RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 17
RANA DAYA BOOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVEL | BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHIBY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI

CHAPTER 2
BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*
Mun tsaya
Munnir ya ce, “Wai don Allah Shatima lafiya ka ke tsaki?” Ya ce, “Ina tunani ne, yarinyar nan Salma tana can cikin damuwa, koma ayi mata wani abin tun da na san ba a sonta
Munnir ya zabga ma Shatima wata harara, sai ka ce irin yara kanana din nan, sannan ya ja dogon tsaki ya ce, “Ka san Allah har na soma tsanar wannan Salmar, duk ka bi ka zama wani soko a kanta.”
Ya ce, “Munnir ba zaka gane ba ne, da dai na sani da na ce ma Anty Momiyo a hada ta da Aliya nasan zata kula min da ita.”
Ya ce, “To ka kira mana ba ga waya a hannunka ba, ka dame mu da tsaki.” Shatima ya fita ya kira layin Anty Momiyo, sai a kira na uku sannan ta daga.
Ya ce, “Haba Anty, kin ki daga wayata.” Ta ce, “Wallahi na gaji ne, na fara bacci.” Ya ce, “Anty don Allah Salma ita da wanene?” Ta ce, “Oho ban duba ba, ‘yan uwanta dai sun fito sun tafi.”
Ya ce, “Ya ya za’ayi don Allah ki hada ta da Aliya.” Anty Momiyo ta ce, “Babu ruwana da Hajiyarku. Kowace Amarya an barta ita da kawayenta da danginta. Sai in je in ce tazo ta hadu da wata! Babu ruwana.”
Ya ce, “To don Allah dan leka min ita Anty ba wai na raina ki ba ne.” Ta ce, “Sai dai in saci idon Hajiyar ka in duba don gaskiya ba da wasa take yi ba a kan wannan Salmar, zata saka kafar wando daya da duk wanda ya ce zai ko kalli inda Salmar take.”
Ya ce, “A taimaka mini zan jira kiranki.” Kamar minti goma ta kira shi, da sauri ya daga ko ringing bata yi ba, har ya bata ‘yar dariya. Ta ce, “Dama zaman jirana ka ke yi?”
Ya ce, “Wallahi.” Ta ce, “To ita daya ce a dakin, kuma sai kuka take, wallahi har ta bani tausayi.” Ya ce, “Anty ba ki bata hakuri ba?”
Ta ce, “Au, ba ka ga kokarina ba, so ka ke sai na
ja ma kaina matsala da ita kaga ni sai da safe.” Shatima ya zauna ya zabga tagumi suna ta hirarsu.
Haushi ya hana Munnir magana. Sha daya saura, Munnir ya ce bari yaje gida. Ya zubawa Shatima makullan motocinsa guda biyu, tare da fadin “Ga wadannan ka rike zan tafi da dayar motar.”
Shatima bai tanka ba. Munnir ya ja tsaki, “Duk ka damu mutane da zancen wata tsuntsuwar yarinya,
ka dauki jarabar so ka dora mata. Shatima ya ce, “Kai ka ki saurarona ne bare ka gane dalilina, kaje kawai.” Munnir ya wuce.
Shatima dai ya rasa sukuni, sai tunanin yanda zai fidda Salma a matsala. Har kusan sha biyu bai samu mafitar da ta wuce yaje gidan ba, duk da su Hajiyar sun nuna cewa zuwan shi gurin Amaran a yanzun ba tare da an yi budar kai ba kamar wani haramun ne bisa al’ada.
Sha biyu da mintuna ya shigo da mota harabar gidan, ya kalli gefen baki inda Aliya take, sannan ya taka ya nufi falo. Babu mutane sai yara da suka yi bacci a kan kujerun falon. Amma yana jiyo magana daga gefen Hajiya, cikin sanda ya nufi samanshi. Salma wadda ta sha kuka fuskarta ta kumbura suntum! Kukanta da yawa, ta tuna Mahaifinta, ga rabuwa da Innarsu, da Yaya Hadiza, da Yaya Auwal, da Umar kaninta. Sannan gashi da a lamun bata samu karbuwa a wannan dangin ba, sannan gashi ba ita kadai gurin miji ba.
