NOVELSRANA DAYA

RANA DAYA BOOOK 1 CHAPTER 10

CHAPTER 10

BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????

 Halima Abdullahi Access bank       sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427  idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son a tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427  zamuyi maku cikin sauki*

????????????????Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551????????????????“`

Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551

Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi????????

Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai

????️????️????️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi????????

Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari???????? akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan????????
Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida???????????? Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata

Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551

Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata????????????????

Mun tsaya

Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya.
Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance.
Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.”

Ta tsugunna ta gaida shi, ya amsa tare da fadin “Mike.” Ta mike tsaye tana wasa da gefen hijabinta. “Ya karin hakuri?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce, “Kin daina kuka ko?”
Ta ce, “Ai tun da ka hana ni ban kara ba.”
“Yauwa, ki dangana. Yanzu wace shawara ki ka yanke, ko in ee me ki ke so in yi miki?”
Ta kalle shi tayi dan guntun murmushi, sannan ta sunkuyar da kai. Ya ce, “Ki fada ni na baki zaɓi kuma na dauki alkawarin ko me ki ke so zan miki, ko nawa zan kashe. Gidanku kuma naso ace zan gyara muku amma ina cikin shirin bikina.”
Tayi ‘yar dariya “Aure zaka yi?” Ya ce, “Aure zan yi, za ki zo min ko?” Ta ce “Zan zo.’ Daidai lokacin Bakaniken ya sauka a Mashin. Ya ce “Ina zuwa, bari muyi magana da Bakanike.”
Sun kusa minti takwas sannan ya bar shi yana duba motar ya dawo gurinta. Salma ta rasa yanda zata yi masa maganar. Ya ce, “To karatu ki ke so ne ki ka kasa fada?”

