FITAR RANANOVELS

RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 17

RANA DAYA BOOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVEL | BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHIBY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI

Ta ce Ai da yake ma gashin naki ba shi da zuciya, ko an yi banza da shi sai yayi ta hauka

Salma ta ce Shi ko Yaya ma da na ce ina son “

kitso sai ya ce ya fi son gashin a haka, sai dai in ina son a gyara min in mishi magana Hadiza

“To shi kenan, kin ko fara zuwa

Makaranta?” Salma ta ce,

“Nasan ya na sane shi

yasa bana mishi zancan

Da za ta tafi, Salma ta ce “Gashi bani da kudi

sai dari biyun Yaya da ya ce in aje masa, bari dai

in debo miki biskit su Amira sa ke zuwa

Makaranta da shi.

Hadiza tace

“‘In kuma yazo yaga an diba fa?”

Salma ta ce, “Nawa ne ya sai min har da alawa, shi

baya cin irin su.

” Hadiza tayi dariya tar da fadin

“Yar gata

Ta saka hijabi da nufin raka Hadiza har bakin

titi. Hadiza ta ce “A’a babu ruwana, kin taba yin

rakiya ne?” Salma ta ce,

“Ban taba fita ko wajen

Gate ba, Allah ina son in fita

Suna cikin jayayya sai ga wata bakar mota.

Shatima ya fito wani abokin aikinsa ya kawo shi.

Ya fadada fara’arsa.

“Sannu da zuwa,

” Ta ce,

“Yauwa Alhaji.
Suka
gaisa. Ya ce

“Ba dai za ki tafi ba?”

Tace

“Wallahi zan tafi ne tun safe nazo.

” Ya ciro kudi a

aljihun wandonshi ya mika mata.

“Ga shi ki hau mota.

” Ta ce,

“Da ka bar shi.”

Yace

“A’a ki amsa, ni na ba ki.” Ta amsa tare da

godiya. Salma ta kalle shi, “Yaya zan dan rakata

titi.”

Ba tare da ya kalleta ba ya ce,

“A’a, ki koma

daga nan.

Ta tsaya cak! Ta mika ma Hadiza ledar

hannunta. Ta ce, “Ki ce ina gaida Inna, ki bata dari

biyar cikin kudin da ya ba ki.

.” Hadiza ta ce, “Ko

ba ki ce ba zan bata.

Ta koma daki ta same shi a cikin dakin bacci,

yana rataye suit din shi a jikin madubinta. Ya ce,

“Wato za ki fita ba izini ko?” Ta ce,

“Ban zaci

zaka yi fada ba. Yace

“To ko waye ya zo ban amince kiyi

rakiya gaba da Gate ba.

Ta ce,

“To Yaya, insha

Allahu.

” Nan ma ta dauko littafin rubutunta, shima

ta rubuta, har ya kalleta ya fito bandaki.

“Me ki ke yi da littafin?”

Ta ce, “Ina yin ‘yan

rubuce-rubucena ne yace

“Yana da kyau haka.

To me ki ka ba Hadiza din?”

•Ta kalle shi “Ai bani

da ko sisi, sai kudin ka dari biyun ka da ka ce in

aje maka.

Yace

“Kuma a dakin ba ki da abin bata?” Ta

girgiza kai tareda dan tabe baki,

“Me gare ni Yaya, na dai ba; Yaranta biskit dina, tunda shi ai

ka ce nawa ne ko?”,

Ya cc, “Eh.” Tace

“Ka ji abin da Ya Hadiza tace?” Ya tattaro hankalinga garè ta da tambayar.

“Me ta ce?”

Ta ce, “Wai in Rage siyan nama da

yawa sai in tara kudin, wai in sai kamar ,na dari uku nace sai na tambayeka in ka yarda

Yace to sauran kudin ayi me dasu? Wai in adana sai a siya min abinda bani dashi

Yace to ai ta baki shawara ne ni bani da matsala da haka in kina ra,ayin rage cin nama kina iya yin hakan tace na gode yaya•Yayi murmushi,

“Sarkin

godiya. Gobe za a kawo form na Makarantar, ki.

Ba ta san lokacin da ta buga tsalle ba har ta kai

inda ya ke ta kuma rungume shi, tana fadin

“Na

gode Yaya.

Yayi dariya,

“Ki samu nutsuwa in

fada miki.”

