
Tamkar Shatima ya sani Amna shawarma kadai ta ci sai madara. Nafisa ma kadan ta ci da alamu ita ba mai cin abinci ba ce. Duk da har da kishi da suka gama, ya ce su koma kan kujeru yana da magana da su.
Ya ce, “wa zai bude musu da addu’a.” Salma ta cafke, don sun saba yin addu’a in anje gidan gaisuwa ko taya mura daga Islamiyarsu. Sai dai shi ne ya karasa addu’ar da fatan Allah Ya basu zama lafiya, ya hada kansu.
Ya ce, To yana son sanar da su kamar yanda suka sani Aliya ce uwargida don ta dan girme su. Yana son su bata girmanta. Ita kuma yaja hankalinta da cewa tayi musu adalci, sannan ya ce dukkansu ga amanar Salma, yarinya ce kankanuwa yana son in tayi ba daidai ba su sa ta a hanya.
Ita kuma ya ce ta bi kowa sau-da-kafa. Ya bukaci jin ta bakinsu. Aliya.ta ce, “Insha Allahu zata yi fiye da yanda yake so.” Amna ta lumshe ido cikin isa ta ce, “Zan kula.” Nafisa ta ce, “Naji, amma da ka ce ga amantar,wannam yarinyar shi ne ban dauka ba, don ba a rainon kishiya ko jaririya ce.
Salma dai burinta a gama maganar ta kalli cikin dakunan gidannan, don haka da ya ce Salma ba ki ce komai ba? Ta ce, “Ni Yaya duk yanda ku ke so wallahi haka zan yi.” Kafin yayi magana ta ce, “An gama mu kalli dakunan?”
Tausayin Salma ya tsirga mishi, yarinyar babu komai a cikin zuciyarta. Daga shi har matan ba su gabanta. Ya ce “Za ku gani ki bari a gama magana.” Ta ce, “To.”
Ya ce, “Sai batun kwana, ni dai in sona ne in yi kwana daya a dakin kowaccen ku, amma ku ya ku ka gani?” Aliya ta ce, “Yayi.” Amna ma ta ce “Yayi.” Nafisa ta ce, “Ai dama sai hakan, don in ya wuce haka sai bayan wane lokaci za ka ga mijinka?”
Ya ce, “Ke wai fadin to ne matsala?” Ya dubi Aliya, “Yau nan ni ke kenan?” Ta ce, “Haka ne. Suna tashi Salma ta ce “Zaku tafi ba mu gani ba.` Nafisa ta ce, “Ke bakauyiya sai kiyi ta kallo.”
Aliya dai yi tayi kamar an kira wayarta, tasa a kunne ta fita tana fadin “Hello! Hello!! Salma kuwa sai da ta leka ko’ina, Shatima yayi mata jagora. Sai fadi take “Aljannar duniya!”
Suka dawo falo inda Amna ta harde a kan kujera ta ce, “Anty guri ya yi kyau Allah ya kara
arziki.” Amna tayi dan murmushi, sannan ta ce “Amin.” Suna fitowa Salma ta ce “Tsorona daya fa Yaya zan kwana ni daya yau, in aka dauke wuta zan firgita.” Ya ce, “Ba za a dauke ba in Allah Ya yarda, to a haske ki ke kwanciya?” Ta ce, “Sosai ma. Jiya sun dauke wuta Allah yasa Anty Badi’atu tana nan, na kankameta.”
Ya ce, “Dama ke sarkin tsoro ce?” Ta ce, “Kai, Allah ko da ranar nan tsoro nayi ta ji.” Ya ce, “Muje in raka ki, kiyi addu’ar bacci babu abin da zai same ki.”
Bayan ya sa ta ta rufe kofa, ya nufi dakin Aliya yayi wanka yasha sabbin kaya, ya dauki makullin mota ya fita.
Kajin Amarci ya siyo da madara mai sanyi, da
sauran kayan zaki, don ya lura Amna tana son
shan zaki ko ya ce an saba musu da shan zaki.
Kai tsaye gurin da motocin ta suke ya wuce, ya saka tashi. Sannan ya fito da ledojin ya nufi falon Amna. Yana shiga ya kulle kofar, don yasan ba zai fito ba sai gobe.
Dakin da ta sanar da shi cewa nan ne nashi, nan ya nufa. Karan ruwan da ya ji daga cikin bandakin shi ne yasa shi tunanin tana ciki. Sai ma ya ga kayanta da ta cire a kan gado.
[8/16, 21:53] Ummi Tandama????: _