NOVELSUncategorized
RAINA KAMA (BOOK 2) 14&15

*_♦RAINA KAMA…..!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
~Book 2~ ????????1⃣4⃣
…………….Yanda ya rik’e hannun yasani fad’in “please yalla6ai akwai zafi fa”.
Sassauta rik’on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, muryarshi a sanyaye yace, “Miyasa kikeson 6oyemin abinda kika Sani? shin bak’ya tausayinane? kullum cikin aiki kwakwalwa ta take, aikin Neman kud’in da zan taimaki kaina da ahalina, aiki akan
mak’iyana, ya kike tunani a kaina? yanzu haka ji nake tamkar kwalwar kaina zata tarwatse saboda damuwa da abubuwan da suka sakata matuk’ar nauyi, ta6a kiji yanda zuciyata takoma bugawa a slowly”. ya kamo hannuna ya d’ora a k’irjinsa, saitin zuciyarsa. da gaskiyarsa kad’an-kad’an zuciyarsa ke aiki, ba kamar kowanne bugun zuciya dake tafiya normal ba. Sai naji tausayinsa ya kamani, cikin sanyin murya nima nace,
“yalla6ai kayi hak’uri da abinda zan fad’a maka, inhar ka kawoni gidanka ne domin muyi aiki tare a matsayin Friend bai kamata ace ka gaza yarda daniba akan sirrinka. kasan minene yake saka kwalwarka da zuciyarka wannan nauyin kuwa?”.
Kansa ya girgiza mini.
Na gyara kwanciyata ina kallon p.o.p, “Matsalarka d’ayace baka yarda da kowa ba sai kanka, mu cire Momma da papi, dansu aiyukansu sunkai amusu uzuri, Momma hankalinta akan jiyya yake, dan haka kana k’ara mata damuwa, papi kuma babbane shawara da dabarun manya kawai kake buk’ata daga garesa. Sai kuma Muftahu da Harun nakula suma kakan d’an saki jiki dasu akan wasu abubuwan, to amma fa………”.
Saitayi shiru bata k’arasaba.
Ya matso jikinta sosai, tare da d’ora hannunsa saman cikinta, murya k’asa-k’asa yace, “Harun da Muftahu amma fa mi? Please ki k’arasa mana”.
Kad’an Na juyo nad’an kallesa, Na d’ora hannuna nima akan nasa daya d’ora akan cikina. Janye fuskata nayi Na koma kallon p.o.p d’in. “kayi hak’uri da abinda nake fad’a, badan ina zarginsu bane zan fad’a d’in, dama zancene Harun da Muftahu kuma kamar bai kamata 100% susan komaiba, dan za’a iya sayensu ko tursasasu suci dunduniyarka. domin koba komai har yanzu bakada tabbas d’in cewar babu hannun wasu a cikin masarautar nan. amma kayi hak’uri idan na shiga hurumin daba nawaba”.
Shiru yay baice komaiba tsawon lokaci, har nayi zaton nayi laifi ko yayi barci, a sanyaye nakuma fad’in “please & please kamin afuwa yalla6ai”.
“is okay”. ‘kawai ya fad’a yana kuma sakani a jikinsa, tareda d’ora ha6arsa saman kaina.
Babu Wanda yasake magana a tsakaninmu, kowa yay shiru yana k’ullawa da kwancewa, har dai barci yafara fisgata.
“Kina ganin su Aiyaan bazasuyi kuka ba idan suka farka sukaga su kad’aine?”.
Naji maganarsa cikin kunnena.
“a’a” na fad’a ina girgiza masa kai, “ko’a gida sukad’ai suke kwana dama”.
“okay”.
Saikuma muka kuma yin shiru, har barci yakuma fara d’aukata yakuma fad’in “kozaki sha Magani ne?”. ‘yay maganar yana ta6a gefen wuyana’.
Kaina Na girgiza masa batareda nace uffanba. shima bai sake cewa komaiba..
Yanda numfashina ke sauka a hankali sai ya fahimci nayi barci, shiko gaba d’aya yakasa nasa barcin, tunanin wani Abu daya ta6a faruwa a baya ya fad’o masa, dukda shi ba yayi imani da hakan baneba.
????????
*_Wata ranar juma’a a India, sai suka tashi da matsananciyar damuwar motsawar ciwon Abie, a time d’in ma sun zata rai zaiyi halinsa, hankalin Galadima ya tashi har ciwonsa shima yakai ga motsawa, amma yak’i yarda doctors su dubashi, yace abarsa kawai gara ya mutu ya huta, hankalinsu momma ya tashi, amma Galadima yak’i sauraren kowa, daga k’arshema saiya sulale daga asibitin ya fice abinsa, haka yayta tafiya rik’e da k’irjinsa saboda azabar ciwon da zuciyarsa ke masa, mutane sai kallonsa sukeyi, shiko baimasan sunayiba, yayi tafiya mai nisan gaske batareda yasaniba. k’arfinsa da kuzarinsa sukai gazawar da bazai iya cigaba da tafiyanba, shine yazube a wajen ya fad’i._*
*_bai tashi farkawa ba sai awani d’aki mai kama dana bunu, ya yunk’ura zai mik’e amma saiya kasa, wani tsoho ba indiye, a cikin indiyawan ma irin masu k’yawunnan sosai, ya dafa kafad’arsa, cikin harshensu yace ma Galadima “koma ka kwanta d’an saurayi, bakada lafiyane”. Galadima yace “kayi hak’uri baba gida zanje nasamu sauk’i, zamana annan bak’aramin tashin hankali bane ga ahalina”. tsohon yay murmushinsu Na manya, yace “zakaje gida d’ana, ni da kainama zan kaika, amma lallai kai acikin al’amuranka akwai abubuwan ban mamaki da al’ajabi, gakuma tsantsar rud’ani, saidai komai yanada lokacinsa, kuma lokaci zai tabbatar maka hakan, albishir d’aya zanmaka, nanda wasu shekaru dabasu Gaza 7 ba mai taimakonka zatazo, kwarai zatazo gareka, ba lallaine ka fahimci abinda nake fad’aba ko yarda dani, Dan Na lura kaid’in musulmine, kuma bad’an wannan k’asarba, amma wannan mai taimakon naka itace zata zama fitilar haska maka hanya kakai ga cinmma burinka, domin taurarinta da naka sunada matuk’ar k’arfi, harma suna gogayya da juna, zaku zama sh……..”. Saikuma yayi shiru yana murmushi, ya shafa kan Galadima yana fad’in “tarin Albarka sucigaba da baibaye rayuwarka data zuri’arka”._*
*_daga wannan maganar sai barci mai nauyi ya kwashe Galadima, koda ya farka saiya gansa a asibiti tareda su Momma, yata tambayarsu INA tsohon yake sukace su basu San wani tsohoba, wasu samarine su biyu suka kawoshi asibitin, wai sungansa yafad’i a gefen hanya, zancen tsohon yata damun Galadima a time d’in har yayta bincike kozai gansa amma ko alamun mai kamarsa bai ta6a ganiba, daga hakama saiya cire abin a ransa yacigaba da harkokinsa._*
Ajiyar zuciya ya sauke, tareda kuma rungume Munaya, a kan la66ansa ya furta “ALLAH kaine mafi sani”. daga haka yay shiru tareda lumshe idanunsa, barcine yayta fusgarsa harya samu nasarar sacesa.
