RAYUWAR MACE 1

“Alhamdulillah!.” Ya samu kansa da furtawa yana gida kansa duk da be ji abinda Yaya Asaben tace ba. Umma da ta kusan sakin abinda yake hannun ta sanda taji maganar ce ta karaso ta zauna tana kallon Abban amma sam yaki yarda su hada ido ma balle ya gane abinda take so ta nusar dashi.
“Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya.”
“Amin Ahmadu, sai a saka lokacin kad’an tunda dama abinda muke jira kenan, kaji al’amarin Allah, babu yadda banyi da shi ba akan ya fitar da matar aure tunda ya dawo yaki ashe ashe dai matar sa na nan tana jiran sa.”
“Haka dama al’amarin Allah yake.” Abban ya amsa cikin yak’e, sai ta waiga wajen da Umma ke zaune tace
“Sai a fara shirye shirye kawai bilkisu, bari mu wuce dan tun a yau zan fara shiri auren yara biyu.”
“Haka ne. “
Tace itama tana yak’en wanda sarai Hajiya Maman ta ga yadda dukkn su maganar ta dake su amma ya zatayi? Dole ta so abinda danta yake so duk kuwa da bashi ta nagartar da za’a bashi mace amma ai hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar dole sune zasu rufa mata asiri.
Duk abinda ake Adam na zaune a wajen sai da Hajiya Maman tace ya tashi su tafi sannan ya mike ransa fes yana haskilo irin hutuwar da zai da yarinyar dan ba k’aramar mace bace.
A harabar tsakar gidan ya tsaya yana sosa keya umma da ta rakosu ta kalle shi tana karewa shigar sa kallo cikin takaici
“Mah please bari na dan sake ganin ta, zan same ku a mota.”
Dariya ta saka ta kai masa duka ya goce,
“Mara kunya, tana ina ne bata zo ta gaishe mu ba ma ko bata ji shigowar mu bane?”
Katse Maman yayi yace
“Ke da zata zo gidan ki gaba daya mah!”
“Auw kareta kake kenan, toh ai shikenan.” Tace tana cigaba da tafiya
“Muna jiran ka a mota.” Tace sanda sukayi sallama da Umma ta fita ita kuma ta shigo, ta tarar dashi a tsaye a inda suka barshi.
“Bari a kirawo ta.” Tace sannan tayi gaba, yayi saurin bin bayanta ganin ta nufi daki, tana shiga shima yana shiga Asma’u dake kwance ta mike da sauri, kafin tayi magana ta hangi mutum a bayan umman yana zuro kansa yana kokarin shigowa dakin da dukkan karfin sa.
“Kar a shigo!” Tace da karaji ya tsaya cikin jin tsoro, sai a sannan umma ta san ya biyo ta, ta juya da sauri mamakin rashin kunyar sa na neman kai ta kasa
“Kaje falo zata zo.” Kawai tace masa cikin takaici, ya juya ba dan ya so ba, ya fita yana taku dai-dai. Girgiza kai Umma tayi cikin tsananin bacin rai tace
“Ki je wajen sa a falo bari na samu Abban ku, jinkirin aure ai ba hauka bane da za’a dauki wannan mara tarbiyar a baki, ba zan yarda ba.”
Sam bata fuskanci in da maganganun Umman suka dosa ba.
“Umma!”
“Kiyi abinda nace kawai ba sai ya sake dawowa ba, ki rik’e Areef ku je tare karki je ke kadai.”
Daga haka ta juya da sauri ta nufi wajen Abban dan a san wacce za’a yi, ta dade da sanin Hajiya Maman bata santa,amma bata san rashin son ya kai haka ba!
Rayuwar mace cike take da kalubale mabanbanta! Kaddara ce tsanin duk wata nasarar ta! Ba zata ce ita din rayuwa bata mata adalci ba, sai dai akwai tarin kalubale cike da rayuwar tata, wanda a karshe zata kirasu da matakin dukkan nasarar ta!