NOVELSUncategorized
RAINA KAMA (BOOK 3) 13&14

BOOK 3 ???????? 1⃣3⃣
…………..“Wato Munubiya abinda yasa kikaga inata 6oye miki shine, bansan manufar mahaifiyarsa ba kai tsaye, nidai bayan tabani tarihin
masarautarsu takuma rok’eni nabama Galadima gudunmawa wajen saka idanu akan motsin kowa dazai mu’amulanceni, abinda ta lura shi yafi maida hankalinsane ga mak’iyan waje, gani yake kamar a masarautarsu babu mai iya cutar dashi. tace min Galadima bashi da yarda ko kad’an, sannan mutumne mai zama akan ra’ayin kansa, tankwarashi sai ita da baya iya bijirema umarninta”.
“Na damu kwarai da gaske Munu.. Dan rayuwa da irin mai wannan halin yanada wahala, musamman mutum mara yarda, wlhy nadad’e a gidannan bai bar zargin an turoni Na cutar dashi bane, saida Momma tafara koyamin dabarun zama dashi, tace nadaina jin tsoronsa, inhar yafad’amin magana Na daurema zuciyata Na dinga maida masa murtani, a tak’aice dai nake masa tsiwa. A lokacin da taimin wannan maganar abin yaban mamaki, Yaya uwa za tace aringama d’anta rashin kunya ko rashin raga masa?, kema kinsan bawai bazan iya baneba, amma yanamun matuk’ar kwarjini, bansan kuma miyasaba nakejin shakkarsa a zuciyata, har gobe idan yamin Abu zan maida masa murtani wlhy saina dage saboda tsoro. Saida zamanmu yad’an fara nisane Na fahimci abinda take nufi, inda bana nuna masa banida tsoroba zansha wahalar zama dashi, sannan bazai ta6a aminta dani ba ya saki jikinsa, zaita d’aukatane a y’ar lek’en asiri, Dan babu abinda ya tsana irin karinga masa Abu kana nuna tsantsar biyya da kwantar masa dakai, shi a wajensa kazo cutar dashine kawai. Maganar zuwana wanka itace tadage akan sainazo, sannan tace duk zuwan da zaiyi wajena Na nuna masa cewar. nifa bazan koma gidansa ba, dan bazan iya da hallayarsa ba, tadai nunamin dukkan dabarun dazanbi Na dinga zungurinsa da zancen, to ni wlhy ban fahimci manufartaba, tunda nasan babuma Wanda yasan mafarin ginin auren namu, daga ni sai shi, saikuma ke dana sanarmawa. yau kuma namasa zancen rabuwarne da nuna masa zan shayar dasu Abdurraheem ne Na wata shida nayi aurena nima, shinefa yahau kaina da bala’insa, wai babu wawan daya Isa shi ya k’etara gona wani yako ra6eta, koda kuwa ace gonar ta jinginace, inkuma hakan ta faru kobaya numfashi bai yafeba”.
Munubiya ta zaro ido waje Dan mamaki, saikuma ta tuntsure da dariya harda rik’e ciki, galala nayi ina kallonta, danni banga abin dariya ananba.
Saida tayi mai isarta sannan ta zauna dak’yau tana fad’in “yi hak’uri sweetheart, wlhy mijinkine yabani dariya, amma anya kuwa mahaifiyarsa batasan manufar aurenkuba?”.
“Ta ina zata Sani Munu.., shidai wlhy nasan bazai fad’aba, Dan nakula yanada masifar zurfin ciki, balle yasan abinda yay bamai k’yau bane, tunda a al’adarmu da addininmu hakan ba tsarinmu bane, nadad’e ban iya fahimtar matsalarsaba, saikuma naita tambayarsa yamin banza, sai daga bayane naringa Neman dabarun samo kansa harya sanarmin da damuwarsa”.
“Eh bank’i ta takiba, amma a ganina koshi bai fad’a mataba kina ganin Muftahu bazai fad’aba? Nifa tun pills daya zuba muku nafara zargin anya bada k’yak’yk’awar niyya yayi hakaba?”.
“Kai Munu.. ALLAH bana tunanin haka, gani nake kawai itama da tata manufar, Dan batason halayyarsa ta shiru-shiru d’innan da k’untata kansa dayake akan yawan damuwa kodan ciwonsa, Dan tace min ciwonsa Na yawan motsawa a baya saboda yawan shiga damuwa da yakeyi, gashi bazai yarda kowa yasan matsalarsa ba saboda tsatstsauran ra’ayinsa, itakuma bataso Dan abaya yanda kikaga Sauban k’animsa da faran-faran haka shima yake, amma tunda ya fahimci miya kwantar da mahaifinsa saiya canja musu gaba d’aya, maganar ma saiya gadama idan kayi yake amsaka, abinda Na lura yanzu kuma wannan abun yarigada yazame masa jiki gaskiya”.
“dukna fahimceki Munaya, amma abinda Na lura kamar wata alak’a mai k’arfi da kusanci takeson ginawa tsakaninki dashi, Dan babu wata uwa dazatasa matar d’anta ta ringa ma yaronta rashinkunya, itakuwa tasan halin d’anta ciki dabai, tanada dabarun dazata d’oraki domin shi su k’ayatar dashi harya ringa kallonki a matsayin mata ba auren wucin gadiba, dukkan maganganun daya fad’a miki d’azun wlhy Na mutumne mai nuna tsantsar kishi, ALLAH ma yasoki dabakizo da kumburarriyar fuskaba wlhy”. ta k’are maganar da sanya dariya.
Harara Na zuba mata ina fad’in “nikuma kamar wata sokuwa saina zauna ya dakeni, danma gaskiya shiba mutum bane mai yawan saurin hannu, saidai k’asaita da shariyar tsiya, kaita magana yayi tamkar bai jikaba”.
“Yo Sweetheart ai mulkin kenan ko, wannan shine ake kira sarautar, idan bashida wannan izzar da k’asaita lallai baicika jinin basarakeba, shi nashi ai da sauk’i tunda yasan darajar d’an Adam. Amma lallai ki godema ALLAH da samun suruka irin wannan, to amma ke kina sonsa yanzu?”.
Harararta nayi, nazame Na kwanta batareda Na bata amsaba, ta d’akamin duka a cinya tana fad’in “Munafuka kema sonshi kike, wannan jan ajin naku dukshi ke cutarku, shi mulki ya hanashi ya fad’a, ke shegen jan aji yahanaki ki nuna masa, basai kuyitayiba har yaranku su taso su ganku a haka”.
Baki Na murgud’a mata ina Sosa wajen data dokenin, Dan naji zafi, cikin harara nace, “ai ba a haifi namijin dazan fara furta masa ina sonshiba koda ace son nasa zai halakanine, k duk taurin kai da miskilancin Yaa Marwan ince saida yace yana sonki sannan kika amsa masa?, saini kikeson Na zubar da tawa darajar, salonma ya d’auka kwad’ayine ya sakani hakan, zai ru6e kuwa inhar jira yake sainace Sameer ina sonka, bank’i idan naga zan iya nabika ta wata hanyarba, amma shida yace auren Contract shine zai dawo ya gyara kuskuren da yayi da kansa, shiyyasa nake son canja masa tunaninsa ta hanyar tunatar dashi yasan mace tanada daraja, ba’a sakata lokacin da akaso sannan ayi tunanin cirewa lokacin da akai niyya, wadda batasan darajar kanta bace zata amince da hakan, nikuma bana cikinsu danba Auren kwad’ayi nayiba”.
