
Dakanta ta taimaka mata.
Wannan Juma’ar an basu me wuya, gashi in
sun je ranar Monday babu lokaci bare Salma ta
taimaka mata don sai da ta bata shawara kan cewa
Yayan da ke sauke ki ya dinga taimaka miki.
Tace
“Ba shi da lokaci ne amma zata mishì
magana.Salma ta ce,
“To ki fada a dinga biya miki lesson, ko a nemo miki Malamin lesson agida.
” Salma tace
“Bari zata yi masa magana.
Cikin Nafisa me laulayi ne sosai, da tsarabar zan ci kaza, ba zan ci kaza ba. Domin wani abin ma sai an siyo shi tacì sai kuma ta sheka amai. Duk ta rame, ta kode abin tausayi kullum cikin
Karin ruwa. Yanzun dole ta yarda Aliya tana saka mata ruwa, tun lokacin da Aliya ta dage a kan sai sun je ta duba Nafisar, shi kuma yana gudun kada
Nafisar ta mata wulakanci ta ce ita dai suje.
Da yake Nafisar ta kanta take yi sai bata yi wata masifa ba. Aliyar ta gyara mata ruwa ta ce, ta gode. Shatima ya ji dadì sosai.
Tun daga ranar kullum sai ta-je gaida Nafisa, bare in ta lura Shatima ya shiga dakin. Amna kuwa ko ta shiga ta kan samu tana bacci, to da yake ba don Allah take zuwa ba, bata komawa sai kuma gobe in yana gida.
Shatima zuwa yanzun ya dauki Aliya ya sata a wani matsayi mai girma. Har yana ganin ta kai yayi kowace shawara da ita, kuma yana ganin zata iya zama wakiliyarshi a wasu al’amura na gidanshi.
Don tana da tsoron Allah, ga tsayawa a kan gaskiya da rikon amana.