Rayuwar Mace

RAYUWAR MACE 5

RAYUWAR MACE*
      Hafsat Rano
         Last Free Page (5)

***Babu wanda yake da niyyar rarrashin wani a cikin su har saida Ya Hadiza ta shigo, ta harari Rauda da Hidaya cikin bacin rai tace

“Menene haka? Ku da zaku karfafa mata guiwa sai kuma ko zauna kuna tayata kuka, kukan menene? Akwai wanda ya isa ya kujema kaddarar sa ne? Kowanne bawa fa da yadda Allah ya tsara masa, ku tashi dan Allah kafin hankali ya dawo kanku. “

Shiru duk sukayi har ita Asma’un sai dai ba zata iya fasalta yadda take ji a kirjin ta ba, abu ne dankare me girman gaske, wanda ko hadiyar yawu sai tayi da gaske take iyawa saboda yadda ya tokare mata ko ina.
  A hankali gidan ya sake cika sosai bayan dawowar yan daurin aure, suka dinga jerin gwanon shigowa wajen yin Allah sanya alkhair, daga nan kuma aka dinga fitar musu da abincicika kala kala. Sakon gidan Hajiya Mama ne ya iso, katinan dinner ne ta aiko dashi sannan ta aiko da kuloli manya dankare da sinasir da waina, sai a lokacin su Ya Hadiza suka san da maganar dinner din dan babu wanda ta fadawa. Tunanin yadda za’a yi da zuwan suka shiga yi, dan a kalla ya kamata ace an shirya sosai, basu ji dadin short notice din ba amma kuma babu yadda za’a yi haka za’a je din dan be kamata a bar ta ita kadai ba babu yan gidan su.
   Kamar yadda yake a al’adar Malam bahaushe bayan daurin aure ana zuwa angwaye su gaida iyayen amarya suyi musu godiya, bangaren Adam kuwa da abokan sa suna chan hotel din da aka sauke su, Adam na tare da Fido, dan ko daurin auren be je ba, dan dama yace in dai a Sumailan za’a daura ba zashi ba, sai abokan sa uku kawai ne suka je dama suma duk target dinsu na ga dinner din ba wai daurin auren ba, musamman da aka kaishi har Sumaila ba zasu iya bin hanyar ba balle su sha wahala shiyasa sukayi zaman su har aka dauro aka dawo, aka aiko musu da abinci suka ci sukayi nak sannan suka soma shirin shiryawa dan su shiga gidan su Adam din sannan su rakashi wajen Amaryar tasa bayan ya samu da k’yar ya lallaba Fido ta tafi, jin sa yake yau babu ya shi dan zai gwangwaje sosai, sai kuma yi maganin tsiwa da rainin ta, dan bata kai matsayin da zata gaggasa mata magana anyhow kuma ya zuba ido ya kyale ta, dole sai koya mata hankalin da ba zata sake ba.
    Suna shiga cikin gidan nasu aka yi musu cha ga ango ga ango, yan uwa sai faman tsokanar sa ake, yana washer baki tamkar gonar auduga, da sun san dalilin da yasa yayi auren nan da basu taru haka ba, so yake da gaske ya dauke hankalin kowa daga kansa, ya sheke ayarsa babu me saka masa ido, ya kuma rabu da mitar Maman na kullum yaki aure, shiyasa ma be yi wani dogon tunani akan hukuncin sa ba, dan dai shi yasan ba son ta yake ba, tana dai da abin da yake so a tattare da mace, amma batun kyawun fuska yafi son fara sosai, ita kuma tana da duhu musamman da take cikin fararen tas dan duk yan uwanta sun fita haske hakan ya saka ake ganin har kyau din ma sun fita. Jingina dogon tunanin da ba zai amfane shi ba yayi, suka shiga dakin Mama in da take tare da manyan kawayenta, ai sai kawai ta rungume shi cikin farin ciki, baka jin tashin komai sai gud’a da sambarka, ita kadai tasan yadda take ji da auren nan nasa, a kalla idon mutane zai bar kanshi, kuma tana fatan Asma’u ta shirya mata shi, ya bar duk wata banzar al’adar sa, dan ita a ganin ta ma, idan har mace ta kasa daidaita dabi’u da al’adun mijinta, zuwa nata da take so to tabbas bata kai mace ha, ko tace ma kawai ta rako mata duniya ne. Sun dan jima a dakin sannan suka fito suka rankaya gidan Abban.
   Sanye yake da riga jamfa da wando babu batun babbar riga dan babu ita a tsarin sa, musamman lokacin zafi ne ko da Mama tayi masa magana sai yace mata ai tana mota zai saka idan sun fita, nan kuwa ko dinka ta be ba, hula ma dan dai kawai babu yadda zai ne, amma tabbas yana dawowa zai cire kayan dan ba zai iya ba, saukinta ma a dinner din suit zasu saka da ace manyan kayan zai sake maimaitawa toh da an samu matsala dan shi a rayuwar sa baya son abinda zai zo ya takura masa.
   Sanda suka isa gidan sauran yan daurin auren basu gama watsewa ba, da yawan su ma suna zazzaune ne a kofar gidan an saka rumfa suna shan iska ana hira cike da Raha, yawanci su yan Sumailan ne sai yan tsirari da suke abokan Abba. Shi kansa Abban yana wajen tashi yayi ya amsa waya ya dawo.
    Labarin isowar angwayen ya riski cikin gidan, aka shiga shisshiryawa shigowar tasu, asma’u da taji abun daga sama sai da taji wani ras a kirjinta, tayi saurin dafe shi ta mike tana kokarin neman hanyar ficewa daga gidan, tun dazu umma take sababin su koma gidan Safiyya a aiko musu da abinci amma ya makale a dakin Umman taki fita, sai gashi yanzu tana son fitar amma bata san yadda zatayi ba, dan dole idan tace zata fita sai sun ganta, abinda ita kuma bata so kenan. Ganin take taken ta na son guduwa ya saka Aunty Hauwa ta dakatar da ita, ala dole ta dawo ta zauna tana kudundunewa a cikin mayafin ta.
    Hargowar su ta fara jiyowa alamun sun shigo ciki, tana jin wasu mata da bsta gane su waya ba suna ta tsokanar su,su kuma suna biye musu, irin dai wasan jika da kakan nan, shine a gaba wajen zakewa da amsawa tamkar bashi ba, kamar ba ango ba ma dan babu wata alama da zata nuna a jikinsa da zaka gane ango ne, tana jin sanda suka dungumo suka shigo falon umman, lokacin su Aunty Hauwa duk sun fita falon, nan dai akayi addu’a wanda aunty hauwan ce ta assasa da babu me wannan tunanin a cikin su, sannan suka yi waje suna cigaba da hayaniyar su. Wani ne cikin abokan ya tabo shi, yace