Can gabannin asuba yay wani mafarkin daya sakashi farkawa a firgice, har itama Munaya ta farka tana tambayarsa lafiya?.
Kansa ya dafe, da hannu yaymin nuni na bashi ruwa.
Sauka nayi daga gadon dan zazzza6inna ya fara hucewa nima, freight na bud’e na d’akko masa ruwa, na had’o da Kofi, zama nayi kusa dashi a gefen gadon na tsiyaya ruwan a Kofi na mik’a masa. kar6a yayi ya shanye, ya mik’o min kofin, zan kar6a ya girgiza min kai tare da min nuni da in k’ara masa.
Kuma tsiyaya masa nayi, yakai rabi ya d’aga min hannu alamar ya Isa, bayan yakuma shanyewa ya mik’a min kofin yana fad’in “Thanks”.
Kar6ar kofin nayi, ba tareda na tashiba nace “Yalla6ai lafiya kuwa”..
“Mafarki”. ‘yafad’a yana komawa ya kwanta’.
Idanu kawai Na zuba masa, kusan 4minutes ya juyo da kansa ya kalleni, “kizo ki kwanta mana”.
K’aramar ajiyar zuciya kawai Na sauke Na mik’e, Na d’ora ruwan da Kofi a dirowan gefen gadon na koma inda nake na kwanta.
Ganin ya sauya hannun da yay mafarkin kuma yana addu’a sai ban sake cewa komaiba, na kwanta shiru ina sak’e-sak’e a raina mafarkin mi yayi to? da har yasakashi firgita irin haka?. banida mai bani amsa dan haka nayi shiru.
Saiya zamto da asuba na rigashi tashi, harma saida nayi alwala sannan na tadashi, da k’yar ya iya tashi yana dafe kai, binsa nayi da kallo kawai harya shige toilet.
Lokacin daya fito na fara salla, dan haka saiya fice kawai. A mamakinsa saiya iske Aiyaan da Aryaan sun tashi suna alwala, hakan ya Burgesa sosai. Sai kawai ya kama hannunsu suka tafi massalaci.
Bayan an idar da salla bai yarda sun had’u da Sarki ba, ya gudo. Sai dai abinda bai saniba shi Sarki ya gansa, dan yau ya makara salla shima.
Wajen Around 9am nagama gyaran d’aki nayi wanka, saina d’an fito falon domin duba dubawa, natarar sabbin kuyangina suma komai sun gyarashi k’al, harma da mana break fast, banyi yunk’urin bud’ewa ba ma balle tunanin son ci, dukda kuwa natashi da yunwa, to amma Momma ta gargad’eni sosai akan cin abinci wani a masarautar, dan haka na fito daga kitchen d’in kawai.
Tunkan na shigo nake jiyo maganarsu Aryaan, zaune na iske Galadima su Aiyaan na kusa dashi suna bashi labari, anmusu wanka tsaf, sunsha sabbin kaya iri d’aya.
Har yanzu Galadima bayada walwala, na zauna ina gaisheshi, batareda yabar latsa wayarba ya amsa min, su Aiyaan suka dawo kusa dani suna gaisheni, kumatunsu naja ina murmushi, “oh my guys kunsha k’yau, waya muku wanka haka?”..
Atare suka amsa min da fad’in “Uncle ne, kuma ya saka mana tirare yanda kuke mana”.
Murmushi nayi, na saci kallon Galadima da yay biris damu kamar baya d’akin, alhalin sanda na shigo na iske suna hira shidasu ‘yan 2.
Sallamar da wata baiwa keta kwad’awa na amsa, sannan na mik’e na fita dannaji minene? A k’ofar falona na isketa, nace, “miya farune?”.
Duk’ewa tayi ta gaisheni, sannan ta mik’omin ledojin hannunta tana sanarmin Sarkin motane yace “na kawo wannan ranki ya dad’e”.
Kar6a nayi, na koma ciki.
Ajiye ledojin nayi a gabansa, “gashi wai inji sarkin mota”.
Idanunsa ya d’ago ya kalleni, yace, “breakfast d’inku ne”.
Tashi yay ya fita yana fad’in na shirya zaije ya dawo mu shiga cikin gida gaida mutane.
Na amsa masa da to.
___________________
Tun a daren jiya wasu bayi sukaga Muftahu, dan haka suka shiga ihu, dandanan sauran bayin dake kusa da wajan suka firfito, manyan bayin cikinsu ne suka kai maganar cikin gida, shine akasakasu d’aukar Muftahu su shiga dashi.
Lamarin yabama kowa mamaki, babu wani mummunan rauni a jikinsa, inbanda d’an jini dake gefen bakinsa, saidai sun sami kwanciyar hankali ganin yana numfashi.
Maganar dawowar Muftahu bata baje masarautar ba sai washe gari.
Bayan Galadima ya fito daga sashensa zaije fada yaji anata k’ananun magana akan dawowar Muftahu, saidai kuma miskilancinsa bai barsa ya tambayi kowaba ya nufi Fada.
Ya isa mai martaba baikai ga isowa ba, dan haka suka gaisa da ‘yan majilissar Sarki dake fadar, sannan ya nemi mazauninsa dake gefen Sarki Na dama ya zauna.
Zamansa baifi da mintuna 10 ba Mai martaba ya iso, gaba d’aya suka mik’e tsaye, dogaran Sarki sunata kirari da fad’in gyara kintsi da k’yau, duksun baza riguna ba’a gani mai martaba, basu bar kowa ya gansa ba har saida ya zauna a kujerarsa.
Baya suka mammatsa mai martaba ya bayyana, atare su Galadima suka rissinar dakai alamun girmamawa, sannan kowa yafito tsakkiyar fada ya mik’a gaisuwarsa ga Sarki, yayinda fadawa ke faman amsawa, tsakanin Sarki dasu kuwa shine d’aga hannu.
Mai martaba yayi mamakin ganin Galadima yau azaman fada, bawai baya zaman bane, sai dai yakan dad’e bai zaunaba, an masa uzurine kasancewar ansan ba zaune yake dindin dinba, kuma idan yazo akwai harkokinsa Na kasuwanci da yakeyi, sai dai dolene yakan shigo yayi gaisuwa.
Bayan fada ta nutsu aka fara fadanci.
K’a idane fadar gagara badau takanyi fadancine a sati sau hud’u kawai, litinin ba’a zaman fada, domin ranace da ake tunawa da abinda ya faru ga tsohon Sarki mahaifin Galadima, talata, laraba, alhamis, asabar, sune ranakun da ake fadanci, ranar juma’a ma ba’ayi saboda muhimmancin ranar ga al’ummar musulmi. A wad’annan ranakun akanyi zamanne daga 10am zuwa 12:30pm, da an tafi sallar zuhur ba’a dawowa, idan kaga anwuce wannan time d’in a fada to tabbas akwai abinda ya farune.