Ta durkusa a gabanshi,

“To Yaya na nutsu.”

Ya ce Makarantar a nan Unguwar take kusa da

titi, sannan maza ne da mata, in kin shiga ki kama

kanki bana son kiyi abota da wadanda ba za ki

karu ba, ki sa kai kiyi abin da ya kai ki.”

Salma ta ce Insha Allahu zan kiyaye.” Ya ce

“Ban ce musu ke matar aure ba ce, kin ga ke za ki
[8/19, 11:57] Ummi Tandama????: __
????️RANA DAYA BOOK 2 ????️

        CHAPTER 14

BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????

 Halima Abdullahi Access bank       sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427  idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son  tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427  zamuyi maku cikin sauki*

kare mutuncin auranki." Salma ta ce, "Na gode

• Yaya, Yaushe zan fara zuwa?"

Ya ce,

"Ina son nan da ranar Monday (Litinin)nake son ki soma zuwa insha Allah." Salma tayi ta godiya!

Ranar ko baccin kirki bata yi ba, ta tashi

tana ta kwatanta irin tafiyar da zata yi in zata Makaranta. Haka kuwa washegari sai gashi da form, da jaka, da takardu, da uniform kala biyu. Tamkar

* sallah Salma taji, ya ce

"Saura safa da takalmi.

" TaCe Yaya duk kasuwa kaje ka siyo?"

Ya ce

"A'a Makarantar suke badawa. Takalmi da safa ne suka fadì kalar da za a siya."

Sun je Makarantar an yi mata tambayoyi, in da suka gano tasan abubuwa sai dai bata jin Turanci.

Da za su sa ta SS1 sai suka ce sai dai ta maimaita JS2. 

Salma, ba ta damu ba, ita ko JS1 ne bata da matsala. Ranar Litinin kuwa randa Salma zata fara

zuwa Makaranta dama kwana tayi bata runtsa ba,gani take kafin gari ya waye za a tashi duniya.

Tun kiran farko ta farka ranar ba dakinta yake ba, tayi wanka ta zauna jiran ayi kiran shiga

*Masallaci, Ranar ko karin kumallo kasa yi tayi

Riga da siket ne, siket din mai fadi kadan ya Wuce gwiwa.

Amma suna saka wando baki irin damammen nan, sannan safarsu tana zuwa Kwauri daidai in da wandon ya tsaya, sai riga fara da farin karamin hijabi, siket din kuma ruwan hoda.

Hakan yasa kayan suka yi mata matukar kyau.

Ta taje gashinta ta kama shi. Ta kalli madubi, sai

ta tuna wata Sajida a kusa da gidansu can Zariya,

suma haka suke saka kayan Makaranta, ita da

kannenta su hau keke kowa da nashi.

Ita dai suna bata sha'awa tun da, amma Sajidar

sai take musu dariya in taga sun fito suma za su

tafi, sai take ce musu Almajiran Gwamnati.

Tayi juyi a fili ta ce, "Sajida dama za ki ganni

yau, nima Salma na hau layin dalibai masu neman ilimi

Ta dibi biskit ta zuba a Jakar ta zauna jiran

Yayanta ya shigo. Murmushi ya saki lokacin da

suka hada ido, tayi matukar birge shi a cikin kayan Makarantar.

Yana tsaye bakin Rofar ya zuba hannayenshi

biyu cikin aljihu. Ta durkusa ta gaishe shi ya amsa

tare da fadin "'Muje ko baby.

» Ya fadì haka ne don tayi masa kama da baby

Ta rataya jakarta a gadon baya, ta dauki

makullin dakin. Ya miko mata kudin namanta.

sannan ya bata wata dari biyar din yace Ki hau

Mashin in an tashi, canjin kuma kiyi amfani da shi.

Ta ce,

"Yaya na dauki biskit ba sai nayi amfani da kudi ba." Yace, "Ki bar shi." Suka fito, ta mika mishi makullin,

"Kulle min Yaya.

" Ya amsa yana

Nuna mata yanda zata yi, domin ba kullum ne yake nan ba.Ta dube shi

"Bari na yi ma Anty Aliya sallama.

" Ya ce

"Yi sauri min ti daya da rabi.

Dan gudu ta kwasa, tare da tsalle ya girgiza kai

*Yarinyar nan da shirme bare taji ta a cikin

uniform me saka dalibi Kiriniya.

