
**
Tunda Kaka taji sallama tare da kamshin kalolin abinci ta tabbatar cewa Hajiya Halima ta diro gidan, domin wannan ita ce shaidar farko da take fara alamta mata cewa Surukar arziki ta shigo gidan.
Ta fito daga cikin dakinta tana dogara ‘yar sandarta mai kyau, wadda ta ke taimaka ma kafafunta wadanda suka yi rauni.
Ta amsa sallamar cikin murna, ta zo ta zauna kan kujera. Hajiya Halima ta zauna kasa kan kafet. Badi’a da Maryama suka shiga jere kulolin da Hajiya Halimar ta zo da su.
Suka sake fita suka shigo da sauran. Kaka ta ce, “Ba ki gajiya Hajiya Halima, kowane lokacin in za’a zo duba ni sai an zo min da abin tabawa. Allah Ubangiji yasa ke ma ‘ya’yanki suyi miki. Ga jarumin namiji nan Shatima, cikin matansa Allah zai sa wata ta miki fiye da abin da ki ke min.
Hajiya Halima tayi murmushi bata amsa ba don nuna kara ga uwar mijin tata.
Bayan sun gaisa ne suka shiga hirar duniya, Badi’atu autar Hajiya Halima, da Maryam yar gidan Hajiya Saude kanwar Baban su Shatima wadda ke gaban Kaka, sun kule a daki suna tasu hirar.
Hajiya Halima ta kalli Kaka ta ce, “Hajiya sai kuma wannan mashirmancin ya zo da zancen zai auri mata uku rana daya, wannan ai labari yake yi. Dubi masu mace daya ma yanda suke fama a wannan zamani, ni dai na ce masa a’a ya dai zabi
daya, in ma karin ne sai ya bari ya ga kamun
ludayin zaman, in yaso can gaba ya kara.” Kaka dai ba ta ce kala ba, har Hajiya Halima ta kai karshe. Kaka ta ce, “Zubo min abin da ki ka zo da shi in lasa ko nafi samun abin fadi.”
Dariya suka yi su duka sannan ta ce, “Farfesun kajin zan zubo miki, ko na kafar Sa? Sannan akwai kus-kus, ga kuma faten acca.” Kaka ta ce, “To fa! Duk a cikina? To zubo min
faten sai ki sa farfesun kafar Sa din a ciki.”_
????️RANA DAYA ????️