A wannan zaman fadancine maganar dawowar Muftahu ta fito, sun tattauna akai harda shirin kuma d’aukar matakai Na tsaro a masarautar.
Bayan anyi sallar zuhur ne Sarki ya shige gida, sauran fadawa ma kowa ya kama gabansa, Galadima bai shiga gidaba saiya nufi sashen su Muftahu domin dubashi.
Bayan an masa iso ya shiga, ya iske mahaifiyar Muftahu da ‘yan uwansa zagaye dashi, har yanzu kuma yana cikin yanayin barci.
Ya jajanta musu, Yakuma kwantarma da mamansu Muftahu hankali, kusan mintunsa talatin ya fito ya koma sashensa.
Ya iske su Aiyaan kawai a falon Munaya suna kallo, suka taso da gudunsu suka rungumesa, fuskarsa cikeda fara’a ya tarbesu, ya tambayesu ina Auntynsu?.
A tare suka bashi amsa, “Uncle tana d’aki ta kwanta kuma tace karmu tadata, inba hakaba jiki magayi”.
Murmushi yayi yaja kumatunsu, “kuce zatayi zana kenan idan aka tada ita?”.
Nanma atare suka amsa da “eh Uncle, kasanfa Aunty Munaya tacika fad’a, gidanmu tsoron masifarta akeyi, amma ita Aunty Munubiya babu ruwanta”.
Galadima yace, “da gaske?”.
“ALLAH kuwa Uncle, idanfa mukayi rashinji ita ke zanemu ba innarmu ba, kuma dukanta da zafi, gashi taita hararmu da katun-k’atun idanunta nan”.
Sosai abin yabama galadima dariya, dan haka ya dara sosai abinsa yana fad’in, “kubari tajiku to, idan ta zaneku babu ruwana nidai, kunga bara naje naga kota tashi, karfa Ku shigo, dan zata iya zaneku”.
Sukace “ai bazamu shigoba Uncle”.
Yace, “good boys”.
Da sallama ya shigo, amma saiya isketa baje a gado tana shak’ar barcinta, yad’an murmusa kafin ya k’arasa ya zauna a bakin gadon saitin fuskarta, yatsunsa biyu yasaka a gefen wuyanta dan yasan da wahala wannan barcin ya kasance na lafiya, aikam jikinta ringim yake da zazza6i, tausayinta ya kamashi, lallai uwa dabance acikin al’umma, Ashe haka sukeshan wala, tundaga d’aukar cikinma zuwa rainonsa, akoma rainon yaro, daganan tarbiyarsa, lallai masu raina mata ko kallonsu masu k’arancin tunani sune masu k’arancin tunanin ai, ya d’an lumshe idanunsa yana cije lips, ganin ta dunk’ule a waje d’aya saiya ja bargo ya lullu6a mata, harya mik’e ya koma ya zauna, risinowa yay kanta a hankali ya mannama goshinta kiss, sannan yamik’e ya fice.
Koda ya dawo saiya wuce d’akinsa, yabar su Aiyaan suna kallonsu.
Kayan jikinsa ya cire ya kwanta shima, dan yana buk’atar hutawa kona 2hours ne, kwanciyarsa kuwa babu dad’ewa barci ya saceshi.
Kiran sallar la’asarne ya tashesu kusan lokaci d’aya, Galadima yatashi da k’yar, a mamakinsa sai yaga Aiyaan da Aryaan kwance a gefensa suma suna barci, murmushi kawai yayi yasako, saida ya watsa ruwa sannan yay shirin tafiya massalaci cikin k’ananun kaya.
Harzai fita saiya dawo yashiga wajen Munaya. tana tsaye gaban wardrobe tana neman kaya, da alama wanka tayi, dan daga ita sai towel.
Banji sallamarsa ba, saboda shi idan zaiyi magana bayason bud’e baki, ganin batajishiba saiyayi gyaran murya, a tsorace na waigoshi, ganin shine nai saurin saka kayan dana d’akko ina kare k’irjinna da tura baki, bakinsa ya d’an ta6e, sai kuma ya shiga takowa inda nake, duk takun da yayi sai gabanna ya fad’i, na waiga kozan samu nabar wajen ko abinda zan suturta jikinta sosai, amma sainaga babu a kusa, kuma ina jikin wardrobe d’inne sosai ai. ban gama yanke shawara ba ya k’araso daf da ni, kuma matsawa nayi na matse jikinna sosai a drowa d’in, shikuma yawani had’e gabas da yamma, wannan ne yakuma sakamin tsoronsa a raina, na zata kowata tsiyarce ta kawoshi.
Hannu yasaka ya d’ago da ha6arta muka kalli juna, ya tsareni da idanu yanda nakasa janye nawa cikin nashin, munkai kusan 2minutes a haka, kafin yakumamatsoni sosai, ya kai fuskarsa gab da tawa tamkar zai had’e bakinmu, dan haka saina lumshe idanu, murmushi yayi ya hura mata iska akan idanun, ta rumtse idon sosai, ya d’an ja baya yana ta6e baki, kafin yasaka hannu ya cire nata dataketa faman kare k’irji da kayanta, still ya kuma matsawar saitin kunnenta yana fad’in “wane darene jemage bai ganiba yalla6iya”. ‘ya k’are maganar da shafa kirjina ya fice abinsa.
Kad’an yarage namasa ihu wlhy, aiko yana fita na durk’ushe a wajen ina sauke numfashi, sometimes nakan rasa yazan fassara Galadima da ayyukansa.
Da k’yar Na iya tashi nayi sallar nakoma kan gado Na kwanta.
Galadima kam daya fita dariya ce taita cinsa, ya kula Munaya akwai tsoro, kuma haryanzu a tsorace take dashi, cikinnan ne kawai kanci galaba akanta yake samunta cikin sauk’i, ya girgiza kansa kawai yana murmushi.
Bayan ya dawo massalaci d’akin nata ya dawo, dan yanason suje su gaida jama’ar gidan, maybe gobe suje masarautar papi ma.
A kwance ya iskeni, nak’i kallonsa, jingina yay da mirror yana fad’in “yaya jikin naki?”.
Ban kalleshinba nace, “da sauk’i”.
“ALLAH ya k’ara sauki, idan zaki iya tashi ki shirya muje cikin gida, kafin waccan tsohuwar tafarama mutane surutu”.
“to” nafad’a ina mik’ewa, Na sakko a gadon, harna nufi wardrobe zan d’auki alk’yabba saina tsaya, batareda Na kalleshi ba nace, “toka fita Na shirya”.
Hard’e hannayensa yayi a k’irji yana fad’in “ashe bazaki shirya d’inba, dan bazanje ko inaba”.
“karkaje d’in, ai akwai bayi” nayi maganar a zuciyata.
Kayan Na d’auka na shiga toilet, shikuma ya ta6e baki.
Babu dad’ewa na fito tsaf, nayi k’yau, nazo ta gefensa na d’auki turare nasaka kad’an sannan na kallesa nace, “na shirya”.
Baice komaiba ya nunamin hanya, gaba nayi yana bina a baya muka fice.