“Ina amarya ne?”

” Ba za’a hadu wajen dinner ba, kyale ta kawai pls.”

” Ok.”

” Ku jirani a waje ina zuwa.” Yayi hanyar dakin su Abbati, suka sheke da dariya, wato ba zasu ga Amaryar ba amma shi zai ganta, ba komai ai akwai anjima. Waje sukayi shi kuma ya shiga dakin ya tarar dasu da abokan su, Abbati yayi saurin tashi suka gaisa sannan yace ya taimaka ya kira masa ita, fita yayi sauran abokan ma suka fita ya zama sai shi kadai a ciki, a tsaye yake be zauna ba, da ba dan ace yana so ya kara jaddada mata maganar dinner din ba , da babu abinda zai saka shi nemanta, tunda dai an daura ai shikenan, duk ma abinda take tunani ko ji dashi zasu gauraya ne, daga shi sai ita yadda zai nuna mata shi din gogaggen dan duniya ne, idan aka ce ta sake gaya masa magana ma ba zata sake ba.
   Sanda kiran ya isketa kusan shidewa tayi, bata hango rangwame wajen Adam ba, shiyasa bata son duk abinda zai hada su waje daya daga shi sai ita, narai narai tayi da fuska, kamar zatayi kuka dan har kwalla ta cika mata ido, ganin yadda ido ya dawo kanta ya sakata tashi ta bi bayansa, duk taku daya da take ji take kamar ta saki fitsari a wando saboda zulumi. A hankali ta tura kofar sai kuma ta tsaya ta kasa shiga, yana kallon inuwar ta, ya ja tsaki ganin zata bata masa lokaci, ya fizgota da hannun sa ta dawo cikin dakin,durkushewa tayi da sauri jikinta na rawa tamkar mazari. Kallon ta yake yana kokarin ganin ko tayi abinda ya sakata, yana nan zanen kamar jiyan babu abinda ya chanja. Dogon tsaki ya ja, sai yayi maganin ta kuwa, yanzu ba wannan ne ya kawo shi ba tukunna

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button