RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 17
RANA DAYA BOOOK 2 COMPLETE HAUSA NOVEL | BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHIBY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI

Yana dubawa yaga sau tara ana kira. “Nafisa!”
ya furta da karfi tare da mikewa tamkar bai taba bacci ba. Amna ta dube shi, “Wai ina za ka?” Yace,
“Nafisa, ina zaton jikin ne.”
Amna ta sakko itama bata yi mishi magana ba,illa dai taje ta murda makullin kofa ta cire key din
tare da fadin, “Ba za ka fita ba. Na gaji da irin wannan abun, don ciki bai fi ciki ba.
Saboda salo bata tashi kiranka sai ranar da ka ke dakina? Sau biyu tana yi min haka, ba zan bari tayi na uku ba, tunda naga abin nata yana neman ya zarme.
Shatima ya ce, “Haba Honey, kin san fa cikinta ba irin naki ba ne.
Ta ce, cikin mamaki,
“Au!
Dama akwai wani ciki na musamman ne wanda kayi mata shi ni baka yi min ba?” Ya ce “Ba haka nake nufi ba, nata cikin me yawan laulayi ne. Don Shatima ya kira. Hamida ta ce,
“Tun dazun yake kira.” Aliya ta ce “Bar shi kar ki daga har sai ya fito, in yana dakin wannan ‘yar gwal din ba ya iya fitowa, yanzu dubi jikin baiwar Allahn nan amma ya wofintar da ita.Hamida ta ce
“Allah nima abin ya bani haushi,
na kira shi ya fi sau ishirin amma bai ko daga ba
Da ya daga ya ce min yana zuwa shine fa shiru Aliya ta ce,
“Sai ga shi ya kira ni wai inzo
Hamida ta cE
“Ai mun gode, Allah ya saka dabalkairi. Ai har Mamanmu na fada mata irin taimakon da ki ke mana.Aliya ta ce,
“Ai yi wa kai ne.
” Sai da aka kira sallar Asubahi sannan ta koma dakinta.
Shi ko Shatima zama ya yi a kan durowar gefen gado, yana ta kiran layin Aliya, ita kuma ta baro ta can dakinta domin da ta Nafisa ya yi ta kira yana tambayar Hamida ko Aliya tazo? Tana fada masa cewa bata z0 ba.
Bayan yayì sallah ya ce “To yanzun sai ki bude ni in dubo ta ko?”
Ta Ce
‘”Ai ba yanzun ka ke zuwa ba.
Ya cE
“To yanzun kuma zamu iya samun matsala tunda gari ya waye
Ta ce,
“Mu samu mana, dama nasan ba zaka kula dani ba kaje ka rabo ni da gidanmu ina can cikin tattali
kaje ka dauko ni.”
Ya ce, “Kin raina kulawar da nake ba ki? To kifada min abin da ki ke son in ke miki don ki tabbatar da ina kula da ke
” Ya fada ranshi a bace.
Ta ce
“Ga shi ka kwana zaune kana dakina
zuciyarka na gurin wata.”
Ta ce, “Yiwa kai ne dai,kuma bana fata kema wata rana in haka ta faru zaki ji dadì in ta hana ni fitowa in wofintar da ke?”
Ta ce”Ni dai ba zan bude ba, dama ka shiga wanka in ba haka ba zaka yi lattin zuwa office.”
Ganin da gaske ba za ta bude ba, ya bi shawarar ta ya shiga wanka. Kan ya fito ta bude sai ya fita zuwa dakinsa ya hau shiri.
Bai ko kalli karin da Ladi Mai aiki ta hada mishi ba, ya nufi fita. Kofar a damke take, ya waigo ta fito tana tsaye a falon. Ta ce,
“Ga abin karinka.
” Ya girgiza kai, “Bana jin yunwa.
Ta ce,
‘”Ai ko ba za ka dakin wata ka karya ba.
Ta soma hada mishi shayi, Har gurin Kofar ta
Zota bashi. Ya amsa tare da fadin “In da ace za ki ke hada min ko shayin ne a duk ranar da nike dakin ki da na yi tasa miki albarka Ya kai
Karshen maganar tare da kurbar shayin
Da sauri ya watso shi domin suga ya ji har
cikin kwakwalwar kanshi. Ya mika mata shayin
“Ga abin ki, bude ni.” Ta kalli agogo, duk abinka sai shida ta cika,
Ya ce,
“Amna har yanzun ina mamakin ki sosai, ashe kin iya mugunta har haka?”
‘ Ta ce,
Na daina bari ana raina min wayo.”
Ya jingina da bango,
“Shidar dai saura minti hudu.
Ta ce,Inma minti daya ne sai ya cika.”