Kasancewar tazarar dake d’an tsakaninmu da sassan nasu muka shiga mota, dan banajin dad’in jikinna, bama zan iya tafiyarba.
6angaren Abba hayatudden muka fara zuwa, daga nan sai sashen matan mai martaba, soyayyar da uwargidansa ke nunamin yasani k’ara k’aunarta, sai addu’a take zabgamin akan ALLAH ya saukeni lafiya. Galadima kad’ai ke amsawa, amma ni saidai a zuciya kawai. daga nan muka d’an shishshiga wasu sassa, 6angaren mama fulani shine k’arshen zuwanmu.
Kunsan dai mutuniyar taku akan mulki, tana kishingid’e kuyanginta nata bauta, mai matsa kafa daban mai firfita daban, ga masu bata labarai, tufa takeci cikeda k’asaita da izza.
Amintacciyar baiwarta data mana iso tana gaba muna biye, mama Fulani ta d’agama kuyanginta hannu alamar subata waje.
Rige-rigen ficewa suka, yayinda mukuma muka k’arasa gareta, idonta a kammu ko k’yaftawa batayi, nidai tsarin ALLAH na nema daga sharrinta, ina dalili wannan kallon k’urilla haka?.
Galadima yace, “barka da yammaci”. nima saurin fad’a nayi.
A yatsine ta amsa mana, ta d’ora da fad’in “Saraki kayi wuyar gani?”.
Galadima ya murmusa yana kallona, “Ranki ya dad’e kinsan mai amarya ai yafi dubu wahalar gani dama”.
“Humm” kawai tace batareda ta amsaba.
Sai zuwa can tace “nafa manta, ina tayaku murnar samun k’aruwa”.
“mun gode ranki ya dad’e, amma taki murnar itace tazo a latti, gashi kuma idonkine yafara hango abin cikin kwan tun a india”.
Mama Fulani ta tsatstsare Galadima da idanu, shikuma yay salute nata yana murmushi.
Jitai kamar zata makesa dan haushi.
Ya lura da haushin da taji, dan haka ya kama hannuna muka mik’e tsaye yana fad’in, “bara mukoma inda muka fito ranki ya dad’e, a huta lafiya”.
Bai jira amsartaba mukayi fitowarmu.
Da kallo kawai ta bimu, takasa koda motsawa, tarasa miyyasa yau Galadima da matarsa suka mata wani mugun kwarjini? batada mai bata amsar tambayar tata…
Yini guda yau Galadima a gida yayishi, baije ko inaba, sai da daddare Nuren yazo sukayi magana, daga nan yace ya nema mana tickets d’in zuwa masarautarsu.
Washe gari muka tashi da shirin tafiya masarautar su papi, mukad’ai muka tafi, babu kuyangi babu dogarai, dagani sai shi dasu Aiyaan, sai Nuren………………
????
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*????????????
*_typing????_*
???? *_HASKE WRITERS. ASSO….._*
*_♦RAINA KAMA…..!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
~Book 2~ ????????1⃣5⃣
……………….Abin yabani mamaki ganin yanda akazo tarbarmu, yo saikace wani Sarki, hakan yakuma tabbatarmin da Galadima d’an gatane a wannan masarautar.
A masarautar ma gungun mutane muka iske wai masu tarbarmu, ni dukma sai kunya ta kamani wlhy, musamman da Mom ta rungumeni tana fad’in “ga maman twins d’inmu ga Maman twins d’inmu”.
Galadima dai murmushi yayi, Nuren kam dariya ya kemin.
Lallai naga tsantsar soyayya a wannan masarauta, sai nan nan ake dani kamar wata sarauniya, duk wani Motsina Inno tace minakeso? hakama mom.
Aiyaan da Aryaan kam ai suna tare da Galadima, duk inda yasaka k’afa suna biye.
Nikam dai a kwana biyun da mukayi babu abinda zance da wad’annan bayin ALLAH sai godiya, naga karamci naga hallaci sosai, hakama k’annena.
Sosai Galadima yasamu tattaunawa da papi a tsakaninnan, sunyi maganganu masu muhimmancin gaske. Musamman akan ciwon Abie da cikin jikin Munaya, harma da Abbanta. sosai kuma Galadima yakuma samun haske akan lamuran.
Kwannamu biyu muka dawo cikeda kewarsu, tare da tarin alkairi ga wad’annan mutane masu tsayawa a rai.
Mun dawo da kwana 1 yaran gidanmu na ma’auri suka kawomin ziyara.
Aunty khaleesa, aunty Hauwa’u, aunty Ramlah, aunty Raheenat, matansu ya hameed, Fiddausi, Siyama, Zarah, Safara’u, Fauziyya, Haleematu,Munubiya, Ayusher, Feena. Wayyo dad’i wlhy saika d’auka biki akeyi, rasa inda zansaka kaina nayi saboda dad’i, shi kansa Galadima ya fahimci ina tare da tsantsar farinciki, nima dagewa nayi namusu hidima iya hidima, dan hardani aka shiga kitchen.
Sukam duksun rikice da mamaki, dama haka gidan sarautar yake, dan saidama Galadima yaje da kansa ya shigo dasu. Su Aiyaan anata murna anga ‘yan gida.
Ranar dai anan suka yini zir, dazasu tafi Galadima yay muzu alkairi mai yawa tareda godiya ta musamman. Sunji dad’i sosai kuma sunyi farinciki, sunata masa godiya nima ina tayasu.
Da zasu tafi jinai tamkar na rik’esu, aiko harda ‘yan kwallana, sauk’inama kawai su Aryaan tare dani.
Kowaccensu tatafi da labarin data gumtsawa uwarta a bayan fage, dansu Zarah dai sun Shiga taitayinsu, sun gane ruwa ba sa’an kwando bane, nanfa hassada da bak’inciki tamkar ta babbake zukatansu, mamansu Yaa hameed hardama Abba ALLAH ya Isa tana sharar kwalla, wai yasan da gidan sarautar amma ya yarda Zarah ta auri d’an sanata, ga aunty khaleesa nanma kullum cikin matsala da miji, dan kishiyarta akwai kissa.
*_ALLAH yarabamu da ciwon hassada fans_*????
Sati d’aya da zuwansu muka koma India, saboda Company suna Neman Galadima da gaggawa. harda innaro iya bala’i muka tafi????.
A jirgi taita kudundune fuska a gyale wai batason ganin tashin jirgi, duk tsare gidan Galadima saida yayi dariya, Aryaan da Aryaan kam sukaita tsokanarta. Yau babu masifarnan dan bata kulasuba, saima Galadima ne ya hanasu. nikam banza na musu dan tawama ta isheni nikam. Jikina sai ciwo yakeyi, ga cikina na mun ciwo shima kad’an-kad’an.
Khumar da Sauban da Samha sukazo d’aukarmu, muka rungume juna da samha muna farinciki.
Daga nan muka wuce gida, yaukam munashan k’auyancin innaro, ni harma tabani haushi, komai tagani saita tambaya, Kodai su Aiyaan basa abinda takeyi.
Mun iske jakadiyane kawai sai bayi, Su Momma da innarmu suna asibiti, Mudai sama muka haye ni da shi, ‘yan biyu kuwa suna wajen Samha ta kasa ta tsare, innaro kuma aka barta da jakadiya.