Tana jin lokacin da Anty Momiyo ta bude kofa, cikin sauri ta dago ta dube ta, sai taga matar ta tabe baki ta juya. Hakan yasa ta sabon kuka ga makogwaronta ya bushe, tana bukatar ruwa.
Sake bude kofar taji anyi, cikin sauri ta sake dago da kai suka yi ido hudu da Shatima. Wasu sabbin hawaye taji sun zubo mata, da sauri ya iso ya tsugunna a gabanta.
“Salma, mene ne? An yi miki wani abu ne?”
Yasa hannu ya dago fuskarta. “Subhanallahi! Haka
fuskarki tayi? An dake ki ko?” Muryarta a dishe, tace “Ba a bige ni ba.”
Ya ce, “Kukan me ki ke yi to, saboda ba ki sona?” Ta zuba mishi ido kawai tana kallonshi. Ya ce, “To share hawayenki, na tuna ke ba ki ma san so ba ko?”
Ta daga kai alamun ‘eh’. “Na gano kukan da ki ke yi na rabuwa da Inna ne ko?” Ta daga kai. Ya ce, “To kada ki damu, zan dinga kawo ki a kai-akai kin ji?” Ta ce, “To.” Ya ce, “To yi murmushi.” Ta dan kirkiro shi tayi.
Ya mike ya soma kwashe kayan shi da ke zube a kan gadon, duk sabbin da ya yi ta canji ne, sai kamshi suke. Ya ce, “Bari in rage miki kayan nan
ko? Za ki ma iya kwana ke daya? Me yasa ba a bar miki kowa ba? kuma ke wai ba ki da kawaye ne?” Ta ce, “Su Yaya Hadiza sun ce an yi musu wulakanci ba za su zauna ba, ni kuma ban gayyaci
kowa ba saboda Babanmu bai dade da mutuwa ba.”
Ya dan yi jim! Don bai so abin da aka yi musu ba, amma sai ya kauda zancan da cewa, “Kina jin yunwa ko?” Sai lokacin ta tuna duk yinin ranar ba ta ci komai
ba. ya matso “An baki abinci?” Ta ce, “A’a, yau ma bana zaton na ci wani abu.”
Ya ce, “To ina zuwa.” Ya fita, ta sauke ajiyar zuciya. Taji dadin lallashin da ya yi mata.
Mota ya zara ya nufi gurin saida kayan kwalam. Ya siyo Kaza da madara zalla mai sanyi da ruwa. Ya sake wucewa cikin sauri ya nufi samanshi.
Sai dai wani tsautsayi, katsam! Hajiya ta fito da nufin zuwa saman don yin gargadi da barazana ga Salman da danginta in tare suke, sai kawai taga Shatiman yana bin kafar bene.
Sororo ta tsaya tana kallonshi har ya wuce. Ranta yayi mugun baci, ban da gidan cike yake da baki ga su Amna da danginta, da sai ta yi tijara a cikin daren nan Ta gama yarda dari-bisa-dari cewa wadannan talakawan sun asirce mata da.
Shatima bai san Hajiya ta ganshi ba, yana shiga ya same ta kwance ya ce, “Tashi Salma.” Ta mike zaune. Shi ne ya cire mata tsokar yana aje mata, ita kuma tana dauka tana ci tamkar irin dai yanda za ka yi wa karamin yaron da ka ke son ya ci abinci.
Ya zuba mata tatacciyar madarar a kofi ta dauka tana sha. Sai da ta koshi tam! Sannan ta sha ruwa, lokacin ne ya duba agogonshi biyu saura minti shida. Ya ce, “Kai! Har dare ya yi haka? Bari in je in
kwanta nima.” Ta ce, “Amma a cikin gidan nan za
ka kwanta ko?” Ya ce, “A’a in da abokaina suke.”
