SALON SO COMPLETE HAUSA NOVEL

SALON SO BOOK 1 PAGE 31-32

 

????????????????????????????????????????            ???? SALON SO ????

????????????????????????????????????????

    BOOK ONE ????

Story & written by

Mommyn fareesa

   ????️31&32

mr Aliyu yace”.kishiga front sit mana”imaan zata shiga anan”tamkar yasmeen tamasa musu” tadai daure tana kallon fuskar imaan taga yanayinta”sai taga imaan d’in ko ajikinta hankalinta nagun wayama….front sit ta bud’e ta shiga”mr Aliyu shima yashiga yaja motar”ahankali yace”.my baby keba kinada kayan make up ba?”Eh yaya inada su”anty yasmeen ce tace”.nara kata muje”juyowa yyi yakalli yasmeen d’in”tayi saurin yin k’asa da kanta”tana wasa da yatsun hannuwanta”beyi mgn ba yaci gaba da driving d’in sa”har suka iso wani babban shago”parking yyi suka fito atare”suka shige cikin

shagon”kasancewar imaan nazuwa siyayya acan”itace agaba suna biye da ita”abin mamaki da mr Aliyu yaga abu sai yace”.yasmeen kid’auki wannan”ko wannan zai miki kyau”tun yasmeen na nok’ewa harta fara d’auka”bayan yajidar mata kayan make up da turaruka masu tsadar gaske”yajasu gun k’ananun kaya…..abin mamaki yaga wasu suit Riga da siket na mata sai na maza riga da wando duk iri d’aya”d’aukarsu yyi bece komaiba”      yahango wasu riga da wando suma na mata masu kyau”yasmeen na tsaye kawai taji yaja hannunta”kafin tayi mgn yace”.kiduba wa’acan naga zasumiki kyau ko?”wai kai yaya Aliyu baka gajiya da kashe kud’i ne dan Allah??”kayi hak’uri wa’annan ma da muka jida sun ishemu dan Allah”sakin hannunta yyi yad’auki kayan”yawuce gun biya”imaan ma ta d’auki wasu tabi bayansa”

     yasmeen tasaki ajiyar zuciya tace”.yanzun akan wannan maganar fushi zaiyi?”tsoron hakan yasa na amince muzo”

juyawa tayi taga yadawo mata asalinsa nada”yahad’e fuskarsa”imaan ta juyo tana cewa anty yasmeen zo muje”tace to ta nufosu”shikuma yyi hanyar waje”

suna fitowa wani mustapha mate d’in yasmeen yazo zai shiga”

da sauri yayo baya yana cewa yasmeen!juyowa mr Aliyu yyi yanajin wani abu yasoki zuciyarsa”sbd kawai yaron yakira sunanta”

mustapha ya gida?”muna saurine sai anjima”tafad’a tana satar kallon mr Aliyu dake binsu da wani irin kallo”

mustapha bece komaiba yyi wucewarsa ciki”

mr Aliyu yabud’e motar yashiga”yasmeen na shiga ya wurgo mata harara”shi wancan dakike washema hak’oran ai da gunsa kika koma baki dawo ba”

shiru kawai tayi batace ba”yana driving yanajan tsaki”

har suka zo anguwarsu yasauke imaan”bayan tayiwa yasmeen sallama tashige get d’in gidan”

sukuma suka d’auki hanyar anguwar su yasmeen”

yaya Aliyu!!naga kamar fushi kakeyi dani akan ban d’auki kayanba”

meyasa wani time d’in baka fahimtata ne?”bansan yazan cewa umma idan ta tambayeni ba”ko yanzun kayan kwalliyar, zance mata kyautar kud’i akabayar a company”shine nasiya….

awannan zamanin mutane nada saka ido dabin k’wakwaf akan y’an uwansu mutane”

karka manta wacce muke zaune da ita”itace ta had’a makircin komai agun yayan mahaifina”

ana ganin ina saka sutura me tsada ,tayaya baza’a zargeniba?”amma ka kasa hango hakan kana ganin ban kyautaba….

Ajiyar zuciya yasaki sbd yagamsu sosai da bayanin  yasmeen”yakuma yaba da kaifin hankalinta aransa.

Ahankali yace”.shikenan komai za’a dinga bi ahankali”amma kinga wa’acan kayan nidake nasiya mawa iri d’aya ne”

Kisaka su agobe”su kuma wa’annan zan ajiye miki su wata rana zan baki”

Amma yaya Aliyu meyasa zan sakasu agobe pls?”

