NOVELSRANA DAYA

RANA DAYA BOOOK 1 COMPLETE

RANA DAYA HAUSA NOVEL COMPLETE [BOOOK 1]

wayoyinsa bai ji ko da a ransa wai ya tafi ya bar ta ba,
Hajiyar Shatima tana ta kai-kawo a cikin
jama’ar da suka taru a gidan ‘yan uwa da abokan
arziki, amma zuciyarta tana can gurin tunanin
Hajiya Azumu.Wai ina ta shige ne oho! Ba ita ba labarin yarinya. Sai kusan goma da kwata sannan Hajiya Azumi tayi sallama a gidan.
Hajiya ta mike da sauri tazo tana fadin, “Hajiya Azimi haka muka yi da ke?” Ta ce, “Muje daki da labari.” Can kurya suka shiga, Hajiya Azumi ta ce, “Hajiya da matsala katuwa, kuma gashi me afkuwa har ta afku.”

Hajiya ta ce, “Kar ki ja min rai muje labari.” Hajiya Azumi ta ce, “Yarinyar nan sunanta Ummu Salma, iyayenta talakawa ne na tsiya har gidan da suka tashi sai da aka nuna min wanda suke haya.
A cikin bikin nan Shatima ya sai musu gida suka koma saboda kada danginsa su gane tsiyar su.”
Hajiya ta dafe kirji, “Ya sai musu gida?” Hajiya Azumi ta ce, “Har gidan na shiga. An ce barin kudi yayi musu ba kadan ba kuma ance abin sai wanda ya gani, kuma kullum yana gidan.”
man Hajiya ta ce, “To wai yarinyar wani mugun kyau gare ta ne?” Hajiya Azumi ta rike baki tare da fadin “Wane irin kyau, ni da na ga yarinyar ma sai kunya ta kama ni, na soma tunanin ya ya aka yi ya ganta har ya ce yana so? ‘Yar mitsitsiya, figigiya ko nonon kirki babu, ke ina ‘yar aikinki Masa’uda!”
Hajiya ta ce, “Kar ki ce min kamarta take?” Hajiya Azumi ta ce, “To ai Masa’udar ta fi ta cika ido. Hajiya ina ga asiri suka yi masa.”Hajiya ta soma zufa, “Lallai wajibi ne in kira Alhaji Musa tun kafin ma su dawo Kano.” Hajiya Azumi ta ce “Ki hana me? Ai lokacin da naje gidan an tashi daga daurin aure ke nan na shiga gidan nayi musu murna don dai in ga dil!”

Hajiya ta zauna dabas! “Wai dama auran da aka daura da safen nan nata ne?” Hajiya Azumi ta ce, “Shi ne, kuma a gabana ya dauke ta a mota suka wuce…”
Aliya da kawayenta guda biyu Aisha da Madina, sun tafi babban saloon don gyara gashin Amarya.
Suna sauka a dan sahu suka bashi kudin, sai taji gabanta ya fadi. Ta kalli Aisha ta ce, “Kin ji wata wawuyar faduwar gaba da naji! Allah yasa alkairi ne.”
Aisha ta ce, “Insha Allahu alkairi ne.” Madina
ta kalli dankareriyar motar da ke kofar saloon din
ta ce, “Dubi wata mota mai shegen kyau.
Aisha ta ce, “Wai! Gaskiya motar nan tayi karshe a kyau.” Aliya dai bata yi magana ba duk da bata san motar ba, amma da ta kalli motar sai da gabanta yayi wata mummunar faduwa
Cikin rashin kasala suka tura Kofar gilashin shagon, Aisha ta soma shiga sannan Madina. Ba su lura da cewa Aliya tayi mutuwar tsaye ba ne sai da Aisha ta waiwayo da nufin yi mata magana, ta zaci guri ta basu su fara shiga. ” Ta waiwaya ta kalli inda Aliyar take kallo, sai
taga Shatima zaune ya tasa Salma an gama wanke
mata kai ana tajewa da handrayer…
Wash! Bari in tsaya a nan sai mun hadu a littafi na biyu don jin ya ya za ta kasance?

Wane mataki Hajiya zata dauka? Ya ya Aliya zata yi da taga Shatima da Salma da ba ta san labarinta ba? Ya Amna zata amshi maganar Salma? Wane
ma irin zama za’a yi? Wai wace ce ma uwargida? Wa ya fi so?

Ku biyo ni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button