Ta ce, “Kada fa wani abu ya faru da kai…” Kwankwasa kofar suka ji an yi, gaban Shatima ya fadi, ya isa gurin kofar ya ce, “Wane ne?” Muryar Hajiyarshi ya ji ta ce, “Ka bude ka gani.” A fili ya ce, “Ya salam!”
Ya bude a cikin tsoro. Ciki ta shigo sannan ta maida kofar ta rufe. Tana juyowa bai ankara ba sai jin saukar mari yayi dau!! Salma ta mike a tsakiyar gadon duk ilahirin
jikinta ɓari yake. Hajiya ta wuce shi ta iso gurin
Salma, cikin sauri ya nufo ya tsaya tamkar zai kare
ta. Hajiya ta nuna ta “Ke! Kalli cikin idona kin ga
alamar wasa?” Salma ta durkusa gwiwa biyu a kan gadon. Hajiya ta ce, “Ba ki da gurin zama a gidan dana, ki fada min ina ku ka je ku ka asirce min da?” Salma ta soma kuka, tare da fadin “Wallahi
Hajiya ba ma zuwa gurin asiri.” Shatima ya ce,
“Haba Hajiya!..” Ta dora yatsanta a kan lebe
“Ka min shiru.” Ya ce, “Hajiya ina mamakin wannan fa ba halinki ba ne, ni na sani kina da tausayi.” Ta ce, “Na ce ka rufe min baki.
Ta sake kallon Salma, “Zan sa a kama duk danginki a rufe min har sai sun karya asirin da suka yi wa dana. Kuma sai ya sake ki, sa’arki daya gidan nan yau da bakin alkairi bakin kunya, da sai na sa yai miki sakin wulakanci.
Ina son ki sani zan zo har Kadunar kuma zan sa ya sake ki, kar ma kije da tunanin za ki shantake wai kin samu gurin zama. Sannan gobe ne bikina na nan gidan, da wasa kar ki sake ki fito bare ki bata min biki, na fada miki.”
Salma bakinta na rawa ta ce, “Ba zan fito ba Allah, kiyi hakuri don Allah!” Tsaki Hajiyar taja “Ki ma fito ki gani.” Sannan ta juya kan Shatima.”Kai kuma fita muje, abin da ya sa ni ke raga maka don nasan ba yin kanka ba ne.” Ya ce, “Hajiya ni fa babu abin da aka yi min.
Ta ce, “Ai ko anyi maka kai ba za ka sani ba. Da haka ka ke? Kai da ka ke tsayayyen namiji mai ji da kansa, gashi kan wannan duk ka zama soko, wuce muje.”Haka ta tasa shi a gaba har cikin dakin Mustapha
kaninshi da ke can cikin harabar gidan, ta ce “Shiga
nan ka kwanta.” Yana shiga Mustapha tuni sun yi bacci da shi da wani dan uwansu da suka zo biki, kan kujera ya zauna cikin tashin hankali da tunanin Salma.
Ita kuwa Salma tana tasa shi gaba suna fita, ta
sauko daga kan gadon tana kuka, ta samu can kusa
da wata durowa ta shige sakon ta zauna. Kanta ya sake kullewa, lallai gaskiyar Inna ne da ta ke ta jinjina al’amarin auran nan, tabbas akwai dinbin da na sani a cikin duk abin da aka yi gaggawar shi, domin wata gaggawar daga shaidan take.
Yanda Salma ta kwana zaune, haka shima Shatima zaune ya kwana, kowannansu cikin takaici tare kuma da rasa wane irin tunani ya kamata suyi.Da Asubahi Salma tana jin kiraye-kirayen sallah, har a ka shiga Masallaci. Ta yunkura ta tashi, tana rangaji ta nufi ko far da take zaton bandaki ne.
Tayi alwala, ta kalli fuskarta a madubi, har yanzun a kumbure take. Ta zo ta yafa gyalenta da aka rufo mata, tayi sallah tana addu’a tana jin sanyi yana ratsa ta, kasancewar lokacin sanyi ne.
Ga wani irin bacci da take ji tamkar na mutuwa. Kan gadon ta hau ta ja bargo ta kudundune, nan kuwa bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.
