AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 61-70

 *PAID.*????️=6️⃣1️⃣↪️6️⃣2️⃣

Sakin wuyarta Azima tayi tana huci,tana sakinta Sumy ta zube kasa a sume, cikin tashin hankali suka ɗagota,Beenah wacce saukowarta kenan daga sama dan dama bata nan akayi wannan show din, Mamanta tace

“Beenah! Hanzarta dauko ruwa a fridge” ganin Sumy a baje yasa beenah kwasa da gudu taje kitchen ta dauko ruwa aka yayyafawa Sumy, da karfi ta fizgi numfashi, ganin ta saki ajiyar zuciya yasa Al’mazeen ya fizgi Azima ya wanka mata mari, wani gurnani Azima tayi tasa hannu zata shaƙi wuyar Al’mazeen da hannu biyu amma tamkar an daskarar mata da hannu ne ta kasa, cike da mugun zuciya da mugun jin haushin kanta ta yi hanyar waje, ganin haka yasa Al’mazeen dafe kai yana ambatar sunanta amma kamar ba da ita yake yi ba.

      Gate ta nufa da niyyar barin gidan, dan ta ga Alkadarinta yana gaff da karyewa, kamata ya yi ace ta kashe sumy dan ita duk wanda ya tabata hukuncinsa kisa ne! haka ma Hamma Mazeen da ya mareta, amma ta kasa aiwatar da komai,to me hakan ke nufi? ai gwara ta bar gidan kafin abunda take rayuwa da shi shekara shabiyar zuwa sha shidda a rabata da shi.

 Al’mazeen ne ya biyota yana kiranta amma kamar ba da ita yakeyi ba dan ta zuciya, karamin kofar gate tasa kafa tayi kwallo da shi,ga mamakin mai gadi sai ganin kofa ya yi a kasa da sauri ya tashi ya matsa ya bata waje, tana sa kafarta a waje da niyyar fita kamar wanda wutar lantarki ta kama haka taji a jikinta, ji tayi kamar an ja kafarta akayi sama da ita sannan aka wurgota cikin gidan, sai da ta yi sama tukunna ta faɗa kan wani dutse  kanta ya bugu, zare ido Al’mazeen ya yi yana fadin

“Azimaaaa!” da sauri ya yi kanta yasa hannu ya dagota, harta baƙin tabarau dinta sai da ya fadi, a lokacin da Al’mazeen ya matso gareta ta rufe ido jin yadda wani mashahurin jiri dake kwasarta dan kanta ya buge sosai, cikin tashin hankali Al’mazeen ke fadin

“Subhanallahi! Azima! Azima! Azima! Dan Allah kiyi hakuri ba da nufi bane,meya sameki?” jinta shuru ba motsi yasa ya dauketa cak ya koma da ita ciki, yana shiga har yanzu ana tsaye a kan sumy wacce bata gama farfaɗowa ta dawo hayyacinta ba.

   Ganinsa sukayi ya shigo da Azima a hannun sai kace baby yana shirin sa kai ya haura sama,cikin masifa Maman Hanan ta ce

“Kai Al’mazeen! Wannan wani irin rashin hankali ne! Ya zaka dauko yar aiki haka a hannunka sai kace matarka!? A gabanka fa ta shaƙe Sumayya tana shirin kasheta amma baka dakatar da ita ba, zata bar gidan ka je ka dawo da ita, ga Sumayya nan dake bukatar taimako amma baka kalleta ba ka wani dauko wannan ƙidahumar jejin matarka ce ko aurenta zakayi!  bayan kasan kuma su Sumayya da Sadiyya sune matan da zaka aura ko? ko dai akwai wani abu a tsakaninka da wannan daukar kaddaran ne?” (wai Azima ce daukar kaddara)  rai a haɗe Al’mazeen ya juyo ya ce

“To auranta zanyi! Ta fiye min su Sumayya da Sadiyya sau dubu! Ina sumayyan ce ta jagaleta? Ita ma Azima ta suma,ku kai sumayyar sama bari na duba Azima tukunna,zan zo na duba Sumayyan daga baya” yana gama fadi ya hau sama ya bar su shanye da baki.

       A gadonsa ya kwantar da ita yana dubata, gefen kanta ya gani ya ɗan fashe, hannu yasa da niyyar yi mata treatment ji ya yi ta riƙe hannunsa, kallonta ya yi ya ga har yanzu idonta a rintse yake, a hankali ta miƙe ba tare da ta kallesa ba tasa kai zata fita yayi saurin shan gabanta,