Ko ina tsaf yasha gyara tamkar mai d’akin na nan, Muna shiga kwanciya nayi bisa kujera, naja bargon saman gadon na lullu6e, kallona yayi da mamaki “k lafiyarki kuwa?”.
“zazza6i”. kawai nace masa na k’udundune har kaina.
Zama kawai yayi ya zubamin idanu cike da tausayi, ganin zaman bazai masaba yatashi ya shiga toilet, saida ya gama dukkan uzirinsa sannan nima ya had’amin ruwan wanka, tadani yayi, na tashi da k’yar tamkar zan masa kuka.
Yace, “tashi kije kiyi wanka kozakiji dad’i”.
Baki na tura masa gaba.
“idan bazaki iyaba tashi muje na miki”. ‘yay maganar cike da basarwa’.
Harara na zuba masa sannan na mik’e na nufi bayin. shikuma ya ta6e baki yana wani mikilin Murmushi.
Abincima sai nan ya saka aka kawomin, dan nakasa sauka.
Innaro sai catake wai nacika langyare, dan naga yana shagwa6anine shiyyasa nake ta6ara, ai badaga kaina aka fara cikiba.
Galadima dai murmushi kawai yayi danshi lamarin innaro abin dariya ya d’aukesa, tana buk’atar uzuri.
Bayan nasamu naci abinci daya bani nasha magani, harzan kwanta a sofa yace na koma saman gadon, kamar zanyi magana saina fasa, na tashi kawai na koma.
Yana kammala duk abinda ya dace yafice asibiti domin duba Abie da Abba.
Yaji dad’in yanda yaga canji sosai a jikin nasu su duka, dan raunuka da yawa sun warke a jikin Abba, da bakinshi ma ya amsa masa gaisuwa yana masa godiya, inna da baba k’arami sunata saka masa albarka. maganar da abie ya fara kuwa rungumesa yayi yana kuka Abie nayi, hakama su Momma, a hankali Abie yace “ina d’iyata Muh’d”.
Murmushi Galadima yayi, yace, “zuwa anjima zaka ganta Abie, yanzu na barta tana barci zazza6i ya rufeta”.
Momma da Aunty Mimi sukace “ALLAH dai ya sauketa lafiya to”.
Babu kunya Galadima ya amsa da amin.
Aunty Mimi dake kusan dashi ta doki gefen hannunsa, “kai mara kunya, shine zaka amsa”.
Hannu ya saka ya rufe bakinsa yana fad’in “ni jikan Abdul’fatah da Abubakar”.
Dak’uwa Momma tamasa tana kai masa duka, ya matsa da sauri yana dariya.
Abie ma murmushi yakeyi, lallai yau yakuma ganin canji tare da d’ansa sanyin idaniyarsa, sukam yaushe rabon da suga irin wannan nutsuwar tare dashi haka, lallai dolene su godema ALLAH da shigowar Munaya cikin rayuwarsa, basu da wani abinda zasu iya biyanta har abadan, saidai suyita mata fatan alkairi da k’yautata rayuwarta.
Saida na tashi sannan muka tafi asibitin muma, wajen su momma muka fara zuwa, Momma da aunty Mimi sukazo suka rungumeni tamkar zasu had’iyeni dan dad’i, nikam duk kunyarsu ta gallabeni, sai 6oye fuska nakeyi, koda zan gaida Abie ban yarda na kalleshiba.
Sauban da Samha sai dariya sukemin.
Duk bak’in halin innaro saida tayi kuka ganin halinda Abie yake ciki, taita kwarara masa addu’a kuwa.
Su momma sunji dad’i, kuma sunata girmamata.
Samha sai dama-dama takeyi dasu Aiyaan, motsi kad’an tace, “ALLAH yasa Aunty gimbiya muma ta Haifa mana irinku”. Su Momma sunata amsa mata da amin. Nidai kaina na k’asa saboda kunya, ina lura da Galadima kuwa duk sanda tafad’a saiya murmusa kuma bakinsa ya motsa alamar yana amsawa da amin.
Sosai naji dad’in ganin jikin Abbanmu shima, dan har magana mukayi, jikinsa yayi k’yau sosai, karayunne ma kawai suka rage nakula, amma k’ananun ciwukan duksun warke, to wajene dayake samun kulawa ta musamman. Munaya harda rungume inna, itako ta tureta tana hararta, su Aiyaan kam duk sun d’are bisa cinyarta suna d’okin ganinta da kewarta. Itama tayi kewarsu over, tsakanin uwa da d’a kenan (iyaye mata ga naku fa????????????
????????).
Haka muka dawo gida ina farinciki, koba komai nasamu nutsuwa mai yawa a yau d’innan, aiko ban yarda mun kwantaba saida nayi nafilfili domin mik’a godiya ta ga ubangijin sammai sannan na kwanta.
Galadima kuwa muna shigowa d’akin sirrinsa ya shiga yanata aiki.
___________________________
Hankalin Minister ya kai k’ololuwar tashi shida families nasa akan 6atan ‘yarsa, farhat, duk wata hanya daya kamata subi sunbita amma babu koda labarin Wanda ya ganta, tun lamarin nabasu mamaki harya koma basu tsoro, ga wani text massage da akama minister d’in d’in kwana 10 daya wuce.
_Idan kana buk’atar ‘yarka kana iya mik’a wuya._
Wannan massage ya tsaya masa a rai, har police sun kar6a amma sun gaza gane komai gameda massage d’in ko wannada ya turo shi.
Mahaifiyar Farhat harda kwanciya asibiti, dan ita kad’aice mace a gidan, dan haka suke masifar son yarinyar da mata gata, dudu shekarunta 16 ne kawai, tana wata private boarding school ne a abuja. a binciken da Galadima yakeyine ya gano hakan, kuma yayta bibiyar yarinyar har saida yasamu nasarar saka Nuren ya kwamuso masa ita.
___________________________
Tunda muka dawo India bani da lafiya, kullum innaro cikin min gorin ni ragguwace take, bana wani kulata dan tawa ta isheni, koma uwarmi zata fad’a ta shekara fad’i, bazan yarda mu Raba hali a gidan surukai naba, nakan bar lamarinta a wasan jika da kaka agabansu, amma ni nasan badan hakan takeyimin ba, ita kanta innarmu bata kulata ko kad’an, idan tanayi shiru take mata ma.
Kulawa kam bazanyi butulciba ina samu wajen Galadima dasu Momma, musamman ma jakadiya da Aunty Mimi. Saukina ma cikin bamai tsurfa baneba, komai inaci hankali kwance, kuma ban ta6a amaiba ko wani zubda yawu, saidai zazza6i da ciwon jiki.
Yaudai dole Akash yazo har gida ya sakamin k’arin ruwa, kozan sami sasaauci.
Yini guda yau a gida Galadima yayisa, duk wani motsina akan idonsane.
**************************
*_5 months ago_*????????????????