Munubiya tayi dariya tana jinjinamin, “yayi k’yau gimbiya matar Sarkinmu mai jiran gado, wlhy kin burgeni dan wannan shine kima, amma dai a sassautama galadimanmu, Dan naga alama shimafa ya zurma fad’arce kawai mai wahala a harshensa, amma mizai hana mubi wasu dabarun Dan bud’e bakinsa”.
“babu wasu dabaru dazamubi sweetheart, Dan nidai bazanbi ta hanyar talla da jikina ba a gareshi danya soni, randa Na tsufafa? K’yawun jikin ya 6ata ko Na nakasa?, bazanbi ta yaudaraba ko wani kwarkwasa, randa yaga wadda yakeso tsakaninsa da ALLAH fa? komai zan masa bazai birgeshiba, Dan soyayya ta gaskiya daban take, baruwanta da k’yau ko k’yale-k’yale, zandai iya k’yautatama zuciyarsa domin dukkan zuciya tanason mai k’yautata mata, amma son gaskiya nakeson mijina yamin, bana k’yalek’yalen duniyaba, ko tsufa ya kamani bazai bar sonaba, ko nakasa ta kamani bazai bar sonaba, ko babu dukiya tattare dashi bazan gujesa ba, idan ciwo ya kamani koya kamashi zamu tattali juna saoda tausayi da rahamar dake cikin Auren da soyyar gaskiya da mukema juna, ko kishiya yatashimin nasan son gaskiya yakemin bazan ta6a saka kaina a matsananciyar damuwa ba tunda inada yak’ini akan son gaskiya yakemin, bazai ta6a tozartaniba, sannan ban Isa hanashi yaso matarsa ba Dan ni yana sona, nafison amin komai tsakani da ALLAH bada yaudaraba kema kinsani, Dan haka muyitayi inhar bai gajiba nima bazan gazaba”.
“Duk mace haka yakamata tasan darajar kanta, takumayi abinda mijinta zai sota son gaskiya Munaya, wannan k’arancin soyayyar ta gaskiya da Muke fuskanta ayanzu shineke yawan ruguje rayuwar aure, mafi yawan mazan sukanso macene domin wata halitta ta jikinta, dasun sami nutsuwa dake kuma shikenan haskenki ya dusashe a idanunsu, wasu kuma Matan mai dukiya ne hangensu ko k’yau, da zarar mijin yazo babu saikiga wuta ta tashi, kokuma bashi dashi dama duk k’aryane, dakinje bakiga abinda kika aureshi danshiba babu sauran zaman lafiya kuma, gaskiya muna cikin matsala yanda taron biki yake a wannan zamanin kawai ya Isa ruguza dukkan albarkar aure, amma ni dazakiji ta tawa tunda shima yana sonki kubar wannan 6oyewar mana”.
“Munu, idanfa bai canjaba nima bazan canjaba, bakinsa daya furta shi nakeso ya gyara da kansa”.
“lallai to sai kiyita 6oyewar, idan ya nemi kasheku duk zaku fiddoshine kowama yaji, ai nama godema ALLAH da Muftahu dan ta silarsa ALLAH yamuku dabaibayi da yarannan, Ubangiji sarkin hikima kenan, naga Wanda zai iya barma wani ai”.
Banza namata nayi kwanciyata, harma barci 6arawo ya saceni. Munubiya ta d’auki wayar munaya tana murmushi, tayi abinda zatayi ta ajiye mata abarta itama ta kwanta.
★★★★
Galadima daketa juye-juye a gado abin duniya dukya ishesa saijan tagwayen tsaki yakeyi ya kalli wayarsa datayi alamar shigowar sak’o, harzai share dai saiya kasa, dan numbers d’in cikin wayar duk masu muhimmancine.
Jawo wayar yayi ya danna ta kawo haske, hoton y’an uku ya bayyana a screen d’in, saida yad’an ja wasu Seconds yana kallon yaransa sannan ya bud’e massage d’in, ganin wadda ta turo sak’on sai mamaki ya kamashi, Munayar da inhar bashine ya kirataba bata ta6a d’aukar waya ta kirashiba ita, amma yau itace harda message? Dukda baiyi tunamin samun mai dad’iba haka yabud’e dai, yasan bai wuce maganar data damu mutane da itaba…
Ina fatan ka koma gida cikin aminci da farinciki? Yaranka namaka fatan alkairi da addu’ar samun k’yak’yk’yawar Nutsuwa mai tarin hak’uri.
ya dad’e idonsa akan wayar yana kuma bitar sak’on, baisan murmushi ya su6uce masaba, watoma yaransa ba itaba?, kai jan ajin yarinyarnan yayi yawa, da ace agidan sarauta ta fito lallai bayi da hadimai sunga takansu, ya ajiye wayar yana gyara kwanciya, jiyay zuciyarsa tayi sakayau, dandanan barci ya d’aukesa, dama video call yayi dasu Momma, dan tun bayan daya sauka bai kuma kiransu ba saboda yau ya yini busy, ga tunani sunma kansa yawa, Munaya tagama saitashi yad’an samu nutsuwa amma shine takuma hargitsoshi da abinda zuciyarsa bazata iya d’aukaba.
…………..
Washe gari
Munaya dai batasan minene ya faruba, dan Munubiya goge sak’on tayi bayan ta tura, da safe kuma ko alamar tayi wani Abu bata nunama Munaya ba.
Wajen tashin hantsi saiga Aunty Salamah tazo, cikin farin ciki duk muka mak’alk’ale mata, ta rik’e baki tana fad’in “oh ni, ALLAH yabani y’ay’an da basu San sun girmaba”.
Innarmu tace, “wlhy kuwa salama, baki moreba kam”.
Laraba dai tanata musu dariya.
Kayan gyaran jiki Na musamman Aunty salamah ta kawo musu, takuma bisu da gargad’in wlhy kowa tazage tayi, harda rok’on laraba ta saka musu idanu Dan ALLAH.
Gaba d’aya yau a gidan tama yini, hakanne ya d’aukema Munaya damuwar data tashi da ita.
★★★★★★*★★★★★★
Tunda yadawo salla ya koma barci, saboda jiya bai wani samu yin isasheba, wajen 10 ya farka, brush kawai yayi yazo ya zauna yana hada wasu takardu, sosai aikin ya d’auke hankalinsa saboda muhimmancinsa, sauban datun d’azun yay shirin tafiya yagaji da jiran fitowar Galadima Dan haka yazo yaymasa knocking, Dan yanason biyawa wajen Munaya kafin ya wuce.
Galadima dake zaune bakin gado ya baje takardu yana kuma rubutu a jikin wasu ya d’aga kai ya kalli Computer d’in dake hasko masa dukkan CCTV camera’s d’in sashen nasa, ganin Sauban ne sai ya d’auke idonsa yace ya shigo.
Zama sauban yayi saman stool d’in mirror ya gaida Galadima, hankalinsa nakan aikin dayake ya amsa. yace, “Dama katashi?”.
“Wlhy Yaya tun d’azun Na tashi, naga baka fito baneba gashi inason kafin Na wuce nabiya Na gaida Aunty gimbiya naga my Triplet’s kuma”.