Shi kuwa Ango bayan sun fito Masallaci, yana son zuwa dakin abokansa inda suka yi masauki. Amma kuma yana son sanin halin da Salma take ciki.
Ya nufi falo lokacin gari ya soma yin haske. Ya samu Hajiya ta saka ‘yan aiki suna ta gyaran falo da gida. Tayi kicin-kicin da fuska, kuma da kyar ta amsa gaisuwarshi.
Ta ce, “Ina za ka nan?” Ya ce, “Badi’atu zan kira.” Ta ce, “Tana dakina tare da su Nafisa.” Ya tsaya. Ta ce, “Shiga mana ko ni zan kira maka ita?” Ya wuce falon Hajiyar kai tsaye. Duk ‘yanmatan
Nafisa ‘ya’yan dangi ne nan suka kama gaida shi. “Sannu da zuwa Yaya.” Ya ce, “Ina Badi’atu?” Suka ce, “Tana cikin dakin Hajiya tare da Amarya Nafisa.” Yayi kamar ya ce su kira ta, sai kuma yasa kai ya shige dakin.
Nafisar tana kudundune a gadon Hajiya cikin bargo, tana danna waya. Su Badi’atu suna kan gadon a gefen duk hira suke. Nafisa tayi maza ta tashi zaune jin muryar Shatima.
Ya ce, “Badi’atu zo nan.” Suka kalli juna na lokaci. Rabon da su hadu tun ranar da yaje ba ta kati ta ki amsa. Shi ne ya fara dauke idanu daga kai, sannan ya ce, “Kina lafiya?”
Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin “Lafiya.” Sannan ta koma ta kwanta rigingine tare da jan bargon zuwa kirjinta. Ya fita tare da fadin “Zo Badi’atu.”
Suka tsaya a babban falo. Ya ce, “Hau dakin
nasa ki kwaso min wayoyina.” Hajiya da ke kallonsu
ta windown waje, ta hangi Badi’atu tayi sama, ta ce,
“Ke! Ina za ki nan?” Shatima ya ce, “Wayoyina zata kawo min.” Ta ce, “Oho!.” Ya ce, “Badi’atu zo.” Ta dawo, muryar shi kasa ya ce, “Don Allah Salma tana ciki ki duba min wane hali take ciki? In kin dawo ki same ni a dakin Mustapha.”
Kusan minti tara, sannan ta shigo. Tana ba shi wayoyin shi kuma yana tambayar ta ganta? Badi’atu ta ce, “Na ganta tana bacci a kan gadon ka ta rufa.”
Ya amshi wayoyin tare da fadin “Alhamdulillah.” Ya kama hannunta “Zo kiji Badi’atu. Don Allah ki min wani taimako.” Ta kalle shi cikin mamaki,
Yayanta mai izza da isa yau kuma ita yake roko. Ta cè, “To mene ne zan yi maka Yaya?” Ya ce, “Ina son ki ke kula da Salma, in ta tashi don Allah ki dan debi abinci ki bata, duk abin da ya dace ki taimaka mata, ni kuma duk abin da ki ke so in an gama bikin nan ki fada min zan miki shi.”
Badi’atu ta ce, “Ba sai ka bani komai ba Yaya, zan kula da ita insha Allah.” Ya ce, “Na gode kanwata.” Da ta tafi ya ji sanyi a ranshi, sannan ya kira
layin Aliya, suka gaisa. Ya tambayi lafiyarta da ta
mutananta. Ta ce, “Duk suna lafiya.” Ta ce, “Jiya
ina daga window naga ka shigo, ka kuma fita ka
dawo. Ka ban tausayi sai naga duk ka fada.”
Ya ce”Ai naso in zo in da ki ke lokacin, Salma ce bata ci abinci ba, na fita na siyo mata.” Gaban Aliya ya fadi. Ta dake ta ce, “Ai da ka kira ni nan ga
abinci sai yanzu ma na kwashe kayan.” Ya ce, “Tana dakina ita daya ce, ta bani tausayi,
har kusan karfe biyu ina gurinta. Aliya ta sake danne kishinta tace, “Allah Sarki!
