SALON SO COMPLETE HAUSA NOVEL

SALON SO BOOK 1 PAGE 33-34

 

????????????????????????????????????????            ???? SALON SO ????

????????????????????????????????????????

    BOOK ONE ????

Story & written by

Mommyn fareesa

   ????️33&34

………washe gari!

            tunda yasmeen ta tashi gaba d’aya hankalinta nagun mr Aliyu”ko kunun tsamiyar da fanke datake so sosai bata wani sha na kirkiba”tayi wanke wanke ta gyara d’akinsu” kafin ta shige wanka”

        shiryawa tayi cikin riga da siket d’in”tafeshe jikinta da turaruka”bayan tashafa powder,tashafa lip stick jaaa”tashafa consila da maskara”batayi jagiraba sbd girarta acike take”ita kanta tasan tayi kyau”sabuwar hijab nata tayi saurin sakawa har k’asa”tayi acuci da gashin kanta”tasaka mad’aurin hijab d’in ta d’aure”sbd bataso mama taganta da kayan”

      gyale red ta d’auka tasaka acikin hand bag nata ta fito tsakar gidan”sbd ganin flashing d’in mani driver alamar yazo kenan”dukda alokacin 8:43 am”9 d’in ma batayiba”sallama tayiwa mama”bayan mama ta tabbatar yasmeen ta d’auki kud’in”

       yasmeen isowa tayi suka gaisa”kafin tace”.yaudai kazo da wuri”Eh wlh hjy”both ne yace”.nazo natafi dake”

Okay kawai tafad’a tana shiga back sit”yaja motar suka wuce”

Mr Aliyu kuwa gaba d’aya da tunanin yasmeen ya kwana”saidai kawai yadinga alak’anta abun da sun shak’u kawai”

da safe tun 7 yatashi yashirya cikin kayan daya siya musu iri d’aya jiya”

Ko break fast beyiba yazauna parlour zaman jiran yasmeen”

Amma shiru”wayarta kuma bata shiga idan yakira”hakan yasaka yakira mani driver yace”.yaje ya d’akkota”

Imaan dai datazo gaisheshi ta nata binsa da kallo”

bayan yagama wayar suka gaisa”tace”.yaya naga bakayi break fast bak’o?”

Eh yasmeen banyiba”yasmeen kuma yaya?”imaan ta tambaya”basarwa yyi yace”.ina nufin sai yasmeen tazo”

To shikenan yaya tunda week end ne bara naje nakoma bacci”idan tadawo tagama aikinta sai muyi maka lunch ko?”

Eh baby”hakan yy”imaan na murmushi ta tashi ta wuce ciki”

Mr Aliyu yatashi tsaye ya wuce bed room d’in sa yabud’e window”kasancewar akan benene”kuma window d’in na kallon wanda ke bakin get”

yana k’ok’arin sakin labulen mani driver yacinno hancin motar cikin get d’in gidan”

ajiyar zuciya yasaki yana kafe motar da ido har yasmeen ta fito”

Haushi yaji sosai daya ganta da hijab har k’asa”

    sakin labulen yyi yafito dg bed room d’in”

yasmeen kuwa tana shigowa sashen”taga bbu kowa a parlourn”

saita wuce parlourn sa”yana k’okarin kunna TV tashigo da sallama”

Amamakinta bata isheshi kalloba”balle ya amsata”gashi ta fahimci sbd suyi iri d’aya yace”.tasaka kayan jiya”tunda gasunan shima ajikinsa”

yamata kyau sosai”cikin sanyi murya tace”Allah yasa ba laifi nayiba yaya Aliyu?”

yafi second 10 sannan yace”.malama kikoma Inda kika fito tunda bazaki iya bin umarninaba”kin wani saka hijab sai kace kinzo gidan mutuwa…..

batace komaiba ta juya ta fice”bbu jumawa ta turo k’ofar tadawo”

Mr Aliyu azatonsa fushi tayi ta tafi gida”yana tsaye dafe da kansa yaji motsinta ta turo k’ofar”

yana d’ago kansa suka had’a ido da yasmeen”tasakar masa murmushi”

Ahankali ta kalli kanta Tace”. yanzun nayi ko?”kokuwa banyiba??”tak’arasa zancen cikin shagwab’a”