A kwana atashi babu wahala wajen ubangiji, rayuwa ta shud’a, kwanaki nata sauri, a wanni da mintuna kam ai ba’a cewa komai, abubuwa masu yawan gaske sun faru a watanni biyar d’innan, ciki harda warkewar Abbanmu sarai, tamkarma baiyiba, saidai k’afarsa da yakan d’an tizgid’a saboda matsala data samu, shima saika k’uramasa I done zaka fahimci hakan.
Innaro dai dasu Aiyaan tuni suka koma saboda makaranta, sai dai duk Hutu Galadima yakansa azo dasu Aiyaan d’in, hakama Munubiya da yaa marwan sunzo sun mana sati biyu sukaga jikin Abba da Abie.
A wattani biyar d’inna Galadima yaje Nigeria kusan sau hud’u, dukda bai ta6a fad’amin wani abuba ina samun bayanai ga Saleem da sarkin Mota. har yanzu kuma Farhan d’iyar minister tana hannunsa, hakama Malam Saminu driver Alhaji Balala.
Yaran gidanmu masu cikkuna duksun haihu, su Siyama an zama iyaye, naji haushin rashin halartar taron suna ko d’aya, dan dana fad’ama Galadima inason zuwa banza yamin, naci kukana kuwa na hak’ura, sai turomin abubuwan da akayi sukaitayi ina gani.
Cikina ya fito kwarai da gaske, dan yanzu yana cikin wattani 7 da wasi kwanaki, yamin d’as yakuma sakani k’iba, duk kamannina sun canja, kumatuna sunyi manya, dukdai wanda ya ganni zaisan na canja, hakama Munubiya, idan ta turomin hotonta nata dariya kenan.
Tsakanina da Galadima kuwa har yanzu muna a yanda kowa ya sammu, canji d’aya zance ansamu shine nuna yawan tausayinsa akan cikin jikina, dan dukkan wani motsina cikin nuna damuwarsa yake. Idan yana wajen aiki kam yakan kirani sau uku sau hud’u dan yaji lafiyata kawai.
A 6angaren iyayensa da danginsa kam banida abin fad’a sai godiyar ALLAH, dan tamkar a kainane aka fara ciki haka suke nunamin kulawa.
Hakan nama Innarmu da Abba dad’i, hankalinsu na kuma kwanciya sosai akan aurenmu. baba k’arami yakanyi wata d’aya ya tafi Dady kuma yazo, haka suka dingayi har ALLAH yabama Abba lafiya.
Jikin Abie ma said dai muyitama ALLAH godiya, dan bayan magana an kuma samun cigaba 6angaren motsa hannunsa, yanzu kuma maganarsa takan d’an fito yanda akeji, saidai duk wannan cigaban da ake samu babu Wanda yasan dashi, har mai martaba k’aninsa, kaf masarautar gagara badau da dukkan wani makusanci bai San komaiba a kai, dan papi yahana fidda maganar, ko zuwa akai dubashi yakan komane tamkar yanda ya saba kamar da, daga mama Fulani har mai martaba sunzo kusan sau uku dubashi, hakama Muftahu da Harun, ‘ya’yan Sarki ma dama suna k’ok’arinzuwa lokaci-lokaci suma. Hakama Hayatuddin Autan mama Fulani. amma babu Wanda aka bama damar sanin wani sirri akan jikin Abie d’in. dagamu sai mu kawai muka Sani.
Dukda fama danake da kaina haka na dage muka cigaba da addu’oin nan, zuwan innarmu ma yakuma sakamu ho66asa saboda taimakon da take bamu, sannan muka raba addu’oin ga wasu musulmai malamai dake nan suma suka cigaba da tayamu, aka cigaba da bama Abie yanasha da wanka, doctors d’in sunyi surutunsu harsun gaji sun barmu, dan munk’i fasa masa amfani dasu, tunda muna ganin haske a lamarin sosai.
A wata ranar talatar da su Abba suke shirin tafiya k’arshen satinne ina zaune a falo ni kad’ai, dan Galadima ya fita aiki tun safe, zafine ya isheni na dawo falon na k’ure AC, dan Galadima ya saka ma na bedroom d’in key saboda k’urewa da nakeyi, gashi inata fama da mura, shi kansa abin cikina ance tana Neman shafarsa. nikam bana iya hak’uri da Abu mai sanyi konasha ko AC.
Sosai na baje ina kwasar dad’ina, sai faman lumshe idanu nake a cikin kujera, gama wayarmu kenan da Munubiya itama tana bani labarin halin son Abu mai sanyin datake a ciki, kullum Yaa marwan fad’a shida mama Rabi’a amma bata d’aga k’afa, data faki ido saita sha, Ayusher da dole ta dawo gidan tayata wasu abubuwan saita gani ta sanarma Yaa marwan, shikuma yay ta jarabar masifa, amma hakan bazai hana gobe tagani ta shaba……..
Jinai kawai iskar dake ratsani ta daina shigata, na bud’e ido sai naga Galadima tsaye jikin k’arfen bene daya shigo ta falon ya hard’e hannayensa a k’irji ya zubamin ido ransa a 6ace, hannunsa rik’e da remote d’in ACn.
Tsorone ya kama ni, na tashi zaune ina wani marmar da idanu, da hura kumatu danaketa yi, takowa yayi inda nake, idonsa tamkar zai fad’o dan hararata “k kin rainani ko? bazan hanaki Abu sau d’aya ki daina ba, ki duba muran dake damunki tun cikinnan nada wata 3, shin ke bazaki tausayama kanki baneba?”.
Shiru nayi bance masa Uffanba, sai faman kumbura baki dai nake yi.
“kinsan ALLAH idan baki maida wannan bakinba na kamashi saiyayi jini”.
Da Sauri na maida bakina, dan ban manta muguntar da yaminba kwana biyu daya wuce, ba k’aramin morata yakeba yanzu, saboda ALLAH yabani ciki mai sakani yawan buk’ata, sai komai ya lafa nayita masa kuka, shikam ya shareni saboda shegen miskilanci da k’asaita, idan na ishesa yace zai makeni, aibashi yace na kawo kaina ba, dan haka nabar cika masa kunne da ihu, anjima ma nazo yi zaiyi tunda ba fyad’e yaminba ninake kawo kaina.
Sometimes nakanji haushin furucinnan nasa, nakuma yi alk’awarin nisantarsa, amma bana iyawa, kona d’auki alwashin saina karya, da yazo yara6u jikina nake mik’a wuya, mugun tunda ya gano lagona saiya dunga bina ta wannan hanyar, duk sanda yaji buk’atata yasan yanda zaiyi ya ra6u da jikina harta kai ga wani abinda nikuma zan mik’a wuya batareda na saniba, saidaga baya nake gane kuskurena.
Ganin namasa banza nak’i tankawa saiya shige bedroom yana tsaki, komawa nayi na kwanta ina share hawaye. ga zafi ya fara addabata.
Kusan mintuna 19 sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa k’ananu, da Alama wanka ma yayi, k’in kallon inda yake nayi harya samu kujera ya zauna, remote ya d’auka ya kunna TV.
Haka mukaita zama tamkar wasu kurame, kusan 30minutes, kiran da Nuren yamasane yasakashi d’agawa, bansan miyake fad’a masaba naga dai ya mik’e ya shiga d’akin sirrinsa.