Da ka rako ta nan sai mu kwana. Ya ce, “Babu
[8/16, 21:11] Ummi Tandama????: _____
*????️RANA DAYA BOOK 2????️*
CHAPTER 3
*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????*
ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925“`
Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana
Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki
Mun tsaya
dawo. Ka ban tausayi sai naga duk ka fada.”
Ya ce”Ai naso in zo in da ki ke lokacin, Salma ce bata ci abinci ba, na fita na siyo mata.” Gaban Aliya ya fadi. Ta dake ta ce, “Ai da ka kira ni nan ga
abinci sai yanzu ma na kwashe kayan.” Ya ce, “Tana dakina ita daya ce, ta bani tausayi,
har kusan karfe biyu ina gurinta. Aliya ta sake danne kishinta tace, “Allah Sarki!
Da ka rako ta nan sai mu kwana. Ya ce, “Babu
komai, yanzun ma tana ta bacci.” Ta ce “Daya ‘yar uwar tawa fa ta Kano?” Ya ce, “Yanzun zan kira ta, in mun gama waya.”
Ta ce, “To ka shigar da gaisuwata. Ya Nafisa?” Ya ce, “Tana lafiya, da na shiga gurin Hajiyarmu na ganta.” Ta ce, “To Masha Allah.”
Bayan sun yi sallama ne ya kira Amna. Ta ce, “Honey sai yanzun ka tuna da ni ko?” Ya ce, “Kiyi hakuri honey, ban samu sukuni ba. Kina lafiya ke da duk mutanenki ko?”
Ta ce, “Duk muna lafiya. Yaushe zan gan ka ke nan?” Ya ce, “Ai sai su Hajiya sun gama wannan bikin al’adar tasu, kin san wai ba dama in ganku sai an yi budar kai.” itaka Ta ce, “Yau ne za’ayi ko?” Ya ce, “Eh, ba ki
bukatar komai ko?” Ta ce, “Hajiya tasa an yi mana
komai.” Ya ce, “Shi kenan sai mun hadu?”
Ta ce, “Eh, amma kana tunawa da ni kuwa?” Ya
ce, “Haba honey, ko yaushe kina nan a raina.” Bayan sun yi sallama ya mike ya fita a ďakin, ya nufi gurin abokansa.
Su Hadiza Yayar Salma kuwa jiki babu kwari suka isa gida, sai dai Hadizar ta hana a fadawa Innar don kada ta sake shiga damuwa.
Sun ci gaba da shirin kai kaya a washegari kenan. Su ba su san ma za’a yi wani biki a gidan surukanta ba, sai da aka dauke ta. Sun za ci Kaduna za a kamar yanda ya ce musu lokacin da ya basu makullin gidan nata.
Sun kammala siyan duk abin da suke ganin muhimmi ne a kai mata. gado da kujerunta mai zaman mutum uku, da guda
dai-dai, sun sai katifa da kayan kicin wanda ya sawwaka.
Sun siyo gara, Buhun shinkafa babba, da Taliya katon daya, sai dan karamin garin tuwo na Semovita. Sun hada da Mangyada da su maggi, sannan ta dan samu gudunmawa daga makota, ‘yan kofuna da dai dan abin da ba a rasa ba.
Gidan su Aliya kam tun ana sauran ‘yan kwanaki suka kai mata kaya, don haka gara za su kai mata a washegarin. Sun yi mata kowanne bugu guda biyu, nufinsu daya su kai gidan Amarya daya su kai ma surukanta tare da kwanukan da ake ba dawa bisa al’ada.
Badi’atu da sauran ‘yan uwa da suke tare da Nafisa tuni sun soma wanka suna sheka kwalliya tun bayan da suka karya.
Shahida ta miko ma Badi’atu waya wadda ta fito wanka tana fadin, “Gashi har an gama yin Decorations din ko’ina da za’a saka mutane.”
