RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 15

CHAPTER 15
BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????
ACT<<0700549935 Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925
Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana
Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki
Nafisa ta tashi zaune, ta ce Hamida ta saka mata pillow zata jingina. Ta ce “Hamida yanzun Karfe nawa?” Ta ce,
“Tara na dare.Nafisa ta CE “Tabdi! Kin san wai me nike son ci?”
Hamida ta yatsina baki ta ce, “A’a
Ta ce
“Zogala! Ji wata fitina, ni da bai dame ni ba
Hamida ta ce
“Ni yanzun ina za a samu wani zogala?” Nafisa ta ce,
“Kira min Ya Shatima.”
Yana dakin Aliya daidai lokacin da wayar tayi ringing, ya zo daidai da lokacin da Salma tayi sallama a dakin na Aliya, hannunta dauke da littafin ta wanda za”a koya mata,
Aliya ta amsa, sannan Shatima ya kalleta bayan ya dauki wayar yana duba suman. Zumbur! Ya mike tare da daga wayar ya ce, “Nafisa!”
Hamida ta ce,”Ni ce, ta ce kazo* Ya ce,
“To gani nan zuwa.Ya kalli Salma
“Ya aka yi?”
Tace,
“Yaya dama assignment ne za a nuna mini.”
Ya kalli Aliya,
“Duba mata don Allah, bari in je gurin Nafisa in ji
Aliya tayi’yar dariyar yake tace
“Sai ka dawo, don Allah ka ce ina yi mata sannu.
Yana fita Aliya ta kalli Salma kallon sama da kasa irin kallon wulakanci da raini, ta ce “Aka yi sati da Lahadi duk ba ki tuna da assignment ba sai yanzun da ki ka ganshi a nan dakin? To bari in ja miki kunne, duk ranar da yake dakina na haramta miki zuwa.
Salma ta ce, “Anty don Allah kiyi hakuri, ina ta tunanin yanda zan ma Yaya magana ne,
” Aliya ta fizgi takardar tana dubawa. Salma ta ce
” Anty bari ki ga yanda aka ce….
Aliya ta katseta da cewa,
“Da Allah ni yi min shiru, ke ce za ki nuna min, tun kafin a haifi uwar me alli Balbela take da farinta.”
Salma ta ce,
“Me ki ka ce?” Aliya ta ce,
“Tun kina^yar mitsitsiyarki ni ke zuwa boko, kuma muke rubuta maths.
Salma ta ce, “Yi hakuri.”
.” Don ta lura Aliyar tayi maganar cikin fushi ne. bata koya mata ba, saidai ta rubuta ta bata tare da cewa gashi nan ni bani da lokacin yi miki wani nune-nune.
Salma taje daki tana dubawa cikin kokwanto,tana tunanin gaskiya da kyar in haka ne, amma zata je da shi Makaranta ta nuna ma Salma Dankasa
Shatima ya shigo,
“Ina Salman?” Ta ce,
“Nayi mata ta wuce, yarinyar nan Allah Yasa dai tayi karatu, naga dan abin da ta kasa ganewa,ga takardarta duk ziro
Ya ce,
“To don Allah ki ke taimaka mata, sai a
hankali.Aliya ta ce,
“Har Lesson na ce zan ke yi mata.” Ya ce, “To ai ko na gode. Yanzu ina zan samu zogala?” Ta ce, “Wake so?” Yace”Nafisa.Ce.
Tace
“Gashi dare ya yi. Amma ka tambayi
Maigadi, in za’a samu danye sai a dafa mata yanzun ayi mata kwado.
Ya ce,
“Haka ne.
Maigadi ya ce, “Can makotan suna da shi
Sai gashi an samu, nan da nan Aliya ta zage ta dafa, ta cE
“Sai kuma in da za a samu kuli-kuli
Nan ma Maigadin aka sake tuntuba. Shi ya bazu cikin unguwa sai kusan sha daya saura ya dawo. Kura-Kura aka samo. Aliya dai aka zage aka daka, ta kwadanta mata. Nan ya dauka ya kai mata. Tasa a gaba kuwa tayi ta ci, cikin ikon Allah kuma sai gashi bata yi amai ba,
Salma tana zuwa Makaranta, ta nuna ma Salma Dankasa, Salma ta ce
“Wa ya yi miki?”
Tace *Matar Yayana
Salma ta ce,
“To ba daidai bane.
Ta dauko littafinta ta nuna mata.
*Kin ga nIfa.
- Salma mamaki ya cikata, amma ta share tace “Bari ta sake kwalewa sai tayi kafin Malaminsu ya iso.”
Amna cikin bacci taji karar wayar Shatima. Ta kalle shi yana ta bacci, da alamu yau ya gaji sosai,don sun je Abuja ne sai ma goma ya shigo gidan.
