
**
Biki saura kwana ashirin da tara, ko ina kansu ya dau zafi, gobe yake son yaje gidan su Aliya da Nafisa ya kai musu makullan gida, don kowa yaje ya ga gida. Haka kuma yana son ya kai musu Amna, amma abin da yafi daga masa hankali yanda zai ga ya shigar da lamarin Salma ga danginsa, dole ya je gurin Munnir yanzun don ya fara samun goyon bayansa. Suna cin abinci a falon Munnir yana gefen fada masa abin da ke tafe da shi. Munnir ya aje cokali, ya ce “Ka ga abokina fada min kawai abin da ka ke son fada min.
Shatima ya ce, “Kai tsaye ina son yin ta hudu da yarinyar nan Salma wadda Mahaifinta ya rasu.
Da karfi Munnir ya ce, “Me ka ce?” Har sai da faisal danshi da ke bacci a kan kujerar da ke kusa da shi ya tsorata ya farka.
Munnir ya dauki yaron tare da kwalana uwarshi kira. Fatima zo ki dauki wannan.” Ta shigo ta amshe shi tana cewa “Ya tsorata ne?” Munnir ya ce, “Magana ce nayi me karfi, shi ne ya fırgita.’
Ta ce, “Kana tunanin mata ukun sun yi maka kadan ne da har sai ka kara da wannan ‘yar babyn da bata fi ka haife ta ba, da a ce kayi aure da wuri. Wai me ke damunka?”
Ya ce, “Lafiyata lau, kuma ba wai wadancan ba za su ishe ni ba ne, taimako zan yi ina jin Tausayin yarinyar.” Ya fada mishi duk yanda suka yi da ita.Munnir ya ce, “Ban ga wata matsala a cikin bukatar tata ba. Ka sai mata kayan daki ka aura mata wancan shi kenan.”
Shatima ya ce “To karatunta fa?” Munnir ya ce “Kayi magana da mijin ya barta kai ka dauki nauyin karatun nata, kaga shi kenan ka huta da wasu surutai da zasu taso daga danginka, da kuma matanka.”
Shatima ya ce, “Ban yi wannan tunanin ba, amma na riga da na fada mata cewa zan kawo mata miji wanda zai barta tayi karatu, kuma tayi
murna. Munnir ya ce, “Ka ce mata kai ne?” Shatima ya ce, “A’a.” Munnir ya ce, “To kawai ka dauko batun wancan ka cire kanka.”
Shatima yayi shiru tamkar mai nazari, har
Munnir ya soma zaton shawararshi ta shiga har yana cewa kayi nazari da kyau abokina.” Sai yaga Shatima ya bude ido sannan ya kalle shi, ba wai na gamsu da shawarar ka ba ne, ina tunanin yanda za ayi fadan karshe ne tsakanina da su Hajiya.
Don tabbatar da yarinyar nan tana cikin mata hudun nan da na gani a cikin baccina. Sai yanzu na luna ban fada maka ba, akwai wata a mafi Kankanta a cikin matan mafarkina, babu shakka
Salma ce Tsaki Munnir yaja sannan ya ce, “Allah Ya taimaka.” Shatima ya ce, “Dama haka ka ce, tun dazu da yanzun mun kusa gidan Kaka.”
Munnir cikin jin haushi ya ce, “Ni babu inda zan fita, bacci ma nike ji.” Shatima ya ce, “Gurin Kaka dole ka zo muje, In na samu goyon bayanta kowa dole ya lafa min.
Sai dai ina ji a jikina, ba za ta ba da hadin kai ba itama. Munnir ya ce, “Allah Ya sa kar ta amince.” Shatima ya mike.
“Don Allah tashi muje koda zugata kayi ka
ji?” Abokina haka sai ya gaji da matsin Shatima ya tashi suka fita.
Allah yasa bata kai ga shiga cikin daki ba, lokacin da suka yi sallama a falonta. Bayan sun gaisa Shattima ya shiga kame kame ya rasa ta inda zai bullo ma al’amarin.
Ya ce, “Kaka nasan dai muna tare ko me nazo da shi, ba za ki kware min baya ba.” Hajiya ta ce, “Kayi magana kai tsaye ni bacci nike ji in shiga ciki, don ka taki sa’a yau a nan nayi sallah.”_