Galadima baice komaiba, sai had’e takardun gabansa daya shigayi, Sauban yamatso bakin gadon yana tayashi, saida suka gama tsaf, ya shiryasu cikin wani k’aramar briefcase sannan ya kalli Sauban dake zaune, “Mik’omin System d’incan”.
Sauban yad’an marairaice fuska cikin tausayawa. Yace, “haba yaa Sam kad’an huta mana”.
Da mamaki Galadima yace, “to idan Na huta kaine zakamin aiki?”.
Girgiza kai Sauban yay alamar a’a. Ya tashi ya d’ako masa.
Kar6a Galadima yay yana girgiza kansa saboda ganin yanda Sauban keta 6ata fusaka, a zuciyarsa yace bazaka fahimtaba yaro.
Batare da sake kallonsa ba yace, “yanzu mikake buk’ata kenan?”.
“yaa Sam kud’in wajenafa basuda yawa”.
“Humm” Galadima ya fad’a hankalinsa akan aikinsa. yace, “Aikai dama baku iya tausayin kud’iba kai da Samha, mutum yarasa uwar mi kuke saya? Kaje zan turo maka, Dan yanzu kama nima buk’atar kud’in nakeyi, gashi sunyi cak, nasan kuma daga inno har papi idan suna dashi baka zasuyi”.
“shikenan yaya, amma Dan ALLAH ko kad’anne”.
“ka duba cikin kayan dana cire, maybe ka samu”.
“yauwa Yaa Sam d’inmu. ALLAH ya k’ara girma”.
Galadima Dai baice komaiba, ya kwaso kud’in duka yana fad’in “na kwashe duka?”.
Kai kawai Galadima ya d’aga masa.
Sauban yazo ya rungume Galadima ta baya yana godiya, sannan ya sakesa. Murmushi Galadima yayi yana fad’in “ALLAH ya gyaraka Sauban”.
“Amin yayana”. Sauban ya fad’a cikin dariya.
Sunyi sallama ya tafi akan cewa shima saiya zo, yakuma gaida su papi.
*******
Munaya taji dad’in ganin Sauban, sund’an ta6a hira sannan yamata sallama ya tafi tana shaida masa ya gaida mata su inno da k’yau, har k’ofar gida ta rakoshi, dukda dai bata fitoba iyakarta jikin gate, saida yashiga mota sannan ta koma ciki, tanamai jin k’aunar ahalin Galadima har cikin ranta.
****\/****
Galadima na shirin fita kira ya shigo wayarsa, saida yagama d’aura belt d’in da yakeyi sannan ya matsa gaban gadon ya d’auki wayar, a dai-dai lokacin kiran ya kuma shigowa, ganin Sir Isa saiya d’aga.
Ko gaisuwa basuyiba yace, “yalla6ai kaga kuwa aika-aikar da ake neman mana?”.
“Aika-aika kuma? Tami?”.
“Tabbas ansaka wani yamaka kutse cikin Computer, Nazatama kagani?”.
Gaban Galadima ne ya fad’i babu shiri ya yanke wayar, system d’insa ya jawo ya zauna bakin gadon, “innalillahi…” Yashiga ambata zufa Na tsatstsafo masa saboda abinda yagani Na shirin faruwa, ya manta daya gama aiki bai saka security a matakin farkoba, saurin sakawa yayi, dukda yasan babu tabbacin zai iya dakatarwa ahakan kawai da yayi, ya ajiye lap-top d’in yana mik’ewa da hanzari, sauri d’aukar rigarsa yayi ya saka, yana saka bottoms d’in a tsananin hanzarce, haka dai ya k’arasa shirin a gaggauce, ya d’auki abinda zai d’auka yafito, babu gaisuwar Wanda ya amsa, hannu kawai ya d’aga musu yanufi mota yashige da kansa yaja ya fice daga masarautar, Wanda yatafi kiran Sarkin Mota duka iso tare, duk mamaki ya kamasu, yau Galadima da kansa yaja mota, anya kuwa lafiya?.
Ganin wannan bazai musuba sarkin mota ya shiga mota shima ya bishi.
Yana tuk’i suna waya da Vijay abokin aikinsa Na India, a haka ya iso gidansa dake bayan gari, kusan lokaci d’aya suka Isa da sarkin mota, ganin Galadima zai fita ya bud’e gate da kansa, shi saiya kashe motar dayake ciki da sauri ya fito yazo ya bud’e masa ya shige, bai bisaba, tunda Alhmdllh yaga dai inda yazo, maybe kuma baya buk’atar kowa a wajene shiyyasa ya buk’aci tahowa shi kad’ai.
Wani d’aki dake cikin bedroom d’in gidan ya bud’e ya Shiga, bazaka ta6a tunanin akwaima d’aki a wajenba, da y’ar k’ura a d’akin, amma hakan bai damu Galadima ba a yau, k’yallen da aka rufe kujeru da Computers d’in d’akin yashiga yayewa, da sauri ya fito zuwa can bayan d’akunan, yad’anyi ajiyar zuciya saboda ganin Gen… d’in gidan akwai fetur, dayake yad’an zazzo gidan kwannan, tadawa yay ya kuma komawa cikin gidan, ya kunna komai sannan ya zauna a kujera, medical eyeglasses ya saka, idonnan yayi jazur saboda 6acin rai, duk jijiyoyin kansa sun mimmk’e, hakama gashin jikinsa, kallon farko zai tabbatar maka ran maza ya 6aci. Koma a yanda yake sarrafa Computers d’in.
Abinda ke kunnensa kawai naga ya danna yanayin kwatancen d’akin da za’a sameshi.
Mintuna 3 tsakani saiga Sir Isa da Baffi sun shigo, saikuma ga Sauban Wanda harsun d’auki hanya Muftahu ya kirashi akan ya dawo, dole ya dawo masarauta, shine suka fito shida Muftahun.
Sir Isa da Sauban duk zama sukayi, Galadima Na Sanar musu abinda zasuyi.
“Gaskiya shegene guy d’innan yalla6ai, wlhy yasan Computer, kagafa yana Neman lalata mana dukkan security d’inmu…….”. ‘hankali tashe sir isa yake magana.
Sauban kam har kwalla ta cika masa ido.
Galadima baice komaiba, aikinsa yake iya iyawar k’arfin zuciya dana k’wanji.
Sai Baffine yad’an bubbuga kafad’ar Sauban yana fad’in “ka kwantar da hankalinka Sauban, insha ALLAH bazasuci nasaraba, kacigaba dayin komai a nutse kaidai”.
Sauban ya kad’a kansa yana share hawaye.
Galadima dayay zufa sharkaf ya kalli Sir Isa, yarigada yaci k’arfinmu kafin muzo, k’ofa ukuce kacal ya rage masa bud’ewa yasamu dukkan komai, abinda zamuyi mu bud’e masa sauran kawai, bayan yashiga ciki insha ALLAH inada wata dabara”.
Muftahu yace, “Amma Ranka ya dad’e hakan riskine gaskiya, idan kuma shi yanada plans akan hakan fa?”.
“Gaskiya ka fad’a Muftahu, amma hakan shine kawai hanya mai sauk’i da zamubi, inhar muka bari harya bud’e da kansa lallai zai lalata komaine, Dan wannan shine shirinsu”. Sir Isa ne mai maganar.