Ta kai hannu ta shafa fuskarshi,
“Honey ana kiran wayarka tun dazu.” Ya bude ido da kyar, taCe
“Ka gaji ko?” Ya ce,
“Na gaji sosai.”
Yana daukar wayar daidai lokacin kiran ya tsinke.
Yana dubawa yaga sau tara ana kira. “Nafisa!”
ya furta da karfi tare da mikewa tamkar bai taba bacci ba. Amna ta dube shi, “Wai ina za ka?” Yace,
“Nafisa, ina zaton jikin ne.”
Amna ta sakko itama bata yi mishi magana ba,illa dai taje ta murda makullin kofa ta cire key din
tare da fadin, “Ba za ka fita ba. Na gaji da irin wannan abun, don ciki bai fi ciki ba.
Saboda salo bata tashi kiranka sai ranar da ka ke dakina? Sau biyu tana yi min haka, ba zan bari tayi na uku ba, tunda naga abin nata yana neman ya zarme.
Shatima ya ce, “Haba Honey, kin san fa cikinta ba irin naki ba ne.
Ta ce, cikin mamaki,
“Au!
Dama akwai wani ciki na musamman ne wanda kayi mata shi ni baka yi min ba?” Ya ce “Ba haka nake nufi ba, nata cikin me yawan laulayi ne. Don Shatima ya kira. Hamida ta ce,
“Tun dazun yake kira.” Aliya ta ce “Bar shi kar ki daga har sai ya fito, in yana dakin wannan ‘yar gwal din ba ya iya fitowa, yanzu dubi jikin baiwar Allahn nan amma ya wofintar da ita.Hamida ta ce
“Allah nima abin ya bani haushi,
na kira shi ya fi sau ishirin amma bai ko daga ba
Da ya daga ya ce min yana zuwa shine fa shiru Aliya ta ce,
“Sai ga shi ya kira ni wai inzo
Hamida ta cE
“Ai mun gode, Allah ya saka dabalkairi. Ai har Mamanmu na fada mata irin taimakon da ki ke mana.Aliya ta ce,
“Ai yi wa kai ne.
” Sai da aka kira sallar Asubahi sannan ta koma dakinta.
Shi ko Shatima zama ya yi a kan durowar gefen gado, yana ta kiran layin Aliya, ita kuma ta baro ta can dakinta domin da ta Nafisa ya yi ta kira yana tambayar Hamida ko Aliya tazo? Tana fada masa cewa bata z0 ba.
Bayan yayì sallah ya ce “To yanzun sai ki bude ni in dubo ta ko?”
Ta Ce
‘”Ai ba yanzun ka ke zuwa ba.
Ya cE
“To yanzun kuma zamu iya samun matsala tunda gari ya waye
Ta ce,
“Mu samu mana, dama nasan ba zaka kula dani ba kaje ka rabo ni da gidanmu ina can cikin tattali
kaje ka dauko ni.”
Ya ce, “Kin raina kulawar da nake ba ki? To kifada min abin da ki ke son in ke miki don ki tabbatar da ina kula da ke
” Ya fada ranshi a bace.
Ta ce
“Ga shi ka kwana zaune kana dakina
zuciyarka na gurin wata.”
Ta ce, “Yiwa kai ne dai,kuma bana fata kema wata rana in haka ta faru zaki ji dadì in ta hana ni fitowa in wofintar da ke?”
Ta ce”Ni dai ba zan bude ba, dama ka shiga wanka in ba haka ba zaka yi lattin zuwa office.”
Ganin da gaske ba za ta bude ba, ya bi shawarar ta ya shiga wanka. Kan ya fito ta bude sai ya fita zuwa dakinsa ya hau shiri.
Bai ko kalli karin da Ladi Mai aiki ta hada mishi ba, ya nufi fita. Kofar a damke take, ya waigo ta fito tana tsaye a falon. Ta ce,
“Ga abin karinka.
” Ya girgiza kai, “Bana jin yunwa.
Ta ce,
‘”Ai ko ba za ka dakin wata ka karya ba.
Ta soma hada mishi shayi, Har gurin Kofar ta
Zota bashi. Ya amsa tare da fadin “In da ace za ki ke hada min ko shayin ne a duk ranar da nike dakin ki da na yi tasa miki albarka Ya kai
Karshen maganar tare da kurbar shayin
Da sauri ya watso shi domin suga ya ji har
cikin kwakwalwar kanshi. Ya mika mata shayin
“Ga abin ki, bude ni.” Ta kalli agogo, duk abinka sai shida ta cika,
Ya ce,
“Amna har yanzun ina mamakin ki sosai, ashe kin iya mugunta har haka?”
‘ Ta ce,
Na daina bari ana raina min wayo.”
Ya jingina da bango,