Ta samu Aliya tsaye a kusa da window tana

leke. Salma ta rusna ta gaida Aliya, sannan ta ce

sai ta dawo. Bata jira amsawarta ba ta juya don kar

ta shiga lokacin da Shatima ya bata.

Da dan tsallanta ta koma gurinshi.

Ya tada mota zata hau baya, ya ce "Kina son ki nuna ma

"Yan Makarantarku ni Direbanki ne ko?"

Tayi dariya tare da komawa gaba. Da suka zo fita, ta mika ma Maigadi kudin nama. Ta ce, *Yau na dari biyar ni ke so

Ya ce

"To."

Shatima ya kalleta

"Za'a soma adana kudin ne?" Ta ce Ai na dari uku ni ke siya duk kwanakin nan, yau da kana dakina ne zan kara.

Ya cE

"Au! Yau ina dakin baby ne ko?"

Tayi dariya,

"Kullum kana dakina Yaya sai ka manta,

" Ya CE

"Lokaci zai zo da zan tuna.

" Ta ce,

"Allah ya kai mu."

Ofishin Shugaban Makarantar •suka je, daga

nan aka nuna ma Salma aji. Ta daga mishi hannu

tare da fadin Bye-bye Yaya.

" Cikin murmushi yace

"Bye baby.

A cikin ajin an nuna ta a matsayin sabuwar

daliba, aka nemi da ta fadì sunanta. Ta mike ta ce,

"Sunana Ummu Salma A. Bashir.

Suka yi mata

sannu da zuwa. Malamin ya nuna mata wata yarinya.

"Ga waccan itama sunanta Ummu Salma, kije

kusa da ita na hada ku kawance.Cikin sakin

fuska ta kalli Salma,

"Zo mu zauna." Cikin turanci

tayi mata maganar.

Salma ta kan ji amma bata iya maidawa ba.

Umma Salma Sadi Dankasa ita ce Kawar da aka

yi wa Salma, tana da kokari ga salo da iya yi,

rawar kai kuwa ba a magana.

Suna shiga falo Amna ta ce, "Ko'ina ya yi kura

me aikin ta soma aikin shara.

Ya ce mata "Bari ya

duba Nafisa itama cikin ne.

Amna ta tabe baki

bata ce komai ba.

Ya samu Nafisa kwance bata jima da dawowa

dega amai ba. ya ce,

"Aman nan yayi yawa, ko dai

asibiti zamu je?" Ta ce,

"Ba za ta iya tashi ba.

" Ya dauki wayarshi, ya kira layin Likita ya fada mishi

halin da Nafisa take ciki.

Ya ce,

"Ya zo asibitinshi da mota ya dauki

Nurse ta saka mata ruwa, shine kawai abin da za'a

iya yi mata.

Ya CE

"To."

Haka ya dauki mota

yaje ya kawo Nurse ta zo da komai ta hada ma Nafisa ruwa.

Aliya da ke leke ta window ta ji haushin hakan,

dama tana cike da takaicin yanda yake ririta

Nafisar, ga Amna ma ta dawo. Ta dauki wayarta ta
tura mishi sakon korafi.

'Haba my love, ban zaci za ka yi min haka ba,

gani a gida sai ka dauko Nurse daga waje?

Gaskiya ban ji dadin haka ba.

Sakon na shigowa ya duba, guntun murmushi

yayi bai damu ba yasan Aliya tana da fahimta, da

ya yi mata bayani zata, fahimce shi.

Sai da Nafisa ta samu bacci sannan ya kira

Mama a waya yace Don Allah Hamida ko Momi

wani ya zo saboda dare, yanzun haka ruwa ake yiwa Nafisa kari. 
Mama tace

"Jikin ne har yanzun?" Ya ce,

"Ciki ne da ita, sai wuya take sha, amai yayi yawa.

Mama cikin murna ta ce,

"Allah Ya bata

lafiya. Hamida sai ta zo tunda itace ba ta zuwa

Makaranta sun gama jarabawar fita.Yayi godiya

suka yi sallama. Ya tafi dakin Aliya don fahimtar da ita.

Tam! Ya same tacikin fushi, ya ce

"Haba

Aliya, keda ni ke gain kin fi su hankali, kuma za

ki fisu bani hadin kai?"

