
Kujerun sun yi tsurut! A falon saboda girmansa, ga kujeru uku rak! Ta shiga dakin gadon yafi kyau. Sauran dakunan dai ba komai, sai dan tarkacen da aka sa mata.
Kicin kuwa shima a rame. Amma dadi ya cika zuciyar Salma, tana ganin kamar babu macen da ta kai ta sa’a a duniya, wai nan gidanta ne.
Kafin lokacin zuwa Dinner duk Amaran suna
cikin shiri, domin Ango da kansa ya kira kowace ya
ce ta zama cikin shi. Salma ce dai da bata da waya ya kira Badi’atu ya ce ta shiryata da kyau kafin karfe tara.
Ya zaci Amna zata yi masa gaddama tunda ta ce, “in dai ‘yan’uwanta suna nan sai ya ji ta ce za su shirya da wuri.
Salma tayi matukar kyau cikin riga da siket na
pink din material. Kayan sun kama ta tsam! Duk da
ba ta da kiba ko kadan, ‘yar singila. Badi’atu ta daura mata dankwali, sai tayi matukar kyau, tana ta kallon kanta a madubi. Mota daya aka so a dauke su, amma Amna ta ce a’a ita tana da motarta.
Nafisa ta ce ba za ta zauna da kowa ba. Shatima ya kira Aliya a waya, ya ce za a dauko su da Salma ta ce ‘To.”
Shahararren Hotel ne in da za’ayi Dinner. Hall din kuma mai kyau da tsari, ba’a bari kowace Amarya ta shiga ba, sai da suka zo su duka.
Fuskar Nafisa tam babu fara’a, Amna kuwa zuciyarta cike da tambayar wannan wacece a cikinsu? A tare suka fito, shi ne a gaba sai Amna da . Aliya, Nafisa da Salma na biye da su, kowace da kalar shigarta.
Kujerar su biyar aka zagaye tebur din da aka jere musu abin sha da tsotsa a kai. Can gefe ga dogon cake wanda aka yi surar mata guda hudu a jiki da namiji guda daya a tsakiyarsu.
Bai zauna ba sai da yaga duk sun zauna, sannan ya fara nazarin inda zai tsoma nashi duwawun. Ya dauki kujerar shi ya sa ta tsakiyar Nafisa da Salma, sannan ya zauna. Amna da Aliya suka kalle shi, sai ya daga ma
Amna gira, Aliya kuma ya kashe mata ido daya.
Sannan ya ce, “Hasken fitila yana kashe min idone?”
Aliya tayi dan murmushi. Amna ta dan saki fuska, sai dai shi ba don haka,,,,,,ba, yana gudun kar Amna ta tambaye shi wace ce Salma, sannan kuma zai ke kallon fuskar Nafisa wadda tayi murtuk da rai.
Ma su kidan turanci ne irin wakar nan da ake yi cikin nutsuwa da sanyaya rai. Tun daga bude taro da addu’a har zuwa jawabin maraba da baki duk abokanshi ne suka yi.
Abokai da ‘yan uwa suna ta zuwa suna daukar hoto da su. Daga nan aka zo batun yanka cake, duk suka je gaban cake din suka tsaya. Mai abin magana ya ce, “Wannan dangatan
Ango ne, ga shi ga kyawawan matanshi. Yanzu za su
saka hannu su duka don su yanka cake din su.”
Duk suka sa hannu, Salma tsawonta bai kai ba don dogo ne. ya ce da Nafisa “Dan koma in da Salma take.” Salma ta dawo kusa da shi. Ta kara daure fuska, sannan ta koma. Da zata koma ta zauna nema, sai dai tayi ta maza ta cije.
Duk da haka karshen wukar hannunta ya taba.
Suka yanka ana yi musu tafi tare da murna. Me abin
magana ya ce, “Yanzun Ango zai yanka cake ya ba kowacce daya-bayan-daya. Sannan suma su ba shi, yanzun zamu ga wadanne irin mata ya samu.” Shatima ya yanko ya soma baiwa Aliya, sannan ita ma ta amsa ta ba shi tare da risnawa, aka tafa. Me abin magana ya ce, “Uwargida mun gano cewa me
ladabi ce, saura me bin uwargida.”
Amnah kuwa daya Ya yanko zai bata sai ta amsa ta sa a bakinta, sannan ta kamo fuskarshi da hannuwanta biyu, ya gutsira a bakinta. Nan tafi da ihu ya cika gurin.
Mai abin magana yana fadin wannan ta soyayya ce. Nafisa kuwa bayan ya bata da zata ba shi, har da hawaye don kishi.
Me abin magana ya ce, “Wannan kuwa tana da tsoron Allah. Yanzu sai ‘yar autar Amare.”
Salma ta girgiza kai cikin yanayi na shagwaba, tare da fadin “Yaya ba zan iya ba.” Ya rusuno da kunnansa daidai bakinta “Me ki ka ce?”
Ta ce, “Tsawona ba zai kai ba.” Ya ce, “Zan taimaka miki.” Ta matso ta dan yanki kasan, ta kalle shi a zatonta zai durkuso ne tasa mishi, sai kurum taji caf! Yayi sama da ita, ya rike kugunta.
Ta kalmashe kafafunta tamkar masu rawar
turanci, sannan ta saka mishi a baki. Gurin ya dauki
sowa. Maimakon ya dire ta sai kurum ya shiga juyi
da ita. Guri kuwa ya dauki ihu da sowa.
Sannan ya sauke ta, kowa ya koma mazauninshi, aka shiga ci da sha. Ba a tashi ba sai sha biyu da mintuna.
Tun da aka dawo daga Dinner Salma ke zaune a barandarta, ga makulli a hannunta amma bata iya bude kofar ba, don tun kafin su Yaya Hadiza su tafi suka kulle suka bata makullin tasa a jaka.
[8/16, 21:45] Ummi Tandama????: _