Ta ce, “Karatu naso Yaya, amma dai akwai burin mahaifina a kaina, kuma har a ranar da zai mutu sai da ya maimaita yana kuka…Hawaye suka soma zubo mata, tayi kokarin Isayar da kukan sannan ta ci gaba da magana cikin raunanniyar murya mai cike da tausayi.
“Naso in zama ‘yar Jarida a rayuwata, amma dole in shafe babin haka in yi aure kamar yanda Mahaifina ya bar wasiyya..”
“Aure!?” Shatima ya katse ta cikin mamaki.
Ta kalle shi fuskarta sharkaf da hawayè. “Aure Yaya.”
“To dama kina da saurayi kenan ko?” Ya tambaye ta.
“Akwai wani Basiru da yake sona.”
Kanshi ya sake kullewa, ‘yar yarinyar nan tana soyayya! Ya kalle ta. “Tun yaushe ku ka fara soyayya da shi?” Ta ce. “Zai kai wata biyu dai yana zuwa gurina, tun ina zuwa Makaranta ya taba cewa yana sona na ce mishi karatu zan yi.
Da na daina zuwa kuma sai ya dawo lokacin
Baba ya soma zancen aurar dani sai na hakura na saurare shi.
Ya ce, “To ke kina sonshi ne?” Ta ce, “Ni ban san wani so ba.” Tayi ‘yar dariya tare da rufe fuska. Ya ce, “Ban gane ba?” Ta ce, “Ni dai
kawai in aure shi amma Yaya wallahi ban san so ba.”
Ya ce “Misali ba ki tunanin shi? Ba ki son ganinshi da makamantansu?” Ta ce, “Yaya ni fa in ya zo yazo, in bai zo ba har mantawa ni ke Allah yayi ruwan tsirar shi.”
Shatima bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba, domin yanda ta fadi kalmar ta ba shi dariya sosai. Ya ce, “Har akwai wani ruwan tsirar mutum? Lallai Salma kin iya magana. To kin ga ba son wannan Basirun ki ke yi ba.”
Ta ce, “To ko bana son shi Yaya zan aure shi haka don in cika umarnin Mahaifina, kai sai ka yi min kayan daki ka aurar da ni kawai.”.
Yayi shiru yana kallonta. Itama ta kalle shi, sai taji kunya. Ta saka tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya ce, “Mamakin ki ni ke yi Salma, yanzu in aka yi miki aure kin san ya za ki zauna a gidan mijin?”
Ta kama gefen hijabinta ta rufe fuska, “Zan koya Yaya.” Ya ce, “Karatunki ya zama tarihi kenan yanzun?” Ta ce, “Ya zan yi, dole in hakura.”
“Sana’ar me shi saurayin naki yake yi?” “Gyaran famfo, da kuma Achaba.”Ya sake kallonta cikin tausayi. “In kin samu wanda zai ba ki dama kiyi karatu, kuma ya aure ki za ki bar Basiru?”
Ta ce, “Sosai ma. Ban san adadin farin cikin da zan yi ba.” Ta runtse ido “Allah Ka tabbatar min da haka.” Ta manta a gabanshi take, sai taji an ce “Ameen.”
Ta bude ido da sauri, tasa hijabi ta rufe fuska. Ya ce, “Kina amsa addu’a ba ki san Yaya mijin yake ba?” Ta ce, “Ai ko wane iri ne in dai Musulmi ne shi.” Ya ce, “To zan je in yi shawara da shi in zai yiwu zamu zo da shi.”
Bata ma lura da wani bakanike ya gama gyara har ya dana motar ya dawo ba, sai da taga ya tsallako ya ba shi makulli. Ya ce, “To zan tafi Salma, sai dai na zo.” Ta ce, “To me zan ce musu a gidan?”
Ya ce, “Ki ce zan canza miki wani miji wanda zai bar ki kiyi karatu har ki cika burinki.” Ta ce, “Na gode Yaya. Dazu naji ka ce zaka gyara mana, ai haya muke yi.”
“Haya? Wannan gidan ne ake haya?” Ya tambaya cikin mamaki. Ya kalli agogon hannunshi, “Bari in tafi zan zo.” Ta ce. “To sai anjima.” Tana tsaye har motarsh ta bace.Hajiya ta kira shi, yana dagawa ta ce Momiyo tana ta kiran ka ba ka daga ba.” Ya ce, “Ina tuki ne shi yasa, sai na isa Kaduna zan kira ta.” Ta ce, “To shi kenan bari in fada mata.”
Momiyo karamar kanwar su Hajiya ce. Ita ce kuma za tayo masa odar akwatunan lefe. Sai da ya isa sannan ya kirata.
“Anty Mamiyo kina ta kirana ina hanya, ka’idata in ina tuki kiran Alhaji ko na Hajiya kawai ni ke dagawa.” Tayi dariya, “Za ka fara daga na matanka kwanan nan.”
Ya ce, “Su a wa? Za dai su san ka’idata a kwanannan.” Ta ce,
“Maganar akwatuna ce zan tura maka online sai ka zaba, saboda gobe zan yi odar.” Ya ce, “Kowace a dauko mata kalar da tafi so.
Ta ce, “Wace kala ce suka fi so?” Ya cc, “Ita dai Amna tun muna Makaranta tana son Lemon green, Aliya kuma na san tana son ja, Nafisa ce dai bari in kirata yanzun, sai kuma daya yarinya
Kin san na samu ta hudu a kawo mata baby
pink.” Ta ce, “Bana son wasa.” Ya ce, “Antywallahi babu wasa. Ke ce ta farko da ki ka san zancan nan, Ta ce, “Ka san me ka ke yi kuwa?” Ya ce
“Don Allah Anty kiyi yanda na ce, kar ki manta
baby pink, bari in kira Nafisa din.”
Take ya kira Nafisa ya tambaye ta best color dinta ta ce purple Ya kira Anty Momiyo ya fada mata.
Salma tana shiga gida ta samu su Innarsu tamkar ita suke jira, ta fada musu komai yanda suka yi ita da Shatima. Su Yaya Hadiza sun hau murna.
Inna kuwa ta dira ta ce “Ba ta yarda ba, ko dai mutumin nan da biyu ya zo?” Salma ta ce, “Inna biyu kamar ya ya?” Inna ta ce, “To ni ban gane ba, daga taimako sai kuma ya ce zai samo mata miji?”
Yaya Hadiza ta ce, “Haba Inna, ki kyautata zatonki a kansa.” Auwal ya ce, “Inna jikan gidan Alhaji Shatima ne fa, sanannu ne
“Shi kenan, Allah dai ya zaba mana mafi alheri.” In ji Inna. Suka ce “Haka za ki fada Inna.” Momiyo ta daga wayarta ta kira Hajiya. Tana dauka ta ce, “Momiyo ki bari zai kira ki.” Ta cc, “Ai ya kira ni Hajiya, wai seti hudu za a kawo masa, wai ya samu ta hudun. Haka ne?”
Hajiya cikin daga murya ta ce, “Abin hauka ne za a ce ya samu ta hudu! Kila dai ita Amna. za a kai wa saiti biyu, tunda kin ga tuwon girma miyarsa nama, a ce komai daya za’ayi?”
Momiyo ta ce, “Ni fa ya nuna min da gaske yake amma dai kyaji in ya dawo daga bakinsa. Ai ni tunda a ka ce flat hudu ya gina na san da wata a kasa.”
Hajiya cikin damuwa ta ce, “To maji-magani.” Suka yi sallama.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button