Tace

"Ai ni gani nayi ilimina bai yi min

amfani ba, in ba zan taimaki mijina da kuma

abokan zamana ba.

Ya kama hannunta

"Na

fahimce ki my love, amma kin san halinku na

mata, nasan ba za ta yarda ki sa mata ba ne.

Aliya ta ce, "To yanzun haka zaka sa mana ido

muna matanka babu taimako a tsakaninmu, babu

jituwa, ba za mu iya cin abinci kwano daya ba,

gaisuwa ma ta gagara tsakaninmu, ko dan su suna

jin su 'ya' yan wasu ne? Amma ni da Salma ai muna gaisawa, duk da

sakarcin kuruciya irin na Salma ta fi min su tunda

za'a gaisa. Ka iya tunawa fa ko makocinka ne

Musulunci ya gindaya sharadin makotaka

tsakaninku, bare matanka.

Wannan fa aiki ne babba a kanka, domin

kiwonmu Allah Ya baka, gashi za'a soma haihuwa

a gidan tun yanzun gara kayi digin hada kan yaranka.

Ya janyo ta zuwa jikinshi,

"Ina sonki sosai

gurin sa ni a hanya, ki taimaka min gurin hadin kan iyalina, ke ce ki ka fahimce ni.

" Aliya ta dan ji dadi, yanda ya nuna mata.

Salma kam bata da wata matsala, babu kowa da komai a gabanta sai karatunta, matsalarta daya in
an bata assignment bata samun me taimaka mata
in ta z0 gida, sai in ta koma Makaranta Salma

Dakanta ta taimaka mata.

Wannan Juma'ar an basu me wuya, gashi in

sun je ranar Monday babu lokaci bare Salma ta

taimaka mata don sai da ta bata shawara kan cewa

Yayan da ke sauke ki ya dinga taimaka miki.

Tace

"Ba shi da lokaci ne amma zata mishì

magana.Salma ta ce,

"To ki fada a dinga biya miki lesson, ko a nemo miki Malamin lesson agida.

" Salma tace

"Bari zata yi masa magana.

Cikin Nafisa me laulayi ne sosai, da tsarabar zan ci kaza, ba zan ci kaza ba. Domin wani abin ma sai an siyo shi tacì sai kuma ta sheka amai. Duk ta rame, ta kode abin tausayi kullum cikin

Karin ruwa. Yanzun dole ta yarda Aliya tana saka mata ruwa, tun lokacin da Aliya ta dage a kan sai sun je ta duba Nafisar, shi kuma yana gudun kada 
Nafisar ta mata wulakanci ta ce ita dai suje.

Da yake Nafisar ta kanta take yi sai bata yi wata masifa ba. Aliyar ta gyara mata ruwa ta ce, ta gode. Shatima ya ji dadì sosai.

Tun daga ranar kullum sai ta-je gaida Nafisa, bare in ta lura Shatima ya shiga dakin. Amna kuwa ko ta shiga ta kan samu tana bacci, to da yake ba don Allah take zuwa ba, bata komawa sai kuma gobe in yana gida.

Shatima zuwa yanzun ya dauki Aliya ya sata a wani matsayi mai girma. Har yana ganin ta kai yayi kowace shawara da ita, kuma yana ganin zata iya zama wakiliyarshi a wasu al'amura na gidanshi.

Don tana da tsoron Allah, ga tsayawa a kan gaskiya da rikon amana.
[8/19, 12:22] Ummi Tandama????: ________
*????️RANA DAYA BOOK 2 ????️*


          CHAPTER 15



 *BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number????????*

ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925“`

Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama????????????????ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana

Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki

Nafisa ta tashi zaune, ta ce Hamida ta saka mata pillow zata jingina. Ta ce “Hamida yanzun Karfe nawa?” Ta ce,

“Tara na dare.Nafisa ta CE “Tabdi! Kin san wai me nike son ci?”

Hamida ta yatsina baki ta ce, “A’a

Ta ce

“Zogala! Ji wata fitina, ni da bai dame ni ba

Hamida ta ce

“Ni yanzun ina za a samu wani zogala?” Nafisa ta ce,

“Kira min Ya Shatima.”