Ta amshi wayar tare da cewa, “Na manta ma ina mallakin wata wani kam.” Tana ganin Yaya Shatima ta zaro ido, tun da taga kiran ta tuna ajiyar da ya bata.
Ta daga tare da fadin “Na’am Yaya!” Ya ce, “Kin kai mata kuwa?” Ta ce, “Yanzun zan kara dubawa don bata tashi ba.” Ya ce, “To kije da wayarki, zan yi magana da ita.” Ta ce, “To.”
Ta fita taje kicin, duk babu wani abin kari. Ta shiga gurin Alhajinsu inda aka sauki su Amna. Su kam ga kayan karin nan sun ci naci sun bar na bari. Ta dauki Plate ta zuba dankalin Turawa soyayye
da kwai da naman kaji. Ta dauki wani kofi ta zuba ruwan shayi, ta dauki madara da sauran kayan tea ta dora kan wani tire. Sumayya kanwar Amna ta ce, “Ba ki karya ba Badi’atu?” Ta ce, “Wata bakuwa aka yi.”.
Ta aje can gurin kafar bene, sai da ta zo ta duba Hajiya suna can falonta da kawayenta suna tsara yanda za su gabatar da lamarin. Ta dawo da sauri ta dauka tayi sama.
Tana zuwa ta samu Salmar zaune ta dauki sauran naman jiya tana ci. Badi’atu ta kalle ta cikin tsananin tausayi, ganin yanda idanunta suka yi jajir, sannan
sun kumbura. Ta ce, “Ajiye wannan ki ci wannan.” Salma ta amsa tare da yin godiya. Badi’atu tayi masa flashing sai gashi ya kira. Ta ce, “Na kawo mata, gata ma.”
Salma ta amsa. Ya ce, “Salma!” Ta ce, “Na’am!” Ya ce, “Kin tashi?” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To ki ci abinci kiyi wanka.” Ta ce, “To, amma ba a zo min da kaya ba, tunda dama yau ne za su je min da kayan can Kaduna.”
Ya ce, “Zan je in anso miki, zan ba Badi’atu ta kawo miki.” Ta ce, “To.” Ya ce, “Duk abin da ki ke bukata ki fada mata.” Ta ce, “To.” Ta ba wa Badi’atu wayar. Ya ce ma Badi’atu don
Allah ta taimaka mata zai je ya kawo mata kayanta
da zata sa. Badi’atu ta ce, “Insha Allahu zata yi.”
Lokacin ya tafi gidan su Salma cikin sa’a dama suna son Auwal ya zo a kira shi batun motar da zata kai musu kaya Kaduna.
Yaya Hadiza ce ta fito da Umar yaje ya sanar da ita zuwan nasa. Suka gaisa, ya ce a bashi kayan da Salma zata saka. Yaya Hadiza ta ce, “To.” Sannan ta ce, “Dama
muna maganar motar kaya za’a tafi ayi mata jerene.Shatima ya ce, “To bari ya je zai aiko kaninshi Mustapha, ko ya kira Auwal ya amshi kudi sai a nemo mota don bai fito da katin shi na (A.T.M) ba.
Badi’atu bata fito daga dakin ba sai da taga Salma ta ci ta koshi ta shiga wanka. Ta dawo ta debi kayan kwalliyarta lokacin ta tambayi ina Hajiyarta? Aka ce mata tana wanka.
Ta ce, “Bari taje an aiketa in ta fito tana nemanta.” Can dakin ta koma inda ta samu ta fito. Ita ta zauna ta tsara ma Salma kwalliya, don haka kawai taji tana son Salman wai tana yi mata kama da wata Fatima kawarta Aminiyarta ce suna JS1 ta rasu. Salma ta ce, “Allah Sarki! Allah Ya jikanta.”
Ya kira layin Badi’atu, ta sauko ta amshi kayan. Leshi ne mara nauyi mai kalar makuba da ruwan madara, ta saka shi, tayi kyau sosai.
Badi’atu ta dauke ta hotuna kala-kala, ta ce “Zan nuna ma Yaya ne don yasan na cika alkawarin da na daukar masa.