Allah yakaimu zaki gani”yafad’a yana ciro kud’i rafar y’an 500″ya aza maya alan cinya”gashi kibawa Ahmed”nabashi kud’i d’azun yak’i karb’a”yace”.umma ta hana”kisanarwa umma tayi hak’uri tabarshi ya amsa”

To shikenan yaya Aliyu”Allah yasa ta amince”kud’in ne sunyi yawa sosai ai”

yauwa kinga namanta ma”inaso kiyiwa umma mgn zan canza muku gida ku koma can da zama idan bbu damuwa”zanturo baba me kuka suyi mgn”

gsky yaya Aliyu hidimarka tayi yawa wlh”amma kadai turo baba me kuka d’in”sbd nasan da wuya umman ta yarda”

To shikenan yasmeen”amma banaso kuna zaune anan gurin”yanzun d’azun daban zoba shikenan yaron nan yagama cin zalinki da mutuncinki”

babu  wanda zai hanashi koya tsawatar masa”

hakane gsky”naji dad’i da sanyi araina danaga Allah yakawomun kai”

yana murmushin jin dad’in kalamanta yyi parking”

tana k’okarin fitowa yace”.kin tsaya muyi sallama ko?

tana murmushin ta d’auki kud’in dayace takaiwa Ahmed tace”.ai yaya zamuyi chats ko?”

nifa yasmeen danayi chats gara kawai nakira mutum mugaisa”

nidai ai dani kawai zakayi chats d’in bada kowaba”kamar yadda bbu wanda zanyi chats dashi sai kai”

To shikenan 8 zan hau online d’in”nima 8 d’in insha Allah”

Okay baki buk’atar komai?”bana buk’atar komai sai abu d’aya”

menene shi? murmushin ka mai tsada nakeso kamun”

Hmmm ai ban huce daga fushin danake dakeba”

kukan shagwab’a tasaka tana turo baki”ashagwab’e 

Tace”. da yanzun dana koma gida zankira teema k’awata tasamun lalle amma nafasa”tunda bazaka mun murmushin ba”

To ai kema bakimun nakiba”batun lalle kuwa inma kikazo gobe ba’a mikiba zamu b’ata”

Kinga dama bamuje amiki gyaran kaiba”

Abarshi sai gobe tunda week end ko?”

Eh hakane”k’arfe nawa mani driver zaizo d’aukar ki?”

10 :am insha Allah”gsky yamun misa yasmeen”ina laifin 8 ma”

yanzun 9:am insha Allah zan iso”kasan umma tasan week end ne”

To shikenan”bazakamun murmushin ba”d’ago kansa yyi suka had’a ido”ta turo masa d’an bakinta”

Besan lokacin daya saki murmushi ba”itama murmushin tamasa tana janye idanuwan ta”

Ahankali yace”. serious kisaka kayan nan gobe”

To shikenan Allah yakaimu nagode k’warai yaya Aliyu”Allah yak’ara bud’i”cike da Jin dad’i yace”.Ameen”

Fitowa tayi ta bud’e back sit ta d’auki kayan ta”kafin ta d’aga mishi hannu ta shige gida”

tsintar kansa yayi cikin farin ciki”da haka yaja motar yabar gurin”

Lokacin da yasmeen ta shiga ciki”umma na bayi asma’u da Ahmed ne atsakar gidan”

D’aki ta wuce tasaka kayan cikin akwati”tabar kayan shafar ajiye cikin leda gefen katifa”

Ta zauna ta lalubo number d’in fatima”tasanar mata idan bata komai tashigo yanzun ta saka mata lalle”teema tace”.gata nan zuwa”

tana k’okarin ajiye wayar umma ta shigo cikin d’akin”

Umma sannu da gida”yauwa yasmeen kin dawo ? Eh nadawo”

d’azun anzo ankama d’ahara ko?”Umma tace”. Eh”mijinta da kansa yace”.sutafi da ita shima yagaji da gulmace gulmacenta”

shikuma yaya d’ahiru yazo yanata zage zage akan nasaka afito masa da d’ansa”

nima namasa tas akan yafita konatara masa jama’a”

shine yafita bbu jumawa sukadawo da yaya tanimu”

Kinsan yaya tanimu da fad’in gsky”namasa bayani akan duk yadda akayi”

Aikuwa yace”.bbu ruwansa dole abi miki hakk’inki agun sanusi da d’ahara”

yaya d’ahiru badan yasoba yatafi kawai”

yasmeen ta girgiza kanta tace”.yabidai ahankali wlh karyajawa kansa shima tam”

ninayi mamakin yadda akayi sukasan gidan nan”umma tace”.kwanaki ai sanusi yaga asma’u yabiyota”yasmeen tace”. Allah yakyauta”

Umma na zama tace”. wa’annan kud’in da ledar fa??”

kayan kwalliya ne da turare”bak’i akayi a company akabamu kyautar kud’i”naga banida kayan kwalliya nasiya”

hakan yyi kyau to”wa’annan kuma inji yaya Aliyu yace”.abawa Ahmed”

zaro ido umma tayi tace”.rufamun asiri”ina Ahmed zaya da uban kud’in nan?

    gsky kimayar masa da kudinsa yasmeen”banason yin abinda za’a mana kallon masu k’wadayi dason abin duniya”nidai fatana kidan tara wani abu kibar aikin nan”

1 2Next page

Leave a Reply

Back to top button