Ajiyar zuciya yasaki yana kallon ta yamatso kusa da ita”

yasmeen dama kinada kyau haka kike b’oyemun??”turo baki tayi tace”.kaifa kawai nayiwa kwalliyar nan”hakan yasa nasako hijab”gyalena na ajaka”amma shine kayi fushi dani ko?”

     banyi wannan zaton ba yasmeen”kinyi kyau sosai”naji dad’i dakika b’oye wa ko wane k’ato adonki”zoki zauna nasake ganin lallen naki”itama baby kisaka amata”

    To shikenan indai tanaso za’a mata”tafad’a tana zama kan kujera”ta yane kanta da gyale tanata k’amshi”

gefenta ya zauna ahankali tace”.ina kwana?”

lafiya qlau”kasan yaya Aliyu umma kud’in nan 2k kawai ta d’aukarwa Ahmed”

Ok anjima zamuje namasa shopping da sauran kud’in”ai ni nayi niyar basa”

Jiya munyi mgn da baba me kuka”insha Allah yau ko gobe zataje suyi mgn da umman”

To shikenan Allah yakaimu lafiya”yanzun kayi break fast ne?”

Ah ah”meyasa kakeson zama da yunwa fisabilillahi?”

kenake jira kizo muyi atare yasmeen shiyasa”

nimafa wlh gaba d’aya hankalina yana gunka”

Allah?”Eh mana”to yanzun idan munyi break fast wane labari zaki bani?”

      Uhmmm yaya Aliyu nida zanyi aiki wane labari kuma”sannan zanyiwa imaan kitsoma”

Ana kitson kina bani labarin”aiki kuma zantayaki shikenan?”

tana murmushi tace”.yau bazaka fita ko inaba?mezanyi awaje tunda week end ne?”

hakane kam”ina imaan?bacci takoma”okay tafad’a tana tashi tsaye”yabi bayanta da kallo har zuwa k’afafuwanta”

kafin yamik’e tsaye yabi bayanta adining area d’in”

meye kakeso?”kizubamun kunun gyadar da farfesun kan rago”

batace komaiba tafara k’ok’arin zuba mishi komai”yanata aikin kallon hannayen dasukayi jajir da lalle gwanin sha’awa”

komai ta tura masa agabansa”yana murmushi yace”.thanks!

Tayi mamaki jin kalmar”tunda take dashi bata tab’a jin yabada hak’uri ko yyi godiyaba”da wannan tunanin ta d’an zuba abinda zata iya ci”

Ahankali cike da nutsuwa suke gabatar da break fast d’in”

      can yasmeen tace”.inaso namaka wata tambaya inajin tsoro”

Uhmm! shikenan tunda amsar tambayar bata damekiba”

tana k’okarin mgn taji an murd’o k’ofar”azatonta imaan ce”tana d’ago kanta suka had’a ido da wata budurwa”

gaban yasmeen yafad’i ta d’auke kanta sbd yadda taga yarinyar nabinsu da wani irin kallo tana nufosu…

Mr Aliyu kuwa tsabar miskilanci be ko kalli wanda yashigoba”jikinsa kuma yabashi ba imaan bace”

sweet heart wacece wannan dakuke sanye da ita da kaya iri d’aya??”

wani malolon bak’in ciki yatsayawa yasmeen acikin ranta”

     mr Aliyu ya ajiye cup d’in dake ahannunsa”yakalli yasmeen murya can k’asa yace”.yatafi parlourn konajiraki??”

Cikin kashe murya yasmeen tace”.nidai kajirani mana”

yaya Aliyu nizaka wulak’antanta akan wata banza??”

Cikin fushi yamik’e tsaye yad’auke ta da wani gigitaccen mari”karki koma kiranta da wannan kalmar”kije ki koyo sallama sannan kishigo mun anan”and last kika koma kirana da sweet heart saina zubar miki da hak’ora”yana fad’in hakan yaja tsaki yarab’ata ya wuce”

Jidda natafe da kuncinta ta fashe da kuka ta juya ta fice”

Jidda(d’iyar k’anwar daddy ce”tana mutuwar son mr Aliyu”mahaifiyarta nason ya aureta sbd dukiya)ko ayanzunma jidda tazone taganshi” sbd tasan week end yana gida”

D’akin imaan ta wuce tana kuka”imaan tayi saurin bud’e idanuwanta”

Jidda na kallonta tace”.wacece wannan yarinyar dasuke tare da yaya Aliyu”naga kayansu iri d’aya???”✍️

[ad_2]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button