Ya samu Nafisa a yan da take, ya kira Likita ya ce zai kawo ta asibiti don fa jikinta ya yi laushi Likitan yace
“Ko ka kawo ta babu abin da zamu ¡ya mata da ya wuce wannan ruwan. Amma zan
fita zuwa asibiti, ka fito bakin titi in same ka sai
muje in ga.jikin.Haka kuwa Shatima ya fita ya yi jiran kusan
minti biyar kafin Likitan ya iso. Shi kanshi Likitan
ya tausaya ma Nafisa, ya ba da wata allura ta
tsaida amai, ya ce ayi mata a gani. Amma ciki irin
wannan Kila sai ta kai wata biyar zata samu dan Salma tana ta jiran Shatima har takwas ta gota
Ta fito taje dakin Aliya nemanshi. Aliya ta ce an fada miki nan yake?”Salma ta ce,
“Ni wallahi yanzun bana tuna in da yake.”
Ta ce,
“Yana dakin Amna.
” Har zata wuce sai
taga sun fito da Likita. Ta rusuna ta gaida su,sannan ta ce.
“Yaya mun yi latti.Ya kalli agogon
hannunsa. “Haka ne, ya ba ki tafi ba? Nafisa ce ba lafiya ban san lokaci ya tafi haka ba.
Ta ce,
“Anty ba lafiya, bari in dubata.
Sun gaisa da Hamida, sannan tayi wa Nafisar sannu.
Ranar latti taje Makaranta, sai da ya roka aka bude
mata don har sun ce ta koma.
**
Wata ranar Litinin misalin Rarfe biyu da minti bakwai. Salma ta sauka daga kan Mashin a bakin
Gate din gidansu. Ta ba mai mashin kudin sai taga bakuwar mota zata shiga gidan.
Maigadi yazo yana tambayar Direban gurin wa suka z0? Salma ta kalli Direban, kamar ta taba ganinshi a wani guri. Sun yi kama da Shatima kadan.
Taji lokacin daga bayan motar an ce,
“Uwar Maigidan ce
Gaban Salma ya fadi, domin ko a
ina taji muryar Hajiyar Shatima ba za ta manta ba.
[8/19, 18:44] Ummi Tandama????: _
????️RANA DAYA BOOK 2????️
CHAPTER 16 Karshen book 2
BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI
Ta nufi cikin gidan gaba daya jiki a sanyaye,ta kasa bude kofarta,tabi motar da kallo har lokacin da taga motar ta tsaya daga cikin jerin motocin Amna da Shatima.
Ta bude kofarta ta shige,kasa cire kayan jikin ta tayi na makarantar haka kuma ta kasa dora girki,sai da tayi ta maza ta kunna risho ta dora tafasasshen nama.
Lokacin da su Hajiya suka shiga gurin Nafisa tana wanka,Hameeda tayiwa Mama da Hajiya oyoyo Aliya ta leko taga bakin Nafisa ne Dan haka sai ta yafa mayafi taje ta nufi wajen Nafisa da sigar duba jiki,tana shiga taga su Hajiya gabanta saida ya fadi tasan Hajiya ba kalar wasa bace, amma duk da haka saita cije ta zube ta kwashi gaisuwa a gabansu tana gaishe su yanda kasan zatayi masu sujada saboda girmamawa,Hameeda ne ta ajiye masu ruwa da lemu Aliya tace” Ya jikin Nafisa yau dai jiki da sauki? Hameeda tace “to gata nan ciki tana wanka”.
Cikin kissa tace “Masha Allah naji dadi sosai,tasha magungunan ta kuwa?”.
“Kinsan kuwa sai kinzo take sha,domin nidai nayi nayi da ita takisha”
Aliya tace “to bari ta fito inna lallasheta nasan zatasha haka za’ayi tayi hakuri da ita bansan inda zan samu tsakin nan bane bare ayimata abinda takeso amma ga rama can maigadi ya siyo mana”.
Duk zubar da takeyi su Hajiya suna jin ta kuma sun yaba da maganganun ta musamman ma mahaifiyar Nafisa dan ance me da Wawa,Mama tace “Allah sarki kina dawainiya da Yarinyar nan Kullum Hameeda tana fadaman duk abinda ke faruwa har dare kina zuwa ki dubata.”
Hajiya tace “haka akeso aishi zaman aure dama zaman tare haka akeson babba ya kasance,ita Yar’uwar takufa?
Aliya tace”Amna tana gurinta itama da sauki domin bacci takeyi,bari dai induba ta inaga yanzu ta tashi,Mama tace”Allah sarki kina dawainiya da wannan kiyi dawainiya da wancan kiyi da wannan Allah ya yi maki albarka.
Aliya ta amsa da”ameen” ta fita cikin jin dadi ta nufi shashin Amna domin dai burin ta kawai ta shiga ne gurin kowa taga yadda yake,hakan ne zai bata damar kunna wutar da take bukata a wannan gida,ta samu Amna a zaune tana kallon T.v mai aikin ta kuma tana bare mata kwai a gefe akan filet.
Tace “sannu da hutawa”
Kallo daya Amna tayi mata,sannan tace”yauwa sannunta” ta maida kanta gurin T.v.
Aliya tace “Hajiyan Shatima ne tazo tana dakin Nafisa tana bukatar ki,tace inzo inkira ki.”