NOVELSRANA DAYA

RANA DAYA BOOOK 1 COMPLETE

RANA DAYA HAUSA NOVEL COMPLETE [BOOOK 1]

RANA DAYA

Da kyar ya ce”Kira min Hajiya.” Da gudu ta sauka, tun daga benen take kwala ma hajiya kira. A falon Alhaji ta same su tana kokarin hada ma Alhajin shayi.
A tsorace ta waiwayo ta ce, “Mene ne?” Ta ce, “Yaya ba shi da lafiya.” Alhaji da ke cikin dakin baccin shi ma ya fito da sauri.
“Ba shi da lafiya kuma?” Badi’atu ta ce, “Eh, yana ta rawar sanyi.” Gaba dayansu suka nufi saman. Sun tsorata da ganin yanayin shi, domin gaskiya ba shi da yawan ciwo.
A tare suka bude bargon, ya kanannade
jikinshi yana ta bari. Alhaji ya kama shi ya
tallafo mishi kai. “Babana me ke damunka?”
Hajiya ta ce, “Badi’atu, maza ki taso Mustapha ya fito da mota, yi sauri.” Ta tafi da gudu.
Uban ne ya tallafe shi suka sauka kasa zuwa mota. Alhaji ya koma ya cire malun-malun yasa jallabiyya ya dauki kudi. Asibiti mafi kusa suka je ana shiga dashi, Likitan baya nan.
Alhaji ya hau fada, yana cewa wane irin Likita ne har yanzun bai zo asibitin shi ba. Nurse ta ce, “Yi hakuri Alhaji, bari a kira shi, gidan shi babu nisa. Sauran Nurses kuma suka sa shi a gado don yi masa taimakon farko. Sun duba shi suka sa
masa ruwa tare da allura.
Iyayan da Mustapha kaninsa suna tsaye a kanshi suna yi masa sannu har lokacin jikinsa yana rawar sanyi, gashi ba su rufe shi ba, kuma sun kunna fanka.
Likitan ya shigo da sauri. Ya ba Alhaji hannu suka gaisa, Alhaji ya ce, “Haba Likita! Bai kamata ace ba ka fitowa da wuri ba, asibiti mai zaman kanshi a ce an zo babu Likita?”
Ya ce, “Kayi hakuri Alhaji, jiya sai kusan karfe uku na dare na bar asibitin nan mutum uku muka yi wa tiyata. Ya isa gaban Shatima ya soma da bude idanunsa yana tambayar abin da ke damunsa.
Alhaji ya ce, “To mu dai lafiya ya kwanta jiya.” Hajiya ta ce, “Ni da har magana mun yi da shi kafin ya kwanta din ma.”
Likitan ya taba jikinshi ya ji rau da zafi. Ya dubi ‘su Alhaji ya ce, “Ku dan zauna a waje.” Suna fita ya cire ma Shatima ruwan sannan ya taimaka mishi ya cire rigar jikinshi. Shatima ya ce, “Sanyi ni ke ji.” Likita ya ce, “Kar ka damu, zaka daina ji yanzun.” Ya kalli Nurse din da ke tsaye ya ce mata ta kawo mishi wata allura, ya fada mata sunan
allurar ta fita. Ya maida masa ruwan yana ci
gaba da yi masa tambayoyi. Bayan an kawo allurar ya yi masa ita a cikin ruwan, sai ya ce “Kar ka damu gajiya ce da zirga-zirga, sai kuma rashin bacci. Yanzun za ka yi bacci ka huta a nan zuwa jibi zaka wartsake sarai.”
Shatima yayi saurin kama hannun Likitan mai kokarin fita. Ya ce, “Likita don Allah ina son kayi wani taimako daya, nima dai taimakon zan yi.
Likitan ya dawo ya tsaya. Shatima ya ce, “Ina son ka ce ma iyayena damuwa ce ke tare da ni, don haka kada suke yawan matsa min, kuma ka ce musu su tambaye ni damuwar don suyi saurin kauda min ita saboda zata iya haifar min da wani ciwo.”
Likitan ya ce, “Amma kai Lauya ne ko?” Shatima ya yi dan yake tare da fadin “A’a.” Likitan ya ce “Ka iya tsara magana. Zan fada
musu haka din tunda ba cewa kayi a ce kana da wani ciwo ba.”
Ya leka ya ce, “Alhaji za ku iya shigowa.” Suka shigo. Allah Sarki, iyaye duk sun damu suji me ke damun dansu har suna hada baki gurin tambayar Likitan “Me ke damunsa?” Ya ce, “Akwai rashin samun ishasshen bacci, zirga zirga da gajiya.
Sannan kuma akwai wata damuwa a tare da shi wadda ya ki fada min ita. Ya kamata ku san ta don kuyi gaggawar raba shi da ita, domin zata iya haifar masa da katuwar matsala.”
Suka ce, “To Likita, zamu bincika.” Yana fita Hajiya ta ce, “Shatima me yake damunka ne ka boye mana?” Alhaji ya ce, “Haba Hajiya, ki bari tukunna ya samu sauki mana. Zai fada mana kuma za a magance ta.”