Galadima ya danna abin kunnensa yana fad’in “Vijay mubashi dama kawai, a lokacin daya shiga kaikuma ka tabbatar da ka zuk’e dukkan nasa shirin, ga wata akwatinan dayake yawo da ita a bayan handle d’in Computer d’insa, karka ta6ata Dan makircine ya shirya a cikinta, munayin kuskuren ta6awa labari zaisha Banban. Alex yay gaggawar had’amin sabbin Securitys muga kozasu ja hankalinsa can, ga hoton yaranan zan d’ora masa, dasu zaiyi amfani, dan dolene mu kauda masa hankali, yasan mi yakeyi sosai”.
“Ok! Ok! muje zuwa kawai” vijey ya amsa a hanzarce.
Da sauri Galadima ya maida kallonsa ga Sauban yana fad’in “dakaje duk ka d’auki su Amaturrahman ne?”.
“Eh yaya dukna d’aukesu”.
“A lokaci d’aya ko daban-daban?”.
Na d’aukesu lokaci d’aya, nakuma d’auki kowa shi kad’ai”.
“Alhmdllh taso nan”.
Tashi Sauban yayi ya matsa inda Galadima yake, wani glass Galadima ya tura masa, yace, “’Dora duka hannayenka anan mugani”.
‘Dorawa Sauban yayi, bayan ya ta6a wani farin Abu da Baffi ya bashi, shatin hannun yaran suka bayyana, dayake yayi musu wasa sosai, amma kuma hakan bazai gamsarba.
Daga can Alex yace bazaiyiba, dole akawo yaran. Shima Galadima ya tabbatar bazaiyinba, sai hankalinsa ya kuma tashi, yaran sunyi k’ank’atar daza’a fito dasu daga gida.
Muftahu yace, “Ranka ya dad’e bara kawai naje Na kawosu inaga zaifi sauk’i”.
Baffi yace, “hakan shine kawai dai-dai sai dai bakai yakamata kajeba, a kira mahaifiyarsu tabama Wanda zai iya 6adda bamanni wajen kawosu, kuringa tunawa sumafa idonsu nakan kowane motsinmu a yanzu, shiyyasa tun a jiya naima Sameer hannunka mai sanda akan hakan”.
Galadima daya zubama Computers d’in ido kawai yana kallon 6arnar da ake shirin masa. Ya mik’e tsaye yana fad’in “Muftahu ka kira mai taxi d’innan yaje inda yata6a ajiyeta za’a kawo masa yaran”. fitowa yay daga d’akin yana k’ok’arin neman number Munaya ya kira.
Bugu biyu Munubiya da wayar ke hannunta ta d’aga, tana mannama Munaya wayar a kunne, bai amsa sallamarta ba yace, “Yanzunnan ki bama Innaro da laraba su Abdurraheem, sufito bakin layinku akwai mai taxi zai d’akkosu”.
Cike da mamaki Munaya tace, “yalla6ai ban ganeba?”.
A tsawace yace, “basai kinganeba, Dalla malama kibasu karki 6atamim lokaci”.
Sosai Munaya ta tsorata da tsawar tasa, kad’an yarage wayar ta su6uce mata ta daiyi azamar rik’ota, batada za6in daya wuce bin Umarninsa, dukda hankalinta bai kwantaba da hakan. Yanda yace ayi haka tayi, innaro da laraba Na fitowa suka samu mai taxi yana jiransu.
Cikin mintuna k’alilan suka iso, Muftahu da Sauban sukazo suka kar6i yaran, akabar su innaro a mota zasu jira.
Akan wani Abu akad’an d’orasu, da hotonsu ya fota a Computer d’in sai’a ciresu, sud’uka duk aka d’ad’d’orasu, sannan su Muftahu suka maidasu wajensu innaro aka koma dasu. Sudai duk mamaki ya cikasu akan miya faru? Basuda mai basu amsar wannan lamari.
Bayan su Galadima sun turama su Alex hotunan yaran sai duk suka koma gefe suka zubama Computers d’in ido, sauran lamari sunbarma ubangiji. Suna kallo wancen ya shige inda yakeso, bayan sun bashi dukkan dama, tashin hankalin Galadima shine, mutumin lalata komansa yakesonyi bawai d’auka ba, idan da ace d’aukace hakan mai sauk’ine, k’iris yarage wancan ya cinmusu, Galadima ya lumshe idonsa zuciyarsa Na k’una yana ambaton sunayen ALLAH, abinda ya d’auki tsawon shekaru yana tanadinsu ga wani banza zai gogesu cikin seconds, hakan ya tabbatar masa da Harun ne yabada wani yanki Na sirrinsa, saboda yasan abubuwa da yawa akan aiyukansa, sauban ma k’asa yay dakai yana hawaye, shikenan dukkan hujjojinsu da suke ganin zaisa su samu a hukunta masu laifi suntafi, baffi da sir Isa da Muftahu ma duk jikinsu yayi sanyi, kowa sai zuciyarsa Ce ke bugawa……
Sauban yace, “Yaa Sam!”.
Galadima ya tashi zaune sosai yana bud’e ido da kallon Sauban, batareda ya amsaba.
Sauban yace, “yaa Sam mizai hana mu gwada dabaran kashe Computers d’insu, kaga seconds 30 kawai yarage ya cimma burinsa”.
Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, murya a sark’e yace, “Sauban abinda ya rage mana yayi kad’an wajen yin hakan, kuma zamu iya kuskuren da komai zai goge d’in da kanmu, kubarsa kawai yayi yanda yakeso……”
Katseshi baffi yay da sauri, “Sameer mu gwad’a d’in kawai, maybe a samu dacewa”.
Badan Galadima yayi tunanin samun nasaraba yatashi zaune jiki a sanyaye yana dannawa, Sauban yakuma fad’in “yaya Please kayi da yak’ini, saura 20 seconds fa”.
Tamkar Sauban yayima Galadima allura ne, yafara komai cikin hanzari, yayinda sir Isa ke taimaka masa.
Muftahu da Baffi dai y’an kallone, Dan basusan komai dangane da wannan harkarba.
Saura second 1 ya rage Galadima yasamu damar kashe Computers d’insu dana wad’ancan.
Suda ke murnar samun nasara duk sai sukayi tsit, su Galadima kuma Sauban ya sanya ihu.
Hararsa Galadima yayi, yayinda su Baffi sukai dariya.
Dukda suna addu’ar samun nasara hankalinsu bai kwantaba, Dan sai an kunna Computers d’in zuwa wanu lokaci, idan an tabbatar da samun nasara sannan.
*****
Hankalim Munaya bai kwantaba saida taga su innaro sun dawo k’alau, babu kunya taita d’aukar yaran tana jujjuyawa wai kozataga wani abinda aka musu, saidai kuma bataga komaiba.
*********
Baffi ya kalli Galadima dayay shiru ido a lumshe, yace, “Sameer dolenefa komai yazo k’arshe yau, kabi ta hanyar da katsara domin zuwansu hannu gaba d’aya, daga baya saimu cigaba da Neman camera, dan Na tabbata bazasu hak’ura ba, shiyyasa tun a jiya Na sanarmaka”.
Galadima ya jinjina kansa batare da ya bud’e idoba yace insha ALLAH komai yazo k’arshe Baffi, safiyar gobe zaku tashi dajin yanda ta kasance, Nuren yana hanyar dawowa. Zamu tafi matakin k’arshe yau”.