Yana dakin Aliya daidai lokacin da wayar tayi ringing, ya zo daidai da lokacin da Salma tayi sallama a dakin na Aliya, hannunta dauke da littafin ta wanda za”a koya mata,

Aliya ta amsa, sannan Shatima ya kalleta bayan ya dauki wayar yana duba suman. Zumbur! Ya mike tare da daga wayar ya ce, “Nafisa!”

Hamida ta ce,”Ni ce, ta ce kazo* Ya ce,

“To gani nan zuwa.Ya kalli Salma

“Ya aka yi?”

Tace,

“Yaya dama assignment ne za a nuna mini.”

Ya kalli Aliya,

“Duba mata don Allah, bari in je gurin Nafisa in ji

Aliya tayi’yar dariyar yake tace

“Sai ka dawo, don Allah ka ce ina yi mata sannu.

Yana fita Aliya ta kalli Salma kallon sama da kasa irin kallon wulakanci da raini, ta ce “Aka yi sati da Lahadi duk ba ki tuna da assignment ba sai yanzun da ki ka ganshi a nan dakin? To bari in ja miki kunne, duk ranar da yake dakina na haramta miki zuwa.

Salma ta ce, “Anty don Allah kiyi hakuri, ina ta tunanin yanda zan ma Yaya magana ne,

” Aliya ta fizgi takardar tana dubawa. Salma ta ce

” Anty bari ki ga yanda aka ce….

Aliya ta katseta da cewa,

“Da Allah ni yi min shiru, ke ce za ki nuna min, tun kafin a haifi uwar me alli Balbela take da farinta.”

Salma ta ce,

“Me ki ka ce?” Aliya ta ce,

“Tun kina^yar mitsitsiyarki ni ke zuwa boko, kuma muke rubuta maths.
Salma ta ce, “Yi hakuri.”

.” Don ta lura Aliyar tayi maganar cikin fushi ne. bata koya mata ba, saidai ta rubuta ta bata tare da cewa gashi nan ni bani da lokacin yi miki wani nune-nune.

Salma taje daki tana dubawa cikin kokwanto,tana tunanin gaskiya da kyar in haka ne, amma zata je da shi Makaranta ta nuna ma Salma Dankasa

Shatima ya shigo,

“Ina Salman?” Ta ce,

“Nayi mata ta wuce, yarinyar nan Allah Yasa dai tayi karatu, naga dan abin da ta kasa ganewa,ga takardarta duk ziro

Ya ce,

“To don Allah ki ke taimaka mata, sai a
hankali.Aliya ta ce,

“Har Lesson na ce zan ke yi mata.” Ya ce, “To ai ko na gode. Yanzu ina zan samu zogala?” Ta ce, “Wake so?” Yace”Nafisa.Ce.

Tace

“Gashi dare ya yi. Amma ka tambayi

Maigadi, in za’a samu danye sai a dafa mata yanzun ayi mata kwado.

Ya ce,

“Haka ne.

Maigadi ya ce, “Can makotan suna da shi

Sai gashi an samu, nan da nan Aliya ta zage ta dafa, ta cE

“Sai kuma in da za a samu kuli-kuli

Nan ma Maigadin aka sake tuntuba. Shi ya bazu cikin unguwa sai kusan sha daya saura ya dawo. Kura-Kura aka samo. Aliya dai aka zage aka daka, ta kwadanta mata. Nan ya dauka ya kai mata. Tasa a gaba kuwa tayi ta ci, cikin ikon Allah kuma sai gashi bata yi amai ba,

Salma tana zuwa Makaranta, ta nuna ma Salma Dankasa, Salma ta ce

“Wa ya yi miki?”

Tace *Matar Yayana

Salma ta ce,

“To ba daidai bane.

Ta dauko littafinta ta nuna mata.

*Kin ga nIfa.

  • Salma mamaki ya cikata, amma ta share tace “Bari ta sake kwalewa sai tayi kafin Malaminsu ya iso.”

Amna cikin bacci taji karar wayar Shatima. Ta kalle shi yana ta bacci, da alamu yau ya gaji sosai,don sun je Abuja ne sai ma goma ya shigo gidan.

Ta kai hannu ta shafa fuskarshi,

“Honey ana kiran wayarka tun dazu.” Ya bude ido da kyar, taCe

“Ka gaji ko?” Ya ce,

“Na gaji sosai.”

Yana daukar wayar daidai lokacin kiran ya tsinke.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button