Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 2

RAYUWAR MACE
     Hafsat Rano
             Free Page  (2)

A kofar dakin Umma ta tarar dashi, ta nuna masa falon da hannu sannan ta wuce falon Abban. Yana tsaye yana kai kawo a tsakiyar dakin tana shigowa ya bi ta da ido dan yasan abinda ya kawo ta.

“Alhaji..”

Da sauri ya dakatar da

“Maganar ba zata chanja komai ba, muyi mata addu’a kawai bamu san me Allah ya tsara ba.”

“Amma dai hakkin mu ne mu nema mata miji na gari, wanda muka yarda da addininsa da nagartar sa, amma Adam fa? Ya cika wannan sharadin?”

Zama yayi a nutse bayan ya cire babbar rigar jikin sa da hula sannan yace

” Mu bar wa Allah komai, ya fimu sanin komai akai, ba zan taba iya hana Yaya Asabe abinda take so ba, ba kuma zan taba kin danta wai don munin halin sa, ni ma ban fi karfin Allah ya jarraba ni da irin sa ba.”

” Yanzu shikenan muna ji muna gani saboda kawai muna so yar mu tayi aure za muyi mata zabin tumun dare!?”

” Idan da rabo sai kiga ta dalilin ta Allah ya shirye shi, sai tayi kokari ta sauya masa DABI’AR sa tunda mace tana da matukar tasiri a rayuwar namiji.”

Wani abu ne yazo ya tokare wuyan Umman, bata tare da masu ganin cewa mace zata iya gyara wa namiji Hali bayan ta same shi da girman sa, kawai idan kaji an ce haka toh fa lallai an shirya zalintar macen. Tana tsaye ya zo zai fita daga falon, ya kalle ta yana gyara hular kansa sannan yace

” Karki nuna mata wani abu da zai sa taki auren, muyi mata addu’a kawai dan babu abinda zai sa a fasa sai dai idan Yaya Asaben da kanta tace sun fasa, amma muddin bata ce ba, toh babu makawa sai anyi.”

Kasa tanka masa tayi har ya fice, ta zauna dabas a wajen tana jin da gaske an cuce ta, ta kuma tabbatar da biyu Hajiya Maman tayi dan ta nuna mata ta isa da Abban da ma duk wani abu da ya dangance shi.
  Da k’yar ta mike daga wajen ta fito bayan ta jawo masa falon, ta isa dakin Asma’un ta tarar da ita tana sallar azahar, sai kawai ta wuce dakin ta domin ta gabatar da tata sallar.
   Tana idarwa Asma’un na shigowa, bata ce komai ba ta hau gadon umman ta kwanta rigingine tayi shiru tana tuna abinda ya faru bayan taje wajen sa. Kadan ya rage be rungume ta ba da ta shigo, ya hau surutan da ta kasa gane komai akai, haka ya karaci babatunsa ya tafi bayan yace mata zai dawo da daddare.

“Umma wai me ya faru?”

“Aina da?”

“Ya Adam, ban gane ba wallahi. “

” Kinsan kowanne bawa da yadda Allah yake kaddaro masa rayuwar sa, sannan duk dan ta yayi ma iyayen sa biyayya toh fa ba zai taba tabewa ba, mahaifin ki ya yanke shawarar aura miki dan uwanki Adam… “

A yadda ta mike daga kwancen sai da ta bawa umman tausayi,

” Umma Adam kuma? “

Kai ta daga mata

” Innalillah wa inna ilaihi rajiun, umma wallahi tallahi bana son shi, bashi da hali me kyau wallahi Umma, wallahi Allah bana son shi dan Allah Abba yayi hakuri. “

Duk ta gigice ta rikice, hawayen da Umman take ta rikewa ne suka soma saukowa tayi saurin maida su tana karfafar kanta.

” Menene haka? Me kike haka? Ashe ba zaki iya yiwa mahaifin ki biyayya ba?”

” Umma Adam fa? Umma dan Allah kice yayi hakuri wallahi ba zan iya ba. “

Wani kallo umma ta watsa mata

” Ki nutsu ki saurare ni, kinsan waye mahaifin ku, kin kuma san wacece Hajiya Mama a wajen sa, kukan ki da magiyar ki ba zasu taba sauya masa abinda yayi niyya ba sai dai idan su suka ce sun fasa, dan haka ba ruwana wallahi, ba zan bari ki hadu da fushin mahaifin ki ba, kiyi masa biyayya ku rabu lafiya nima na rabu da nawa lafiya, kuma in sha Allah zaki ga ribar biyayya. “