Atare suka had’a baki wajen addu’ar ALLAH ya bada nasara.
Galadima ya amsa akan la66a da amin……………✍????
Lallai gobe da kallon kenan. Galadima manmu ka cika musu aiki kawai????????♀????????♀????????♀????????♀.
ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????
BOOK 3 ????????1⃣4⃣
……………..Duk da dai sumbar komai a halin k’ila wa k’ala haka kowa yafito jiki a sanyaye, Baffi da Sir Isa suka wuce, Galadima ma kallon Sauban yayi daya zuba uban tagumi, yad’an murmusa yana fad’in “Haba autan Momma, miye kuma Na damuwar haka? katashi kuwuce kawai kar yamma tayi”.
Shagwa6e fuska Sauban yayi yana kallon yayansa, yace, “please Yaa Sam kabarni sai gobe saina wuce insha ALLAH”.
Galadima yay shiru alamar tunani, saikuma ya girgiza kansa, “uhm-uhm Sauban ka wuce yau, Dan gobennan akwai riski”.
Kamar Sauban ya tambaya dai amma yay shiru, yasan halinsa mawuyacine ya sanar masa. Dan haka saiya amsa da to kawai. Badan yasoba yaymusu sallama shima driver dazai kaisa yad’aukesa suka tafi.
Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, zuciyarsa Na k’una da tsantsar damuwa.
tausayinsa ya kama Muftahu dake zaune shima yayi shiru damuwa da tausayin d’an uwan nasa fal ransa.
★★★★★★
Gaba d’aya zuciyar Munaya takasa sukuni gameda yanda taji muryar Galadima, tunda kuma aka maido yaran saita kasa zaune ta kasa tsaye, Munubiya dai da innarsu duk suna hankalce da ita, kamar Munu zata shareta saidai tamata magana.
“Nikam aganina da wannan zagaye-zagayen da kiketayi Sweetheart ai gara ki kirashi kisan damuwarsa, koma ladan kwantar masa da hankali k’yasamu”.
Munaya dake kwance akan gado ta kifa meenal saman cikinta datai barci ta kalli Munubiya, amma sai munu ta basar tamkarma ba ita tayi maganarba. Ajiyar zuciya Munaya ta sauke, yayinda Munubiya ta tashi tamayi ficewarta daga d’akin duka, harta fice Munaya nabinta da kallo, saida tabar ganinta sannan ta janye idonta a k’ofar tana cigaba da shafa bayan meenal.
Shawarar Zuciyarta dake cigaba da k’arfafa mata shawarar y’ar uwarta ta addabeta da k’awato mata Galadima a damuwa, da alk’awarin dataima Mahaifiyarsa. Kasa daurewa tayi saboda tausayin ahalinsa dashi kansa daya kamata, ta jawo wayar tana lalubo number sa, dukda k’irjinta Na dukan gama-goma Na tsoron tsawar daya mata d’azu da yanda suka rabu jiya. Haka dai ta dake tayi dialing number sa.
Galadima suna zaune cikin halin shiru da Neman mafita a zukata shida Muftahu kira ya shigo wayarsa, sharewa yay tamkarma bai jiba, ganin zata tsinke muftahu ya taso yay picking da sauri ganin My Mata yasan dai Munaya Ce, a kunne ya saka masa, Galadima ya bud’e jajayen idonsa ya kallesa, Muftahu yamasa alamar please da fuska.
Baice komaiba ya kar6a wayar yana maida idanunsa ya lumshe, Muftahu kuma ya fice abinsa.
Munaya tayi shiru takasa magana, kamar yanda shima yak’i cewa k’ala, sai sautin ajiyar zuciyarsa take jiyowa kad’an-kad’an, daurewa tayi tace, “Assalamu alaika”.
Dukda yasan itace saida yaji sanyi a ransa, Dan ita kad’aice kemasa haka a waya ya jure, saida ya d’auki wasu seconds kafin ya amsa sallamar.
Yanda ya amsa sallamar kawai ta tabbatar akwai matsala, Cikin aro jarumta tace, “Ranka ya dad’e barci kakeyi?”.
Yad’an murmusa, a zuciyarsa yace yarinyarnan a kwai wayo, “Uhm-uhm”. ‘yafad’a a sanyaye’.
Ganin tafara samun dama saita kuma saita muryarta tace, “’Dan gatan Abie, to mikakeyi ne haka? naji muryar taka can k’asa”.
Zamewa Galadima yayi ya kwanta cikin kujerar, yanzunma tamkar bazai amsaba, saida ya gama basarwarsa sannan yace, “k mikikeyi?”.
Munaya tayi murmushi mai sauti har yana jiyowa, ta shafa kan Meenal tana fad’in “kwance kawai nake ina tunanin rayuwa da abinda ta k’unsa, harma da Wanda ke gudana a cikinta”.
Yace, “Humm kamar mikenan?”.
“Kanason ji?”.
Ya kuma cewa “Uhm”.
“humm yalla6ai nakula duk yanda bawa yakai da samun komai Na rayuwa saikaga wata damuwa ko tawaya mai kutse acikin al’amuransa, bana manta maganar nan taka da kata6a fad’amin wani lokacin murmushin da jama’a kanyi iyakarsa fuskane, amma zuciyarsu sune kad’ai sukasan sirinta, lallai wannan gaskiyane, amma kasan mike birgeni da k’aramin k’warin gwiwa a rayuwata koda ace Na tsinci kaina a fagen sanyin jiki?”.
Galadima yace, “uhm-uhm”.
Munaya ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya da Galadima yajita har cikin ransa, yayinda wani Abu ya tsarga masa ta cikin kai har zuwa yatsan k’afa, ya gyara kwanciyarsa yana jiran jin mizatace.
“Komai girman fad’uwa inhar da yak’inin HAK’URI dana k’arfin ZUCIYA to lallai akwai tagomashin sirrin samun NASARA, hak’uri da juriya basa ta6a zama fad’uwa, inhar kaga bawa yayi hak’uri babu kuma NASARA a ciki to lallai hak’un nasa kad’anne, sometimes gaggawa aikin shaid’anne, saikuma ansha wahala ake shan dad’i, abinda kawai muke kasa fahimta shine riba akan sameta ne a muhalli biyu, walau a duniya kokuwa a lahira, duk wadda bawa ya samu sunanta nasara, amma kowa yafi fata da samun ta duniya, saidai ta lahira ita yakamata mufi d’oki da addu’ar samu, meybe tazame mana tsani Na zuwa inda bamuyi zatoba, hikimar Ubangijice yabaka nasarar anan kokuma a can, Dan babu yanda za’ayi a zalunceka mai kowa da komai sarkin Rahma da jink’ai ya bari, bai yarda da zalunciba, yakuma haramtashi agaremu mu bayinsa”.
Wasu k’ananun hawaye suka gangara ta gefen idon Galadima, fuskarsa d’auke da murmushi, yayinda kalaman munaya ke tasiri adukan magudanar jininsa da zuciya, wata nutsuwa ta musamman daya rasa tashiga ratsashi da bashi k’arfin gwiwa, a hankali yace, “ke y’ar baiwace matar Contract”.
Dukda maganar k’arshe ta sosa zuciyarta saita murmusa, cikin kuma kwantar da murya tace, “Ni a suwa Mijin contract ”.