Salma tayi ta godiya. Badi’atu ta ce, “To, anjima in za a yi budar kai amma za ki canza kaya?” Salma ta dubeta cikin muryar tausayi ta ce, “Ai ba da ni za’ayi.
Badi’a ta ce, “In ji wa? Kuma saboda me?” Salma ta ce “Hajiya ta ce ban da ni.” Badi’atu tayin shiru, don dama taji Hajiyar tana ta fadace-fadace.Mamakin halin da Hajiyar ta canza take yi, don
iyaka saninta da Hajiyarsu ba muguwa ba ce. Ta samu Shatima a can waje Gate yana waya da
Mustapha, wai in ya ciro kudin ya kai gidan su
Salma. Da ya gama ta dube shi da murmushi. “Yaya wai duk cikin su kafi son Salma din nan ne?” Ya ce. “Me yasa ki ka ce haka?” Ta ce, “Naga kafi damuwa da al’amarinta fiye da na sauran.”
Yayi murmushi, “Duk ba za ku gane ba ne. Kin gama abin da na sa ki?” Ta ce, “Eh, bari ma ka gani.” Ta ciro wayarta ta fito da hotunan Salma ta mika mishi.
Yana ta kallon su cikin mamaki. Ya ce, “Amma kin yi editing ko?” Ta ce, “Sam! Ban yi ba.” Ya ce, “Ashe “yar small din tawa kyakkyawa ce.” Ya mika mata wayarshi, “Ki tura min su duka yanzu.” Ta ce, “To.”
Tun sha biyu gidan ya soma dinkewa da manyan mata, don yau ne bikin Hajiyar karo na farko da zata aurar da danta, kuma zai auri mata uku, don ta ce su ta sani bata san ta hudun ba.
An tsara gurin zaman amaran guda uku sai gurin da ango zai zauna da abokansa guda biyu. Sai rumfuna wanda jama’a za su zauna.Tuni wadanda aka baiwa kwangilar abinci sun kawo tare da wadanda aka dauko haya don su raba abinci, su ne za su ba kowa har abin sha. Sun tsara budar kan za’a fara shi karfe daya, don haka aka ce kowacce Amarya ana son ta shirya kafin lokacin. stil
Hajiyar da kanta tasa aka kawo mai kwalliya. Amna a ka fara yi mawa, sannan Nafisa. Lokacin da ta zo gurin Aliya ta samu suna shawarar siyo mata audugar mata don taje alwala taga al’ada.
Sai da ta gyara jikinta bayan Aisha ta fita ta siyo mata sannan aka zauna zaman yi mata tata kwalliyar. Duk kayan da suka saka a lokacin Hajiyar ce ta bada aka dinka musu tun kafin zuwan ranar.
Duk da ba a auna su ba, doguwar rigar ta zauna
ma kowa har tana jan kasa, kowace da kalarta. Koda
yake sai da sauran suka zaɓa sannan aka kawo ma
Aliya.
Masu kidan ‘yan kasar Mali ne aka dauko, guri dai ya tsaru sosai. Mc abin magana ya soma fadin “A fito da Amare don ayi musu budar kai.”
Salma tana jiyowa tamkar ta fito kallo. Lokacin ne Badi’atu tazo dauko ma Ango wasu kayan shi da zai sa shi ma. Ta ce da Salma “Ki fito kiyi kallonki, don Hajiya tana fama da mutane ba za ta gan ki ba.”Ta ce, “In wani ya fada mata fa?” Ta ce, “Ai babu wanda ya sanki bare ya fada mata din, ni kaina ai sai da Yaya ya aiko ni sannan na ganki.” Haka tabi Badi’atu cikin fargaba. Da suka fito
harabar gurin shagalin bikin ta ce, ta shiga kujerun
tsakiyar gurin ta zauna. Ta shige ta saje da Jama’a.
Amna ce ta soma fitowa rigarta kalar bulu mai haske, an sha dogon takalmi, fuskarta rufe da wani mayafi da ke manne a jikin rigar.