Daga haka bata kuma cewa komai ba, ta fice ta bar ta a dakin tana jin yadda take kuka wiwi, wayar ta ta dauka ta kira babbar ‘yarta hadiza ta sanar da ita komai sannan ta kira sauran yan uwan Asma’un da sukayi aure, kafin kace me sai gasu a gidan gaba dayan su, duk kansu kowa be ji dadin labarin ba, amma kuma sai Umma ta hana su fuskar da zasu kushe abun dan ta riga tasan halin Abban su sarai zai iya saba musu akan maganar, sannan tunda tasan babu fashi gwara kawai tayi kokarin ganin basu bawa Asma’un kofar da zata bijire wa mahaifin nasu ba.
  Lallashi da ban baki suka dinga yi mata har suka samu ta dan nutsu amma bata bar kuka ba. A haka Abban da yan mazan suka dawo suka tarar dasu, Abban ya danyi fadan dalilin zuwan su haka sai suka ce ai zuwa sukayi su gaishe su, ya ji su ne kawai amma ya riga ya san umma ce ta kira su akan maganar.
   Bayan sallar magriba Yaya hadiza ta samu Abban da maganar, ya nuna mata babu fashi su dai kawai su tayata da addu’a, haka ta baro dakin jikin ta a sanyaye bayan ta roke shi ya barta su tafi da Asma’un ya amince amma iya sati daya kawai dan sati uku ya saka bikin tunda babu wani shiri da za’a yi dan kowanne bangare a shirye suke dama.
   Mijinta ne yazo ya dauke su wajen tara, a hanya take bashi labarin abinda ya faru, ya dan juyo yana sake bawa Asma’un baki yana tsokanar ta, ta dan yi murmushi kawai amma ita kadai ta san yadda take ji a ranta.
  
***Washegari bayan an makaranta sun tafi umma ta shirya Abbati ya kaita chan Mandawari gidan su ta samu Hajiyar su da maganar auren Asma’un da lokacin da Abban ya saka, duk basu ji dadin hukuncin Abban ba, da kuma rashin bawa Asma’un dama ta fadi ra’ayin ta dan kawai ana ganin kamar ko an barta ma ba wani ne zaizo neman auren nata ba.

“Toh yanzu dai ya riga ya gama yanke hukunci, namu kawai shine mu bi ta da addu’a, Allah ya basu zaman lafiya ya kade fitina.”

Hajiyan tace bayan sun gama magana da Umman.

“Amin, ni na rasa ta ina zan fara ba, sai a aika su miko su sanar da su umman Asiya da su Aunty Falila da gidajen su kawo muntari.”

“Eh yana shigowa zan aika shi, sati uku kamar yau ne ai, duk sai a sanar da dangi, Allah ya basu zaman lafiya.”

“Amin.” Tace a sanyaye.

***Bangaren gidan Hajiya Mama shiri take na ban mamaki, tuni zancen ya karade dangin su bangaren Abban da kuma bangaren Baban su Adam din, mutane da yawa suna tausayawa Asma’un saboda dai sam babu hali na nagarta da zai saka ka dauki yar ka, ka bawa Adam din, ciki kuwa har da yan uwa makusantan su Abban dan wani kawun su sai da yayi wa Abban magana kasancewar kowa ya riga ya san nutsuwa da kamala irin ta Asma’un dan kaf yan uwanta babu kamarta, duk da su ma basu da matsala amma kuma ita din daban ce, magana da koman ta a nutse take yin sa, bata da rawar kan yan mata dan ba zaka taba tunanin ta je jami’a ba ma, bata dauki duniyar da zafi ba haka kuma bata da son kyale kyalen duniya. Haka ya saka mutane suke ganin kamar akwai zalunci a dauke ta a hada ta da Adam wanda ake tunani hatta giya yana sha bayan mugun halin sa na neman mata da yayi shura akai, amma yadda Abban yayi biris da duk wannan ya saka kowa ya shafa ma kansa lafiya aka shiga bin su da addu’ar fatan alkhairi.

  Zuwan Adam din uku tare da zugar abokai baya samun ta karshe dai ranar da yazo ya tarar da Abban nan yake gayawa Abba ai yazo baya samun ta, nan fa Abban ya shiga dakin Umma yayi ta mata fad’a sannan ya dauki waya ya kira Yaya hadizan yace ya fasa sati dayan gobe gobe ta dawo gida. Jiki a sanyaye ta amsa masa da toh, bayan ya kashe sai kuma yaga kamar ya zafafa da yawa, sai ya sake kiranta yace ta kyale ta zuwa satin amma zatayi bako gashi nan zaizo yanzo. Nan ma dai toh din tace ya kashe ya koma ya samu Adam din ya yi masa kwantancen gidan Yaya Hadizan sannan ya bashi number wayar Asma’un da ta Yaya Hadizan yace idan yaje ya kira. Bakin sa tamkar gonar auduga ya karba suka dauki hanyar gidan Yaya Hadizan baka jin komai a motar sa ife ifen su irin ma gogaggun yan duniya, burin sa kawai ya nuna musu kalar matar da zai aura ya san ba karamin taya shi farin ciki zasuyi ba, hutu kam zai huta a wajen sosai, yadda yake ji ma kamar sati ukun yayi masa mugun yawa amma haka zai hakura ya lallaba ya cigaba da maneji da su Fido kafin ranar da zai gwangwaje.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button