Na dad’e ina kallon k’ofar, zuwa can nima na yanke shawarar binsa kawai.
Doguwar rigace yellow a jikina, batada hannu, sannan bata kaimin k’asa ba, kad’an ta wuce guywata????, banason kaya masu nauyi saboda jin zafi, sai silifas d’in k’afata jaa mai taushi. cikinan ya kaimin ko ina, jinake kamar na jawo haihuwar na juyeshi na huta.
Ciki-ciki nayi sallama, bai jiniba, hankalinsa nakan Computers d’in d’akin dayake k’ok’arin dai-daitawa, duksun kawo wuta, har k’aton glass d’in dake jikin bango guda na d’akin, ban ta6a d’aukar shima Computer baceba sai yau, dukna d’auka saboda ado aka sakashi a wajen.
Sallamar na k’ara yi, ya juyo yana kallona, idonsa na cikin medical glasses mai haske, dan har kwayoyin idanunsa ina hangowa.
Kamar zai shareni saikuma ya amsa mini, juyawa yayi yacigaba da abinda yakeyi, mikuma yagani saiya juyo, ya jawo kujera ya gyaramin, yay min alamar da ido na zauna.
Babu musu na zauna, ya d’auki remote ya rage gudun AC d’in d’akin, sannan ya juya ga abinda yakeyi.
Yanda yake sarrafa Computers d’in saiya tafi da imanina, kai guy d’innan yasan Computer over.
Bansan lokacinda bakina ya su6uce nace, “yalla6ai ALLAH ya baka”.
Juyowa yayi yana kallona da mamakin furucina, ya saka pen d’in hannunsa a baki yana wasa da shi, kafin ya shiga takowa gareni, k’asa nayi da idanuna nabar kallonsa, yaja kujera ya zauna kusa dani, idonsa a kan cikina, ban Ankara ba naji hannun nasa a saman cikin, idanu Na d’ago Na kallesa, ya d’agamin gira d’aya yana fad’in “ALLAH ya bani k’yautar magaji?”.
Murmusawa nayi ina girgiza masa kai, “niba haka nake nufiba fa”.
“mikike nufi to?”. ‘yay maganar yana janye hannunsa daga cikin nawa’.
Fuska nad’an ya mutse, cikin salon yanga nace, “ina nufin ALLAH yabaka nasibin sarrafa Computer’s ”.
Yanda nayi maganar cikin salo saiya sakashi murmusawa yana ta6e baki, “toni miye namin yanga yalla6iya? saikace kina tare da masoyinki?”.
Haushi ya kamani Na dalla masa harara.
Bai kulaniba ya mik’e yana fad’in, “masu cikifa saida uzuri”.
Harna yunk’ura zan mik’e yace, “oh haushi kikaji? to sorry zauna kiga wani abu”.
Komawa nayi Na zauna INA k’unk’uni.
Hotunane da yawa ya nunomin daga cikin Computer, ya danna hoton farko ya fito sosai. Batareda ya kalleni ba yace,
“wannan sunansa *Kabiru Ibrahim*, nasanshi shekaru kusan 9 da suka shige a dalilin neman bayanan sirrina tacikin Computer, nabashi dama yashiga sosai saboda a time d’in yaci k’arfina, inada yak’inin wanine yabashi wani yanki sirri daga abinda nake da shi, ganin ya zuk’i bayanai 90 a cikin 100, saina tura masa goman gaba d’aya, saida ya zamana 99 duk sun shige ga Computers d’insa sannan Na nuna masa banbancina da shi, Na lalata abinda yake da shi da Wanda ya samu agareni, tundaga wannan ranar kuma nafara bibiyar rayuwarsa. Abin mamaki saina gano yanada Ubangida, shine wannan, *Timothy yoha*, dukkan abinda ya aikata agareni Umarnin uban gidansane Timothy, Na maida akalar tunanina ga Timo, saina iske shima aiki yakema wani, ba kowa bane face tsohon shugaban k’asarmu *Labaran Ahmad kachia*. shine wannan, nasan kuma k’ila kisansa dukda dai lokacin dayayi shugabanci bana tunanin an haifeki ma gaskiya, ta silar *Former p… Labaran Ahmad Kachia* nasamu wani kundin bayanai akan tsantsar abotar dake tsakaninsu su a k’alla 15, babu maijin sirrinsu saboda Kansu a matuk’ar had’e yake, ALLAH yayima 4 daga cikinsu rasuwa shekarun baya kad’an, saisu 11 suka rage”.
Ya kumayin wasu ‘yan danne-danne nidai duk ina kallonsa da mamaki, hotunan mutane 15 suka bayyana, sai dai an lik’e fuskar mutum 4 alamun wad’anda suka mutu kenan.
Gaban frigate d’in d’akin yaje ya had’a Coffee a mug, sannan ya tako zuwa gareni ya mik’amin, kaina Na girgiza masa alamar a’a, ya d’aga kafad’a sannan ya juya zuwaga Computers d’insa.
“wannan mutane hud’un sune jiga-jigan wannan abota, d’aya ya rasu a cikinsu saura uku, *Josaya Bamma* shine mataimakin *Alhaji Lawan tanderu*, bayan mutuwar tanderu shugabancin wannan abota ya dawo hannunsa, dukkan wani shigi da fici na man fetur dake faruwa a Nigeria josaya Bamma yasanta, dan sune masu yinsa, yanda ake fita da mai a k’asar da yanda suka mallaki rijiyoyin mai ba bisa k’a ida ba, gwamnati kuma batada damar magana domin sune masu fad’a aji, sune tsoffin shugabanni da suka San dukkan sirrin k’asar, sai *Bana baba gana*, dukkan wasu magunguna dake shiga Nigeria saida saka hannunsu, akwai wad’anda batareda k’a idaba suke kaita shi da *Alhaji balala* da *William Solomon*, domin manyan likitocine masana sosai, *Hajia A’i Barnawa*, babbar d’iya ga tsohon soja *Garba mai dala sokoto*, tashiga wannan group d’in sanadin k’awarta *Victoria*, dukkan wani cin zarafi mata ko cin dunduniya suke saka ido, kullum suna ik’irarin sune masu Kare hak’in mata a zahiri, amma a bad’ini ba aikin da sukeba kenan, suna aikin gyara aljihunansu ne. wannan shine *Mansur Habibu Abu*, wannan kuma *Abdul-Naseer Nafi’u*, da *Miracle Asun*, wad’annan dukkansu manyan ‘yan kasuwa ne, amma a bayyane, amma a 6oye su sukasan tsiyatakun dasuke shiryawa a k’ark’ashin k’asa *Sagir sulaiman Sulaiman* minister mai mulki a yanzu, sai wannan da wannan duk sun mutu banida matsala a yanzu tsakanina dasu, Munaya inason sanin alak’arsu da Mahaifina, wad’annan mutanen, domin sune mahaifina yay zama dasu ana gobe wannan ciwon zai sameshi, a daren ranar kuma Abie yashiga wajen mama Fulani domin gaisheta, jakadiya data masa rakkiya ta tabbatarmin da lallai yafito ransa a 6ace daga wajenta. Sannan a wannan ranar matarsa ta uku ce ta kawana a turakarsa, alhalin kuma kwannan matarsa ta biyuce, amma saboda kud’in data bama jakadiya da dad’in bakinta saita kaita turakar Abie a wannan daren, takuma sanarma matarsa ta biyu cewa takawa bashida lafiya yana fama da mura. kwana biyu kuma kafin faruwar dukkan wad’annan abubuwan Abie yayi zama Na musamman da Hakimansa saboda kama Wazirinsa da yayi Dacin amanar Masarauta wajen d’aukar sirrin cikinta ya bama wasu bak’in turawa da ba’asan dalilinsu na yin hakanba, a bincikena d’aya a cikin turawan ya Mutu, amma d’ayan yana nan da ransa. Abie ya kwanta jiyya da sati biyu aka kashe babban malaminsa, limamin masallacin sarki maikuma bama Abie shawara akan addini. dukkan wad’annan dana ambata miki sunayensu a kwai hotunansu anan d’akin, akwai abokin mahaifinki da kika fad’amin, shine Alhaji Mamman k’afur Wannan babban yaron Alhaji Lawan tanderu ne, dan wannan group sunema suka tsaya masa ya fito takarar shugaban k’asa, babbar matarsa k’anwar matar tanderu ce, wadda a gidan tanderun ta taso tun tana k’arama. Senetor halluru garba abokin Alhaji Mamman k’afur Ne sosai, akwai wani 6oyayyen sirrin dake tsakaninsu kuma, sai dai ban saniba ko Abbanki yasan wani Abu a ciki. Idan nace zan cigaba damiki bayanin sirrikan dake cikin d’akinnan kanki bazai iya d’auka ba Munaya, amma nabaki damar kimin kowace tambaya ni kuma zan baki amsarta batareda shamakiba”.
