ke kwana naka d’akinba ne?”.
     “k miyasa time d’in da kikaje India kika gajemin d’akina?”.
      Shiru tamasa bata amsaba, amma yanajin alamar murgud’a bakinta akan k’irjinsa.
        “punishment ya tabbata agareki yalla6iya”.
     Da sauri nace “wlhy a’a, inba hakaba zaka koma saman sofa ne, ai kaima haka kamin a d’akinka”.
      “uyim Madan tsiwa, to ai nima dankar ki murk’ushemin abin cikin kwan cikin barci yasani kwantawa anan?”.
    Zan bashi amsa aka kwad’a wata tsawa data sakamu ruk’unk’ume juna babu shiri, sai kuma ruwa ya 6alle.
    Da wannan damar Galadima yay amfani wajen canja salon kwanciyar tamu, tun ina nuna banaso har salonsa ya sakani sakin layi, (????anya munaya wannan cikin naki bashine tarkon da Galadima ya d’ana miki ba?????).
     
           Da asuba tashi nayi inata zum6ure-zum6ure, baice dani uffanba yashiga toilet ya tsarkake jikinsa. Bayan yafito nima na shiga.
    Baki ya ta6e yana wani d’age gira d’aya tamkar ina kallonsa ya fice.
      Saida nasha kukana sannan nayi wankan tsarki, narasa mike sakani biyema Galadima? insha ALLAH zan d’auki mataki (????idan babu abin cikin kwan ba????, nasan inhar yana nan babansa zaita samun bonus????).
Bayan na idar da sallar ban koma barciba, saina gyara d’akin nayi wanka,  shirin fitarma na  sake yi yau, dan baba k’arami yacemin k’arfe goma na safe zuwa 11 zasu tafi.
    Kammalatawa kenan ya shigo, ko kad’an banji alamar shigowarsa ba, saida na gama fesa turare ina k’ok’arin ajiyewa na hango kamar mutum tsaye a bayana.
    Da sauri nayi azamar juyowa, dayake yana gab dani kad’an ya rage na fad’a masa a jiki, na dai samu nad’anyi baya na jingina da mirror ina tura baki.
       Ko motsi baiyiba shikam, bai kuma janye idonsa daga kallona da yakeba.
     Haushi ya kamani, nima nabi jikin nawa da kallo kozanga abin da yake kallon, ganin babu wani Abu daya faru na d’ago na kuma kallonsa, “wai yalla6ai mi kake kallone haka?”.
      d’an yatsansa d’aya yasaka yad’an shafi girarsa yana gyara tsayuwa,  “abin cikin kwan mana”. ‘ya fad’a cikin basarwa’.
     “ta gefensa na ra6a zan wuce ina fad’in “ai lokaci kad’an ya rage maka ka bar ganin nasa”.
    Da sauri ya rik’o hannuna, na juyo muka kalli juna, mayun idanunsa ya saka cikin nawa, “kina zaton idan nabar ganinsa kema za’a cigaba da ganinki?”.
      Guntun murmushi nayi ina janye idona daga cikin nasa, nace “kana zaton kasheni zakayi nima?”.
      “cire maganar ma zato”.
     Kallonsa na kuma yi, cikin yanayin da shi kansa bai ta6a zaton ina dashiba nace “saika fara shiri”.
    Shima a dake yace “dama a shirye nake kullum”.
    Na murmusa ina k’ok’arin cire hannuna daga cikin nasa, amma ya hanani damar hakan, kallonsa na kuma yi nace “ko har lokacin yayi ne?”.
       Fisgoni yayi na koma da baya, ya mannani jikin mirror d’in tare da maida hannuna baya ya rik’e, ya matseni da jikinsa, fuskarsa gab da tawa tamkar zai had’a bakinmu, yayinda idonsa ke cikin nawa, wani miskilin murmushin gefen baki yayi, yasaka yatsansa yana zagaya janbakin dake kan la66ana a hankali, cikin muryarnan tasa mai kama da an masa dole ya fara magana cikin karsashi “ko Ubangiji yakanyi hukuncine ga bawan daya bijirema umarninsa, koda ace zubarda wannan cikin kikayi dolene saikin kuma d’aukar wani, zubar da shi na dai-dai da haihuwar yara goma anan gidan kafin na aikaki inda shima ya tafi” ya matsa la66ana da k’arfi, wani zafi ya ratsani saiga hawaye a kumatuna, murmushi yayi, yasaki la66an ya dangwali hawayen a d’an yatsansa, nunamin yay yana fad’in “lallai momcyn abin cikin kwan kin cancanta 100%, amma bayan abin cikin kwanfa akwai k’annensa, please bar kuka my dear friend”. ‘ya k’are maganar da sumbatar la66ana sannan ya sakeni yaja baya.
        Koda ya sakeni sainayi murmushi kawai, sannan na juya ina fuskantar mirror, foda na d’auka na gyara fuskata, na sake saka jambaki kad’an kamar yanda na saka d’azun.
     Tsayawa yay cikeda mamakin abin da nayi na ko inkula yana kallona, mi wannan yarinyar take shiryawa ne haka?…..