Shatima na jin su ya yi lamo, a hankali naman jikinshi ya daina rawa, bacci ya kwashe shi.
Labari ya watsu a dangi cewa Shatima yana asibiti. Nafisa ta samu labari, hankalinta ya tashi take ta fasa zuwa Makaranta ta ce “Mama ba zan jira ku ba, bari in je in ganshi.” Ita ce ta fara zuwa a cikin Amaren Shatima.
Lokacin da ta zo Hajiya tana zaune a bencin kofar dakin da wasu kawayenta. Nafisa cikin kunya ta durkusa ta gaida su, ta kuma tambayi jikin nashi. Hajiya ta ce, “Da
sauki, ki shiga yana dai bacci, Mustapha ma yana ciki.”
Tana shiga idanunta na kanshi, yana kwance sambal jikin shi babu riga, tausayinshi yasa idanunta kawo ruwa. Ta kalli Mustapha.yaya me ya ke damunsa?” “Zazzabi ne kawai, kar ki damu. Da ya farka
zai warware.” Muryarta na rawa ta ce, “Allah
yasa haka. Allah dai ya ba shi lafiya.” Mustapha ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya ce, “Ki zauna.” Ta ce, “A’a da ka bar shi.” Ya ce, “Bari in dan fita in mike kafa ma. Ta zauna shi kuma ya fita. Ta tsura ma halittarshi ido, a ranta tana godiya ga Allah da ya zaba mata Shatima a miji.
Tamkar ta kai hannunta ta dafa nashi, amma
sai ta tsawaci zuciyarta don addininta bai bata damar yin hakan ba.
Lokaci-lokaci mutane na shigowa duba shi su fita. Iyayen Nafisa suka iso har su Hamida. Dauke da kuloli da kalolin abinci da kayan
shaye-shaye. Su kansu masu asibitin sun shaida cewa dan gata ne ya zo jinya asibitinsu, tunda ba a yi awa shida ba amma motocin da suka shigo ba a magana.
Abokan Alhaji kawayen Hajiya ga kuma dangi. Haka nan sai waya ake buga ma Jama’a, ana fada musu Shatima yana asibiti. Nafisa ta ce ma Mustapha lokacin da ya dawo dakin Ban ga Munnir ba.”
Ya ce, “Ai ko ina ga bai sani ba.” Nan take ya kira shi ya fada masa. Ashe kuwa bai sanin ba, ya ce yana ta buga wayar Shatima ba a daga ba.
Mustapha ya ce “Duk wayoyinsa suna gida. Bari ma yaje ya dauko.” Ya fita ya fada ma Hajiya, ta ce yaje ya dauko ya samu missed call sama da talatin.
Yana dubawa ne ma ya kira lambar Aliya da aka sa my love, ya fada mata. Ya kira sweety sai da ta daga ya ce, “Amna ce?” Ta ce, “Ni ce Nafisa.” Mustapha ya ce, “Ok.” Ya kashe ya samu ta Amna.
Itama ya fada mata. Ta ce, “Me ke damunsa?” Ya ce “Zazzabi ne. Ta tambayi sunan asibitin ya fada mata. ya kira Kaka, Maryama ta daga, ya ce “Maryam ki ce ma Kaka Yaya Shatima yana asibiti.
Kaka ta rude ta ce, “Maryama ta kira shi. Da ya fada ma Hajiya nan ta rufe shi da fada. Ta ce, “Wa ya ce ya fada ma Kaka?” Sai ko ga kiran Kakar a wayar Hajiya tasa Maryama ta kira.
Tana dagawa ta ce, “Maza ki sa a zo a ďauke ni in ga jikin dan nan.” Hajiya ta ce “Da kin hakura jikin nashi da sauki.” Ta ce “A’a ban yarda ba, a zo a kawo ni. Jiya ban yi baccin kirki ba na rasa me ke damuna, ashe jikinsa ne.”
Hajiya ta ce, “Shi ke nan gashi nan zai zo yanzun.” Ta kalli Mustapha, sai kaje ka dauko ta dan sarki a surutu da ka tada mata hankali.”
Aliya tana asibiti lokacin da Mustapha ya kirata ya fada mata ciwon angonta, duk hankalinta ya tashi. Taso taje gida ta canza kaya amma zuciyarta ta fada mata ciwon da aka kwantar da mutum, kuma har aka kira ta aka faca mata gaskiya da matsala.
Ta dauki uziri, sannan ta dubi kawarta Aisha ta ce, “Kina ga in tafi a haka?” Ta ce “Kijo mana ai kayan ki a goge suke tsaf!” Ta kira????️RANA DAYA ????️

      CHAPTER 12

BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????

????????????????Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551????????????????“`

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button