
Hajiya ce ta sake jifarta da wayarta dake hannun ta “karya zanyi maki kenan dan ubanki?”
Aliya cikin sauri ta dauki wayar tare da fadin haba Hajiya wayarki kar tayi lahani mana.
Hameeda wacce tausayin Salma ya kamata haka kawai taji ba gaskiya bane abinda Hajiya take fada ba,dan haka ta saci wayar Nafisa tayi cikin daki ta fada bandaki domin yin abinda ya dace.
Aliya ta kalli Hajiya kiyi hakuri bari in zuba maku abinci.
Sakawa Maman ku dan ni bazanci abincin nan ba sai anyita ta kare yau din nan.
Nafisa tace”gwara ayita ta kare domin kada kowa ta yadda kiri kiri hmm”
Aliya tace “aikuwa bayin kansa bane bakiji abinda akace bane”
Amna wadda ta yadda da zancen nan dari bisa dari ta kalli Salma cikin tsana indai tana gidan nan kam nidai bazan zauna ba dan a gaskiya banason asirce asircen nan da akeyi.
Hameeda ta kira sau uku kafin ya daga tace Yaya don Allah kazo gida yanzun nan ga Salma nan an tsareta su Hajiya ne”
Gaban Shatima ya fadi ya manta da tsanar da Hajiya tayiwa Salma, yace “nagode Hameeda ganinan zuwa.”
Lokacin tashinshi beyi ba haka dole ya tashi yaje gida da gaggawa domin kashe waccen wutar wadda shedan ya rura a cikin sa ya dauki uzuri gaggawa ya fita bema san irin gudun da yakeyi ba kawai saidai ya ganshi a layinsu,yana parking lokacin Mustapha ya fito daga falon Aliya.
Shatima ya nufi gurinshi “inasu Hajiya?” Mustapha yace suna falon Nafisa.
Shatima yace “to bari inje mu gaisa” Mustapha ya biyoshi domin ya gama cin abincinshine.tun daga baranda yakejin muryoyinsu daya bayan daya.
Hajiya tana fadin”ba bakin dan akuya ba ko bakin dan jakane kukayi asiri dashi yau sai kin bar gidan nan”.
Cikin kuka Amna take fadin”yanzu zan kira Dadyna nima yazo ya daukeni dan bazaiyiwu in zauna ba,Ina tsoron asiri”.
Nafisa take fadin” jiya nan fa saida nayi mafarki da ita gaskiya bazan iya tuno meya faru a mafarkin ba amma tabbas ita na gani,ni kaina idan tana gidan nan to wallahi Mama saidai mu tafi daku yau din nan.”
Mustapha ne yafara shiga hakanne ya hana Aliya magana taso tayi magana dan ta hangoshine a tsaye.
Cikin tashin hankalin ya shigo cikin dakin gaba daya suka maida kallon su gareshi sannan kowacce ta shiga nanata abinda zata nanata, kowacce ta nanata abinda ta fada.
Hajiya tace “duk kuyi shiru yanzun dai kai kazo ka zaba koni dana haifeka ko kuma iyalanka ko kuma wannan Yarinyar ita kadai? Ta nuna Salma wacce take durkushe tana cikin firgici da matsanancin tashin hankali,itama kallon shi takeyi cike da tsananin bukatar taimakon shi,idanuntane suka nuna shi kadai take bukata,shine taimako na karshe da takesa rai zaiyi wani abu akan wannan halin da take ciki.
Hajiya ta katseshi da fadin “Zan la’anceka!!!…” Zan la’anceka!!! In ka sake kallon ta,kuma na baka nan da minti daya rak ka yanke hukunci……….
Alhamdulillah anan muka kawo karshen littafi na biyu,a yanzu kuma labarin zai fara, akwai cakwakiya fah,anan kuma muka kawo karshen free pages idan kina bukatar 3&4 din littafin RANA DAYA ki turo kudin ki 300 ta wannan account number din????????