    Kafin ya samu amsa Na juyo gareshi, fuskata d’auke da murmushi na ra6a zan wuce sa, bina kawai yay da kallo, naje gaban wardrobe na bud’e, alk’yabba na d’akko na sanya, sannan na d’auki handbag ina kallonsa har yanzu fuskata d’auke da murmushi.
       Gira ya d’agamin shima yana wani k’asaitaccen murmushi, ya juya ya fita batareda yakuma magana ba.
     Yana fita na sauke ajiyar zuciya ina dafe k’irji, wlhy ni kad’ai nasan dukan da zuciyata takeyi, kad’an yarage ya ranfo a tsorace nake, kalamansa ne suka shiga dawomin cikin zuciyata, mi wannan yake nufine wai……….?
     “Shin bazaki bane?”.
   Muryarsa ta daki dodon kunnena, da sauri na gyara yanayina na d’ago muka had’a ido, Ashe yana bakin k’ofar bai tafiba.
    Bance komai ba na biyo bayansa.
    A falon farko na iske kuyangina suna gaidashi, hannu kawai ya d’aga musu ya fice abinsa.
    Tsayawa nayi muka gaisa, d’aya a cikinsu ta yunk’urin k’ar6ar handbag d’ina.
    Na iske harya shiga mota, nima aka bud’emin na shiga, handbag d’ina ta mik’omin tana fad’in “ranki ya dad’e ana buk’atar rakkiyarmu ne?”.
    Murmushi namata, na juya na kalli Galadima danjin mizaice, kansa ya girgiza alamar a’a.
     Juyawa nima nayi na girgiza mata kai, tamana addu’a tana rufe k’ofar.
    Tunda muka tafi babu wanda yace uffan, yanata latsa wayarsa.
    Airport muka nufa kai tsaye.
    Bayan motocin sun tsaya sarkin mota na yunk’urin fita yace “2 minutes ”.
        Sarikin mota yace “to ranka ya dad’e”.
   Ni ban fahimci mi suke nufiba, naga dai sarkin mota ya fita mukuma ba’a bud’e mana ba, sai kawai nakai hannu zan bud’e.
     Hannuna ya rik’o, na juyo ina kallonsa, har Yanzu idonsa nakan waya,, ajiye wayar yayi ya juyo yana fuskantata, ina yunk’urin tambayar lafiya naji la66ana cikin bakinsa.
     Ya salam, na fad’a a zuciyata, saida ya shanye janbakin la66ana tas sannan ya sakeni. yanda kukasan gunki haka na koma masa, ya buga yatsunsa biyu saitin fuskata suna bada k’arar d’as d’as yace “gargad’i, first and last dazanganshi abakinki yayin fita”.
     Harya fita ban iya motsawa ba, saida aka bud’e murfin 6angaren danake sannan na iya sauke numfashi, na kasa fahimtar damuwar guy d’innan kwata-kwata. fita nayi nima, yana tsaye yana jiran fitowata. a tare muka jera muna tafiya, yayinda dogaransa ke take mana baya. ya wani miskile fuska tamkar bashine yagama ta6argaza ba a mota yanzun.
    Mutane sai kallonmu suke, masu gulma nayi masu nunamu nayi, ni dai duk sainaji wani iri, shima tsaki yayi danya tsani kallo.
     A mamaki na duk sai naga ‘yan gidanmu ma a wajen, gaggaisawa muka shigayi, muka rik’e hannun juna nida munubiya muka k’arasa inda innarmu take, gaisheta nayi, nace “su Aiyaan fa?”.
      “suna gida zasu zauna da mamanku mana”.
    “kai innarmu, ya zaki barsu wajen muguwarnan, bama gara Maman fauziyya ba komu suzo wajenmu”.
    Murmushi kawai innarmu tayi, tace, “ashe bazaki canjaba Munaya?”.
      6ata fuska nayi, ina fad’in “kai inna, duk canjawarnan danayi”.
     Murmushi sukayi itada Munubiya. akuma dai-dai time d’in Ambulance ta shigo airport d’in, sai mota biyu a bayanta sai motar police guda d’aya.
    Gaba d’ayanmu hankalinmu saiya koma can, Galadima ya k’arasa wajen Ambulance d’in, yayinda sauran motocin biyu Sauban da Nuren baba k’arami Dady ya Shafi’u da yaa Naseer yaa hameed suka fito.
     Zuwansu baifi da mintuna 15 ba aka fara kiran sunan wad’anda zasu tashi a jirgin.
    Sai kuma ma’aikatan wajen mutum uku suka iso wajen Ambulance d’in aka fara k’ok’arin fidda Abba. Hankalin jama’a da yawa ya tashi a airport d’in nan saboda tausayin Abba, mukam kuka ma wasunmu sukeyi ai, muna kallo aka gungura gadon da aka d’oroshi har zuwa ga jirgin.
    Suma su innarmu suka shiga itada baba k’arami da Sauban.
    Rungume juna mukayi nida munubiya muma muna kuka.
    Galadima bai fito cikin jirginba saida yaga komai ya dai-daita. yana fitowa babu dad’ewa jirgin ya d’aga zuwa sararin samaniya, yayinda mukuma muke binsu da addu’oin fatan alkairi da samun sauk’i……………..????
    ????kutt harda na gobe nayi????????♀⛹????♀⛹????♀⛹????♀⛹????.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button