‘Yan’uwanta ke yi mata jagora suna fesa mata abin kamshi har izuwa kujerarsu. Can sai ga Aliya itama, tata rigar koriya amma komansu iri daya.
Da suka zauna kuwa zai yi wuya ka gane wannan wace ce, wannan wacece a cikinsu. Nafisa ce karshen fitowa ita kuma tata kalar siminti, sun yi kyau amma ita da ta zauna kasan ita ce karamarsu.
Me abin magana ya ce, “Kai! Wannan Ango dangata ne, nan da shekara me zuwa ka cike ta hudu, duk shekara ka dinga kwasar jarirai guda hudu.” Aka sa dariya. Ya ce, “Yanzun ango muke jira, kafin ya iso ina ‘yan rawar nan su nishadantar da mu?”
Nan fa ‘yan Mali suka shiga rawarsu mai ban sha’awa. Salma daga inda take zaune tana jin wasu mata suna musu. Wata ta ce, “An ce fa matan guda budu ne.” dayar ta ce, “Surutun mutane ne, su ukune. Ya dai so yin ta hudun Hajiyarsa ta hana.” Salma a ranta ta ce, “Gani ni ce ta hudun.
Can Ango ya iso da gayyar abokai. Shatima ya yi matukar kyau cikin shaddar shi Gizna mai ruwan zuma. Hula da takalmi masu ruwan kasa kalar zaren Hula da aikin.
Salma har mikewa tayi tana kallonshi, ya birge ta sosai. Sai da ‘yan bayanta suka ce “Zauna mana, kin tare mana.” Sannan ta zauna tana sauraron yanda matan gurin ke koda haduwar Angon.
Shi kan shi mai abin maganar fadi ya ke, “Ga kasaitaccen Angon mu nan ya iso, kyakkyawan Ango ya iso sauran abokan suka je inda aka tanadar musu. Shi da guda biyu suka zauna a inda aka tanadar musu. Nan fa aka soma shirin budar kai, wata kawar
Hajiya aka kira ta bude taron da addu’a, sannan aka
bukaci Ango ya zo ya bude kan wadda ya zaba a
uwargida. Abokanshi suka rako shi, ya zo gabansu ya tsaya. Nan ya dabirce domin ya kasa gane Aliya. Ya gane Nafisa don bata kai su girma ba, ya dan yi shiru, ya
kuma tsura musu ido yana son gano Aliya. Da bai gane ba sai ya ce, “Aliya!” cikin sauri ta amsa, Ya ko sa hannu ya daga ‘mayafin fuskarta. Nan aka dauki tafi da guda. Aka ce danginta su zo su nuna cewa ita ‘yar dangi ce.
Nan fa dangi suka yi tsuru-tsuru tunda ba su san da wannan irin lamarin ba. Abin da ke hannun su suka zo suka zuba mata, ba ma sabbin kudi ba ne, mutane sai kunkunai suke yi.
Aka ce yazo ya bude ta biyu, ya zo ya bude Amna. Ita ma aka yi guda aka ce dangin ta su zo su fidda ta. Ruwan kudi suka shiga zazzage mata sabbi fil! Haka Nafisa.
Salma da ke kallon ikon Allah ta ce, “Allah na gode maka da kasa Hajiya ta ce kar in fito, da wa zai zo ya fidda ni?”
Daga nan sai aka ce Ango ya zo ya ba matanshi abin sha ko naci. ‘Yammata masu sanye da kaya iri daya su uku, su ne suka zo suka kawo wani dan tire. a rufe, daya da ‘yan kofuna guda uku, dayar kuma da hankici na share baki.
Ta bude dan tire din, nakiya ce guda uku, ya dauki daya ya ba Aliya ta gutsura, aka yi tafi gami da rangada guda.
Mai kofunan ta matso, ya dauka madarar shanu ce wadda ba a jima da tatsowa ba, ya kurba mata, sannan me hankici ta kawo ya dauka ya share mata. Duk su ukun hakan ya yi musu.
[8/16, 21:35] Ummi Tandama????: _
????️RANA DAYA BOOK 2????️