
Ni dai zan gasa biredi kuma zan soya kwai.” Ta kalli Shatima. “Yaya ka siyo mana me yanka yanka.” Ya ce, “To Sumayya.”
Daga nan dakin Nafisa ya shiga. Kaf! Din su suna dakin da Nafisar take, ya shiga suka yi ta gaishe shi. Ya duba bai ga Nafisar a cikinsu ba. ya ce, “Ina Amaryata?” Suka ce, “Tana wanka.” Ya ce, “Me ku ke bukata?”.
Shahida ta ce, “Dama yunwa muke ji.” Ya ce,
“Akwai kayan tea ne nan?” Momi kanwar Nafisa
ta ce, “Sosai ma, gasu can a store.” Ya ce, “Bari in
kawo muku biredi.” Hamida ta ce, “Yaya Nafisa
kuwa bata cin biredi.” Ya ce, “To fa! Yanzu me zan kawo mata, me take ci?” Momi ta ce, “Ai naga akwai Indomie sai ayi mata.” Ya ce, “To bari yaje ya kawo musu biredi.
In ta fito a ce, yana gaida ta kafin ya dawo. Ya shiga gurin Salma itama sai da ya Kwankwasa kofa. Tazo ta bude, ya kalle ta. Sanye take da kayan bacci, sun yi mata yawa. Sai gashinta da ya sauka a bayanta. Sannan ga abin risho a hannunta tana ta kici-kicin sawa da zabori, tasa daya tana fama da na biyu.
Ya ce, “Mene ne wannan? Ta ce, “Abin risho ta durkusa “Ina kwana Yaya?” Ya ce. ne.
“Lafiya. Na ce miki ni ba Yayanki ba ne ko? Yanzun me za ki yi da wannan?”
Ta ce, “Zamu sa ruwan wanka ne, kuma zamu karya.” Ya ce, “Tashi daga tsugunno mana, ba ki da butar jona ruwa ne?”
Ta girgiza kai, “Bani da shi.” Ya ce, “To ai babu kalanzir din da za ki kunna rishon ko?” Ta ce, “Babu.” Ya ce, “Kina da flask din ruwan zafi?” Ta ce, “Bari in duba.” Ta fito dashi a cikin kwalinsa ya ce “Ciro.” Ta ciro, ya amsa ya ce, “Bari in je sai Aliya ta dafa miki. Ina Badi’atu?”
Ta ce, “Tana bacci.” Ya ce, “To ina zuwa.” Yaje gurin Aliya ya bata filas din ya ce, a sa ma Salma ruwan zafi a nan.”
Ta ce, “To.” Ya ce, “Bari in je in siyo musu biredi.” Ya dauki makullin mota. Ta ce, “To amma wanda ba shi da kayan tea ga wannan da su Munnir suka shigo da shi.” Ya ce, “Su duk suna da kayan tea Salma ce kawai.” Ta ce, “To in ka zo sai ka kai mata.
Da yawa ya siyo, kofar Amna ya tsaya ya ba Sumayya ta dibi wanda zai ishe su, itama Shahida ta dibar musu. Sannan ya koma gurin Aliya.
Ya ce, “Gashi in za ta kara.” Ta ce, “Nasun nan ma ya yi yawa.” Ta bashi kayan tea har da ragowar kazar da suka ci jiya, ta ce ya ba Salma.
Ya dubeta cikin jin dadi ya ce, “Allah Yasa yanda ki ke bani hadin kai da na zauna lafiya, sauran ma su bani.” Ta ce, “Za su ba ka insha Allah.”
Ya kai ma Salma, sannan ya dawo suka karya suna ‘yar hirarsu irin ta masoya. Da suka gama ya ce bari yaje inda su Munnir suka kwana. Ta ce, “Har da Munnir aka kwana a nan?”
Ya ce, “A wannan dare ina zai koma Zariya?” Ta ce, “To kaje musu da abin kari.” Ya ce, “A’a masaukin da suka sauka akwai gurin cin abinci, nasan yanzun sun ma karya. Kila tare za mu wuce Zariya da su in kwaso kayana.”
Yana gaida Hajiya, Mustapha ya shigo. Ya gaishe shi, Shatima ya ce “Don Allah Mustapha ka hada min duk kayana. Sannan kuma in an gama zirga-zirga ka dauki motar nan tawa ta da.”
Dadi ya rufe Mustapha, ya shiga godiya. Hajiya ta ce, “Kafar yawo ta karu, ai dole kayi murna.” Mustapha yace Ai na huta, in na ari motarki, ko ta Alhajinma, sai a kira ni a ce dawo min da motata yanzun nan.”
[8/18, 09:54] Ummi Tandama????: _