Ajiyar zuciya Na sauke, Dan tabbasa kaina bazai iya d’aukar wannan bayanan nashiba inhar suka wuce zurfin haka, Na yink’ura zan mik’e, saiya matso ya taimaka min da kansa, zaman silifas d’ina Na gyara a k’afata, sannan Na taka ga wasu hotuna, hotona na nuna masa dana muftahu, yad’an murmusa yana ta6e baki, kafin ya ajiye cofin hannunsa ya hard’e hannayensa a k’irji, “Ba manufar wannan hoton ke d’inba, dan haka manta da wannan kawai, sai nan gaba watak’il zaki iya sanin wani abu”.
Zanyi magana ya girgizamin kansa, alamar karnace komai.
Idona na janye daga garesa kawai, na maida kan hoton Muftahu tareda nunashi da yatsa.
Takowa yay har inda nake, ya kama hoton yana kallo tamkar yau ya fara saninsa, “Muftahu d’an uwa nane, kuma abokina, sai dai bakomai ne nake sakin jiki da Shiba, domin lokacin muna yara mutumne shi mai yawan k’arya, hakanne yasaka ko yaushe muke fad’a, babu abinda na tsana ga hallayar d’an Adam irin k’arya dacin amana, wannan halayyar tasa saita gaza barin zuciyata har girmanmu, kullum kallonsa nake bai canjaba, wannan yasakani fin yarda da harun fiye dashi, saikuma yake gwadamin wasu halaye na rashin gaskiya a lokuta da dama, ban k’ara tsinkewa da lamarinsa ba sai a time d’in da abinnan yafaru tsakanina da ke a birnin gayu, Muftahu shine Wanda yakawomin shawarar mizai hana na aureki ko ta wannan hanyar zansan wani Abu, da farko na d’ana masa tarkone, na yarda da auranki na shekara d’aya, yanda yacigaba da rawar jiki sai lamarinsa yacigaba da tsoratani, randa ya saka mana pill’s a fresh milk daga ranar na yarda 100% shi maicin dunduniya tane, kuma akwai wani 6oyayyan al’amarin da yake son cimma buri, wannan yasakani kauda idanu a kansa, nabashi dukkan dama, dukda kullum Harun kan nusar dani illar hakan, amma na share komai tamkar bana gani, sai dai wannan zuwan danayi maganar da kika ta6amin a wani dare ya sakani cikin dogon nazari, daga time d’in kuma na saka idanuna akan Muftahu da Harun, zuwannan da nayi na k’arshe Nigeria, naga wani abin mamaki da ban al’ajabi. akwai wani d’aurin Aure da mai martaba yace mu wakilcesa ni da Hakeem (Wambai) amma sai Harun da Muftahu sukace zasumin rakiya, ba rakkiyarce ta sani Ankara a kansuba, yanayinsu ya nusar dani kowanne akwai manufarsa, ban kulaba mukaje muka halacci d’aurin auren, anatashi Hakeem yace shi zai wuce, Dan yanada wajen zuwa, banbi ta kansaba Dan bana d’aukar raini, karramawar da aka shirya yima mai martaba sai ta juye kaina, aka karramamu sosai, ni bammaci abincinba, sai Harun da Muftahu ne sukaci, suna tsaka da cin abincin sai aka kira Harun, bai d’aga wayar a gabanmu ba ya tashi ya fice, ko alama ban kawo komai a rainaba, muka cigaba da hira ni da Muftahu, abinda na lura da shi rabin hankalin Muftahu akan Harun yake, dan yanayinshi ya nuna, zuwa can sai shima ya mik’e ya fice, yacemin yana zuwa, fitarsa babu dad’ewa d’ayar wayar Harun tayi ring, ni mutumne dabai damu da shiga abinda babu ruwansa ba, amma a ranar saina tsinci kaina da duba wayar, bansan Number d’inba, amma nasan fuskar wadda take jikin hoton da Number ta bayyana, ba kowa bace face d’aya daga cikin matan Abie na”.
“Matan Abie kuma?”.
“kwarai kuwa, wannan shine abinda na gani, Wanda ya zaunamin a rai, koda Harun ya dawo yaga wayarsa kusa dani sainaga kamar baiji dad’iba, na bashi ina fad’in hajia ta kiraka, kinga kuwa yanda yanemi zubewa? humm saida Muftahu ya taimaka masa, dana tambayesa se cewa yayi wai tunkan mu taho dama kansa na ciwo, nasan ba haka baneba amma na sharesa. tunda muka taho na lura ana kallon kallo tsakanina Muftahu da Harun, kuma duk sanda hakan tafaru, Muftahu kanyi wani murmushi mai tattare da ma’anoni masu yawa, Wanda har yanzu nakasa fasarasu”.
Huci na fidda daga bakina, na koma Inda na taso na kuma zama, shima saiya tako zuwa inda nake, ya durk’usa a gabana tare da d’ora hannayensa bisa Gwiwoyina, idanu na d’ago a hankali na sakasu cikin nashi, k’ok’arin janyewa na farayi, saboda wasu abubuwa danake hangowa cikin idanunsa. Amma saiya hanani wannan damar, yay wani sassanyan murmushi yana fad’in………….????
????
Barkanmu da dawowa sister’s????????????????????????.
*_ALLAH k’a gafartama iyayenmu????????????_*