Ya d’an dara batare daya shiryaba. Yace, “one-one kenan?”.
Munaya tayi dariya tana fad’in “nidai bada manufa na fad’aba”.
“Fad’i gaskiya dai yalla6iya tsiwa”.
“Gara mai tsiwa da miskili, koba komai akansan muna waje ai saboda tsiwarmu”.
Galadima ya kuma Murmusawa. Yace, “ki kiyayi randa zan kamaki ALLAH”.
Itama dariyar tayi. Tace, “yalla6ai ka fad’i wani Abu nabaka k’yauta mana”.
Yay d’an jimm tunanin mikenan?, saikuma yayi ajiyar zuciya yace, “mikenan?”.
Cikin wani salo Munaya tace, “R. Ita kawai nakeson ji a harshenka”.
Lallai yarinyarnan taga gadon barcinsa wlhy, yay maganar a zuciya fuskarsa na k’awatuwa da murmushi. yace, “Okay, kibari sai ina gabanki”.
“Tab, Indai ba yanzuba na fasa”.
“uhmyim, miye na karayar hajiyar tsiwa?”.
“Aiba karaya nayiba, lokacin kawai kabari ya wuce, ni karmafa yarannan suma su gadoka”.
“Dai-dai kenan ai y’ammata, kokin manta k’yan d’a ya gaji ubansa”.
“Humm Alfahari kenan, ita uwa an rainata”.
Dariya tabashi, amma ya daure baiyiba. Yace, “keda kike gudunsu mizaisa su gadoki?”.
Munaya ta d’an ta6e baki, cikin juya idanu tamkar tana gabansa tace, “yanzu kana ina?”.
Murmusawa yayi saboda basar da maganar da tayi. Yace, “kinason ganinane?”.
“A’a, son sani kawai nake”.
“Humm, naje tad’i to”.
Shiru munaya tayi, sai kuma ta d’an dara, “Yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”.
“Saikin fad’a”.
Cikin danne dariya tace, “irinku kwantai kukeyifa, sai anyima y’ammata tallarku asamo mai taimakonku ta aura, kaima nasan saisu takawa sunmaka haka…..”. Sai yaji kitt, ta yanke wayar.
Wani k’asaitaccen murmushi ya saki yana shafa kumatunsa, ya d’ora wayar saman cikin sa yana fad’in “lallai yarinyarnan kin girma, zaki tabbatar nayi kwantai kuwa”.
Daga canma Munaya dariya taketa k’yalk’yatawa, harta tada Meenal, Mununiya datun d’azun take kallonta ta bayan labule bata saniba tayi murmushin jin dad’i itama tana share hawaye, tanason y’ar uwarta sosai, sannan wayonta da iya mu’amullarta na birgeta, tabbas Munaya tanada tsiwa, amma tanada wayo, inhar zaka takurata bazata ta6a raga makaba, amma tanada tausayi dason ganin farincikin wani koda ita zata rasa nata farincikine, gakuma son girma uwa gyambo, tanason komi zaka mata ka nuna muhimmancinta a gareka, a fili tace, “ALLAH yakawo farinciki mai d’orewa a ratuwarki kema y’ar uwata”.
Amin munu????☺.
★★★★★★★★
Tunda Muftahu ya shigo yakebin Galadima da kallon mamaki, ganin yasake yanata fara’a tamkar ba shine a matsananciyar damuwa yanzunba, ya zauna zuciyarsa na addu’ar samun mace tagari, dan lallai MATAN KWARAI RABIN ADDINI ce.
Galadima ya hararesa yana tashi zaune, “malam lafiya ka k’uramin ido?”.
Dariya Muftahu yayi sosai, yace, “to miye na tsarguwar ranka ya dad’e, wlhy kuna sha’aninku kaida gimbiyarka, yanzu nan harta saukeka daga hawa saman da kayi”.
Filo Galadima ya jefama Muftahu, shikuma ya cafe yana dariya.
Galadima ma murmushin yayi yana danna kiran Sauban. Dan yasan har yanzu yanacan cikin damuwa. Hasashen nasa kuwa yayi dai-dai, Dan har yanzu muryarsa a cinkushe take. Amma jin ta Galadima a sake sai farinciki ya kamashi, cike da zumud’i yace, “yaya an dace ne?”.
Murmushi Galadima yayi mai sauti, yace, “muna fatan hakan autan Momma”.
Alhmdllh Sauban yashiga jerowa, saiya saki jikinsa kuma harda tsokanar Galadima yana dariyar k’eta.
Galadima dai murmushi yakeyi yana girgiza kai, ya yanke wayar zuciyarsa na addu’ar ALLAH ya saka farinciki a zuciyar Munaya fiye da yanda ta sakasu. Massage ya tura mata sannan ya kalli Muftahu yana gyara zama.
Munaya na kwance har yanzu takasa fita, tunda tasamu Meenal ta koma barci saita lumshe ido tana dulmiya duniyar nazari, shigowar sak’one ya sata bud’e ido ta jawo wayar. Ganin Galadima ne saita mik’e zaune babu shiri, sak’on ta bud’e.
“Kin yaudareni da zance banko tambayi yaya jinin jikina sukeba yalla6iya, to ki shafamin kansu.
ALLAH ya sanya farinciki a rayuwarki fiye da yanda kika Sani.
Wasu hawayen farinciki suka gangaro a kumatun Munaya, bata ta6a tunanin shirmen datake masa yanayin tasiri a zuciyarsa ba, Dan bai ta6a nuna mataba, a fili ta furta “ALLAH na gode maka dana zama sanadin saka wani bawa naka farinciki a lokacin jarabawar damuwa ta lullu6e jinsa da ganinsa da zuciyarsa”.
Amin munaya, muma Ya ALLAH kabamu ikon bama bayinka muminai gudunmawar farinciki mai amfani koyaya ne, amma bata hanyar sa6onka ba ko take k’a’idar daka shinfid’a mana, amin????????????.
*********
Muftahu da Galadima suka fito, yauma bai zauna bayaba duk yanda Muftahu yaso hakan, dama yay masa maganar zama bayan hararsa yayi, dole yaja bakinsa yay shiru yana murmushi.
Wani wajen cin abinci Muftahu ya tsaya, ya kalli Galadima dake kwance jikin seat ya lumshe ido yace, “ranka ya dad’e Dan ALLAH ina zuwa”.
Kai Galadima ya jinjina masa kawai batareda ya bud’e idoba, Muftahu ya fita, mintuna 15 saigashi ya dawo hannunsa d’auke da ledoji, ya bud’e seat d’in baya ya ajiye, sannan yadawo mazaunin driver yana maba Galadima hak’urin jira.
Baice dashi komaiba, Dan tuni yama lula wata duniyar.
Gidan gonar Nuren suka nufa, inda su Harun suke a ajiye, a falo suka yada zango, ko ina k’al yake a tsaftace ga k’amshi, cikin masu kula da gidan gonar ya shigo d’auke da wankakkun y’ay’an itatuwa masu k’yau, zubewa yay yana kuma kwasar gaisuwa, Muftahu ne kawai ya amsa, Galadima hannu ya d’aga masa.
Muftahu ya bud’e abinda ya siyo yana fad’in “Ranka ya dad’e mizakaci?”.
Cikin d’an ta6e baki ya girgiza masa kai alamar bazaici komaiba.
“Okay, to bara na kira Gimbiya meybe ita ta saka kaci”.