“Azima yi hakuri! Ki fahimceni ba da nufi na mareki ba, laifinki ne inata miki magana ki saketa amma kin ƙi ki 

saurareni, taya zaki shaƙeta haka idan ta mutu me kike tunani zai faru? Ba ke kaɗai ba harta ni sai an kulleni dan anyi kisan kai a gidana! da kin kasheta sunanki fa zai koma criminal ne, kuma ba zan so hakan ta faru ba amma kiyi hakuri kinji? karki yi fushi” ya faɗa yana haɗe hannuwansa alamun roƙo,Azima kuwa juya kanta tayi gefe har yanzu taki yarda ta buɗe, yana gama magiyarsa ta rab’a ta gefensa ta fice, riƙe kai Al’mazeen ya yi yana jan ajiyar zuciya,box dinsa ya dauka ya fito yayi side din su Hanan, ya nufi dakin baki wanda su Sumayya suke zama idan suka zo, da sallama ya shiga har zuwa yanzu suna tsaye a kan Sumy, rai a haɗe fuskarsa ba annuri ya shiga, allurai ya yiwa Sumy sannan ya ɗora mata ruwa, nan da nan bacci ya kwasheta, kwashe box dinsa ya yi zai fita Maman Beenah ta ce

“Al’mazeen? Amma ina fatan batun auren yarinyar nan kawai ka faɗa ne ba da gaske kakeyi ba?” 

Cak Al’mazeen ya tsaya ya juyo ya ce

“Da gaske nakeyi! Zan aureta! taya zan auri Sumayya? daga zuwanta yau ta bi Azima da sharri! Laifi biyu wanda na tsana a rayuwata! tayiwa Azima ƙarya da ƙazafin abunda bata yi ba,ƙazafin ma kuma na sata!” yana gama fadi ya fice, aka barsu da zare idanu.

     Part dinsa ya koma, yana tajin babu dadi na ganin Azima tayi fushi, shirin bacci ya yi ya kwanta dan yana tashi sallar dare.

@@@@@

       Da washe gari kamar yadda Azima ta saba haka ta shigo ta kawo masa abinci amma bayan sallama ko gaishesa taƙiyi, shi kuwa kallonta yakeyi yadda ta duƙar da kai fuska babu rahma ranta a haɗe, ganin har zai fita bata yi masa magana ba ya saka shi fadin

“Ba ki huce bane? na fa baki hakuri, ba zaki min magana ba? to ga wayarki, kalli ki ga yadda zakiyi amfani da shi” turo baki tayi tana fadin

“Bana so” sannan ta fice, Al’mazeen ya sosa kai ya ce

“Tab lallai abun babba ne, duk yadda jiya ta nuna murna da farincikinta akan wayar yanzu kuma tace bata so?” haka yasa kai ya fice, a office sai tunaninta yakeyi, Azima kuwa wuni tayi fuskarta a murtuke dan abunda ya dameta ya dameta, tunda tazo fita akayi sama-sama da ita sannan aka maidota gidan ta rasa inda zata saka kanta.

       Wasa-wasa Azima ta dauki zafi dan har aka kwashe sati daya bata magana da Al’mazeen tsakaninta da shi sai dai ta kai masa abinci ta gyara masa daki,duk kulawar da take ba shi bata daina ba magana ce dai bata masa, a sati dayan nan kuwa Al’mazeen ya yarda ya kamu da soyayyar Azima, kullum sai ya bata hakuri amma taƙi ta sauraresa dan ita kadai tasan bakincikin da take ciki.

        Ta bangaren su Aziza sun fara shirin bikin Sultana wanda zai gudana nan da sati biyu ciff, Aziza daurewa kawai takeyi tana abubuwa, amma bata da wani kuzari da karfin dafi.

     Ana saura sati daya biki duk hankalin sultana a tashe yake.

 Al’mazeen ya shaidawa Nawaz a kan cewa idan ana saura kwana uku ɗaurin aure zai zo.

Ko da Sultana ta kara yiwa Khalil magana a kan tafiyarsu kano yace ta hakura kawai sun yi magana da Al’mazeen yace zai gaya musu ita ba sai taje ba,sultana ji tayi kamar ta kurma ihu dan bakinciki.

@@@@@@@

         Fitowa daga daki Aziza tayi zata hau sama da wani jiri ya ɗibeta zata fadi dai-dai lokacin da Nawaz ya sawo kai parlorn amma kafin ya iso ya tarota tuni ta fadi kasa,sunanta ya ambata ya dagota yana jijjigata a hankali yana kiran sunan Mom da sultana, da sauri suka sauko kasa suka samu Aziza kamar ta suma ne yaya ne oho

“Nawaz me ya sameta!?” mom ta tambaya hankalinta tashe, Nawaz yace

“Wlh mom ban sani ba,ina shigowa ne na ganta tana faɗuwa!” Mom ta ce

“A gaskiya Nawaz shawaran Malam Yunusa zamu bi, kawai ranar daurin auren sultana a haɗa a daura da naka da Aziza! mu tausayawa yarinyar nan halin da take ciki! Sai daurewa takeyi tana hadiyar zafin ciwo, a kananun shekarunta tayi ƙanƙanta da jurewa!” mom ta fada tana sakin kuka mai ban tausayi, Nawaz wanda shima idonsa ya canza kala ya ce

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button