Bud’e ido yayi yana zubama Muftahu harara, shikuma ya fuske tamkar bai ganiba.
Saida Muftahu yasha fama kafin Galadima ya yarda yad’anci abinci, rabima duk fura da kayan itatuwan ne yasha. Sunkai 1hour da shigowa ya buk’aci ganin Harun da SD.
Sun fara shiga d’akin da harun yake, bayan Muftahu ya saka key ya bud’e matsawa yay yabama Galadima hanya yafara shiga, takun takalmansa ya saka Harun dake zaune bakin gadon d’akin kansa a duk’e d’agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, Galadima ya janye nasa cike da basarwa yana wani miskilin murmushi mai k’ona zuciyar mak’iyi.
Harun ma janye idanunsa yayi yanajan tsaki, Muftahu kuma ya ta6e baki yana gyarama Galadima kujerar zama.
Galadima ya zauna idonsa akan harun, hannunsa ya mik’a ya kar6i lap-top d’insa dake wajen Muftahu, ya d’orata bisa cinya sannan ya janye idonsa ga harun dayak’i sake kallonsa, lap-top d’in yafara dannawa cikeda kwarewa, cikin seconds dabasufi 10 ba ya d’ora lap-top d’in saman stool d’in da Muftahu ya sake ajiyewa, sannan yay playing abinda ya kunna yana hard’e hannaye a k’irji da zubama Harun ido.
Harun har yayi tamkar zai share sai dai ya kalla lap-top d’in, Wato shine a ranar sunan y’an uku gab da za’a sace yaran shida d’aya daga cikin kidnapers d’in.
“Bibo inaso Ku tabbatar da kun kwashe yaran, karku kar6i wad’anda suke hannun k’annen matarsa, Dan na bogine, baby dolls ne aka sakama kaya irin na yaran domin kauda hankali, Sameer yanada wayo fiye da yanda kuke tsammani, Dan haka kuyi komai cikin kulawa da taka tsantsan, dai-dai lokacin da wutar hotel d’innan zata d’auke, zan kwashe yaran insha ALLAH, harsai nabar cikin hotel d’in ni da ku sannan za’a kunna, ina fata ka fahimta”.
“Eh na fahimta ranka ya dad’e, namaka alk’awarin ko y’ay’an sarkine bana Galadima ba yau saisun kwana a alahira”.
“No, banason su mutu yanzu, sai shi ubansu ya d’and’ana d’acin rashinsu, yana gab da mutuwa sai a kawo masa gawarsu, daganan shima kaga ai sai tafiya shida wannan tatsitsiyar matar tasa y’ar bayi”.
“Okey nagane boss”.
Mamaki ya kama Harun har Muftahu. Zuciyar Harun tamkar zata fad’o waje dan mamaki, ya akai Galadima ya d’auki wannan video d’in, bayan dukkan CCTV cameras d’in dake hotel d’in saida suka saye mai kula dasu na hotel d’in aka tsayar dasu daga aiki……..
Murmushin da galadima yayine ya katse tunanin Harun , cikin lumshe idanu da kad’a kai ya gyara zamansa, cikeda izza yace, “Abin mamaki ko? haka nake ni dama, kullum cikin bada mamaki, tabbas 6oyen dakai masa bazai yuwu muganiba, saidai kamanta da koda ace banida hanyar ganin naka idan ubangiji bai k’addaro ruhi na kona y’ay’ana ko matata zai salwanta a hannunka ba babu yanda ka iya, kana tunanin duhu da tsayar da cctv d’in hotel d’in zai baka dukkan dama ko? To kayi kuskure dan Muhammad Sameer kansa cctv ne, eyeglasses d’in dake idona komai duhun waje shi zai haskokane, dan camera d’in jikinsa tana tareda komai, kasan miyasa nabaka damar d’aukar yaran? Saboda hakan yana cikin k’addararsu, nakuma barka dasune danna kafa maka tarkon neman hujja da tabbatar da abinda Muftahu ya sanarmin”.
Muftahu ya d’age gira saboda kallon tsana da Harun ke masa.
Murmushi Galadima ya kumayi yana cigaba da fad’in “ka kira matata tatsitsiyar yarinya y’ar bayi ko? Saikuma abin mamaki ita wannan y’ar bayin, tatsitsiyar ce ta zame maka RAINA KAMA, dan lallai gashi zakaga GAYYA. itace ta haskomin kai a cikin madubin fik’irarta tunkan Muftahu ya sanarmin, takuma koyamin yanda zan fahimci makircinka da nagartar Muftahu, tabbas na yaba ma basirarka Harun, kanada basira k’warai da gaske, tunda kasan kanka kake a jikina kana cin dunduniyata, ni matsayin aboki d’an uwa mafi kusanci nake kallonka, kamar yanda mahaifina yarink’a kallon mahaifinka, ashe kud’in duk kaskane a garemu, nayi imani da cewar lallai ku jarabawane a garemu, kamar yanda k’addarar auren Munaya tazamema rayuwata alkairi, a kullum cikin aibanta Muftahu da bak’antashi kake a gareni, ashe kaine bak’in ba shiba, mimuka muku ni da mahaifinane haka da zafi? Nawa suka biyaku kuke cutar damu………….?”.
“Sameer!!”. Harun ya kirayi sunan galadima cikin fushi, ya mik’e tsaye sunama juna kallon ido cikin ido shida galadima, cikin matsannan ciyar tsanar juna.
“Kabar alfahari magen matarka tamaka bajinta, shawarama zan baka ka janyeta cikin wannan hargitsin, danko ubanta daya shiga a had’ari yake balle ita karan kad’a miya, wlhy Sameer ban ta6a k’aunarka ba, bakuma zan ta6aba har abadan, domin tsakanina dakai BASHIN GABANE, dan haka banida lokacinka yanzu har sai Camera ta dawo hannunmu, bar ganina anan a rufe, akwai mai sarrafa dukkan tunanina a waje, yarage naka kanemi hanyar kare Surukinka kafin aikinmu yazo kansa…”.
A fusace Galadima ya mik’e shima yana dunk’ule hannu, amma sai Nuren daya shigo yanzu ya rik’eshi, “relax my brother, kainefa ka ta6a fad’amin ba’a maidama abokin gaba murtani da murtani, sannan ba’a bashi damar sanin sirrin yak’i sai an had’u a filin daga”.
Galadima ya saki hannunsa daya dunk’ule da bakinsa daya cije, yatsunsa ya kad’a suka bad’a k’ara d’as! ‘Das! Sannan ya zagaya hannunsa a wuya alamar I will kill you.
Cikin d’aga murya Harun yace, “d’an halak ka fasa Sameer!”.
Daga Nuren har Muftahu da Galadima babu Wanda ya amsa masa, a falo suka tsaya, Galadima ya Nufi d’akin da SD yake batare da yace uffanba,
Nanma dai Muftahu ya bud’e masa, ya shiga cikin tsananin fusatar da Harun ya sakashi. zauna suka iske Alhaji Darma cikin kujera yana duba jarida, kaikace a d’akinsa yake.
Galadima ya taune lips nashi tamkar zai hudasu da hak’ori, zuciyarsa Na k’una, lallai sai Harun da ubansa sun k’are rayuwarsu a jail inhar yana numfashi, dan barin irinsu a duniya had’arine babba, musamman a gida irinna sarauta………
Nuren ya katse masa tunani ta hanyar yima SD magana.
cikin ta6e baki Alhhaji Darma ya kalli Galadima yana wani murmushin mugunta, ya ajiye jaridar hannunsa tare da hard’e k’afa.
A bakin gadon Galadima ya zauna, ya kalli Alhaji Darma, sosai Darma ya tsorata da rinannun idanun Galadima, amma saiya dake.
Galadima daya lura da rikitar Darma ya murmusa, cikeda k’asaita ya d’age girarsa, “Alhaji Shehu kenan, angaya maka mutum yakanci bashi ya kwana lafiya, duk wata jarumta da zaka aro kasama ranka tuni nagama bitar karatu a kanta, karigada ka shigo ramin damusa iya gudunka babu wajen 6uya, bama duk wannan ba, minene had’inka da surukina? Sanann minene yasa kuka kashe mijin y’ar uwata? Dan ko tantama banayi da hannunka a cikin kisanshi!!”. Galadima ya k’are maganar cikin matsanancin tsawar data rikita Alhaji Darma.
Dukya rud’e yarasa ina zai kama, cikin in ina yace, “Ni sharri zakaimin bansan komai akan mutuwarsa ba”.
Galadima yay dariya, saikuma ya gimtse fuska. Yace, “Okay, babu hannunka amma kake tursasa yarinyarsa Samha ta dinga d’akko maka sirrikana tana kawo mata? Kullum kana ma yarinya barazana da mutuwa ko? Alhaji shehu aini tun ranarda mijin aunty Mimi zai koma ga ALLAH naga idonsa ya tsaya cak akanka lokacin da numfashinsa ke bankwana da duniya na d’ora alamar tambaya a kanka, sai kuma yanda kake kaffa-kaffa da Samha a gaban mutane, yayinda itakuma take a d’arare dakai, dukkan wayar dakake mata kana sakata sato maka sirrina INA kan sani, dan nine da kaina nake ajiye mata tagani danta tura maka batareda ita kanta ta saniba, shiyyasa na jata jikina fiye da kowa a gidanmu, duk abinda Sameer zaiyi cikin ilimi yakeyinsa Darma, koda yake bamuzo wannan matakinba, miye had’inka da surikina?”.
Alhaji Darma dake a rikice saboda tsoro da tashin hankalin zantukan Galadima ya had’iye yawu da k’yar yana fad’in, “B..babu ruwanka da abinda ke tsakanina dashi kuma”.
“Hummm”. Galadima ya fad’a cikin cije lips, wayarsa ya d’akko ya kunna wani recording daya nad’a a wayar Darma ranar da suka kamoshi kafin su d’akkoshi.
Waya yake da wani cikin tsananin fusata, “Boss wai miyasa bazamu aika shegenan barzahu ba idan yak’i bamu Camera d’innan? Tunda munada hanyar da zamubi mu kar6a d’in, Nibansan miyasa kuke cewa abishi mataki-mataki ba, kasanfa y’arshi yaronan Sameer take aure, yanada hanya mai sauk’i dazai bashi camera d’innan, shi wancan banzan Alhaji Halluru babu tsiyar da y’ay’ansa zasuma mutane, kullum sai tsarin banza yake mana”.
“Karka damu Alhaji shehu, mu bashi damar k’arshe daya buk’ata, tunda ya tabbatar mana a wannan karon zai kar6o camera d’in ta hanyar matan y’ay’ansa, yana son takara, yakuma San inhar burinmu bai cigaba shida takarar Governor saidai kallo”.
“shikenan boss, bara naje ance nayi bak’o”.
“Ok ngd”.
Galadima ya gimtse recording d’in dai-dai nan yana murmushi da kallon Alhaji Darma dake tsuma dukan jikinsa na 6ari.
Cikin d’age gira Galadima yace, “wannan ma ba matsalata bace? Kasanfa shikad’ai ya isheni hujjar gurfanar dakai gaban K’uliya, shikenan babu girma babu mulkin da ake mana Homa da tak’ama dashi right? ”.
Mi Nuren zaiyi kuwa inba Bushewa da dariya ba, dan yatuna Alhaji Shehu ne yafad’ama Galadima maganarnan randa suka kamoshi.
Cikin Fusata Darma yake kallon Muftahu da Nuren dake dariya, ya mik’e tsaye yana nunasu da yatsa, “y’an samari lokacin dariyarku baiyiba, dan camera d’in da kuke farfagandar nema tana gab da zuwa hannunmu, kunga kuwa ai kune abin dariya”. Ya k’are maganar da kwashewa da dariya.
Dukda furucinsa ya daki zuciyar Galadima bai nunaba, saiya mik’e yana murmushi da kallon Darma. Yace, “lallai kaine ka cancanci ayima dariya, indai camera ce tadad’e da zuwa hannuna”.
Yana gama fad’a ya fice, su Nuren suka kuma sanya dariya, dukda yanayin Galadima ya tabbatar musu akwai matsala. Sunama Alhaji Darma dariya suka fice abinsu daga d’akin.
A falo suka iske Galadima yanata safa da marwa cikin tsantsar damuwa, sai danna waya yake yana sakawa a kunne alamar Neman wani tak’i shiga.
Cikin sassarfa duk suka k’araso garesa suna tambayar lafiya?.
Bai tanka musuba, saboda Munaya ta d’aga wayarsa, “Abba ya dawo kuwa?”. abinda kawai yace mata kenan.
A tsorace tace, “Miya farune?”.
Tsawar data rikitata ya daka mata, “ya ina tambayarki kina tambayata?”.
Cikin in ina tace, “Kayi hak’uri, bai dawoba”.
“ya salam” yafad’a cikin dafe kai. yace, “Kinyi waya dashi? Ko kinji wani yayi waya dashi?”.
“A’a gaskiya, Jiya da safe dai nayi waya dashi nida Munubiya, amma yau ko innarmu banji sunyi wayaba…….”
Cikin katseta yace “kinga maza bincikamin waye yay wayar k’arshe dashi a gidanku, sannan kuma awa nawa dayin wayar”.
“Okay” munaya tafad’a tana yanke wayar.
Shima wata Number yashiga nema yana fad’in “Lallai akwai matsala, tunda kukaji Harun da Alhaji Shehu sun fad’a to sunsan misuka shiryama Abba, gashi nabaza su Ameer sumin wani aikin…” ya k’are maganar da saka wayar a kunne saboda daddy ya kira.
Bayan sun gaisa ya tambayesa ko sunyi waya da Abba a yau?.
Daddy yace, “eh da asuba yakirashi akan zai dawo yau”.
Galadima yace, “Alhmdllh Dady wace number ce?”.
Dady yace bara Na turo maka.
Koda Galadima ya yanke wayar saiya kira baba k’arami shima, shima ya tabbatar masa sunyi waya da Abba bayan fitowa salla, Dan wannan al’adarsu Ce ko a ina wani cikinsu yake saisunyi gaisuwar safe da bankwanan kwanciya barci, sannan idan wani cikinsu yayi tafiya zai kira y’an uwansa yayin dazai kamo hanya.
Hankalin su Nuren ma duk a tashe yake, balle uban gayya Galadima………….✍????
????????Turk’ashi, ana wata ga wata kuma????????♀.
Lallai yaukam tura na shirin kaiwa bango????????♀.
ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????